Bakar Inuwa 44

 


Chapter 44

44


..........Su dukansu fuskokinsu washe suke da fara'a da farin ciki. Gasashshen naman rago ne a banƙare a tsakiyarsu. Sai lemuka masu tsada da daɗi ajiye gaban kowa. Gaba ɗayansu hankulansu nakan tv da ake nuna abinda ke faruwa a ƙauyen Kauci na

ƙaramar hukuma Gaman. Cikin ƙyalƙyalewa da dariya Mr MM ya kai tsokar nama daya cako da pork spoon bakinsa yana faɗin, “Wato ranka ya daɗe dabarar nan taka tayi ɗari bisa ɗari, yaje ya dawo yana farin cikin samun na sarori sai yaci karo da ƙyaƙyƙyawar tarba ta musamman”.


    Kwashewa sukai da dariya baki ɗayansu, Alhaji Haladu Gwandu dake dariya harda hawaye ya ce, “A to ba gani yake shi yanada dabarar shinfiɗa aiki ba ta hanyar ɗaura ƴan uwansa matasa kan manyan muƙamai, to sai yayi aikin mugani. Basai da zaman lafiya a ƙasar talakan zai ga aikin ba?”.


   Wata dariyar suka sake kwashewa da ita. Sai dai banda oga kwata-kwata da yake murmushi kawai yana cin namansa shima. A cikin God fathers ɗin nasu ɗaya ya tsaida dariyarsa ya ajiye wuƙar daya yanko wani ƙaton nama ya ɗauka da hannu yakai baki. “Ai indai mune baima ga komai ba. Sai mutuwar fitinannen tsohon kakan can nasa ta tabbata nan da kwanaki uku, a kuma ranar plan B zai bayyana shima, yanda mutuwar Alhaji Hameed Taura bazatayi tasiri a zukatan mutane ba balle ya samu addu'a da nuna tausayawa”.


    Dariyar suka sake tuntsirewa da shi. Forma president ya ce, “Wa yaga gaba kura baya sayaƙi. Bashi gani yake mulkin wasan yara bane ba, zai yabawa aya zaƙinta. Yanzu nan fa ina shirin fitowa ma nakejin wani ƙishin-kishin ɗin gulma, wai da yayi niyyar bincike akan kwangilolin da muka bada, sai dai ya dakatar dalilin wani abu da ba'asan tabbaci ba.........”


    Vice president Alhaji Yaro glass ya karɓe zancen forma president da faɗin, “Wannan maganar kam tabbas ce, sai dai nima ina kan bincike miye dalilin hanashi fasa binciken. Dan yanzu haka ma gobe za'a zauna da masu kwangilan meeting tare da J.P.S”.


     “What!! Alhaji Haladu Gwandu (Mahaifin Amnah) Ya faɗa aɗan razane. Dan kuwa akwai yaronsa a cikin wanda aka bama kwangilolin, kuma tabbas yau kusan kwanaki uku yana kiransa bai samu damar ɗaga wayar tasa ba saboda busy da yayi.....


    “Wlhy da gaske haka zancen yake”.


   Alhaji yaro glass ya faɗa a yanayin takaici da jin ɗaci. Waya Alhaji Haladu Gwandu ya lalubo a aljihun babbar rigarsa. Da sauri ya shiga laluben lambar yaron nasa. cikin sa'a kuwa bugu ɗaya ya ɗauka tamkar dama kiran nashi yake jira. Ko sauraren gaisuwar tasa baiyiba ya jeho masa tambaya. Sai dai amsar daya bashi tai matuƙar firgitashi ya saki baki da hanci yana saurare har yaron nasa ya gama bayanin saƙon da suka samu na kira da ga ofishin Minister.


      A hargitse ya ajiye wayar bayan sun kammala yana faɗin, “To tunda ya fasa binciken kiran ubanmi yasa Minister ɗin yake musu?”.


     “To wa ya sani”.


Cewar Alhaji Yaro glass.


  A harzuƙe Forma President ya ce, “Amma ya kamata ace irin waɗan nan abubuwan kana ƙoƙari saninsu Alhaji Yaro. Kasan kuwa wanene Ramadhan da Alhaji Hameed Taura?!!...”


    “Haba Alhaji Usama ya zakaga laifina? Bayan kaima kasan yaron nan komai yinsa yake a ƙudundune, daga shi sai matsiyacin cos ɗin nan da nafi tsana fiye da komai yanzu a duniya. Sai ko shegen kakansa ɗin nan da ubansa da nasan sune masu bashi shawara sama da mashawartansa na mulki.....”


      Mr MM zaiyo magana Oga kwata-kwata ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masu hannu. “Inaga wannan cece kucen ba shine mafita ba. Amma tabbas Alhaji Yaro akwai sakacinka anan. Sai dai muma munada laifi da bamu ɗoraka bisa hanyar data dace ka dinga sanin komai da komai ba. Amma ka sani matarka tana ɗaya daga ciki, dolene ta cigaba da kawo mana mike gudana a cikin gidan gwamnati ta hanyar matarsa tunda ƴa take a wajenta. Sauran magana kuma zamuyi daga baya idan na kammala nazari, amma a dakatar da kashe Alhaji Hameed Taura ba yanzu ba”.


   Cikin gamsuwa duk suka ɗaga masa kawuna, duk da a ransu suna son sanin dalilin dakatar da kashe Bappin, sai dai babu damar yin jayayya........




*______________________________*




     A matuƙar ruɗe Raudha ta kai hannu tana riƙo na Ramadhan jikinta na rawa. “Dan ALLAH kayi haƙuri, nasan wanda suka rasa ransu bazasu taɓa dawowa ba. Sai dai akwai mafita da zata taimaka a taimaki wanda sukaji raunika da tsananta tsaro ga wanda ba'a cutarba”.


      Duk da bai ɗago ya kalleta ba yanda ya dakata da yamutsa kan ya tabbatar mata yana saurarenta. Sai kuma ya ɗago ɗin ya zuba mata idanunsa. Hawayenta tai saurin sharewa tana miƙo masa wayarsa data ɗakko. Sai kuma takai ɗayan hanunta ta share masa nasa hawayen shima da har yanzu suke sakkowa.


     “Kasan yanayin ƙasarmu da ƙarancin kulawar da talaka yake samu akan harkar lafiya da tsaro. Lokuta da dama wasu a cikin jami'ai najin abu na faruwa sai dai tsoro da rashin kayan aiki na daƙilesu akai taimako, wasu kuma son zuciya ke hanasu yin kowane irin yunƙuri. To kamar hakane ga jami'an lafiya suma. Shiyyasa idan sakacin shugabanni ya haɗu da masu raunin taimako a jami'an lafiya ma yana ɗaiɗaita rayuwar talaka. Mafita itace yanzu ba wakili zaka saka ya bincika ba ko ya bama C.P na jihar umarni, kai da kanka ne ya kamata kai magana da I.G da C.P ɗin zasufi jin tsoron tashi suyi abinda ya kamata suma bawai su tura yara ba. Hakama asibitin da kanka ka kira Commissioner lafiya na jihar kai magana da shi dan ALLAH Ya Ramadhan......”


    Ɗari bisa ɗari ya gamsu da maganarta, dan haka ya ɗago da sauri, wayar da take miƙa masa ya amsa yay dailing number cos. Kai tsaye yace, “Ka sameni”.


   “Ranka ya daɗe yanzu haka ina cikin gidan nan ai”.


  Cos ya faɗa da sauri gudun kar shugaban ƙasa Ramadhan ya yanke wayar. Duk da cos baya shigowa har nan yau dai ya bashi umarnin ya samesa. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai ga cos ɗin. Saurin janye jiki Raudha tai daga rungumar da Ramadhan ya sake mata bayan yayi magana da cos. Sai dai hanunta ya riƙo cikin nasa dole ta zauna a hanun kujerar da yake a zaune hanun nata rumtse a nasa.


     COS ya rissina yana gaishe da Raudha data amsa a kunyace, dan yanda ya gansu da yanda yake bata girma har mamaki takeyi.


   Cikin bada umarni Ramadhan yace, “Ina bukatar magana da I.G & commissioner of police na jihar, tare da commissioner lafiya”.


    Kai Cos ya jinjina yana mai fara danna wayarsa. A taƙaice Cos yayma I.G bayani ya mikama Shugaban ƙasa Ramadhan wayar. Koda ya amsa bai wani tsaya sauraren gaisuwar ɗin ba da jikinsa keta ɓari da ga can shi zaiyi waya da shugaban ƙasa. Kamar yanda Raudha ta bashi shawara haka yayi, yana gama kora masa bayani cike da ƙasaita kamar bashi ya nema birkicewa ba yanzu ya miƙama COS wayar. Amsa yay da girmamawa ya sake kira masa C.P na jihar Kuddo da Commissioner ɗin lafiya. Daga ƙarshe yasa aka kira Gwamna ɗin jihar shima inda Shugaban ƙasa Ramadhan ya balbalesa da masifa jin tamkar ma shi babu wata damuwa tattare da shi.




    ★Tabbas umarnin shugaban ƙasa Ramadhan yayi matuƙar tasiri, dan cikin ƙanƙanin lokaci dukkan abinda ya lissafa aka ninkashi ga jama'ar wannan ƙauye. Kafin wayewar gari tako ina garin jami'an tsaro ne har cikin dazukan yankin da sauran ƙauyikan, ga helicopters na sojoji sai yawo suke ta sama. Na asibitima suna samun ƙyaƙyƙyawar kulawa. Waɗan da sukai musabbabin fara haɗa rikicin da CP ya bada umarnin dankosu sai ga gawarwakinsu a cikin waɗanda suka mutu. (Dama haka fitina take, a mafi yawan lokaci wanda ya takalota shi take fara zubarwa a ƙasa. ALLAH ka zaunar da ƙasashenmu lafiya. ya gafarta mana kurakuranmu ka wadatamu da tsarkakakkiyar zuciya😰).




★★★




     Da ga Raudha har Ramadhan idan sunyi barcin kirki a wannan dare sai dai ɓarawo. Ga mura ta mugun addabarsa da zazzaɓi mai zafi ma ya kwana. Yayi waya da Bappi yayi da Pa duk akan lamarin. Anne ma ta kwantar masa da hankali ta hanyar nasiha sosai da muhimmincin tashi tsaye akan addu'a .


   Basu kaɗai ba hatta Bilkisu da damuwar ta kwana. Duk da dai nata tsananin tashin hankalin nada nasaba da halin da taga Yayansu da Raudha a ciki. Adalilin hakan ma yau a ɗakin Raudha ta kwana. Ita kuma Raudha a ɗakin Ramadhan suka kwana tare.


   


     Da sassafe shugaban ƙasa Ramadhan yabar gidan batare da sanin su Raudha ba, dan ɗakinta ta tafi yin sallar asuba bayan ya fita massalaci shima. Sai da suka fito sukaci karo da shi a tv ana nunasa a cikin ƙauyen Kauci, abinda zai birgeka har da shi cikin tawagar masu zana'ida duk da karancin lokacin dake garesa. Ana kammalawa suka baro garin sai dai yabar jama'arsa suna sake zagaya ciki da bai ɗin ƙauyen. Tare suke da gwamnan jihar Kuddo ɗin. Daga ƙauyen asibiti suka wuce nanma shugaban ƙasa Ramadhan ya duba wanda suka sami raunika. Da ga haka bai ƙara ko minti biyarba a jihar Kuddo suka nufo Bingo dan da ƙyar yay squeezing time ɗinsa dama. Sai dai abinda yayi ɗin ya kara masa kima da daraja a idanun talakawan ƙasar NAYA. Gaba ɗaya a yinin nan babu abinda kakeji sai ruwan albarka da ake jera masa tako'ina. 


   Yayinda a ɓangaren su Alhaji Yaro glass kuma sukai yinin baƙin ciki da ƙunci dan basuyi zaton shugaban ƙasa Ramadhan zaije har ƙauyen ba domin nuna kulawa. Ba ƙaramin shiri ya wargaza musu ba akan hakan.




    A ɓangaren mai gayya mai aiki kam Ramadhan yau ya yini ne cikin damuwa da ɗunbin fargabar wannan mulki mai cike da ƙalubale kala-kala. Tun ba'aje ko inaba fa kenan, inaga nan gaba kuma da shekaru huɗu da watanni kusan bakwai ke jiransa. Kai anya kuwa zaya iya?. 


   Da wannan tunane-tunanen ya yini a office ga mura da ciwon kai ga zazzaɓi ga kuma aiki. Yini gudan nan kuma bai ci komai ba ƙishi ma sai da yaji maƙoshinsa na neman fara yayyankewa sannan yasha ruwa, dan daya tuno jinin daya gano a Kauci sai tsigar jikinsa ta dinga tashi.


     Duk da wannan damuwar hakan bai hana wakilan da yasa minister ya naɗa zaman mitin da masu kwangilar nan ba. Sun kuma gudanar da zaman tamkar yanda ya bada umarni. Yanayin zazzaɓi daya rufesa ya sashi barin office tun 2pm ya shiga gida.


    


   ★Koda ya shigo gidan ya iske Raudha bata gidan, shi shaf ma ya manta da batun fara zuwanta school yau. Ɗaki ya shige ya kwanta, duk da abinci ya kamata ya fara ci ya sha magani hakan bai faruba, sai dai yaji ciwon kansa na ƙara tsanani ya ɗauka man zafi ya shafa ya sake lulluɓe jikinsa gaba ɗaya cikin duvet.




     Duk da burin da taci akan wannan rana ta fara zuwanta makaranta abinda ya faru jiya sai ya rage masa armashi, Bilkisu ce ma da zuwan Ramadhan ƙauyen ya ɗan ƙarfafa mata gwiwa. Sai dai kuma kafin ta wuce ta ɗauka shawarar zuciyarta, so take tai karatu tankar kowane ɗalibi batare da ansan ita wacece ba. Hakan kuma bazai kasance ba sai idan bata tare da dogarawanta da aka tanada mata. Gudun karta aikata ba daidaiba ta sanarma Bilkisu shawarar data yanke a yau game da karatunta. Ɗari bisa ɗari Bilkisu ta yarda da tunanin Raudha, amma itama sai ta kira Anne ta sanar mata. Hakan ya burge Anne ta kuma bama Raudha goyon baya tare da yabama ƙyaƙyƙyawan tunaninta. Daga ƙarshe Anne tace zata turo mata Adamu driver ya kaita kafin a samu drivern da zai kaita. Idan kuma zata dinga tafiya da su Basma ne sai su na biyowa ɗaukarta inhar tanada lecture tare da su tunda makarantar tasu ɗaya ce.


   Hakan yay mata, takumayi godiya sosai har sai da Anne ta ƙwaɓeta. Babu jimawa kuwa Malam Adamu yazo ɗaukar tata. Kasancewar securitys ɗin sun ganesa saboda yawan kawo family ɗin shugaban ƙasa da yake gidan yasa bai samu wata matsala ta shigaba. A ɓangaren Raudha shigar mutunci tayi dogon hijjab harda niƙaf, tafukan hanunta kawai kake iya gani hakan yasa bayan Mama ladi babu wanda yasan da fitarta. 


     Taji daɗin kasancewar ta a wannan makaranta da ta daɗe da fidda ran ganin kanta a ciki. Babban farin cikinta kuma department ɗinsu ɗaya da Rumaisa da Basma. Fadila ce kawai take daban dan abinda take karanta yanada banbanci da su Basma. Suturta jikinta ya matuƙar ɓoyeta ga kowa sai su Basma da suka sani. A nutse komanta ya gudana a wannan yani cikin kwanciyar hankali da farin ciki. Har a waya ta kira Asabe tai mata addu'ar fatan alkairi. Hakama M. Dauda ta kirashi sai dai Larai ta ɗaga cikin masifa tace baya nan. Ko jira su gaisa bataiba kuma ta kashe wayar. Murmushi kawai Raudha tayi dan halin matar baban nasu ba sabon abu bane a wajenta.




   Ƙarfe huɗu da wasu mintuna su Basma suka kawota gida, sai dai basu shigoba suka juya. Yunwa takeji sosai dan har wani dishi-dishi take gani saboda ta fita ko karyawa batai ba. Kuma har taje ta dawo ruwa kawai tasan tasha. Sam batai tunanin samun Ramadhan a gida ba tunda tasan yana office, dan haka kai tsaye ta wuce ɗakinta. A daddafe ta watsa ruwa ta canja kayanta zuwa doguwar riga mara nauyi, sai hula data saka da Slippers ta fito. Ba komai a dining, ita kuma tacema mama ladi kar ai komai sai dare tunda itama bata gida hakama bilkisu. Taɗan riƙe ƙugu da hanunta dake riƙe da wayarta, ɗayan kuma tana murza goshinta dake mata ciwo ta ciki kaɗan-kaɗan tabbacin yunwa da rashin isashen barci na damunta. 


   Rasa inda zata kama ya sata kiran Mama ladi a waya ta sanar mata ta dawo. Sai kuma ta kai zaune cikin kujera cike da rashin ƙarfin jiki tana shafa ciki da ɓata fuska. dan da gaske yunwa takeji fa irin ta fita hankalin nan. Minti goma ba'a ƙulla ba sai ga mama ladi da basket na kayan abinci, ai tunkan ta ƙaraso inda take ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Wayyo mama gaskiya kina sona”.


   Ƴar dariya mama ladi tayi tana ƙarasowa gareta. Cike da girmamawa ta ce, “Barka da dawowa ranki ya daɗe ai bansan kin shigoba wlhy”.


   “Bamma jimaba mama, dan ko mintuna talatin bana zaton nayi, dan na fara wanka ne shiyyasa. Kamar kinsan da yunwa na dawo gidan”.


    “Ai nasan za'a rina, tunda naga kun fita baki karyawar kirki ba. shiyyasa na tashi na haɗa miki wannan karki dawo ba'a kammala abincin dare ba”.


   “Nagode sosai mama ALLAH ya saka da alkairi”.


  Cike da jin daɗi mama ladi ta amsa mata. ta tsiyaya mata kunun tsamiya daketa ƙamshi dan ta fahimci Raudha naso sosai, zata zuba mata sauran abinci ta dakatar da ita. “Mama bara nasha wannan tukunna dai to”.


   Cikin ƴar dariya mama ladi tace, “Yunwar dai bata kai ko'inaba ma kenan to”.


   Dariya kawai Raudha tayi itama tana saka sugar. Mama ladi ta miƙe tana faɗin, “Bara na barki kici abinci naje kitchen muga mi za'a girka kar adalin shugabamu ya dawo da wuri. Amma mi za'a girka masa da kema kanki?”.


    A cikin zuciya Raudha tace (shi wannan mina sani zaɓinsa inba nama da fura ba) a fili kam sai tace, ko tuwon alkama za'ai masa ne, sai a haɗa da farfesun kayan ciki asa yaji da ɗan yawa dan yana mura..... Kodaima mama ku jirani naci abincin zanzo kitchen ɗin kawai”.


    “To shikenan a fito lafiya”.




  A nutse Raudha ta cigaba da shan kununta hankalinta nakan wayarta tana karatun wani littafin hausa da Bilkisu ta tura mata. Bayi take ba, amma yanda Bilkisu ke zuga littafin ya sata fara dubawa shekaranjiya. Sai kuma kamar wasa labarin ya tafi da ita ta nutsu a karatunsa. Dan ita bama tasan bayan marubutan dake buga littafi ba akwai na online sai yanzu. Kodan bata da wayar ne shiyyasa. Kuma ko sanda suke hutawa bata damu da waya ba shiyyasa bata taɓa maida hankalinta ga nasu Fatisa ba, amma tasha jin suna sauraren littafi a waya ta zata na masu bugawa ne da ake karantawa a gidan redio.




     Yunwa ce ta hana barcinsa tasiri shima. Duk da dai babu laifi ya ɗanyi tunda gashi har makara sallar la'asar yayi. Da ƙyar ya tashi zuwa toilet ya ɗan watsa ruwa duk da zazzaɓi dake jikinsa ga ciwon kai. A kallo guda zaka fahimci murar ta sake masa rugu-rugu dan saman hancinsa ya ƙara jaa sosai abinka da fari. Hakama idanunsa sun kumburo fiye da jiya fatarsu tai jajur. Ga shi dama baiyi wani barci isashe ba da daddare. Sama-sama ya shafa mai ya saka wando da riga masu ɗan kauri na kamfanin adidas harda hula a jikin rigar, sai dai bai ɗora hular a kansa ba ya saketa saman bayansa. Slippers ya zura cike da dauriya ya fito falon hannayensa duka a aljihun wandon, gara ya samu ko tea ya sha kozai samu nutsuwa ta wani ɓangaren. Tun daga nesa idonsa ke kanta, yayinda sam ita batasan dashi a wajen ba dan gaba ɗaya hankalinta ya tafine akan littafin da take karantawa mai suna *_SIYASA KO ƘABILANCI?_* na (marubuciya Bilyn Andull ƴar ƙasar Nigeria). Labarin ya matuƙar ɗaukar hankalinta saboda kamanceceniyarsa da tsarin da mijinta kamar yake kai a yanzun.


    Tafiya yake a hankali kamar baya so, saboda rashin ƙwarin jiki harya iso inda take, ya kai zaune a kujerar 3seater ɗin da take zaune sam bata fargaba. Sai da ya kai kwance ya ɗaura kansa bisa cinyarta tai saurin ɗagowa a zabure dan tsabar firgitar ganin kan mutum bisa cinyarta a baza .


    “Shut up!”.


Ya faɗa da yanayin tsawatarwa ganin zatai ihu sai dai muryar a ɗashe take fita da sanyi-sanyin dushewarta a dalilin mura da damuwa. Hannu Raudha tai saurin ɗaurawa a bakinta, sai kuma ta lumshe idanunta zuciyarta sai lugude take a ƙirjinta kamar zata faɗo. 


    “Sai shegen tsoro”.


Ya sake faɗa a hankali yana lumshe idanunsa da harɗe hannayensa a ƙirji ya miƙar da ƙafafunsa har bisa hannun kujerar da ƙyau. Raudha da sanin shi ɗinne baisa ta dai-daita ɗari bisa ɗari ba ta buɗe idanunta a hankali ta sauke bisa sumar kansa da ko ba'a faɗa ba kasan tana cin kuɗi kodan ƙyallin da takeyi duk da kasancewarta irin sumar baƙaƙen fata mai tauri da cika.


   Cinyarta ta ɗan motsa cikin ɓata fuska, a ganinta adalilin miye wannan taɓara da zaizo ya kwanta mata cinya babu gaira babu dalili. Motsa ƙafafun nata ya sashi buɗe idanunsa sai suka shige cikin nata da take hararar masa kai. Da sauri ta kauda kanta gefe da gyara yanayin fuskarta tace, “Ina yini”.


   Kamar koyaushe yanzun ma bai amsa ba, sai dai ya zare hanunsa guda daga saman ƙirji ya kamo haɓarta ya dawo da fuskarta yanda take. Cikin sake tsuke fuska ya ce, “Hararata kikeyi?”.


   Idanu Raudha ta ɗan zaro. “Ka rufamin asiri, ni yazanyi na hahareka?”.


   Kamar zaiyi magana sai kuma ya saki fuskar da maida hannayensa a ƙirji yana faɗin, “Inma kin hararenin ne iyakarki hararar, kuma duk matar dake harar mijinta dai kinsan aljanna sai dai ta gani dajin ƙamshi a maƙota”.........✍


No comments

Powered by Blogger.