Bakar Inuwa 12


 *_Episode 12_*

..........Duk yanda ƴan jarida suka so ɗaukar wani rahoto bayan wanda aka gani a filin idi hakan ya gagara. Dan an toshe ko'ina da zai basu damar ma sake ganin Raudha ɗin. Koda Alhaji Hameed da shugaban ƙasa kuma suka fito anso jin ta bakinsa akan wannan al'amari amma ya nuna bazaice komaiba a halin

yanzu. Dole suka barsa ya shige dan kowa yasan shiɗin kaifi ɗaya ne. Idan yace e to lallai e ɗin ce. Idan kuma ya ce a'a baya canja ra'ayi daga a'a ɗin tasa..


             Sosai sallar tazo a wani yanayi ga wasu mutane ta ɓangarori huɗu. 

    Na farko gidan Taura. Dan duk yanda suke baje kolin farin ciki da gagarumin biki a shagalin kowace bikin salla wannan karon sai armashin nata yay ƙaranci saboda jimami na abinda ya kusa faruwa. 

    Ɓangare na biyu gidan su Raudha musamman Asabe da ƴan uwanta su Fatisa. Duk da suma dai su Hajiyar birni hankulansu ya tashi, sai dai wani sashe na zuciyarsu abin ya musu daɗin. Dan koba komai suna kallon abinda Raudha ɗin ta aikata tamkar wani silar samun arziƙinsu ne a wannan gaɓar. Daga hajiya mama har Hajiyar birni sai wani nannan suke da Asabe da ƴaƴanta a wannan yini. Ana kuma lallashinta akan ta kwantar da hankalinta ta cire damuwa Raudha na samun dukan kulawa.

    Ɓangare na uku shine su Mr. JK da rashin nasara ya jefa rayuwukansu cikin ɓacin rai da taraddadi na ƙaulani. Sai faman tsugunne-tsugunne sukeyi na sabon shiri duk da kuwa bayan azhar suna cikin tawaga ta farko data isa gidan Taura domin kai jaje kamar yanda manyan ƙasar da ƴan siyasa keta faman yi. Wasu kuma ta waya suke kira suna jajantawa sakamakon ba cikin Bingo suke ba.

       Na ƙarshe shine gidan gwamnati da al'amarin nasu ya rabu biyu. Kason farko shugaban ƙasa da abokansa su Alhaji Yaro glass. Kaso na biyu first lady da aunty Hannah da komai ya basu mamaki. Sun riga sun gama tsara yanda haɗuwar Raudha da Alhaji Hameed Taura zata kasance sai gashi ALLAH ya sauƙaƙa musu ta inda basuyi zato ko tsammani ba. Duk da abun ya ɗan ruɗasu sun shiga matsanancin farin ciki dan gani suke komai zaizo da sauƙi. First lady zata ƙarasa sauran aikin na ɗora shugaban ƙasa akan hanyar da zai fargar da Alhaji Hameed haɗa alaƙar auren Raudha da Ramadhan....


(Tofa masu karatu. Yaya kuke ganin hakan zata farune bayan shi uban gayyar da aketa wannan tsugunne-tsugunne dominsa ma yana can wata ƙasa hankalinsa kwance batare da ya sani ba? Kumuje zuwa dai muga yanda zata kasance🏃.)




*_AMERICA (NEW-YORK CITY)_*


            Duk wani cikakken musulmi wannan ranace da bata ɓoyuwa a garesa a duk inda yake a faɗin duniya. Sai dai ƙarancin yawan mabiya addinin musulinci a wajen ya rage masa armashi da jin daɗin wannan ranar. Amma dolene zuciyarsa ta kasance cikin shauƙi da godiya ga UBANGIJI daya sake zagayo masa da ranar.

         

*Broadway street* anguwace dake a cikin birinin new york dake ƙasar amuruka. Layine mai tarin abubuwan birgewa da ƙayatarwa kamar yanda mai karatu yasan turawa da gyara muhalli. A katafaren block dake ɗaya daga cikin gine-gine na musamman a broadway street gida mai lamba goma sha tara Ƙyaƙyƙyawan farin mutum amma baƙar fata mai tarin kwarjini da cikar kamala ne zaune bisa sofa a falo. Falo ne haɗaɗɗe da bai cika yawan tarkace ba ko hargitsi.

        A kallo ɗaya zaka iya kiransa da tuzurun saurayi dan shekarunsa a ƙala zasu iya tasarma 35. Sanye yake cikin farar ɗanyar shadda data samu aiki na musamman da bazaka iya mata kallo ɗaya ita da mamallakinta ka ɗauke kai ba. Sai dai duk da tsadarta da ɗaukar idon da takeyi bai hanata yamutsewa ba saboda a yanyin dayay zaman bisa sofa. Gaba ɗaya hankalinsa kacokan ya tattara ne ga television ɗin dake a falon, inda yake kallon tashar dake da alaƙa da ƙasarsa ta NAYA. Bakomai ya sakashi nutsuwa ga tvn ba sai bikin salla da na idi da aketa nunawa na ƙasar tasa dama sauran ƙasashen duniya.

       Duk da fuskarsa bata nuna shauƙin kallon ko zumuɗi ba kwayoyin idanunsa sun gama fallasa asirin zuciyarsa baki ɗaya. Dan yanda ya tattara dukan hankalin nasa ya isa shaidar komai na ƙayatar da shi. Basai ance maka ƙyaƙyƙyawa bane, fatarsa kawai ka kalla kasan shiɗin mai ƙyaune. Dan mutane da yawa kan kira mai irin yanayinsa da suna black american duk da kuwa a ƙasarsa fari yake kai tsaye. Yana da yanayi mai sanyi a fuska tare da duk wani ado dake ƙawata fuskar gayun wannan ƙarnin. Abu mafi ɗaukar hankali dake tattare dashi gyararriyar sumar kansa da tasha wani salon aski na musamman duk da kai tsaye bazamu kirata mai taushi da laushi irin ta larabawa ko turawa ba. Dan kuwa a tsaitsaye take cunkus kamar yanda akasan sumar baƙin mutum, sai dai ɗunbin gyara da kuɗaɗen da take lashewa yasa tazam mai ɗaukar hankali da birgewa ga mai kallo. Sai girarsa ta haggu da akai mata wani salon tsagu da kan iya saka mara fahimta ɗaukar gayune yasa shi tsagawa, sai dai sam ba haka bane  tabon raunine a wajen da ya samesa tun yana primary. Sai ga tabon har girmansa bai dishe ba. Batun yanzu ba mutane da yawa sunsha ɗauka an kwashe gashin wajen ne tamkar tsagar kitso kawai dan gayu. Kowa yasan abune mai sauƙi yanzun kaga lips ɗin gayu pink kodan abubuwan da ake tu'ammali dasu domin yin hakan.

       Baza'a kirashi siriri ba, ba kuma za'a ce dashi mai ƙiba ba. Kawai dai mutum ne tsaka tsaki musamman daya kasance yana tu'ammali da inginan motsa jiki.

        Karon farko ya sake waro manyan idanunsa da ada suke a ɗan lumshe bisa television ɗin sakamakon abinda ya gani. Cikin sassanyar muryarsa mai ɗan kauri da buɗewa ya furta “What?!!” yana zabura gaba ɗayansa tsaye bisa ƙafafunsa. Dan ba ƙaramin harbawa ƙirjinsa da ƙwaƙwalwar kansa sukaiba a lokaci guda saboda tozali da abinda ya faru ga kakansa a filin idi.

      *_Ramadhan B. Hameed Taura_*. Ya matsa gaban television ɗin da sassarfa dan ji yake tamkar idanunsa basa gane masa komai daƙyau. Tabbas babu tantama hakanne, dan kuwa ganin mahaifinsa da ya iso wajen a kiɗime da sauran ƴan uwansa mata ya sake tabbatar masa da komai gaskiyane. Da sauri ya koma gaban sofa ɗin da yake zaune a da ya sungumi ɗaya daga cikin wayoyinsa uku dake a saman table. Cikin ƙwarewa ya far sarrafata tare da kutsawa cikin shafukansa na sada zumunta.

    Duk da ya daka barkono daga ƙasar haihuwar tasa duk da begen da ahalinsa ke masa yaƙi saurarensu hakan bai hanashi dinga bibiyar al'amuransu ba batare da sun sani ba. Dan kuwa ya ɓoye kansa daga yanda zasu iya ganosa kai tsaye, ainahin shafukansa da suka sani kuma duk yayi blocking nasu babu mai ganin abinda yakeyi sai dai da salon sabon suna da bazai gane ba.

     A babban shafin sada zumunta na watsa labaran ƙasar ya fara cin karo da ainahin bayanin abinda ya farun, harda gajeren video a shafinsu na istagram. Wani irin tsuma jikinsa da zuciyarsa keyi dan kuwa tamkar an tuna masa da wata rana data kasa shuɗewa a tarihinsa.  Ranar da tsayawar numfashinsa ce kawai shima zata iya ɓaddata a cikin jerin abubuwan da suka zauna masa raɗam a cikin ƙwaƙwalwa. Kakarsa (Anne), kakansa (Bappi), Mamansa (Gimbiya Su'adah), Babansa (Alhaji Basheer Hameed Taura) duk suna raye a duniya. Bai taɓa ɗanɗana ɗacin mutuwar wani makusanciba a duniya sai akan matarsa masoyiyarsa da ƴarsa gudan jininsa. Shiyyasa yake matuƙar jin ɗunbin raɗaɗi da zafin gusawarsu a duniyarsa ta hanyar da bazai taɓa yafema wanda ya ƙirƙiretaba duk da yasan tana cikin ƙaddararsu.

      “Bappi!!”.

Ya faɗa cikin yanayi najin ƙaimi da tasowar mazantaka. Haka kawai zuciyarsa ke raya masa wanda ya halaka masa Amnah da Haseenah ne suke farautar Bappin sa. Sai ma ƙasan ransa ke tunzurasa da koma dai an samu galabar cutar da bappin ne aka ɓoye. Karon farko da tun bayan barowarsa ƙasar NAYA shekaru biyar kenan yakejin tamkar ya rintse ido ya gansa a ciki. Duk da halittarsa ta nutsuwa da cikar kamala hakan bai hana idanunsa nuna birkicewar da ƙwaƙwalwarsa ke neman yi ba. Da sassarfa yay jifa da phone ɗin tasa bisa sofa ya nufi dogon glass ɗin da aka raba tsakanin falon da bedroom ɗin barcinsa. Kasancewar yaja labulen gefe da gefe yasa ake iya hango gadon ɗakin da ya gama haɗuwa shima.

     Da wani irin gudu ƙofar glass ɗin ta zuge kanta gida biyu saboda yanda ya danna maɓallin makunnar da ƙarfin tuwo tamkar itace tai laifin....


       Wani irin ruri ɗaya daga cikin wayoyinsa keyi na neman agaji alamar kira, sai dai duk da jinta da yakeyi baiko nuna alamar zai fito daga bedroom ɗin ba dan yasan wanene ke kiran nashi. 

      Still kira ya sake shigowa a karo na kusan biyar. Ɓaro-ɓaro sunan A.J ya bayyana a kan screen ɗin. A.J abokine ga Ramadhan wanda shima mazaunine aƙasar ta amuruka. Kamar yanda suka saba haɗa liyafar cin abinci a kowanne ranakun bikin salla babba da ƙarama wannan karon ma hakane. Maƙudan kuɗaɗe suke haɗawa su ƙayata zaman nasu da shi batare da jin hakan a jikinsu ba dan kowa ya tara.

    Mafi yawansu sunada mata da ƴaƴa. Harma da masu manyan ƴan mata da samari. Dan kuwa akwai sa'oin Alhaji Basheer a ciki harma da tsoffi da ƙaddarar zama ta zaunar a ƙasar tsahon shekaru. A irin wannan zaman ƴammata da yawa sunsha yima Ramadhan tallar kansu amma baya kulawa. Dan ko fuskar a tunkareshima baya basu balle suyi tunanin dacewa. Manyan ciki kuma kan dunga kwaɗaita masa maganar sake aure amma baya kulawa nan ma. 

       Tunda ya fara riskar bikin salla a ƙasar bai taɓa missing wannan zaman ba, dan yana matuƙar ɗebe masa kewa sosai akan ahalinsa. Hakan yasa rashin isowar tasa ta dami kowa har A.J ya fara danna masa kira a jajjere. Sai dai kuma ana tsaka da haka dattijo alhaji sufyan harɗo yaci karo da labarin abinda ya faru ga Alhaji Hameed Harith Taura a filin idi yau. Dan haka yay azamar fargar da sauran ƴan uwansa maybe labarin ya riski Ramadhan ɗinne shima.

     Dukansu sun nuna jimami, yayinda A.J da Mufeed yanke shawarar zuwa gidan na Ramadhan da suke kira da suna Top gee dansu gani. Fitowa Sakai a cikin garden ɗin Sultana biye dasu, basu hanata ba dan kowa yasan irin ɗunbin so da ƙaunar da Sultana kema Ramadhan ɗin duk da baya kulata. Cab suka tara tare da sanar masa inda zai kaisu....


      Fara danna ƙararrawar gidan yayi dai-dai ne da fitowar Ramadhan daga bedroom ɗauke da madaidaiciyar bag daya haɗa abubuwansa masu muhimmanci da zai iya buƙatar amfani dasu. Ya canja kayansa zuwa ƙananun kaya daya ɗora jibgegiyar rigar sanyi daketa maiƙo da santsi tamkar leda kalar light blue. Sai hularta mai gashi a cin bakin baƙi tamkar kayan ciki t-shirt mai gajeren hannu da black jeans wando. Ƙafarsa sanye cikin baƙaƙen takalma boot.

      Duk da ba kwalliya yay ba hakan bai hanashi yin ƙyau ba. Baibi takan doorbell ɗin da aketa bugawaba ya cigaba da karkashe komai na na'urar lantarki dake a cikin falon kamar yanda ya kaso na bedroom. 

       

          Da ga A.J har su Sultana binsa suke da kallon mamaki dai-dai sanda ya buɗe ƙofar. Bakinsa da gashin gemunsa kawai suke iya gani zuwa rabin kumatunsa, dan yaja hular rigar ne ya rufe masa rabin fuska tare da toshe idanunsa da glass mai nuna blue a jiki.

       “Mr R kana lafiya kuwa?”.

Mufeed ya faɗa yana ɗan kai hannu ya dafa kafaɗar Ramadhan ɗin dake ƙoƙarin fitowa batare da ya damu da hanin nasu ba.

       Ƙarasa fitowa yay yana zuge zip ɗin bag ɗin hannunsa mai kama da school bag da faɗin “Zan wuce NAYA? Akwai matsala”. 

      Atare suka haɗa baki wajen ambaton “Matsala kuma? Miya faru?”. Dan sunfi son suji idan da gaske ne kar suyi katoɓara. Hannunsa na haggu ya ɗora saman kansa ya zame hular tai baya ya saketa bisa dokin wuyansa yana ƙoƙarin saka lock jikin ƙofar duk da baya tunanin zai jima acan inhar ya iske komai lafiya.

         Ƙoƙarin sake maimaita tambayar tasa A.J yayi, bai tankashiba yanzu ma sai da ya kammala rufe ƙofar ya rataya hannun bag ɗinsa ɗaya a hannun haggunsa, hularsa yaja saman kansa tare da ɗan bubbuga kafaɗar A.J ɗin. “Na riga nayi Booking flight, kuma gab yake da tashi zamuyi waya”. Daga haka yay gaba a binsa.

    Hankali tashe ganin yanda yake komai cikin zafin nama yasa Sultana ƙoƙirin binsa zata kira sunansa Mufeed ya riƙo hanunta. Kansa yake girgiza mata alamar karda ta tsaidashi ta barsa. A take hawaye suka ciko mata idanunta da take bin Ramadhan dake ƙoƙarin shiga cab daya tsayar da kallo. Kamar walƙiya cikin ƙanƙanin lokaci cab ɗin ta ɓacema ganinsu abinka da lafiyayyen titi duk da dokar ƙasar akwai ƙa'idar da driver kanbi yayin tuƙi...



*_ƘASAR NAYA. (Taura house)_*


         “Ya kamata ka ajiye komai gefe kaci abinci hakanan dattijo”.

    Anne dake zaune gefen Alhaji Hameed ta faɗa cikin tausasa harshe da nuna kulawa. Ganin baida alamar tankawa ta cigaba da faɗin, “Mu godema ALLAH da ƙudirin koma wanene bai cikaba duk da wani ya cutu a dalilinmu. Haka rayuwa take cike da jarabawa. Talaka mai nema cin yanzu da anjima yana cikin jarabawa babba dake taka rawar gani wajen iya wargaza komansa. Sannan ni'imar arziƙi ga masu arziƙi a lokuta da dama ɗaukakar a garesu itace gagarumar jarabawarsu. A koda yaushe cikin ɓoye kansu suke, badan komaiba sai don gudun a cutar dasu ko makamtan hakan, dai-dai da masoyansu na gaskiya taka tsantsan suke wajen kokwanton neman tabbaci koda kuwa sunada yaƙini masoya da maƙiya zasu iya shiga a jarabawarsu. Dattijo bamu isa canja ƙaddara ba, dan haka kalmar da tafi cancanta a bakunanmu a yanzu itace *_Alhamdulillahi_*. Sai fatan ALLAH ya bama yarinyar lafiya itama”.

          Sosai kalamanta suka sanyaya masa ransa. Yaja numfashi mai nauyi da sakin guntun murmushi. Baki ya buɗe da niyar cewa wani abu maganar tasa ta maƙale a maƙoshi saboda abinda idanunsa suka hango masa a bakin ƙofar katafaren falon nasu. Saurin maida idanun nasa yay akan agogo tamkar wanda akaima shune da mummunan abu. Ƙarfe goma na dare da wasu mintuna. Tunda suka samu gidan nasu ya lafa da ƴan jaje da masu zuwa yawon salla sai kowa ya nutsu a sashensa saboda hadari da garin ya haɗa na alamun saukar ruwan farko na damuna da kowa ke fata.

     Sake maida idanun nasa yay ga ƙofar ransa fal tunanin gizon da idanun suka saba masa ne na tsananin bege da kewar jikan nasu duk da fuskarsa a rufe take da hular rigar sanyin jikinsa hakan bai hanashi ganesa ba. Hakan yasa itama Anne duban inda ya ƙurama idanun baki wagame tayi........✍




*_iyakata Hummmm!! A wannan gaɓar😜_*


No comments

Powered by Blogger.