Bakar Inuwa 34

 


*_Episode 34_*..........Bai bata wannan damar ba, sai ma saurin riƙota da yay ya tallafe da hannunsa da ƙyau, dan ya tabbatar dabai mata hakan ba zata iya zamewa a samu matsala. Karan farko, a kuma lokaci na farko da hakan ta faru. 

     “Relax”.

Ya faɗa cikin wata irin muryar data nema gusar da hankalin Raudha, maimakon ta samu nutsuwar daya ambata. Ganin ba nutsuwar zatai ba ya juyata ya jingina da jikin glass da akai kwalliyar stairs ɗin da shi. Sai dai har lokacin tana a jikin nasa. Numfashi taja da ƙyar, ta haɗiyi kakkauran yawun daya kasa gusar mata da bushewar maƙoshin data riski kanta a ciki, tsahon minti guda da wasu sakanni bai sake magana ba yana kallonta kawai, sai da ya ɗanga numfashinta ya dai-daita ya janye jikinsa a nata ya matsa baya kaɗan. Hannayensa ya zura cikin aljihu duka yana furzar da ƙaramar iska shima a bakinsa.

       “Miya faru?”.

Ya faɗa idanunsa na cigaba da yawo akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da har yanzu take a ɗan firgice. Kanta ta girgiza masa, ta lalubo amsa da ƙyar da ga ƙwalwarta zuwa harshe. 

      “Ba komai, kawai naji ance su Anne sun zo ne”.

          Shiru baice komai ba, sai dai har yanzu idonsa kafe a kanta. Jin shirun ya sata ɗan ɗagowa da tunanin ko baya tare da itane? Duk da kuwa tanajin tasirin kaifin idanunsa a kanta. Janye idanunsa yay cike da basarwa ya maida downstairs duk da baya iya hango su Annen sai hayaniyarsu sama-sama.

        “Ni sukazo dubawa”.

Ya faɗa har yanzu idonsa a downstairs.

      Cikin subutar baki da waro idanu Raudha tace, “Baka da lafiya ne?”.

     Yanda tai maganar kanta tsaye, da waro idanunta farare tas ya matuƙar tada tsigar jikin sa. A gefe kuma taso bashi dariya amma sai ya gimtse. Takawa ya ɗan ƙarayi gabanta, ta matsa baya tana sake mannewa da glass ɗin. Hannunsa ɗaya ya ɗaura jikin glass ɗin gab da ita, ɗayan na cikin aljihunsa bai cire ba. Ya ɗan ranƙwafo kanta yanda har tana iya jin saukar numfashinsa a saman fuskarta.

     “Kin damu dani ne balle ki sani?”.

(Ya ALLAH) Raudha ta ambata a cikin ranta, dan kaɗan ya hana zuciyarta yin tsalle ta fito ta bakinta daga ƙirji. 

     “D...dan ALLAH kayi haƙuri”.

Ta faɗa kamar zata fashe da kuka, duk da idanunta a rumtse suke.

    Karon farko Ramadhan ya saki wani ɗan guntun murmushi da lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta, tare da sake kusanta fuskarsa da tata. A bazata ya sauke lips nashi a kan nata ya sumbata. 

         Gaba ɗaya ta waro masa idanunta baki a hangame jikinta na tsuma. Wata ƴar shaƙiyyar dariya yayi yana sake maida lips ɗin nasa saman nata ya tsotsa. Sai kuma ya janye ya ɗan ɗallesu da yatsansa manuniya har yanzu fuskarsa ƙayace da murmushin da bata taɓa sanin ya iya ba

       “Ustaza ana so ana kaiwa kasuwa”

 Ya faɗa cikin raɗa da ɗan rungumota jikinsa. Jin numfashinta kamar yana barazanar ɗaukewa ya sashi sake sakin murmushin mai faɗi ya janye jikinsa ga baɗaya ya bata iska. Aiko sai ga Raudha da sakin wata wawuyar ajiyar zuciya da ita kanta sai da taji kunyar kanta.

    Bai sake cewa komai ba ya nuna mata hanyar downstairs ɗin alamar suje. Kasa kallonsa tayi, bakinta kuma ya gagara furta komai balle tace masa wani abu, kai ji take ma kamar ta zama matatta dan bata gane komai😹🤭...


        Kusan gaba ɗayansu suka zubo musu ido lokacin da suke sakkowa. Duk da kan Raudha a ƙasa yake sai da taji kaifin idanunsu a jikinta. Dama gashi mai gayya mai aikin ya gama sukurkuta mata rayuwa a sama. Dan har yanzu zuciyarta bata bar luguden daka akan abinda ya faru ba.

       Anne, Bappi, Pa kallo guda sukai musu suka ɗauke zukatansu fes da farin ciki, hakama fuskokinsu ɗauke da murmushi. Gimbiya Su'adah ma dai a kallo gudan ta ɗauke idanunta cike da takaici da sakejin tsanar Raudha, dan ji take kamar ta kunna mata wuta ta babbaka banza. Hajiya Mufida da Hajiya Shuwa kuwa tsantsar kishi ne sosai a ransu. Yayinda sauran yaran mafi yawa babu komai a ransu sai ɗan abinda ba'a rasaba na ƴan ubanci da shakkar Ramadhan ɗin a tare da su. Sai ko su Lubnah dake zubama Raudha kallon tsantsar tsana a kaikaice.

      Rufaidah da Basma and Fadila suka taso suka rungume Raudha bakunansu kamar gonar audiga....


       Cikin nutsuwa Raudha ta kai duƙe gaban Bappi da Anne ta gaishe su. Fuskokinsu cike da fara'a dajin ƙaunarta suke amsawa. Suka ɗora da tambayar ya jikin mijin nata?. Kanta a ƙasa ta amsa musu kafin ta koma gaishe da Pa shima, shima dai ya amsa mata da kulawa yana tambayar jikin Ramadhan ɗin. Nanma dai kanta a ƙasa ta amsa fuskarta dai da ɗan murmushin girmamawa wanda yake sukar zuciyar gimbiya Su'adah matuƙa. Dan koda Raudha ta gaishe ta da ƙyar ta amsa. Bakuma ta tambayeta jikin Ramadhan ɗin ba. Dan a ganinta Raudha bata isa ba.

        Raudha dai ba kallonta take ba, sai dai a ranta tanajin shakkar uwar mijin nata da take hango ɗunbin tsana da ƙyamar da take mata ƙiri-ƙiri. Ta gaishe da su Hajiya Shuwa ma. Sukam cike da bariki suka amsa ma Raudha ɗin da kulawa suna tambayarta jikin Ramadhan. Sauran yara kuwa ta gaida wanda suka girmeta, yayinda su Lubnah suka basar da ita itama sai tayi kamar bata gansu ba ta wayance da amsama Anne tambayar da ta jeho mata akan Ramadhan ɗin na kula da shan maganinsa dai ko?.

        Raudha ta ɗan saci kallon inda ya ke zaune cikin kujerar dake gab da Bappi. Ido suka haɗa, tai azamar janye nata tana fafutukar nemo amsar data dace ta bama Anne.

       “Oh Anne, har yanzu dai kina ɗaukata wani baby doll na lura?”.

      Yanda yay maganar a ɗan narke ya saka Bappi da Anne darawa. Pa yay murmushi kawai, dan kowa yasan ƙaunar dake tsakanin Ramadhan dasu Anne sai dai ALLAH yasan iyakarta. Hanunsa Bappi ya kamo cikin nasa har lokacin fuskarsa da murmushi mai faɗi. “Gaskiya ka girma kam, kai da ke shugabantar babbar ƙasa irin NAYA ai ka wuce doll”.

       “Yauwa Bappi na dama nasan yanzu munfi shiri” Ya ƙara faɗa a narke.

              Mikewa Raudha da abin ya nema girman kanta tai, karon farko na rayuwarta ta koma sashenta domin bada umarnin shirya abinci. Amma rashin sanin yanda tsare-tsaren suke yasata neman mama tambaya. Mama tambaya ce tai mata bayanin wannan alhakin shugaban ma'aikata ne. Shine yasan tsarin aikin na kowanne ɓangare a gidan.

     Babu jimawa aka nemo mata shi. Ya iso gabanta cike da girmamawa duk da kuwa babban mutum ne. Amma mulki sha'aninsa daban ne ai. Ta masa bayanin abinda take buƙatar ayi. Ya tabbatar mata cikin girmamawar da harga ALLAH kunya take bata. Sai dai babu yanda zatayi tunda ga'a inda ta tsinci kanta bisa alƙalamin ƙaddara. 


     Cikin ƙanƙanin lokaci aka kammala cika umarnin Raudha da tuni ta koma wajen su Anne. Duk da tasan basuzo da yunwa ba dai ta saka an shirya musu abubuwan motsa baki kala-kala domin karramawa. Sai fruits da kayan sha. Dan danan falon ya kaure da ƙamshin abubuwa. Har cikin rai Ramadhan yaji daɗin abinda tayi, hakama Anne ta sakejin ƙaunar yarinyar a ranta matuƙa.

      Kowa ya ɗan taɓa wani abu, idan ka cire gimbiya Su'adah dako ruwa bata kurɓa ba. Sai ma sake miskile fuska da tai tanta harare-harare. Sam Ramadhan baiji daɗin yanayin nata ba, gashi yasan haushinsa takeji tun akan abinda yay ma su Lubnah dan bai yarda sun haɗu ba tunda suka dawo da ga London. Sannu da zuwa ma ta waya yay mata duk da yaje Taura house ɗin har sau biyu a sirrance. Dan na farko ko Anne ma batasan yaje ɗin ba. 


        ★★


  Bayan wucewar su Anne Raudha da tai musu rakkiya ta dawo, bata sameshi a falon ba, dan haka ta haura sama itama, a ranta tana ganin ya kamata shima ta haɗa masa wani abun tunda taga baici komai a abinda aka ajiyema su Anne ba. Tsaye ta samesa a falon saman yana amsa waya, ɗan dakatawa tai ya kammala sannan. Kanta a ƙasa dan har yanzu matsananciyar kunyarsa ce ke dawainiya da ita. 

       “Naga bakaci komai ba, ko kana bukatar wani abu?”.

        Mikewa yay batare da yace komai ba. Dan hankalinsa ma gaba ɗaya yana kan waya da alama akwai abinda yake nema. Sai da ya ɗanyi nisa da ita yace, “Biyoni da shi ciki”.

     Ƙirjin Raudha ya harba ganin ya nufi hanyar bedroom ɗinsa, dan tunda randa ta kai masa kuɗin nan bata tunanin ta sake ko kallon sashen, balle tai sha'awar shiga ɗakinsa wataran. Cikin dauriya da bin umarni ta amsa da “To” tana mikewa ta wuce downstairs ɗin dan sama masa abinda zaici ɗin. Samun kuku da tai tare da mama ladi ya bata ƙwarin gwiwar haɗo abinda ya dafa na lunch wanda tasan zai masa daɗin ci matsayin mara lafiya, tasan dai mama ladi bazatayi sakacin da za'a cutar da shi ba a gabanta.

       Ɗauke da basket ɗin data shiryo abincin ta shigo falon, kai tsaye tabi bayansa duk da zuciyarta na lugude har yanzun. Sai da tai knocking sau biyu ta ɗan dakata duk da bataji motsi ba. Lokacin da'aka murza handle ɗin ƙofar sai da ta rumtse ido hanjin cikinta na juyawa. Ta ɗan zabura baya tare da daburcewa ganin da ga shi sai towel alamar wanka ya fito ma. Komai baice mata ba ya saki ƙofar ya juya ciki. Sam kasa shiga tayi, ta cigaba da tsaiwa a wajen har sai da yay magana. 

     “Akwai dodo ne a ɗakin?”.

   Da ɗan rawar baki ta ce, “Am sorry”.

Bai sake tankawa ba hakan yasa cikin sanɗa kamar wata ɓarauniya ta shigo kanta a ƙasa. Wani irin mayatattun ƙamshin turare kashi-kashi suka fara rige-rigen afka mata cikin hanci. Ta ware manyan idanunta laɓɓanta dake motsawa a hankali na ambaton kalmar “Masha ALLAH”. Dan kuwa duk haɗuwa da tsaruwar ɗakinta da take gani sai ta gansa ba komai ba akan wannan, dan ma ta kasa kallon ko'ina yanda ya kamata. Amma duk da haka ɗaki ne kam da zaman lissafin tsarinsa ma ɓata lokacine. Abinda kawai za'a iya faɗa shine ALLAH ka gafarta mana ka azurtamu da aljanna maɗaukakiya.

       Da ƙyar Raudha ta iya ɗaga ƙafa ta ƙarasa ga wasu haɗaɗɗun royal chairs farare tas da adon pitch kaɗan-kaɗan ta ajiye basket ɗin saman centre table dake tsakkiyarsu. Ga wani lumbutsetsen Turkish carpet da laushinsa ba'a magana.  

      Ramadhan dake tsaye gaban mirror yana gyara jikinsa duk yana kallonta, a duk lokacin daya ganta a yanayin kunya irin wannan sai zuciyarsa tai ta kaikawo akan tambarin karuwanci da akace ahalinta na da shi. Yana son mace wayayya kuma mai shekarun dake gab da nashi, dan haka yake kallon mace mai ƙarancin shekaru ba'a tsarinsa ba, sai dai akan Raudha zuciyarsa ta fara kokwanto da saƙa masa kalmar wauta a ra'ayin nasa, duk da kuwa shi bazai iya cewa komai game da wani abu akan Raudha na so ko makamancin hakan ba.

        Ya ɗan yatsine fuska da ɗaukar t-shirt fara ƙal da ya ajiye ya saka a jikinsa, sai wando three quarter da baima gama kaimasa gwiwa ba shima ya saka cike da rashin damuwar Raudha na ɗakin. Kodan yaga ta juya masa baya ne oho masa.


        Sayun takowarsa wajen ya saka Raudha dake bin ɗakin da kallo har yanzu ɗauke idonta ta sake nutsuwa. Ya kai zaune a kujerar dake facing wadda take zaune, yanda baiyi magana ba itama batai ba, sai sakkowa da tai ɗan gabansa ta fara cire kwanikan da ga basket ɗin. Bayan ta bubbuɗe ta nema zaɓinsa akan abinda zai ci.

    “Duk wanda yay miki saka”. 

Ya bata amsa a taƙaice hankalinsa nakan canja tasha a television. Ƙundunbala tai ta zuba masa wanda yay mata ɗin, bayan ta kammala ta koma ta zauna inda ta taso saboda tunawa da dokarsa ta ranar. Sai da ya shanye kusan 2minutes sannan ya ajiye remote ɗin ya ɗauka spoon yana mai ƙurama abincin ido kamar mai son gano muninsa ko daɗinsa.

      Ramadhan mutum ne mai tarin nutsuwa akan komai. Girman kai da yawan mutane ke kallonsa da shi yasa komansa zaka iya masa kallon yanayinsa da isa ne irin ta waɗanda suka isa. Cin abincin yake tamkar bayaso, duk da ma yafi maida hankalisa ga nama. Sai da yay nisa da cin abincin harma ya kusan gamawa da naman ciki (wayaga kure🤣), sannan ya ɗan ɗago ya dubi Raudha da hankalinta ke akan tv. 

      “Bismillah”. 

   Ya faɗa a daƙile kamar an masa tilas.

      Juyowa Raudha ta ɗanyi ta kallesa, dan batai tunanin da ita yake ba. Da ido ya mata nuni da abincin, hakan ya sata itama kallonta ya sauka akan kwanon naman. Batare da tasan tayi ba ta ɗan tura baki gaba alamar sai da ka cinye naman. 

     “An gaya miki duk mutuncin da nake da mutum ina masa ƙyautar nama ne”.

       Raudha tai saurin janye idanunta jin ya mata fassara daban, ga dariya data taho mata a bazata tanata ƙoƙarin kare bakinta da hannu, domin son kore tunaninsa tai sauri cewa, “Ni ama ƙoshe nake, nagode”.

       Kafaɗa ya ɗan ɗaga da taɓe baki irin na I don't care. Daga haka ya ɗan ƙara abincin ya ture yana goge bakinsa da tissue da ambaton Alhmdllhi.

    Bayan Raudha ta gama tattare kwanikan da nufin kama gabanta ya dakatar da ita. 

     “Ɗauka min abu a cikin bedside drawer ɗin can.”

    Babu musu tabi umarninsa. Bedside ɗin da taga ya kalla ta nufa. Ta buɗe drawer ɗin wajen, takardu kawai ta gani, dan haka ta kwasosu ta dawo. Koda ya amsa sai ya buɗe file ɗin da suke ciki ya zaro guda ɗaya ya turota gabanta akan centre table ɗin. Ɗan dakatawa tai da ga kwashe kwanikan da take, ta kalli takardan sannan ta ɗan ɗago ta dubesa dan neman ƙarin bayani. Hankalinsa akan sauran takardun yake. Ƙundunbala tai ta ɗauka ta duba, jikinta ne kawai ya kama rawa, ta ɗago ta kallesa, ta sake maidawa ta kalli takardar. Tayi haka yafi sau biyar, dan ta rasa abin faɗa. Ruɗani ta shiga ko farin ciki ne yay mata yawa?, abinda ta daɗe da fidda ran samu, abinda zuciyarta ta daɗe da jaddada mata yay mata nisa... Cikin wani irin slow ta zamo a kujerar ta durƙushe gabansa hawaye na sakkowa saman kumatunta a hankali. Tabbas da ace bashi ɗin bane yau a gabanta babu abinda zai hanata daka tsalle ta rungumesa...

          Ƙafafunsa dake harɗe ya ɗan motsa yana mai zuba mata mayatattun idanunsa. Farin cikin data tsinta kanta a ciki ya hana tasirantuwar kallon nasa gareta.

       _“Ina roƙon ALLAH ya azurta zuciyarka da tarin farin ciki fiye da wanda ka sakani a yanzu. ALLAH ya baka ikon sauke nauyin al'umma dake kanka, ya kareka da duk wani abin ƙi na zahiri dana ɓoye. ALLAH ya ɗauraka a saman maƙiyanka kai da zuri'arka baki ɗaya. ALLAH ya cika maka burikanka na alkairi ya ƙyautata maka da sakamakon aljannah a ranar da ita kaɗaice abar kishirwa ga kowanne irin rai”._

      Tunda yake, tunda yazo duniya, ko yace tunda ya mallaki hankalin kansa a rayuwa, wani mahaluki bai taɓa masa makamanciyar addu'ar nan ba. Saboda shi mutum ne da idan yay alkairi baya taɓa zama a wajen dan jiran a gode masa ko a yabesa. Baya son yawan yabo a gaban ido, yayi imani da yana iya sakama mutum fara aikin riya, dan yabo na saka shauƙi a zuciyar wanda akaimawa da tunzurawar shaiɗan a wani lokacin. Ya lumshe idanunsa a hankali na kusan mintuna biyu. Sai kuma ya buɗesu a kanta. Komai baice ba sai nuni da yay mata da hannu alamar ta koma saman kujera. Batai musu ba ta miƙe ta koma, kwalin tissue dake a centre table ɗin yasa ɗan yatsa ya turashi gabanta.

        Anan ɗin ma bata musaba ta zara ta goge fuskarta tas tana haɗiyar zuciya. Tsahon wasu mintuna ɗakin ya ɗauka shiru, sai jan numfashinta kaɗan-kaɗan irin na wanda yay kuka. Tsam ya miƙe daga inda yake zaune, hakan yasa Raudha sake maida kanta ƙasa saboda kunyar wandon jikinsa. Duk da ya fahimci hakan sai bai maida kai ba, ya taka a hankali ta bayan kujerar da take zaune, kamar zai wuce sai kuma ya tsaya a dai-dai saitinta. 

         A bazata, cikin rashin tsammani Raudha taji saukar numfashinsa ta gefen fuskarta, alamar ranƙwafowa yay ta bayan kujerar. Sosai ta daburce, jikinta ya fara tsuma dan tun asali ta riga ta sakama ranta tsoron kusanta kanta da wani namiji saboda kare kanta daga faɗawa tarkon lalacewa, ta wani gefen kuma mamakinsa na sake dilmiyata a ruɗani, dan abubuwan da yake matan basu tai tsammani ba, basu ta hanga cikin idanunsa kafin aurensu ba, bata tunanin shima ɗin su yay mata tanadi, to miya canja shi? Kodai yana zargin akwai masu son amfani da ita domin cutar da shi? Kodai?.. Kodai?... Harma ta rasa lissafin da zatayi saboda tasirin da saukar numfashinsa ke mata a dokin wuya yana tada mata tsigar jiki da yamutsa jinin jikinta.

         Ramadhan da ke lure da yanayin nata, ya basar abinsa, dan kuwa da gaske tunanin Raudha na kamanceceniya da wani ƙulli dake a ransa tun farko. Koya faɗa ko karya faɗa tabbas zuciyarsa bata yarda da ita ba kafin yau, shiyyasa yake binta matakin da ya tsara domin tabbatarwa (Humm da alama wajen gwaji za'a gwaje shugaba ƙasa😉lol). 

      Cikin magana kamar raɗa yace, “Miye tukuyci na?”.

       Hannayenta ta matse cikin juna, dan yanda yay maganar cikin kunnenta tsigar jikinta ba ƙaramin yamutsawa tai ba, ga yawu kaɗan ya rage ya sarƙe mata numfashi. Taso jan jikinta gefe sai dai ya hana hakan ta hanyar zagayowa gefen damarta, kasancewar har yanzu a ranƙwafen yake sai yay mata runfar da ko numfashi ta kasa saki da ƙarfi. Gara ɗazun kujera ta musu katanga, yanzu ko hanunsa ma ɗaya idan tace jikin kujerar zata manne a kansa zata kwanta, ta gaba kuma ya tare ko ina. Sai kawai taji ƙwalla sun sake ciko mata ido. Maganar take sonyi amma ta kasa, sai laɓɓanta ke ɗan motsawa kaɗan-kaɗan.........✍


No comments

Powered by Blogger.