Bakar Inuwa 45

 


Chapter 45

45


.........Yanda yay maganar kamar bashiba yasa Raudha ɗan taɓe baki da marairaice fuska. “Ni dai tunda banyi ba ai Alhmdllhi”.


   Bai tanka mata ba, sai dai ya sake buɗe idanu yana kallonta. Sosai zuciyarta ke gudu a ƙirjinta dan ta fahimci abinda yake kallon. (Oh ita Raudha taga takanta, mima ya kaita fitowa ba hijjab ko mayafi?) ta ayyana a zuciyarta a fili kamar zatai kuka.


    “35, 32, 38... Uhhm da alama zaki iya....” 


    Saurin buɗe ido tayi jin ta ɗan zama kanta na son ganin kuma mi yake ma lissafin numbers haka? Da cewa zata iya. Saurin son zame masa kai tayi a ƙafarta sai ya ɗan mintsini cinyarta. “Hi kokin manta sadaki na biya malama. Stay quite ko kiji a jikinki”.


     Daina motsa ƙafafun tayi, sai dai tasa hannu ta kare ƙirjinta tana tura baki dan ta fahimci lissafin seize ɗinta na ƙirji, ciki, hips yake yi. Ji take inama ƙasa ta tsage ta shige kawai ta huta dan kunya. Ita kam al'amarinsa yanzu ya daina bata mamaki sai dai tsoro. 


    Ganin yanda ta kare ƙirjin nata ya sashi ɗan yamutsa fuska da taɓe baki. “Yarinyar nan anya kuwa bazaki lalatani ba. To banda son lalatani inda na dosa daban inda kika dosa daban tabbacin abinda ke ranki kenan”.


       Ji Raudha tai mizai hana kawai ta saki kuka ta huta, kafin ta lalubo abinyi ya tashi zaune cike da ƙarfin hali yana gyara zamansa sosai a gefenta dab. Fuska a yamutse idonsa ƙyam a kanta yace, “Da alama yarinyar nan zaki tsufa da wuri, dan ƙiba zakiyi bata wasa ba mtsoww nidai an cucan..” ya ƙare maganar da ɗaukar kofin kunun da take sha. Zamansa ya gyara tamkar bashi ya gama zuba zancen ba ya kai kofin bakinsa bayan ya ƙarema abinda ke cikin kofin kallo ya fahimci kunun tsamiya ne da Anne nayi, kuma Alhmdllhi yana matuƙar son sa.


     Yunƙurawa Raudha tai zata tashi dan ya gama dabaibaiyeta a cikin cakwakiyar kunya ya dakatar da ita. “Amma gaskiya baki da tausayi Ameenatu! Haka akace ki kula da miji idan baida lafiya!?...”


   Yanda ya ƙarasa maganar da saki wata wahalalliyar atishawa da jin sunanta a bakinsa ya sakata dakatawa. Zuciyarta da ɗan fargaba ta dubesa dan tun dama yazo wajen ya fara magana da ɗumin dataji kamar a kansa daya ɗaura jikinta take tunanin yana lafiya kuwa? Sai dai tsokanar magana daya ɓige da mata yasata ture tunanin. Dubansa tai cikin ƙarfin hali, ganin yanda fuskarsa tai jaa musamman saman hancinsa, sai kuma idanunsa da ya buɗe suka haɗa ido suma sun sake koɗewa fiye da jiya alamar babu lafiya. Saurin kauda nata tayi tausayinsa na ɗarsuwa mata a rai, dan tun fil azal haka take da saurin jin tausayin mutum koda mugune (akwai lokacin da aka taɓa kama ɓarawo a makwaftansu, gashi dai itama haushinsa takeji saboda ya taɓa haurawa gidansu yay sata. Amma yanda aka dinga jibgarsa sai itama taita kuka tana roƙon a barsa ya tafi).


   A bazata taji ya damƙi hanunta ya kai saman goshinsa da ya ɗauka zafi sosai har tanajin harbawar jijiyoyin wajen. Cikin tsoro da tausayinsa da ya bayya a cikin idanunta ta buɗe baki zatai magana sai dai ya rigata. Cikin taushi da sanyin murya da batasan yanada su ba. “Ki bani abinci naci kiban magani”.


    Tausayinsa sosai ya sake kamata. Cikin damuwa da sake sanyaya muryarta itama mai sauƙin faɗi tace, “Murance har yanzun?”.


    Idanunsa daya ɗan maida ya lumshe ya sake buɗewa. Sai kuma ya kwanto kansa kan kafaɗarta yana faɗin, “Kin damu da nine balle ki sani? An baki amanata kin kasa riƙewa”. Nanma zafi taji jikinsa. Tai saurin rumtse idanu kunya na sake dabaibayeta da dariyar maganarsa (wai an bata amanarsa. Bama itace aka bashi amanarta ba) Tasan ya kamata tun a jiya data fahimci ya dawo da mura tabi shawarar Bilkisu na kai masa magani. Amma ganin kamar Bilkisu ta manta sai itama ta share batun dalilin abinda ya sake harmutsasu na faɗan ƙauyen Kauci. Dai-dai tana janye hanunta a goshinsa yace, “Kiramin Anne”.


      A sanyaye tace, “Amma za'a tayar mata da hankali ai”. 


   Komai bai ceba ya ɗaura hanunsa saman cinyarta idanunsa a lumshe ya hau laluben wayarta. Saurin riƙe masa hannu tai a ɗan firgice jin yanda yake lalubeta kamar da gayya. 


    “Ki daina fassarani da abinda bashi nake nufi ba, ni waya nake nema”.


    Duk da idonsa a rufe yay maganar hakan bai hana Raudha ƙyaɓe fuska ba da tsuke ta. Sai dai batace komai ba ta tura masa wayar ta dunguri hanunsa datai saurin saki a nata. Shima komai bai sake cewa ba ya ɗauka wayar ya ɗaura bisa hanunta. Murya babu wasa yace, 


   “Kiramin Anne”.


Badan taso ba tabi umarninsa tai kira number Anne ɗin. Sau biyu tai wringing aka ɗaga, a hanunsa ta ɗora wayar dan ita kam bata san mizatace da Anne ɗin ba. Shima komai baice mata ba ya tashi da ga kafaɗarta ya kwantar da bayansa a kujerar yana kai wayar kunnensa. Dai-dai Anne na ambaton sunan Raudha cike da kulawa....


    “Anneee!”.


Ya kira sunanta cikin katseta. Ɗan jimm tayi kafin tace, “Ramadhan!”.


   “Uhhyim”


Ya amsa yana sakin atishawa cikin rashin ƙarfin jiki. A take Anne ta rikice, dama tun jiya ta tsargu a muryarsa da suna waya. Amma koda ta tambayesa sai ya nuna mata lafiyarsa ƙalau. 


    “Baka da lafiya ko! Haba Ramadhan abin nan kasa a ranka harya kwantar da kai haka?”.


   “Anne cool down mura ne tun a uk nataho da shi”. 


  Sanin wahalar da shi da mura keyi ya saka Anne sake shiga damuwa. Cikin ƴar rikicewa tace “Haɗani da Aminatu”.


    Maimakon bama Raudha da akace sai cayay “Anne ni dai kizo dan ALLAH, ko kuma na taho nan”.


   Murmushi tayi mai sauti, ita kanta tasan badan raino irin na uwa taima Ramadhan ba tabbas a taɓare zai tashi. Sai dai batai sakancin masa rainon kaka ba ta tsaya kansa da tarbiyyarsa tamkar uwa, kai ko uwarsa batajin idan da a hanunta yake zai samu tarbiyya makamanciyar wadda yake a yanzu. “To naji bani Aminatu nace”.


   Fuska ya tsuƙe yana ɗorama Raudha wayar a kunne sai kuma ya tashi zaune ya ɗauka kunun ya cigaba da sha badan yana masa daɗi a baki ba, saboda gaba daya baida appetite. Gashi kuma yaji tasa sugar sai dai baiyi ƙarfi ba shiyyasa bai damu ba tunda yana ɗan sha wani lokacin duk da yana wahalar da shi idan akai rashin sa'a...


     Cikin damuwa Anne take amsa gaisuwar Raudha. Kafin ta ɗora da roƙo akan Ramadhan ɗin. “Ameenatu kiyi haƙuri nasan bazaki barsa cikin ciwo ba amma dan ALLAH ki kula dashi sosai kinji. Ramadhan nada matuƙar rauni akan ciwo bai da juriya, ga rakin tsiya. Dan gaba ɗaya shafkewa yake tamkar yaron goye musamman mura da bata masa kamun wasa. Wajigasa take matuƙa ga wannan ma naji kamar ta masa ƙarfi sosai halan baisha ko magani ba tun jiyan?...”


   Cikin ɗan in ina da kunya Raudha tace, “Eh Anne gaskiya inaga bai sha ba, dan yau tunda safe ya fita a gida”.


    “Amma garin yaya haka ta kasance Aminatu?”.


  “Uhm..uh...m Anne jiyanne ransa ɓace ya kwana saboda abinda ya faru a ƙauyan can, daga baya ma kulle kansa yay a ɗaki”. 


   Sosai Anne ta sauke numfashi mai nauyi tunda tasan halin kayanta idan ransa ya aɓaci. Alhmdllhi ma an samu canji bai sauke damuwar kan ƴar mutane ba, koda yake bawai komaine ke ɓata ran nasa ya aikata ba. Cikin katse tunanunta tace, “Ai mijin nan naki kam sai addu'a Aminatu, wani lokacin idan ya birkice tamkar mai iskoki a ka haka yake. Sai kinta haƙuri kinji. yanzu dai asamu kayan ƙamshi ai masa shayi da su citta ya fito sosai a ciki harda tafarnuwa. A abincin da yace yana so ma asaka yaji ya ɗan fito. Nasan sa da son wanka da ruwan sanyi ki hanashi, hakama ruwa mai sanyi karki bari yasha koda fura ne ko madara. Ruwan shansa ya zama da ɗan ɗumi haka, ƙafarsa ta kasance cikin safa. Yasha magani idan yaci abinci insha ALLAH zai taimaka masa hakan dan haka nake masa idan yana mura. Zuwa anjima zan kira, idan zazzaɓin bai sauka ba sai a turo Dr Shamsu.”


     Raudha dake jin lisaafin kamar na ɗan goye ta jinjina kanta kamar tana a gaban Anne. “To Anne insha ALLAH yanzu duk za'ayi. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana.”


   “Amin Aminatu ALLAH ya saka miki da alkairi yay miki albarka.”


  Cike dajin daɗi Raudha ta amsa mata kafin suyi sallama........
      Wayar ta sauke da ga kunnenta tana sauke numfashi. Sai kuma taɗan kallesa ta maida kanta ƙasa da sauri ganin ita tsurama idanunsa kumburarru. “Mizaka ci to sai a girka kafin magrib insha ALLAH an kammala?”.


    A hankali ya janye idanunsa a kanta batare da yasan ya shagala a kallonta ba tun tana waya da Anne. Shi kansa zuwa yanzu ya tabbatar yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce, sai kuma baijin zai..... Kasa ƙarasa abinda zuciyarsa ke son faɗa yayi badan yasan dalili ba. Cikin dasashshiyar muryarsa ya sake dubanta yana magana a hankali tamkar mai raɗa. “Koma miye ki dafa zanci”.


   Kanta ta jinjina masa tana miƙewa. Ya bita da kallo harta nufi stairs. Sai da ta ɓacema idanunsa ya sauke numfashi da ƙyar yana ɗaukar remote ya canja television zuwa inda zaiga labaran shida na yamma.
   Sanin maitarsa da nama ya saka Raudha haɗa masa farfesun da taimakon mama ladi. sai kunun gyaɗa, madarar shanu dake gidan ta tafasa itama ta juye masa a flask sai shayi. Aikin bai wani jasu da nisa ba tunda kaɗan iya cikinsa ne. Kuku kuma sukai sauran iya dai su dake sashen.


    Da taimakon mama ladi ta hauro da kayan anata kiraye-kirayen sallar magriba. Ya tashi a falon, dan haka Raudha ta amshi sauran kayan hanun mama ladi tana mata godiya. Ɗakinsa ta nufa, tai knocking har uku bataji motsi ba, sai kawai ta tura ƙofar ta shiga da tunanin ko yana alwala. Ɗakin na nan tsaf yanda ta gyarashi da safe, sai dai duk ya watsar da kayan daya dawo office akan gado da ɗan stool ɗin jikin gadon zuwa ƙasan carpet. Kayan hanunta ta ajiye tana kwashe kayan, sai lokacin idonta ya sauka kansa a gado nannaɗe cikin bargo. Tausayi ya sake bata, ta ƙarasa ta gefesa, ɗan ranƙwafowa tai a ɗarare takai hannu taja bargon daya rufa har saman kansa, rawar sanyi ma taga kamar yanayi, yana ƙoƙarin ture hanunta da son hanata janye bargon sai hanun ya shiga cikin nashi, damƙewa yay da iya ɗan ƙarfinsa ya fisgota. Abinka da ba ƙarfi ɗaya ba sai gata gaba ɗayanta a kansa.


    “Wayyo ALLAH na”. Ta faɗa cikin matse fuska saboda ƙirjinta daya bugi jikinsa, sauƙinma laushin bargon ya bata kariya sosai. Ƙoƙarin tashi take kamar zata fasa kuka, hakan ya bashi damar ɗaga bargon ya turata ciki. Rawa jikinta ya farayi, dan al'amarin yazo mata a bazata, ta shiga son fita da janye jikinta daya tura a nasa ya matse, duk da a halin ciwo da yake ciki hakan bai hanashi sauke ajiyar zuciya ba. Cikin rawar muryar da ke tabbatar da baida lafiya yake magana a kunenta cikin raɗa da sambatu na ciwo (Dan idan yana ciwo tofa akwai sambatu kamar su oh eh😂. bazan faɗi suna ba dai🤭 lol.)


     “Anne sanyi nakeji ki ƙara min bargo, Anne kaina ciwo kamar zai fashe, wayyo Anne kaina jikina zafi Anne ko'ina ciwo”.


    Dariya, tausayi, tsoro, mamaki, duk suka dira a zuciyar Raudha lokaci guda. Gata matse a jikinsa tamkar zai ɓalla mata ƙasusuwa ga zafin jikinsa na matuƙar ratsa nata jikin. Sosai ƙirjinta ke bada sautin fatt! Fat!! Da ƙarfi, da ace lafiya yake babu abinda zai hanashi da kiranta matsoraciya. Cikin rawar murya tace, “To ka bari na tashi na baka magani gashi magrib ma tayi”.


    Jin muryarta saɓanin ta Anne da yake tsammanin ji ya ɗan buɗe ido, ba ganin fuskarta yake ba dan ya rufe musu har kai a bargon, “Kinada tausayi kuwa?”. Ya faɗa yana sake ƙanƙameta har saida tai ƴar ƙara saboda ƙirjinta. gaba ɗaya a birkice yake, “I'm sorry”. Ya sake faɗa a hankali cikin kunenta yana sassauta mata riƙon, sai kuma ya sake faɗin, “Kiyi shiru bana son magana kaina na ciwo”.


    To yau dai Raudha taga takanta. Ɗan ƙwalisar nan Ramadhan mai shegen ɗaukar kan nanne haka. Shugaban ƙasar NAYA jinin Taura da ko kallon arziƙi sai ya gadamar wanda zai yimawa. UBANGIJI mai rahama, UBANGIJI mai jinƙai. Maiyin yanda yaso, ga wanda yaso. Cikin ƙanƙanin lokaci in yaso kamaka da ƙanƙanin abu sai ya firgitaka ka mance kai waye? Miye matsayinka?. Taja numfashi a hankali da shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na REED. Zuwa yanzu ta nutsu a jikin nasa badan taso ba, babu abinda ke ratsata sai zafin jikinsa da sautin bugun zuciyarsa. Sai saukar numfashinsa a wahale. Magana yake a hankali bisa laɓɓa da bataji, sai dai tanajin alamar motsin bakinsa. Ta fahimci sambatune na ciwo kawai ke ɗawainiya da shi. Kusan mintuna talatin suka samu a haka, ganin lokacin salla na sake shigewa ta fara magana a hankali cike da lallashi. 


    “Lokacin salla nata sake nisa, ga abincin na kawo maka kuma da magani kayi haƙuri na tashi na baka kar mu makara salla”.


    Sarai ya jita, dan idonsa biyu. Sai dai bai nuna alamar yajin ba har bayan shuɗewar wasu mintuna.
    Da ƙyar Raudha ta samu ya rabu da ita ta tashi, toilet ta shiga tana sauke tagwayen ajiyar zuciya da taɓa jikinda da yay zafi kamar itama ta kamu da zazzaɓin. Ruwan ɗumi ta daidaitamsa domin yin alwala. Tayo tata sannan ta fito. Har yanzu yana cikin bargon ƙudundune. Cikin lallashi tace, “Ya Ramadhan ka daure kayi sallan sai kaci abincin da magani”. Kamar bazai motsa ba sai kuma taga ya miƙo mata hanunsa da ga cikin bargon, duk da kunya dake ɗawainiya da ita hakan bai hanata kamawa ba danta fahimci abinda yake buƙat kenan ta taimaka masa ya tashi. Da taimakon nata kuwa ya tashi, ganin kamar yana tangaɗi sai taƙi sakinsa sukaje ƙofar toilet, sai da taga ya shiga sannan ta sauke numfashi. Kasancewar akwai hijjab jikinta tasa abin salla tayi anan, tana raka'ar ƙarshe ya fito da alama ba alwalan kawai ya tsaya ba yayi wani uzirin nasa daban. A ɗayan abin sallar data saka masa ya tada sallar shima yana faman riƙe kai, kafin ya idan da sallar aka shiga kiran isha'i, hakan yasa Raudha komawa ta zauna domin gabatarwa.
    Su dukansu sai da sukai salla har isha'i sannan ta haɗa masa abinci. abin mamaki yau yanka uku Ramadhan yaci na nama, sai romon farfesun kawai ya cigaba da sha. Raudha dake gulmarsa a zuciya ta shiga jinjina kai tana mamakin eh lallai magana ta girma kure na gudun nama yau. To ashe akwai ciwon da zai iya hana Ramadhan cin nama a duniyar nan?. Batace komai ba ganin ya ɗan sha ruwan kunun ya kuma sha romon nama. First aid box data gani a ɗakin ta ɗakko ta duba, cikin sa'a ta samu maganin mura data san yanada inganci tunda tasha amfani da shi itama. Da ƙyar ta samu yasha maganin yana yamutse fuska har yaso bata dariya, ta dai daure ta gimtse.


   Koda ya koma saman gado da nufin kwanciya a ɗofane taɗan zauna. gadon da nufin gyara masa bargo kawai sai jitai ya ɗaura kansa a cinyarta, tare da riƙo hanunta yay filo da shi a kuncisa. Idanu Raudha ta ƙwalalo sai kuma ta ƙwaɓe fuska. Oho basai tanayi ba dan harya fara lumshe idanu, dole ta hakura da ƙudirin idan yayi barci ta zame jikinta ta gudu...........✍


No comments

Powered by Blogger.