Bakar Inuwa 18

 


*_Episode 18_*



............Tun bayan wucewar su Alhaji Hameed Taura Aunty Hannah keta faman kai kawo a ɗakinta da kiran number First lady. Sai dai kuma tayi kira yakai biyar amma ba'a ɗagaba. Ta sake duban agogo ƙarfe goma da mintuna ashirin da huɗu. Tasan yanzu first

lady batai barci ba, da wahala kuma ace tana tare da president, sai dai idan wayar ta bari a wani waje. Wannan tunanin ya sata canza akalar kiran ta tura mata guntun saƙo, da ga haka ta ajiye wayar ta faɗa wanka zuciyarta fal wasiwasin ta yanda zata ɓulloma Raudha da Asabe su amince da auren nan cikin sauƙi.


       


*_WASHE GARI_* first lady ce ta tada Aunty Hannah a barci, dan ko sallar asuba bata tashi tayi ba har kusan 7am. Da ƙyar ta lalubo wayar takai kunnenta tana faɗin, “Hello waye?”.

      Amsar da first lady ta bata ya sata wartsakewa babu shiri ta tashi zaune. “Ranki ya daɗe sorry barka da safiya! Wlhy barcine a idona”.

          Kanta ta jinjina saboda amsar da first ladyn ta bata tana faɗin, “Okay to babu damuwa gani nan zuwa yanzun nan insha ALLAH”.


       ★


   Su Asabe na a falo suna karyawa aunty Hannah ta fito cikin gayu na ɗaukar hankali. Fatisa da Fatima dake sanye da Uniform ɗin wajen abincin Hajiyar Birni suka fara gaisheta da yaba ƙyan nata. Tai murmushi tare da musu alamar love da yatsunta. Kafin ta ɗauka doya guda a cikin plate ɗin Asabe. “Ƴar uwa barka da safiya”.

       Duk da Asabe tayi mamakin gaisuwar saita share ta amsa mata. “Barka dai Adda fita zakiyi ne?”.

         “Eh wlhy zan ɗanje wajen aiki ana nemana ne”.

     “Aiko da zakibi ta wajen asibiti ne dana biki sai na sauka dan inason yin magana da Raudha game da zancen nan na jiya karma suje su yaudareta abun yay nisa gara na sani”.

        Hajiya mama dake fitowa daga kicin a masife tace, “O ke Asabe wai mike damun kanki ne dan ALLAH? Ƙiri-ƙiri kina neman mana baƙin ciki da arziƙin dake tinkaromu!. Alhaji Hameed Harith Taura fa akace. kinsan wanene Taura kuwa a ƙasar nan dama Africa gaba ɗaya?”.

       Kafin Asabe tace wani abu aunty Hannah tai murmushi da amshe zancen tana ƙyaftama Hajiya mama babbar yayar tasu ido. “A'a Hajiya Mama karkiga laifin Asabe. Tana da gaskiya wlhy, ya kamata muji ta bakin Raudha mu kuma binciki halin yaron, dan aure ba abin wasa bane. Tunda ba kuɗin zata aura ba mai kuɗin zata aura”.

              “Yauwa Adda dan ALLAH ki fahimtar dasu. Dan naga su dukiyar waɗan nan mutanen kawai suke kallo har shi uban nata da dama kwaɗayayye ne. Yanzu idan ta auresa bata son sa, ko taje tana shan wahala fa? Ai kunga mun tauye mata rayuwa”.

         Hajiya Mama ta danne ɓacin ran maganar Asabe da ƙyar tana ƙaƙaro murmushi. “Hakane kuma Asabe yanzu na fahimceku. Ki bar Hannah kawai ta wuce maje wajen Raudha ɗin tare tunda dama jiya banje ba”.

    Badan Asabe taso hakan ba ta amince. Aunty Hannah tai musu sallama ta fice kusan tare da su Fatisa da zasu hau keke napep dan hajiyar Birni tuni ta jima da wucewa ita.




*_GOVERNMENT HOUSE_*


            Tun tattaunawar da sukai da aunty Hannah ɗazun da safe ta kasa zaune ta kasa tsaye, dakon shigowar shugaban ƙasa kawai take gidan, amma har zuwa yanzu ƙarfe goma sha biyu na dare babu shi babu labarinsa. Duk da dai tun kusan tara na daren ya shigo gida, sai dai sun shiga meeting ne shi da su Alhaji Yaro glass, kuma har yanzu basu fitoba. Tai ɗan gajeren tsaki tana tura hular kanta baya ta faɗa saman kujerar, duk da sanyin ac dake gauraye da falon wata irin zufa takeji mai mannewa iya fata da jini. Ta zame rigar sama ta kayan barcinta dan itama nauyi take mata saboda tsabar ƙaguwa. Rashin mafita ya sata zamewa ta kwanta a kujerar, dan ta ɗau alwashin ko zai kai asuba tana nan tana jiransa. 

       “Gimbiyata kina lafiya kuwa?”.

Shugaban ƙasa da ya shigo a matuƙar gajiye ya faɗa lokacin da yake zubewa saman kujerar gefenta. Zumbur ta miƙe zane tana ware idanunta a kansa, sam bataji motsinsaba, duk da dama tasan shi bai damu da sallama ba dan zai shiga waje. 

       “Lafiyar nan da sauƙi wlhy tun ɗazun zaman jiranka nakeyi anan excellency ”.

      Fuska ya sake ƙwaɓewa yana ture hularsa. Cikin tabbatar da matuƙar gajiyar dake tare da shi da barci yace, “Bushira kiyi haƙuri babu abinda nake buƙata a yanzu irin barci da wanka”.

         “Shiruna bazai yuwu ba, inko nayi to zai iya cutar damu baki ɗaya. Dan maganar ta shafi shugaban ƙasar da kuke son ɗorawa na wucin gadi” Bata bashi damar yin magana ba ta cigaba da tata maganar saboda ganin ya bada hankalinsa gareta. “Tunda ka sanarmin ƙudirinku akan Alhaji Hameed da jikansa daya kawo a maimakonsa naketa nawa ƙoƙarin nima. Dukanmu munsan Ramadhan a yanzu baida mata, tunda kune kukai sanadin rasa matar tasa, shiyyasa nake ganin a yanzu ma inhar kuna buƙatar mutuwarsa kamar yanda kuka tsara (wa'iyazubillah 🤦🏻) to dolene sai mun haɗa da matarsa, dan itace mafi kusanci da shi da zatai mana aiki batare da wani zargi ya shiga ba. Kaga kenan mune ya dace mu bashi mata a karo na biyu”.

        “To amma.....”

“Karka katseni excellency ”. Ta faɗa tana murmushi.

      “Nasan tambayarka itace bai wuce ina zamu samu ba? To na gama da wannan matsalar, yarinyar data bama Alhaji Hameed kariya a filin idi ɗiya ce ga ƙanwar Hannah tsohuwar matar Alhaji Yaro, kuma a yanzu haka Alhaji Hameed ya buƙaci su bama Ramadhan auren yarinyar, sai dai mahaifiyarta na neman bijirewa dan tace sai idan yarinyar naso. Amma babanta ya yarda saboda shegen ƙwaɗayi, hakama hajiyar birni da su su Hannah ɗin, duk da dai ita Hannah muna tare, dan itace ma ta tabbatar min inhar Asabe ta nunama yarinyar bataso itama bazata amince ba saboda tanada kafiya da son uwar sosai......”

       “Bushira sorry na katseki, ni abinda ban fahimtaba anan, ribarmi zamuci na shiga maganar tunda sun gama ƙulla zancen auren? Inhar kuma yarinyar zata iya bijirema auren muma zata iya ƙin amsar buƙatarmu ai. Sannan karki manta Hannah zata iya yin komai danta rama korar kare da Alhaji Yaro yay mata. Imagine ma ace kina tare da Hannah har yanzu batare dana sani ba”.  

       “Duk yanda kuke tunanin Hannah ba haka take ba, tana son Alhaji yaro har yanzu, kuma ta san ba laifinsa bane laifin Fanta ne. Amfanin auren yarinyar nan a garemu Hannah zata iya sakata tai mana aikinmu cikin siyasa batare da ita kanta tasan ita ta kashesa ba, kai koda ta sani ko muna tunanin zata sani itama zamu iya kashetan dan mulkin dai ya koma hannun Alhaji Yaro. Kasan kuma inhar zaka taimaka Hannah ta koma gidan Alhaji yaro zata aikata komai har mutuwar yarinyar, dan da arziƙi a garin wasu gara a naku, a garin wasunma gara a gidanku, a gidankun ma gara a ɗakinku, a ɗakinkun ma gara a kanka. So zataima kanta yaƙine itama”.

         Karon farko ya kwashe da dariya yana kamo hannunta. “Oh woow gimbiyata! yanzu dai na fahimci komai wlhy. Gaskiya kinada kai tawan. To amma mu yanzu wace rawa zamu taka?”.

       “Yauwa yanzu kai magana shugaban ƙasar NAYA. Abinda zakuyi shine ku samu mahaifin yarinyar ku jikesa da mahaukatan kuɗaɗe. A bashi gidan zama, itama uwar a jiƙeta tare da mahaifiyar su Hannah ɗin, dama duk wanda keda faɗa aji akan auren. Sannan ku samu Alhaji Hameed ku nuna masa goyon bayanku akan auren da nuna cewar yayi hallaci ya cancanci yabo, kar kuma ya yarda yarinyar ta suɓuce ga Ramadhan dan irinsu akeso ga mulki zasu taimaki talaka. So ko yarinyar ta bijire bataso bazata taɓa samun haɗin kan kowaba ita da uwar dole su amince”.

      Tashi yay kawai ya rungumeta, ji yake tamkar ya haɗiyeta dan daɗin wannan shawara tata. Tun a daren ya turama su Alhaji Yaro glass saƙo da ɓoyayyar number ɗinsa da su kaɗai keda a laƙa da ita akan gobe akwai mitin ƙarfe 6 na safe kafin ya fita office.


*_BAYAN KWANAKI UKU_*


          Dukan shawarar da First lady ta bada su Alhaji yaro glass sun aiwatar da ita ta hanyar nuna cewa sunyine dan Alhaji Hameed Taura da kuma Ramadhan dake matsayin surukinsu a da, dama zamansa haka babu aure na damunsu. Hundred percent Alhaji Hameed Taura ya yarda.

      M. Dauda kam da su Hajiyar birni haukacewa sukai dan farin ciki, dan manyan kuɗaɗe da aka mallaka musu. M. Dauda, hajiyar birni. Asabe, Hajiya mama. M. Gambo. Kuɗaɗene da zasuja jari. Koda Asabe ta nuna hakan bai mataba hajiyar birni masifa ta dinga mata, harda rantsuwar inhar bata yarda Raudha ta auri Ramadhan ba wlhy sai ta tsine mata, kuma sai dai ta ɗau Raudha subar garin dan bazata zauna inuwa guda da mai mata baƙin ciki ba.

     Kalaman hajiyar birni yay matuƙar tada hankalin Raudha da aka sallamo daga asibiti yau, dan Alhmdllhi ƙafarta tayi sauƙi sosai saboda kula da take samu da ingantattun magunguna gashi bata da ƙan jiki. Bazataso a sanadinta a tsinema mahaifiyartaba. Sannan idan sun bar nan ina zasuje, tunda babu wanda ke garesu sama da su a yanzun. Dan haka tace ita ta amince zata auresa duk da batajin son Ramadhan a ranta ko kaɗan, sai dai a gani guda datai masa har zuwa yanzu tanajin kwarjininsa cike da idanunta, yayinda kalamansa ke zaune daram cikin ranta shiyyasa takejin matuƙar tsoro. Amincewa aurensa na nufin tabbatuwar kalamansa gareta, sai dai kuɗi ya rufe idanun iyayenta sun kasa fahimtar ni'imar da suke ganin suna ciki *_BAƘAR INUWA..._* ce, gara ranar da suke ciki da ita. Zata amince domin gujema hawan tsinuwa akan mahaifiyarta, zata kuma amince dansu samu farin ciki koda ita zata rasa nata farin cikin. Dan duk wanda ya dubeta ya dubi Ramadhan ya tabbatar shi ba tsaran aurenta bane ba, kawai dai kakansa ya kalli abinda tai masane da tunanin zai mata tukuyci da auren alhalin bazai zame mata irin inuwar da shi yake hango mata ta jin daɗi ba.   


       A lokacin da waccan cakwakiya ke gudana a gidan su Raudha anan fadar shugaban ƙasa shugaban jam'iyya ne ya fitar da sunan ɗan takara a yau a zaman taron da akayi yau ɗin na manyan jam'iyyar. Inda kamar dai yanda aka saba wasu suka nuna jayayya akan Ramadhan ɗin kodan ƙarancin shekarunsa, tare da kawo hujjar bai san siyasa ba, bakuma zai iya ba tunda bama zaman ƙasar yake ba, bai san komai na wahalar talaka ba.

        Idanu Ramadhan ya rumtse da ƙarfi saboda wani irin sarawa da kansa yake masa a dalilin hayaniyar da ɗakin taron ya kaure da shi. Dama da ƙyar Bappi ya sakashi zuwa wajen taron har sai da ya nuna ɓacin ransa shi da Anne da Pa. Koda ya shigo yaga mutanen dake wajen daga sa'an Pa sai sa'annin Bappi baiji ko ɗar ba, a lokacinne ma yaji kibiyar son yin mulkin ta soki ƙirjinsa. Dan yana ganin yakamata sumafa matasa ace anayi dasu a ƙasar NAYA dan sune ƙasar. 

     A yanzu kuma boren nasu ya sake harzuƙa zuciyarsa dajin eh lallai zai amince ya amshi mulkin ƙasar NAYA inhar ALLAH ya saka hakan a cikin ƙaddarar rayuwarsa. Da ƙyar shugaban jam'iyya ya tsawatar akai shiru, kafin ya yanke hukunci akan gobe za'ai primary election duk da a ransa yasan dolene candidate nasu ya tsallake. Duk sun amince da hakan, daga haka kuma taron ya watse wasu ransu ɓace wasu ransu fal murna, sai dai masu murnar zukatansu sun rabu gida biyu akan dalilin murnar. 


    Wani meeting ɗin su Alhaji yaro glass suka sake shiga iyakarsu kaɗai akan batun, kafin kuma da yamma shugaban ƙasa da shugaban jam'iyya su sakeyin wani zaman da wasu jiga-jigan jam'iyyar. 



*_JIHAR DILLO. HUTAWA L.G.A_*


         Koya ya shiga matuƙar mamakin yanda M. Dauda ya dawo garin hutawa a jiƙe da kuɗaɗe shi da abokinsa, dan maimakon su rufe sirrinsu sai sukazo sunama jama'a fankama da kuɗi da nuna sumafa sun kai yanzun. bama shi ba abokinsa M. Gambo ma dai ajiƙen ya dawo. Nan take aka fara ƙananun magana da dangantasu da ɓarayi saboda hankalin jama'a ya tashi musamman da suka san dai ba ko sisi su M. Dauda ke magani ba, dan inhar ba sata ba ko wannan kidnapping da akeyi ba babu ta yanda za'ai daga barinsu gari na kwana uku su dawo haka. Aiko nan take manyan anguwa suka haɗa kai suka kai ƙararsu gidan hakimi, hakimi baiyi ƙasa a gwiwa ba ya aika a ka kira masa su M. Dauda daya saka innarsa da iyalansa haɗa ƴan kayansu dan so yake a gobe ya fara gyaran gidansa. A gefe kuma yana tunanin sake sabon aure da lallaso Asabe ta dawo (bayan saki uku ne tsakaninsu🙄).

          Hakimi da ƴan fadarsa babu kalar binciken su M. Dauda da basuyiba amma sun dage akan sufa basu kuɗin nan akayi. Ganin kamar suna son rainama fada hankaline saboda ambatar sunan manyan mutane da sukayi yasa hakimi saka ƴan sanda suje da su. Haka kuwa akayi, a ranar a police station suka kwana, washe gari hakimi kuma ya kai magana fadar mai-martaba sarkin Dillo. Bako a ɓata lokaciba wajen yayubar su M. Dauda sai cikin birnin Dillo fadar sarki.

        Nan ɗin ma dai amsar da suka bama hakimi ita suka bama sarki akan inda suka samo kuɗi, sai dai shima bai gamsu ba saboda sunayen da su M. Dauda ɗin suka ambata na manyan mutane. Sai ma hankalinsane daya sake tashi dan gani yake kamar su M. Dauda nason yin amfani da sunan manyan ne dan ɓata musu suna. Baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen fara neman waɗanda yakeda kusanci da su ciki harda Alhaji Hameed Taura da tarihi ya nuna karatu ya taɓa haɗasu a jami'a.

         Da ƙyar ya samu damar magana da shi a ranar ta hanyar P.A ɗinsa, bayan sun gaisa cikin mutunta juna matsayinsu na manya da ƴar tsokana ta tsoffin abokai mai-martaba yayma Bappi bayani game da su M. Dauda. Da farko sam Alhaji Hameed Taura bai gane ba saboda baiyi tunanin su M. Dauda sun koma ba, kuma shi har yanzu ma bai basu ko sisi ba su shugaban ƙasa ne sukai musu ƙyauta. Sai da aka haɗashi da M. Dauda, yana ko jin muryarsa ya gane, amma duk da haka sai yasa aka tura masa hotunansu ta email.

      Yana gani kuwa ya gane, dan haka yayma mai-martaba bayanin da zai iya fahimta. Jin alaƙar dake shirin faruwa tsakanin su dan babu wanda baisan abinda yaso faruwa da Alhaji Hameed ɗin ba ran salla sai shima mai-martaba ya shiga mamaki, harma yake cema Alhaji Hameed anya kuwa baya ganin tun farko dama akwai dalilin daya saka yarinyar masa garkuwa.

     Alhaji Hameed Harith Taura mutum ne mai sauƙin kai da tsarkake abu koda ace yazo a yanayin daya kamata a zargesa, hakan yasa shekaru aru-aru su Alhaji Yaro glass keta cutarsa yana ƙyautata musu zato dan bai taɓa damuwar zama ya zargesu ba. Cikin nutsuwa ya fahimtar da mai-martaba shi dai zaiyi ne bisa ƙyaƙyƙyawar niyya, kuma baijin yarinyar zata aikata haka dan yarinyace ƙarama kuma nutsatstsiya. 

     Cikin ƙanƙanin lokaci mai-martaba ya yarda dan shima mutum ne mai fahimta, harko yay alƙawarin za'a dama dashi a harkar bikin shine ma uba ga Raudha tunda dai a ƙarƙashin mulkin jiharsa take. Alhaji Hameed yayi matuƙar farin ciki yayi kuma godiya.


     Wannan shine ya wanke su M. Dauda wajen hakimi da sarki, sai dai ga jama'ar gari sun ƙara gaba wajen ƙananun magana musamman da akaita dawo da zancen abinda Raudha tayi da kuma dalilin rabuwar Asabe da M. Dauda ɗin da ba'a wani jima ba. Kafin kace kwabo zance yaje bakin ƴan jarida da yanar gizo harya fara yawo...........✍


No comments

Powered by Blogger.