Bakar Inuwa 51

 


*_Episode 51_

.......Anne ta cigaba da maida hankalinta ga Raudha har zuciyarta ta fara hasashen abinda yake dai-dai. Sai dai ta danne komai batace ba har la'asar da aka tashi salla.

Ramadhan ya fito sanye cikin ƙananan kayan daya canja suka sake fita massallaci da Bappi dan Pa na sashensa shima da iyalinsa. Har lokacin su Rumaisa na tare da Raudha harma sun kara samun yawan ƴan hirar su Sumayya. Magana kawai yay musu su tashi suje suyi salla ya wuce abinsa yana satar kallon Raudha da tun fitowarsa tai ƙasa da kai tana wasa da yatsun hanunta da jan lalle ya ƙawata dogayen faratanta.


       Koda ya dawo bai samesu a falon ba, acan bedroom ɗin kusa da na Anne yaji hayaniyarsu. bai saniba ko Raudha na tare da su ko tana ɗakin Anne. Haka ya wuce sashensa ya buɗe garden ɗinsa dake a gyare tsaf da korayen tsirrai masu kamshi da ni'imar ruwa ya shiga. Tunanin kiran wayarta yayi, sai dai akashe ma akace masa. yaja guntun tsaki dakai hannu ya shafi sumar kansa. Duk saima yaji zuwa gidan ma ya gundiresa, dan ba haka yaso ba kwata-kwata. Ya riga ya gama tsara kasancewarsu a sashensa daga shi sai matarsa su huta yanda ya kamata, amma sai gashi hakan ya gagara.

       Tun Raudha na daurewa dai har abin yaso fin karfinta. Dan da ƙyar ta iya dauriyar zagaya duka sassan gidan gaishe da matan Pa. Cike da takan tsantsan da faɗuwar gaba ta isa sashen Gimbiya Su'adah wannan karon, fatanta da addu'ar ta ALLAH yasa karta shaƙa mata tsakin kuka kamar wancan karon. Dan yau kanta shima wani azabar ciwo yake mata bayan zazzaɓi da ƙasanta da takejinsa kamar ana yankata ana watsa barkono a wajen.

      Badai a mata turaren tsakin kuka ba, amma ta fuskanci cin zarafi wajen su Muneera dake zaune tare da Gimbiya Su'adah a ɗakin. A kuma nan suke tabbatar mata da auren mijinta da Ayna'u. Sosai hankalin Raudha ya tashi, da jin wannan zance sai dai ta bala'in dakewa kamar babu komai a ranta. Ta saki murmushi mai kayatarwa da faɗin, “ALLAH ya sanya alkairi”.

        Dukansu kallon mamaki sukai mata dan basuyi zaton tanada bakin amsawaba musamman yanda tsoron gimbiya Su'adah baya ɓoyuwa a saman fuskarta.

       “Idanma baki faɗa har zuciya ba dai sai anyi, nanda sati uku Aunty Aynah nakan karagar mulkin first lady ba illiterate irinki ba...”

      Bumm kakeji Bilkisu da basu san da shigowartaba ta buge bakin Muneera dake maganar. “K dai baki da kunya sam Muneera. K har kina da bakin kiran wani illiterate? Koda kikai karatun ubanmi kika sani. Dan duk gidan nan kinfi kowa jakanta, badan Pa ba kin isa ki gama jami'a ne iyanzu kullum cikin daukar Cary over. Ina tausayin randa zaki ɗanɗani azabar gidan aure dan duk abinda kayi kaima sai an maka shi mtsoww”.

      Tana gama faɗa ta kama hanun Raudha suka fice a ɗakin batare data saurari ihun da Lubnah da Ayna'u ke mataba. Gimbiya Su'adah kam uffan batace ba har bilkisun ta fice da Raudha. Hakama surutan su Aynah ɗin baisa ta tanka ba.


          Kafin su karasa sashen Anne Raudha ta tsaida Bilkisu tana bata haƙuri dan sai mita take da cewa yau saita sanarma su Bappi abinda su Muneera ke mata da ɗaurin ƙugun Maah. Roƙonta taitayi akan tabar zancen ita hakan baya damunta, kuma Maah mahaifiyace a gareta ai, ta isa ta mata komai. Amma Bilkisu ta dage akan saifa ta faɗa an ɗaukama abun mataki. Da ƙyar Raudha ta shawo kan Bilkisu ta haƙura suka karasa ciki Raudhan na tafiya da ƙyar. Dan har cije lips take da haƙori sannan bata iya haɗe ƙafafun.

        Ramadhan dake bayansu batare da sun sani ba ya bita da kallo cike da tausayinta da wani ƙarin ganin girmanta. Koba komai yana son mahaifiyarsa, sai dai shima baya ƙaunar wasu halayenta amma babu yanda zaiyi yana ƙoƙarin mata addu'a. Suko su Lubnah lokaci yayi dazai ci ubansu gwargwadon iko.


       Yafendo data kasa haƙuri yanayin na Raudha ce ta fargar da Anne cikin raɗa dan suna tare a falo suna magana akan meeting ɗin da zasu zauna yau iya su manya dangane da abinda gimbiya Su'adah ta kawo na auren Ayna'u da Ramadhan.

      “Anya kuwa basai yanzu megidana ya taɓa Ameenatu ba? yanayinta yayi kama da hakan”.

     Anne dake bin Raudha da kallo ƙasa-ƙasa itama tace, “Tun ɗazu na lura da hakan wlhy Yafendo, sai dai kuma idan na tuna abinda ya faru tun washe garin aurensu da ɓarin da tayi saina ture hakan a raina. Ƙila wata matsalace daban kuma”

         “To lallai al'amarin akwai ɗaure kai, kodai akwai abinda bamu fahimta dai-dai ba tun a wancan lokacin, kokuma bai bar halin nasa na idan ya fusata ya sauke fushinsa kan mace ba?. Ya kamata a binciketa kam a bata kulawa dan yanayinta gaba ɗaya ya fallasa taji ciwo a wajen ko makamancin hakan”.

      Numfashi kawai Anne ta sauke suka bar zancen suka kama wani. Suna wajen har aka kira magrib, a lokacin Raudha na can kwance zazzaɓi ya mata rijif. Da ƙyar ta iya tashi tai salla. Tana idarwa ta koma saman gado ta kwanta harda jan bargo hawaye na zubo mata. Tambayar duniya Bilkisu da su Rumaisa sun mata amsa ɗaya take basu (babu komai).

      Bayan sallar isha'i suna falo zaune Raudha nata dauriya Anne ta fito daga ɗaki tai kiranta, da ƙyar ta iya dauriyar ganin ta saita tafiyarta amma hakan ya gagara. Har suka shiga ciki Anne batace mata komai ba, sai da ta zauna tana gaisheta ta haɗe fuska dan bata son Raudha tai mata gardama. Murya a dake tace, “Ameenatu faɗamin mike damunki tunda kukazo gidan nan naga baki da walwala kuma idonki ya nuna kinyi kuka?”.

        Da sauri ta girgiza kai tana haɗiye hawayen dake neman zubo mata na zugin da take ji tace, “Ba komai ALLAH Anne. Kawai dai banajin daɗi ne”.

      Shiru Anne tai cike da nazarinta. Sai kuma ta miƙe batare da tace komaiba ta nufi toilet ɗinta. Ruwa mai zafi ta haɗa yanda tasan zai taimaki Raudhan. Sannan ta fito ta kama hanunta suka shiga ciki. Duk yanda Raudha ke wani zame-zame ga kunya kamar zata halakata Anne bata saurareta ba. Babban towel ta bata ta ɗaura ta lulluɓa da gyalenta sannan ta sakata shiga cikin ruwan. Wani kuka maiban tausayi Raudha ta sanya har numfashinta na fisga kamar zata shiɗe. Ga kunyar Anne ga azaba, jikinta har wani karkarwa yake. Anne ta gama fahimtar matsalar Raudha amma mamaki ya hanata gaskatawa.

      Haka ta sake canja mata wani ruwan har sau uku, sai ga Raudha taji wata irin nutsuwa na saukar mata. Anne ta fito tana bata umarnin tayi wanka da ruwan ɗumi kafin ta fito.


       Ramadhan da tun shigar Raudha ruwan farko ya nufo ɗakin Annen ya tsaya cak jin ƙarar da Raudha ta ɗan saki sanda ruwan ya ratsata, ya dafe kai da riƙe ƙugu a fili yake faɗin, “Ameenatu kin kasheni, miyasa kikaƙi yarda na tainaka miki gashi nan kin gama tonemin asiri wajen tsohuwarnan da darunta baya karewa”.

     Duk da Anne kakace renon uwa tai masa ba kaka ba. Hakan kuma baya hanashi yin wasa da ita wani lokacin. Dole ya fasa shiga ɗakin dan yasan rikicin Anne yanzu saita sauke masa na cikinta. Tun ɗazu itace a ransa. Duk abinda yakeyi hankalinsa na kanta, sai dai kuma haushin yanda ma ta wani sharesa na cinsa, dama sanda ya gansu da Bilkisu yaga kamar tafiyarta ba dai-dai ba, sai dai bai samu damar gama ƙare mata kallo ba suka shige. Falon ya koma dole wajen Bappi suka cigaba da hirarsu har Pa. Dama zai kira Anne ɗinne kamar yanda Bappi ya sakashi, koda ya dawo sai ya ce masa bai gantaba amma yaji ƙarar ruwa a bayi....


       Babu abinda take sai sakin ajiyar zuciya a jajjere, Anne dake kallonta cike da tausayi ta nuna mata bakin gado tana miƙa mata shayi data saka aka haɗo mata, sai gasashshen nama da akaima haɗi na musamman dan zuwa yanzu ta tabbatar da abinda ke faruwa. Kokwanton da ranta keta mata yasata kiran Dr Hauwa tunda itace ta duba Raudha a wancan likacin da sukai zargin cikine da ita da kuma zubewar cikin. Dr Hauwa da take ɗaukar Anne matsayin uwa ta faɗa mata gaskiyar lamari akan kowancan karon ciwon marane kawai irin na period, hakama lokacin da akace tayi ɓari maganin zubda ciki tasha batare data sani ba, amma Ramadhan yace suyi shiru dan zaiyi bincike akan wanda ya aikata zuba maganin da Raudha tasha., kuma bayan shi Raudha ta karayi har sau biyu tama dubata akan hakan, itace kuma ta sanarma Ramadhan mafitar da zai iya dakatar da Raudha daga azababben ciwon marar da take fama dashi a kowanne period.

     Godiya Anne tai mata ta yanke wayar, shiyyasa kafin ma Raudha ta fito Anne tasa aka kawo mata wannan abincin da tasan zai taimaka mata. “Maza kici kafin a samo miki magani”.

     Yunwar takeji, amma sam bata son cin abincin. Sai ma wani irin barci dake fisgar idanunta. Haka ta daure taci abinda zata iya tace ta ƙoshi. A kusan tare Ramadhan da Anne suka shigo ɗakin. Sanye yake cikin kananun kaya da tun ɗazun ya canja. Anne ce kawai ta amsa masa sallamar da yayi cikin tsuke fuska. Raudha kam dake fama da kunyarsa dama bata yarda ta motsa ba, ba kuma ta ɗago ba.

        Zama yay a ɗaya daga sofa's ɗin. Idanunsa akan matarsa da yakeji kamar yaje ya rungumeta, sai dai ya daure ya fuske dan tunda yaga yanayin Anne yasan fushi take da shi. Yanzun ma maimakon ta kirashi da wayarta Bappi tasa ya kirashi yana sashensa yana ƙullawa da kwancewa akan yanda zaizo ya tafi da Raudha can.

        A hankali ya janye idanun nasa a kanta yana jingina kansa jikin kujera ya lumshe su. Cikin ɗan furzar da numfashi yace, “Anne gani”.

     Shiru kamar bazata kulashi ba, tanata ƙoƙarin sakama Raudha safa mai kauri a ƙafa bayan ta mulke ƙafar da wani mai da ita tasan amfaninsa. Sai da ta gama tsaf ta kamo hannayen Raudha suma ta shafa mata man ta saka mata safar hannu sannan tai magana batare data dubesaba tana rufe man. “Magani nake buƙata da zata sha”.

      Idanunsa ya buɗe tare da ɗagowa. Sai ya saukesu akan Raudha da sam taƙi kallon ko inda yake har yanzu. Kafin cikin ƙanƙan da murya yace, “Waye baida lafiya?”.

        Wani shegen kallo Anne ta zubo masa cike da harara kai kace idonta ne zai faɗo. Daƙƙuwa ta watsa masa a zafafe tace, “Ramadhan ungo wannan.”

       Tattausan murmushi ya saki mai sanyi yana lumshe idanu ya sake buɗewa a lokaci guda. Fuska ya ɓata sosai cike da marairaicewa kamar ba shugaban ƙasa Ramadhan ba. “Waini Anne kamarma fa kinajin haushi na..”

    Harara ta sake dalla masa tana janyo burner ɗin turare kamar zata jeho masa. “Oh saima yanzu ka fahimci haushin naka nakeji ashe....” ta ƙare maganar dayin kamar zata jeho masa har abin yaso bama Raudha dake kallonsu ta wutsiyar ido dariya. Amma saita gimtse yana sake kauda kanta dake mata tsananin ciwo gefe...

        Hannu ya ɗaga mata alamar surrender. “Kinga yi haƙuri ajiye burner ɗin. Ina arziƙi ranar Monday a ganni da fasashen kai azata matata ce ta fasamin”.

     “Oh to bara na fasa ɗin ai gara sumayi zaton hakane koba komai ta rage zafin muguntarka”.

      Tasowa yay daga kujerar murmushinsa na sake faɗaɗa. Ya zauna kusa da Raudha a gefen gadon yana mai ruƙo hanun Anne ya amshe burner ɗin. “Yi haƙuri tagaba goshin Bappi yanzu mi akeso nayi?”. Yay maganar da juyawa yana ɗaura hanunsa a goshin Raudha da kunya ta dabaibaye kamar ta nutse saboda yanda ya zauna gab da ita sosai duk da baya taɓa jikinta dai.

        Mikewa Anne tai tana mita ta fice. Ka tambayeta abinda ke damunta kasa a nemo mata magani kafin na dawo kuma ku tattara ku barmin ɗaki barci zanzo nayi”.

     Gwalo ya ma bayan Anne, kafin ya maido dubansa ga Raudha. Jawota kawai yay jikinsa ya rungumeta baki ɗaya. Rawa jikinta ya farayi kaɗan-ƙaɗan har yana iya jin gudun da zuciyarta keyi. Ga zafin da jikinta ya ɗauka sosai na ratsa shi. 

    “I'm sorry Ustazah”.

  Ya faɗa a hankali cike da tausayinta. Ita dai babu bakin magana, sai ma lafewa da tai duk da tsoron dake tattare da ita nashi. Kusan mintuna uku suna a haka kafin ya ɗagota daga jikinsa, hannu yasa ya share mata hawayen dake sakko mata a kumatu. “Yi haƙuri kukan ya isa haka Sweetheart, amma miyasa ɗazun baki shiga ruwan dana haɗa miki ba”.

       A hankali yake maganar cike da nutsuwa. Da ƙyar Raudha ta iya buɗe baki tace, “Akwai zafi ne”.

       “Ai zafin shine zai taimaka miki Ameenatu, gashi ƙinyin haka ya saka miki zazzaɓi har kin tone mana asiri wajen Anne dama duk mai hankali da zai lura da tafiyarki a gidan nan ɗazun”.

      A ɗan tsoroce ta ɗago manyan idanunta a karon farko ta kallesa. “Ya Ramadhan kowa ya sani kenan?”. Tai maganar cikin rawar murya wasu hawayen na rige-rigen sakkowa. Dariya da tausayi ta bashi lokaci guda. Maimakon ya bata amsa sai ya sake rungumeta. Kusan minti biyu ya sake ɗagota. “Kinga tashi muje kisha magani dan tun ɗazu nasa aka kawo miki. Ga shi Anne dama ta koremu duk da nasan itama ba iya kwana zatai anan ba sai a bayan Bappi. Shiyyasa kema takeso kije jikin mijinki ki kwanta ki more..”

     Hannunsa ta turo dan yanda yay maganar da abinda hanunsa ke mata sai kunya ta sake lulluɓeta. “Ni ALLAH ka bari”.

       “Uhhm iyayi, nasan dai kinana daɗi ya rufeki bazaki kwana batare da mijinki ba.”

     “Innalillahi... ALLAH Ya Ramadhan ka iya sheri”.

             “Su Yaya anji jiki, wane Yayane zaiyi bidirin da nai a daren jiy.....”

   Hannu tasa ta toshe masa baki da sauri kafinma ya ƙarasa. Da ƙyar ya iya danne dariyarsa yana janye hanunta. “To shikeman nayi shiru”.

       Yasan ya kora su Basma tun ɗazu, Anne kuma tana sashen Bappi, sai kawai ya duƙa wai Raudha ta hau ya goyata. Ƙin yarda tayi itakam. Ganin zata cigaba da ɓata lokacinsa ya ɗauketa cak suka fice tanata mutsu-mutsu da roƙon ya sauketa bai saurareta ba. Dole tai saurin saƙalo hannayenta a wuyansa jin kamar zata faɗi. Ta lumshe idanunta da hawaye ke zaryar fitowa kunya kamar zata halakata, fatanta suje lafiya inda zasu batare da wani ya gansu ba..........✍


No comments

Powered by Blogger.