Bakar Inuwa 35

 


*_Episode 25_*



.........Shi dariya ma ta bashi, amma sai ya dake abinsa, duk da ya fahimci kusancinsu ne matsalarta yaƙi kuma janye jikin nasa.

      “Kin zama kurma ne?”.

Da sauri ta girgiza kanta, tana ɗan matse jikinta waje guda.. 

   “Mikake so?”.

       Ta faɗa da rawar harshe.

Karan farko ya saki wani guntun murmushi dashi kansa a ƙarjinsa kawai yaji abinsa. Sai kuma ya miƙe da ga kanta ya taka zuwa kujerar gefenta ya zauna. Wayarsa dake faman vibration ya ɗauka, a yanda yake magana zaka fahimci mai muhimmanci ce, sai dai kuma ɗan walwalar dake kan fuskar tasa ya ida ɓacewa gaba ɗaya. Sunan Maa da taji ya ambata ya tabbatar mata da gimbiya Su'adah ce, kusan mintuna uku ya ajiye wayar batare da ta bashi damar yin wata kwakwkwarar magana ba.  

    Lip ɗinsa na ƙasa ya tura cikin baki da ƙarfi ya shiga taunarsa, yarasa miye manufar Maah ɗin na zuwan su Lubnah gidan su zauna. Abin takaicin ma a yanzu harda sharaɗin kar'a kuskura a ajiye mata yara a sashen baƙi. Dolene yaci uban yaran nan gwargwadon iko a wannan karon, dan zai saka musu ido sosai tare da abinda ko tace suzo zasuce a'a 

         

                ★Ganin yanda yanayinsa ya canja zuwa ɓacin rai sosai ya saka Raudha da zuciyarta har yanzu ke kai kawo ɗan duban agogon ɗakin. A ɗan ɗarare ta ce, “Zanje nayi salla, magrib tayi”.

            Komai baice mata ba, sai dai ya kafeta da ido tamkar mai son gano maganin takaicin da Maah ta cusa masa yanzu a jikinta. 

       Kanta ta duƙar ƙasa, wani ɓangare na nasihar Anne da Mummynsu na mata kaikawo a zuciya. _(Idan kin gansa cikin fushi, koda bake kika ɓata ransa ba ki faɗa masa magana mai daɗi da zata kore fushin nasa koda bazai saurareki ba. Idan har kika gusa a wajen zai maida hankali ga maganarki kuma fushinsa ya kwaranye, kimarki ta sake girma a idanunsa har yaji wataran kece kikafi kowa cancanta daya tunkara da matsalolinsa)._ Ɓoyayyen numfashi taja a hankali, zuciyarta na sake tunzurata akan gwadawa koda bazai kulatan ba. Kallonsa taɗan sata, ganin yanda ya lumshe idanu yana faman taunar lip data fara fahimtar ya zame masa ɗabi'a yasata haɗiyar busashen yawun da ya tokare maƙoshinta. 

       _“A kowanne lokacin haƙuri shike kwaranye abinda zuciya bataso ba. koda ɗacinsa yafi ƙarfin ƙwaƙwalwa”._

        Raudha ta faɗa cikin matuƙar dauriya da ƙundunbala. Bakuma ta jira amsa ba ta kwashi kwankan da admission latter ɗin da ya bata ta kama hanyar fita a ɗakin cikin sassarfa, zuciyarta na luguden daka kamar zata fito. Dan sam batai tunanin zata iya faɗa masa maganar data faɗa ɗin ba yanzu sam.

         A hankali ya buɗe idanunsa da suka canja launi ya zuba mata, harta fice a ɗakin bai iya koda motsawa ba. Abu biyu ke masa kaikawo a rai. _Mamakinta_ da kuma _Ƙarfin halinta_.


         Raudha kam koda ta koma ɗaki bayan ta idar da salla admission ɗin ta sake ɗauka ta duba sosai, sai lokacin ta sake samun damar fara tsallen murna dariya na suɓuce mata da hawaye a lokaci guda. Inama tanada waya ta kira Mummy ta sanar mata, kai harsu Fatisa da Abbansu ma da duk saita faɗawa.

     Bata sake bi takan Ramadhan ba, sai dai ta kasance cikin ɗunbin farin cikin daya bata a wannan dare. Washe gari batai ganda ba ta shiga kitchen da taimakon mama Ladi da kuku suka shirya breakfast, dan bata san yau ma ba fita zaiyi ba. Ɗaki ta koma tai kwanciyarta dan murna bata bari tai barcin arziƙi ba jiya da dare. Sosai tasha barci, dan sai wajen sha biyu ta tashi. Wanka ta shiga bayan ta kimtsa ɗakin, tana tsaka da shiryawa ta samu saƙo daga mama ladi cewar tanada baƙi. Yin baƙi yanzu ba baƙon abu bane a gareta, dan haka ta canja akalar shirin nata datai niyya da doguwar rigar jallabiya ta sanya lass.

        Tuni Mama tambaya ta musu masauki da tarbar data dace da su, dan kuwa aunty Hannah ce matar vice president da wasu hamshaƙan mata su kusan shidda. Tabbas duk sun girmeta da finta wayewar rayuwa. Amma itama zama da Mama ladi da Mama tambaya ga huɗubar Bilkisu Da Anne data samu, ga wadda su aunty Hannah suka saka a mata tunkan ta shigo gidan yasa zuwa yanzu indai dressing ne baza'a nuna mata komai ba. A ɓangaren nutsuwa kuwa dama kowa yasan Raudha Alhamdulillahi bata da matsala tanan. A gefe kuma duk abinda ya haɗa da aunty Hannah *_TAKUN SAƘA_* take masa, dan karku manta a fuska Raudha yarinyace mai haƙuri, sai dai su aunty Hannah basu taɓa tunanin murɗaɗɗen haline da ita a baɗini ba.

          Da sallama suka shigo falon guards ɗinta da mama tambaya da mama ladi na take mata baya. (Tabbas Raudha first lady ce da jinta yafi ganinta). Ta kai zaune fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi, ƙasan zuciyarta ɗauke da addu'a. 

       “Mom barkanku da zuwa”.

Ta faɗa idonta akan Aunty Hannah dake mata kallon mamaki. Dan wani ƙyau da cikar kamala Raudha ta sake mata har da ƙiba. Ga wani buɗewa da taga idonta ya ƙarayi. (Da alama yarinyar nan tasan namiji zuwa yanzun) Aunty Hannah ta rayama ranta dan a tunaninta sanin namiji ga ɗiya mace shike sake buɗe kanta da idanu. Murmushi ta saki na basarwa ta amsa Raudha ɗin cike da tsantsar kulawa.

      “Oh my baby kodai nayi jika ne? Irin wannan ƙyawu haka?”.

    Kunya ce ta kama Raudha, amma sai ta dake ta saki murmushi kawai batare da tace komai ba. Sauran matan dake ɗan darawa suka shiga faɗin ashe munada gagarumin biki kuwa. Nanma dai komai Raudha batace ba, sai murmushin dake fuskarta da har yanzu bai gushe ba. Har suka taɓa ɗan barkwancinsu kuma bata tsoma baki ba, dan dukansu a haife sun haife ta, mutum ɗaya a cikinsu zata iya kira da yaya dan ita bata kaisu shekaru ba.

        Bayan sun ajiye barkwancin nasu a gefe aka gaisa a mutunce, Raudha bata bada wata ƙofar da wani aciki zai amfani da ƙarancin shekarunta ya kawo mata raini ba koda a magana ne. Aunty Hannah ce tai mata bayanin dukansu matan ministoci ne, sunzo ne domin yin godiya a gareta da miƙo gaisuwa ga shugaban ƙasa.

     Raudha ta ɗan jinjina kanta, cike da nutsuwarta da salon jin kai da aunty Hannah ke ganin kamar Raudha ta fara take binsu da kallon ƙasan ido. Sai da taja kusan mintuna biyu kafin ta fara magana.

      “Muma muna godiya da ziyara, ALLAH ya bar zuminci. Shugaban ƙasa kuma zaiji saƙon gaisuwarku”.

       A kaikaice aunty Hannah ta ɗan waro ido waje, ta shiga ƙyaftama Raudha idanu amma sai Raudha ta basar da ita tamkar ma bata lura ba. Ganin haka aunty Hannah ta miƙe tana faɗin, “Ya kamata kuɗan taɓa wani abu ko, bara uwa da ƴa su zuge labule”.

       Murmushi duk suka saki, dan tuni ta riga ta gama baza musu alaƙar dake tsakaninta da Raudha, kuma kamanin da suka gani tsakaninta da Raudhan ma ya sake tabbatar musu da haka. Kamar Raudha bazata miƙe ba, sai kuma ta tashi a nutse suka nufi ɗaya da ga cikin bedroom ɗin dake a falon.

        Suna shiga aunty Hannah ta damƙi hanun Raudha ta maida ƙofar ta datse. “K kinada hankali kuwa? Kinsan su waye waɗan nan matan?” Kafin Raudha tace wani abu ta cigaba da faɗin, “To ki saka hankalinki a jikinki waɗan nan duk zasu iya sayen garinku hutawa ne da kayan cikinsa. Kin wani zauna kina musu yatsina da jan aji dan sunce suna son ganin shugaban ƙasa”.

      Raudha da ke binta da kallon mamaki ta ce, “Amma Mom shugaban ƙasa dake office yanzu ta ina zan kaisu wajensa? To ko a gida yake ma ganin shugaban ƙaramin abune Mom?”.

     Aunty Hannah dake hararta ta ce, “K wawuya kina kwana da mutum a gida ɗaya amma baki san komai nasa ba. Abban Samha ya sanarmin sai monday zai fita office yana gida. Wai kuwa ma kina aikin da muke buƙata a gidan nan ko zaman samun canji waje da canja kayan da Asabe bata taɓa saka makamantasu ba kika tsaya”.

     Sosai maganar aunty Hannah na ƙarshe ya soki Raudha fiye da komai, amma sai ta danne tama saki murmushi. Takuma ƙi cewa komai.

      Wani irin takaici ya turniƙe zuciyar aunty Hannah, jitai kamar ta shaƙe shegiya ta huta. Dan ita ba hangen Raudha zata iya cin amanarsu take ba, zuciyarta kawai tana bata dan Raudha ta shigo daula ne take son fara raina mata wayo da tunanin tana dai-dai da ita.....

         Ganin aunty Hannah ta lula duniyar tunani Raudha tai tunanin maido da ita, dan ta fahimci fiddoma aunty Hannah ainahin kanta a yanzu ba nata bane. Cikin murmushi da nuna ɗoki tace, “Mom dama fa wlhy inata son ganin wani a cikinku, ya samarmin makaranta fa”.

       Firgigit aunty Hannah ta dawo hayyacinta, sai kuma ta saki murmushi da faɗin, “Kai Alhmdllhi da wannan labari, naji daɗi dan yayi abinda ya dace. Dama da batun nan nazo a raina, dan ya kamata ace kema zuwa yanzu kin fara fiddo kanki wa jama'a sosai, bawai ki kume cikin gida ba kamar kowace mace. Karfa ki manta ke first lady ce, ki masa maganar ya baki office ki fito duniya tasan ƙoƙarin ki...”

      Cikin mamaki Raudha tace, “Mom office kuma?”.

      “Eh office! Ko kina nufin haka zaki cigaba da zama ƙumshe a cikin gida ne, k wai kuwama kinsan mike miki ciwo? Kina matsayin matar shugaban ƙasa amma ko waya baki da shi?. Ina karatun da su Feena suka koya miki badai a banza ya wuce ba?”

             Raudha taja ajiyar zuciya kawai batare da tace komai ba, hakan ya sake tunzura zuciyar aunty Hannah, cikin takaici tace, “To wlhy inma zaki dawo cikin hankalinki kiyi maza ki dawo. Bazai yuwu ki zauna kina mana ƙauyanci ba da shirme, kinsan nawa first lady ta narkar na kuɗi akan a koya miki abubuwan can kuwa? Amma Raudha gaba ɗaya kina nuna ma komai bai shiga kanki ba......”

       “Mom nifa bawai bai shiga bane ba. Kawai dai duka yaushe na shigo gidan. Kofa wata biyu ba'a cika ba. Yanzu dan ALLAH idan yaga ina rawar kai da wuri ai saima ya gane komai. Shifa ba irin yanda kuke tunani bane ba, mutum ne mai lura da saurin fahimta. A yanzu haka bawai ya gama yarda banda alaƙa da wanda yaso kashe Bappi a filin idi bane ba......”

        “Kusun uban can, kujimin ɗan iskan yaro. Duk yankan da kikasha bai gani ba zaima dinga ɗaukar haka?  To aiko zai gane kurensa wlhy. Yanzu abinda zan faɗa miki shine komi zai baki na magani karki sha, ko shi ko danginsa. Dan na kula waccan shegiyar uwar tasa zamu dama da itane, kaɗan daga aikinta tabi duk hanyoyin da zatabi danta daƙileki ga ɗaukar ciki. Ni kuma babban burina yanzu na ganki da ciki, dan koba komai kema ya kasance kinada wani kaso a dukiyar Taura. Sannan shima shugaban ƙasar komansa yazam namu ne. Abu na biyu ki fito ki nuna masa kina son fita fa kema a dama dake a harkar mulki, dan haka a baki office naki. Kuma wlhy ki nema waya bana son wawanci, ko kina nufin duk sanda nake buƙatar magana dake sai na dinga tako ƙafa nazo nan a matsayina na matar vice president?”.

       Kai kawai Raudha ta jinjina mata, a takaice tace, “To duk zanyi”.

      “Karma kiyi mana”.

Cewar aunty Hannah a ƙufule.


      Koda suka fito tsaf aunty Hannah ta canja yanayinta kamar komai bai faru ba. Itama Raudha dai bata bada wata ƙofa na fahimtar komai ba. A zaman nasu ne daga cikin matan ta ke kawo shawarar ya kamata first lady ta buɗe musu office. Ma'ana dai irin ƙorafin aunty Hannah. Atake kuwa duk sukai na'am. Raudha dake ɗan murmushi tace insha ALLAH zatayi shawara. daga haka ta tsuke bakinta. dama can ba komai take saka musu baki ba.

      Wasu a cikinsu suna ɗauka dan tana ganin kanta sa'ar ƴaƴansu ne kawai shiyyasa take girmamasu da ƙin cewa komai. sai dai kuma hasashensune wannan, Raudha tana karantar kowa da lafazinsa ne kawai.


     Bayan wucewarsu baifi da mintuna goma sha bakwai ba sai ga su Maneerah. Ko kaɗan Raudha batai farin ciki da zuwansu gidan ba. Musamman ganin babu Bilkisu da Basma a wannan karon. Amma sai ta danne ta musu tarba ta mutunci duk da kallon banza da suke mata suna wani dariyar iskanci.

        Cikin dauriya ta bama mama tambaya umarnin a gyara musu ɗakin da zasu zauna. Amma sai Aina ta katseta. “Talaka bai iya cin arziƙi ba idan ya samu waje”.

     Lubnah ta doka tsaki tana ma Raudha wani shegen kallo. “Shi wanda ya ajiyeki a gidan bai miki bayanin inane masaukinmu ba ne?”. Kafin Raudha tace wani abu Manirah ta ajiye wayar hanunta tsakkiyar centre table. Saukar maganar gimbiya Su'adah kawai taji a cikin kunenta a bazata....

         “Bata wayar.”

“A wlhy Maa wannan trash ɗin bazata taɓamin waya ba. Gashi nan nasa hansfree yi mata magana”.. 

     Munirah ta faɗa tana harar Raudha da tura wayar gabanta. Cikin kaushin murya da ga can gimbiya Su'adah ta cigaba da magana a kausashe, dan kuwa warning mai ƙyau taima Raudha cikin kausasa harshenta, ta kuma tabbatar mata a wannan karon idan tai wani abinda Ramadhan harya dawo da su Ainah sashen baƙi wlhy itama sai ta ɗanɗana kuɗarta sannan tabar gidan. Daga karshe ta bita gorin kasancewarta ƴar talaka jinin karuwai kuma mayya.

       Waɗan nan lafuzza na Gimbiya Su'adah sun yima Raudha zafi da ɗaci mai tsanani, harta kasa iya riƙe hawayen da suka ciko mata idanu sai da suka zubo. Batama jira Munirah da suke dariya ta ɗauka wayarta ba ta bar wajen zuwa upstairs da ɗan gudu kuka mai ƙarfi na ƙwace mata.. Babu zato taci karo da mutum har goshinta na buƙagar ƙirjinsa. Da sauri taja baya tana ƙoƙarin maida kukan nata ta haɗiye, sai kuma tasa hannu biyu ta goge hawayen da suke rige-rigen sakko mata.

      Shugaban ƙasa Ramadhan dake tsaye hannayensa duka cikin aljihun wandonsa ya kafeta da ido batare da yace komai ba. Cikin muryar wanda ke son yin kuka Raudha ta ce, “Ina yini ya jiki?”. 

       Bashi da niyyar amsawa, sai cigaba da kallonta da yakeyi kansa tsaye, kusan mintuna biyu Raudha ta fahimci ba amsa mata zai ba, ga shi kukan da taketa dannewa son kwace mata yake, raɓashi tai ta wuce hawayen na ƙwace mata. Komai zata iya ɗauka daga Ramadhan da danginsa. Sai dai kalmar karuwanci da ake jifan iyayenta da shi yana taɓa mata zuciya. Tasan gaskiya suke faɗa, amma kalmar na mata zafi, zafi irin wanda ke ƙona zuciya.

           Tsaiwa ya cigaba da yi a wajen kunnuwansa na sauraren darerakun su Aina'u da ke downstairs da maganganun banza da sukeyi akan Raudha ɗin. Iska ya ɗan furzar da tura lip ɗinsa cikin baki kaɗan yana ciccizawa. Sai da wayar jikinsa da ke ring na gab da tsinkewa sannan ya cirota a ljihu, ya haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa kafin yay dialing no ɗin dan kiran ya riga ya katse. 

     “Barka da yamma”.

Ya faɗa a tausashe dan son danne ɓacin ransa. Da ga can gimbiya Su'adah ta amsa masa a gadarence cikin kaushin murya da ragowar fushin Raudha dake a muryarta. Shima dai ɗin gargaɗin tai masa akan su Lubnah. Ta kuma jaddada masa idan taji wani abu yaje kunnen su Anne ransa sai ya ɓaci matuƙa. Da ga haka ta yanke wayar batare da jiran cewarsa ba.

       Karon farko ya saki guntun murmushi yana kai hannu bisa sumarsa ya shafota da tura wayar a aljihu tare da hanunsa duka. Kamar yanda bai furta mata komai ba, a yanzun ma data yanke komai bai ceba duk da akwai abin cewar a bakinsa. Tsaiwar wasu ƴan mintuna ya karayi a wajen tamkar mai nazari, kafin ya nufi hanyar ɗakin Raudha cikin tafiyarsa da babu garaje, wadda da yawan mutane ke kallon girman kai ne ke sashi salon takun kawai da nuna shiɗin wani ne. Sai dai sam ba haka baneba, halitarsace hakan kawai...

          Koda ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga tsaye yay kawai yana kallonta batare da ya shigo gaba ɗaya ba. Tana kwance a saman gado rubda ciki tana kuka, ya shaida hakane saboda yanda shashshekar kukanta ke tashi a ɗakin. Sam bai cika son ganin mutum a damuwaba a tayuwarsa, saboda ya ɗanɗani ɗacin damuwa baiji da daɗi ba, kai zai iya cewa har yanzu tana ƙunshe da ciwon damuwa, baya tunanin kuma zai samu waraka har sai randa ya koma ga ALLAH.

    Ƙarasa shigowa yay ɗakin yana ɗan bin ko'ina da kallo. A ɓangaren tsafta ya jima da bama Raudha lambar yabo, ba komai yasa haka ba sai kasancewarsa mutum mai tsananin son tsafta da ƙamshi. Zamansa a bakin gadon ya fargar da Raudha shigowarsa, tai saurin share hawayenta da miƙewa zaune har kafarta na ɗan shurin jikinsa. Bai juyo ya kalleta ba, bai kuma ce mata komai ba duk da yana kallonta ta wutsiyar ido. 

    Hawayen da ke cigaba da sakko mata take sharewa da ƙoƙarin ganin ta tsayar da kukan. Tsahon wasu sakanni kafin ta samu nasarar danne hawayen da ƙyar.

     “Kana buƙatar wani abu ne?”.

     Ta faɗa cikin girmamawa da tausasa harshe a garesa tamkar yanda ta saba. Sai lokacin ya ɗan juyo yana dubanta, ya kafeta da shanyayun idanunsa da ke nuna alamar bai jima da tashi a barci ba, ko kuma dai akwai abinda yake saɓanin barcin a cikinsu.

       “Karfa ki zata lallashinki nazoyi yarinya”.

     A yanda yay maganar batasan murmushi ma ya suɓuce mata ba. Ta kauda kai gefe tana sake share hawayen nata. Kishingiɗawa yay yanda zai iya kallon fuskar tata sosai. Shima fuskar tasa da ɗan murmushi dake iya laɓɓa. Cikin kafeta da idanunsa ya ɗan leƙa fuskar tata, “K kuka baya miki wahala ne? Ko dama haka ustazan suke saboda tsabar ƙarfin imaninsu?”.

       (Kai jama'a wai miya shiga kan mutumin nan ne kwana biyun nan?) ta ambata a zuciyarta tana kai hannu saman fuskarta ta rufe murmushinta na ƙara faɗaɗa. Hannunsa yasa ya buge hannayen nata data rufe fuska. 

      “Gulmammiya nasan kinanan kinajin daɗi kamar ki taka rawa shugaban ƙasar NAYA yazo lallashinki kina kuka”.

       “Ni Aminatu yaushe nace?”.

Ta faɗa cikin waro masa manyan idanunta gaba ɗaya da ɓata fuska cike da shagwaɓa...........✍


No comments

Powered by Blogger.