Bakar Inuwa 39..........Sai da suka tabbatar ta fita a hayyacinta sannan suka fito a inda suke ɓoye fuskokinsu washe da fara'a tamkar ba mata ba. Ba imani babu tausayi duk da ganin jini na gudu a ƙasan Mable's ɗin dining ɗin, har yana gangarowa cikin falon da gudu.

         Shigowar kuku da yazo kwashe kwanika da tunanin an kammala da su ya saka Lubnah da ta farga da shi sakin wata irin ƙara tana nufar kan Raudha da tayo ƙasa zata faɗi cikin fita hayyaci. Munirah zatai magana itama ta farga da kuku sai ta sanya nata ihun itama. Ihunsu ya rikita falon gaba ɗaya har Mama ladi da Mama Tambaya dake falon ƙasa jiyosu suka hauro babu shiri.


★★


     Dole akai gaggawar mika Raudha clinic na cikin gidan. Dan duk wanda yaga yanda take zubda jini abun sai yayi matuƙar firgitashi. Doctors ɗin kansu ruɗewa sukai, haka suka rufu a kanta kusan su uku domin ƙoƙarin ganin sun tsaida jinin sun ceto rayuwarta, dan tuni numfashinta ya bar gangar jikinta. 

       Mama Ladi da duk ta gama ruɗewa ce ta kira Anne ta labarta mata abinda idonsu ya iya gani. Haka ma Mama Tambaya ta kira Aunty Hannah ta sanar mata. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga aunty Hannah ta iso saboda ta ɗanfi kusa da Anne. Itama Anne ba'a haɗa mintuna talatin ba ta iso harda Yafendo da Inna duk da suna fama da tsufansu.

       Har kusan azhar doctors ɗin gidan na gwamnati basu ce komai ga su Anne ba, dan Dr Hauwa ma da sukazo tare da su Anne itama ta ƙaru cikin doctors ɗin. Kowa yay jigum-jigum cike da fargabar abinda suke tsoron ji. Bama su ba shaƙiƙanta hatta da ma'aikatan gidan duk wanda al'amarin yaje kunnensa a tsorace yake. Gaba ɗaya sai gidan yay tsitt.

      Ramadhan baisan halin da ake ciki ba sai da suka fito salla COS ya samesa a office yake sanar masa kiran da ya samu da ga Chief security na gidan game da Accident ɗin da Raudha ta samu wanda har yanzu ba'a san musabbabin sa ba. Sosai hankalin Ramadhan ya tashi, amma a fuska bazaka taɓa tabbatar da haka ba, sai nanata kalmar cos ɗin yake a cikin ransa tamkar karatu. Gashi yana da shiga meeting a dai-dai lokacin kuma mai matuƙar muhimmanci. Haka dai ya dake cikin dauriya ya shiga meeting ɗin badan ya fahimci komai da aka tattauna a wajen ba. Baima haɗa mintuna talatin ba ya fito ya barsu su ƙarasa.

     Ya sake ganawar sirri da wani babban mutum da ga ƙasar Nigeria akan wani aikin haɗaka da suke sonyi da ƙasar ta Nigeria ɗin. Sai dai zaman nasu bai wani armashi ba saboda hankalin shugaban ƙasa rabi yana cikin gida. Awarsu guda suka kammala ya fita sallar la'asar. Abubuwan da suka rage masa na sauran awoyin ba wasu masu tsawwalawa bane idan ka cire ganawa da vice ɗinsa Alhaji Yaro glass, dan haka yasa cos sokesu sai gobe idan ALLAH ya kaimu shi kuma ya shiga gida.

      Iske su Anne da yay a gidan ya sake tabbatar masa da al'amarin babbane. Gashi sun sanar masa har zuwa lokacin basuji da ga doctors ɗin ba. Zama yay kawai cikin kujera ransa duk a dagule. Gaba ɗaya yama rasa wane kalar tunani zaiyi shi kam, yasan jiya ta shiga wani hali, amma lafiya lau ya fita ya barta yau ai. 

        “Anne har yanzu basu ce komai ba? Kuma babu wanda yasan miya faru daga nan ciki?”.

        Cikin jimami da damuwa Anne tace,, “To ALLAH kaɗai dai yasan musabbabin gaskiya. Amma su su Lubnah sunce tana cin abinci ne abin ya faru, suma sai ganin jini sukai malale a ƙasa, shine ma suka shiga ruɗanin da har ya fargar da su Ladidi”.

      Iska ya turo daga ƙirjinsa ya fesar ta baki a hankali tare da kai hannu saman goshinsa yana ɗan murzawa. Cikin jimamami Yafendo ta karɓe zancen da faɗin, “Shi dama cikin fari na mai rabo ne, sai dai fitar nata yazo da haɗari. Dan tsinkewar jini irin wannan kam tashin hankaline babba ga mai ɓari, sai kace wadda aka ba wani abu”.

       Aunty Hannah da tun ɗazun batace komai ba sai satar kallon shugaban ƙasa da takeyi, dan yau ne ta fara ganinsa ido-da-ido itama a cikin gidan tunda take zuwa. “Da alama cikinne ma dai baiyi wani ƙwari ba shiyyasa. Amma al'amarin yayi kama da wadda tasha wani abu kam gaskiya”.

       “Ciki?!”.

Shugaban ƙasa ya firta cikin kasa ɓoye al'ajab nashi. Kallonsa sukai gaba ɗayansu duk da kuwa yayi maganar ne a hankali. Anne tace, “Ikon ALLAH, kai bama kasan da cikin ba kenan? Amma jiya ba Hauwa'u tazo ta dubata ba?”.

        Kansa ya ɗan jinjina mata sai kuma ya haɗiye dukan abinda ke masa kaikawo a cikin rai. “Itama sai yau zata bamu sakamako dama Anne”.

    Yay ƙoƙarin danne gaskiyar zancen saboda wasu abubuwa da ke masa kai kawo a rai da zuciya. Shiru falon ya sake ɗauka na wasu mintuna. Kafin ya miƙe da kansa ya fita da ga falon zuwa Clinic ɗin. 

        Koda ya fito securitys sukai masa caa hana kowa binsa yay, sai dai duk da haka odilan ɗinsa bai yarda ya barsaba duk da dai a cikin gida ne. Ba wata tazara bace mai yawa tsakaninsu da clinic ɗin. Zuwansu yayi dai-dai da fitowar doctor Sambo da ga ɗakin ya baro su Dr Hauwa dake ƙarasa gyarata. Cikin ɗan rikicewar ganin oga kwata-kwata da kansa ya fara miƙa gaisuwa. Hannu kawai Ramadhan ya ɗaga masa, sai kuma yay masa nuni da office alamar su koma ciki..


    Suna shiga Aynah na Munirah dake laɓe suka kaima bango duka. Tunda suka kira Gimbiya Su'adah suka sanar mata ta basu umarnin zuwa su sami likitan su masa maganar komi za'ai kar bakinsa ya faɗi cewar da safe tasha maganin nan. Ya nuna tun jiya ta sha shi da yamma kuma ba yau ne na farko data sha ɗin ba. Shine sukazo fa, suna gab da isa ga doctor Sambo da suke zaman jira tun ɗazun sai kuma ga yayansu da kansa. Hakan ya saka su ɓuya dan kar ya gansu..


      “Wane issue kuka samu?”.

Ramadhan ya tambaya kansa tsaye dan shi baya son ɓoye-ɓoye ko jan rai a magana”.

      Cikin in-ina da fargaba Dr Sambo ya fara magana. “Ranka ya daɗe zuwa yanzu dai munyi nasarar ceto rayuwarta, mun kuma tsaida jinin. Sai dai ta zubar da jini sosai a yanzu haka muna ƙoƙarin samun wanda za'a ƙara mata ne. A binciken da mukai kuma mun gano magani ta sha wanda ya wuce ƙa'ida ma shine ya kawo tsinkewar jinin kamar haka. Badan anyi azamar kawota ba ma zata iya rasa ranta saboda maganine mai ƙarfi kuma abinda aka sha dominsa ma babu shi...”

        “Maganin miye?”.

“M...maganin abortion ne?”.

     “Abortion?”.

Ya maimaita maganar ta sigar tambaya.

    “Yes sir, sai dai kuma ma babu cikin, bincike ma ya tabbatar mana mahaifanta bai taɓa ɗaukar ciki ba sam. Hasalima a cikin yanayin perio....”

       “Ya isa haka..”

Ramadhan ya faɗa cikin ɓacin ran bayyanar kishinsa ƙuru-ƙuru daya kasa ɓoyuwa. Da ƙyar ya danne takaicin taɓa masa mata da sukai da sanin sirrin da basu dace da sani ba daga gareta ya fara magana mai kama da gargaɗi.

       “Wannan maganar ta tsaya iya ni da kai. A wajen kowa yazam cikinne ya zube da gaske. Kar a ƙarama matata jinin kowa a ɗiba nawa. Da ga nan zuwa gobe ina son sanin sunan ƙwayar data sha.”

     “Okay ranka ya daɗe insha ALLAH. Sai dai da zai yuwu zanso ganin abinda taci na ƙarshe dan kamar daga nan matsalar take”.

      Ɗan tsura masa ido Ramadhan yayi kamar mai nazari, sai kuma ya kauda idonsa yana miƙewa, “Muje ka ɗiba jinin, sauran aikin kayi magana da Chief security na gidan”.

      “Okay sir ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana. Ya kareka a duk motsinka da rayuwar iyalinka baki ɗaya”.

     A saman laɓɓa ya amsa yana ficewa daga office ɗin.


      Ba ƙaramin tashin hankali zuciyar Ramadhan ta shiga ba lokacin da yaga Raudha. Cikin ƙanƙanin lokaci ta zube ta sake haske mai ban tsoro alamar dai da gaske babu jinin a jikinta. Cikin cije lip dinsa da masifar ƙarfi ya kai hannu saman kanta ya shafa gashinta lokacin da yake kaiwa zaune a kujerar da Dr Sambo ya ajiye masa. Sai kuma ya sinkuyi kanta ya kai bakinsa saman goshinta ya sumbata. ALLAH sarki Raudha, inama ace idonta biyu taga wannan al'amari. Na tabbata jininta zai iya daskarewa ma baki ɗaya.

     Kamar yanda ya hana a saka mata jinin kowa nasa aka saka mata, dan kuwa dagewa yay sai da aka ɗiba leda biyun da suke buƙata ɗin. Sai bayan an saka mata ne su Anne suka samu damar shigowa suka dubata, zuwa lokacin har Ramadhan ya koma cikin gidan dan shima yana ɗan buƙatar kwanciya ya huta. Ya bama Chief security damar binciko duk abinda suka tattauna da Dr Sambo. Dan haka babu ɓata lokaci Chief security ya fara aikinsa akan sauran abincin breakfast da Raudha ta ci.

         Ba'a samu wani tangarɗa ba wajen gano Raudha tasha maganin zubda ciki ne ta hanyar ruwan shayi da yay saura a flask ɗin. Wanda a zahiri Raudha ta shanye sa tas, sai dai lokacin da Ramadhan ke sanarma Chief security aikin da zaiyine zancen ya shiga kunnen Lubnah. A firgice taje ta matsa ruwan zafi da ga dispencer ta jefa sabuwar ƙwayar magani a ciki jikinta na rawa. Batafi mintuna biyar ba kuma Chief security ya iso falon dan ALLAH yasa ma ba'a kai ga kwashe kwanikan ba saboda halin da Raudha ta shiga ya ruɗa kowa.

        Kuku bai farga da abinda ke faruwa ba sai da Chief security yasa aka kira masa shi. Gaba ɗaya ya rikice ya ruɗe, dan zuwa yanzu labari ya fara karaɗe gidanne first lady ɓarin ciki tayi, ana kuma zargin an saka mata wani abune ta ci a abinci.


      Su kansu su Anne a rikice suke da jin wannan al'amari musamman ma aunty Hannah da tasan suna da alaƙa da kuku. hasalima yaronsu ne su yakema aiki a gidan. A gefe kuma ta shiga mamaki da ruɗanin mizaisa kuku ya zubdama Raudha ciki? Saboda koba komai suma suna buƙatar cikin matsayinsu na jinin Raudha mafi kusanci. 


(To koma dai miye, wannan wata sabuwar cakwakiyace kuma🤥🚶🏻 Aunty hannaty).


★★★


       Ramadhan bai sake cewa komai ba akan batun duk da yaji cewar Raudha tasha ƙwayar ne da ruwan shayi. Hakan na nufin kuku's ne da aika-aikar, a yanzu haka kuma shugaban kuku'e ɗin dake da alhakin kula da abincinsu yana hanun securitys na gidan.

       Bayan sallar isha'i su Anne suka wuce gida har aunty Hannah. Sai dai zuwa lokacin Ramadhan yasa an dawo da Raudha cikin gidan tana ma ɗakinta. Alhakin dubata ya koma wuyan Dr Hauwa'u a yanzun gaba ɗaya, sannan Mama Ladi aka bari a ɗakin zata cigaba da kula da ita. 

        Ramadhan ya nunama Dr Hauwa'u yana son kowa ya cigaba da ɗaukar hakan har su Anne cewar cikinne da Raudha kuma ya zube. Batasan dalilinsa ba, amma kuma ta karɓa alfarmarsa dan ta fahimci akwai ƙulli a cikin al'amarin mai girma. Badan ma ALLAH ya taƙaita ba komai zai iya faruwa da mahaifar Raudha ɗin, a yanzu hakama basu da tabbacin komai zai iya zama normal.


★★


          Washe gari da safe ya tashi babu wani damuwar jinin da aka ɗiba masa. Dan har massallaci ya fita sallar asuba. Bayan dawowarsa massallaci ya jima zaune cikin sofa yana ƙullawa da kwancewa akan al'amarin. Wajen shidda aka kawo masa tataccen haɗin shayin lemon tsami da wasu ganyayyaki na shayi da yake sha a duk safiya dan shi ba ruwansa da wani coffee. 

        Har kukun dake kula da shayin nasa ta kammala ta fita bai motsa ba. Baima amsa ko gaisuwarta ba. Hakama bayan fitarta bai sha shayin ba dan tunaninsa ma baya tare da duniyar mutane. Bazai so ya zama silar hana wani cin abinci ba, amma dolene ya ɗauka wani mataki game da wasu ma'aikatan gidan musamman kuku's dake da alhakin basu abu suci.     

         A hankali ya furzar da iskar daya tara a ƙirji yana miƙewa batare da yabi takan shayin ba. Ba tsoron an zuba masa wani abu yake ba, kawai dai yau bama shi da ra'ayin shan komai ne kawai. Wanka yayo yay shirin office, tamkar kullum yau ma yayi ƙyau matuƙa yana ta baza ƙamshin turarurrukansa da suka amsa sunansu turare. Koda ya fito ɗakin Raudha ya nufa, kowa bai samu ba a ɗakin ba sai dai an gyara shi yanata ƙamshi. Raudha kwance a gado cikin bargo babu alamar ta farka. Tsaye yay akanta ya tsurama cute face nata ido, ta sake haske sosai, ta kuma rame. A hankali yakai zaune bakin gadon tare riƙo hanunta dake saman cikinta ya riƙe cikin nasa. Kasa jure abinda ya ratsa sa yayi, sai kawai ya rumtse hanun da ƙyau a cikin nashi har sai da taɗan motsa.

       Tabbas ya yarda ita ɗin ƙyaƙyƙyawa ce, sai dai a ganinsa tayi yarinta da yawa. A zuciya yake wannan tunanin, a zahiri kam ido kawai ya tsura mata. Yanada meeting da shuwagabanin tsaro baki ɗaya, dole ta sashi miƙewa yana ƙoƙarin zare hannunsa a cikin nata sai dai ta riƙe nasa ita kuma. Tsamm ya tsaya yana kallon hanun nata yanda ta matse yatsun nasa biyu tamkar tana ido biyu. A bazata murmushi ya suɓuce masa, sai dai komai baice ba ya zare yatsun nasa yana ɗon furzar da huci.


       ★

   Koda ya fita kafin yaje office ma wajen meeting ɗin ya fara zarcewa, dan ya makara, kuma zama ne mai matuƙar muhimmanci. Harkar tsaro da lafiya da ilimi sune sahun farko da yake burin fara shimfiɗawa al'ummarsa kafin komai. Dan haka yasa aka shirya masa zama da shuwagabanin jami'an tsaro ta kowanne ɓangare, dana lafiya takowane nangare, dana ilimi takowane ɓangare. Zai fara zama da jami'an tsaron ne kafin sauran suma.

      Meeting ɗin ya jasu lokaci saboda muhimmancin sa. Dan a ƙalla sun sami good 3hours. Koda ya shiga office bai iya taɓuka wasu abun arziƙi ba. Yadai gana da vice president Alhaji Yaro glass akan wasu muhimman batutuwa. Sanda suka kammala lokacin salla yayi. bayan dawowarsa massallaci ya gana da COS daga nan ya tafi hutun awanni biyu. Maimakon zaman hutun sai yay zaman yin waya da Bappi.


      Ƙarfe biyar na yamma ya shigo gidan yau. Sai da ya fara zuwa ɗakinsa yay wanka ya kimtsa cikin ƙananun kaya sannan ya fito domin duba jikinta. Bai samu kowa a ɗakinba yanzu ma. Motsin ruwa da yaji ya tabbatar masa tana toilet, agogon dake a tsintacciyar hanunsa ya kalla tare da ɗan bin ɗakin da kallo. Saukar idanunsa akan hoton dake saman bed side drawer ɗinta ya sashi takawa a hankali garesa hannayensa duka cikin aljihun wandon jeans ɗin sa, hoton ya tsurama ido duk da bawani fitaccen hoto bane, hasalima ya ɗau shekaru, dan mace ce da mijinta sai yara huɗu, ɗaya jaririya a hanun mijin, sai ƴar shekara 7 da kamanin Raudha ke tare da ita tabbacin dai itace ɗin. Sai biyu da bazasu wune shakara tara ba da alama twins ne. 

      Kiran da akaima wayarsa ne ya katse sa da ga kallon hoton, ya zarota a aljihu yana mai janye idanunsa a hoton gaba ɗaya. A kuma dai-dai lokacin Raudha ta fito da alamun wanka tayi.

       A hankali take takowa cikin ɗakin dan da farko bata lura da shi ba. Sai dai kuma yanda ƙamshinsa ya cika ɗakin ya sata tsarguwa harta kasa ƙarema ɗakin kallo. Sallamar da yay lokacin da yake kai wayar a kunnensa ya sata tsayawa cak daga takowar da take, gaba ɗaya jitai ta daburce, gashi ta riga da tazo kusan tsakkiyar ɗakin tasan dai ya riga ya gama ganinta kuma. Kallonsa ta ɗan sata kaɗan, ya ɗan zuba mata idanu tamkar mai shirin gano wanda ya aikata mata abun a jikinta.

      Da sauri ta maida idanun nata ƙasa. Shima ya janye nasa yana cigaba da sauraren masifar da gimbiya Su'adah ke masa ta cikin wayar, shi gaba ɗaya ma ya rasa dalilin faɗan nata shiyyasa saurarenta kawai yake batare daya fahimceta ba har tayi ta gama ta katse kiran bayan ta bashi umarnin ganinsa.

      Kansa ya ɗan girgiza kawai yana sauke numfashi, a zuciyarsa mamakin daru irin na mahaifiyarsa yake. A zahiri kam idonsa ya maida ga Raudha datai tsaye tamkar an dasata

    “Ƙaraso mana”.

Ya faɗa a hankali tamkar baya so.

            Duk da bathrobe ce a jikinta gaba ɗaya kunya ta dabaibayeta. Amma saita daure ta ƙarasa bakin gadon dan jiri take gani ma. Tana gab da isa jirin ya kwashe tai tamkar zata faɗi ALLAH ya taƙaita sai jinta tai jikin mutum............✍


No comments

Powered by Blogger.