Auren Sirri Complete Hausa Novel

   AUREN SIRRI

       💖💖💖

 💗💗


Bismillahirahmanurrahim

Aysha A bagudo

Page 1-2

Lekki  Unguwace  mai dauke da karancin mutane da suke rayuwa acikinta   ,a silent place, saboda bata cika   hayaniya mutane ba  , dauke da tarin sanyin ni'ima mai dadi  sakamakon kusancinsu da ruwan teku"

unguwace da tattara kan manya ma'aikata da kusoshin gwanati, hade da manyan masu kudi ,ga tarin  yan yahoo boy'z  domin mafi yawancisu   sunfi sha'awar  zama acikinta. rayuwar mutane  unguwar abin sha'awa  bbu ruwan wani da wani  domin suna rayuwasu ne tamkar a kasar waje   .



PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE 


Estate ne mai dauke da tarin dangi acikinta , hadin kai tattare da zaman lfy,  Sam bbu hayaniya acikin wannan family kowa kagani cikin nishadi da farinciki zaka gansa ,ga tsantsar fahimtar juna dake tsakanin wannan family. kwakkywan family ne masu matukar kaunar junansu .



Let alh Muhammed bello khaliyal ,haifafen garin Lagos ne ,Amman asalinsa fulanin khaliyal ne dake jahar kebbi. sananne  mai kudi ne yayi tashe tun alokacin da duniya ke kwance. sannan kuma take zaman lfy, marigayi Muhammed bello  soldier ne daya taka rawar Gani a kasar nan .

 ya rike mukamai da dama a wancan lokacin. ya rasu yabar tarin dukiya da da ya'ya da jikoki  bila adade.

    gabadaya family Muhammed bello bbu talaka aciki  domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsu  .


 kafin rasuwarsa    dake shine babba a dakinsu kuma Allah yabashi tarin dukiya da en'uwan , dan ganin ya inganta rayuwar kannensa kafin daga baya ya Gina wannan katanfarin estate din  mai mazan kanta.

 ya tattara  kan yan'uwasa suna zaune a ciki ,yana da mata hudu  hjy  shema'u  wacce aka musu aure tun saurayi da budurwa tana da ya'ya  goma   Sha biyu, mata takwas maza hudu  sai hjy  hauwa mai dauke da ya'ya goma maza biyar mata biyar ,sai hajiya rabi mai ya'ya takwas maza biyar mata uku   sai hajiya Fatima wacce suke kira da hjy  shuwa  itama tana   da yaya takwas mata bakwai namiji daya .

 bbu abinda bbu acikin wannan estate din kama daga makarantar islamiyya wajen wasa buga kwallo wajajen exercise wajen swimming pool library Sannan ga wani katanfarin Holl dake gefe wanda aka shiryashi da kayan kyale kyale zagaye da kujerun zama . an ginashine  saboda  taron sada zumunci , wanda zasu dinga yi a duk karshen wata  .


 haka suka taso har zuwa girmansu cike da son junansu .

 anan cikin  dangi mazan suka zabi matan suma  matan suka zaba akayi  bikinsu anan cikin estate din suka zauna  tare da iyalinsu  har zuwa  sanda tsufa yacima marigayi Muhammed bello yayi retire.

 yayinda ya'yansa da ya'yan en uwa suka cigaba da kula da estate din .

  a lokacin  aliyu  da  habib ne kadai suka rage da basuyi aure ba saboda  karatu . 


Byn rasuwar marigayi bello ne aka raba gado aliyu  ya dukufa  gurin juya dukiyarsa ,ba abinda  yasaka a gaba sai neman kudi wanda acikin kankani lokaci ya gawurta yayi fice yayi suna a duniya,  yayiwa sauran yan'uwansa zarra  aliyu ya mallaki tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. hade da tarin compenis  a Lagos da kudancin Nigeria yana da gidajen saida man petir Bila adadi shine mallakin aliyu airlines yana da hannu jari da dama a compenis na kasashen duniya yana da  gidaje a abuja da sauran garuruwa .

tsananin neman kudinsa ne yasa  bai ajiye iyali da wuri ba ,burinsa bai wuce  ya auri mace mai matukar kyau da tarin illimi ba .


Garin neman kudinsa ne ya hadu da fadila  a india tun daga lokacin da aliyu ya daura  idanunshi akanta "ya dauki son duniya ya daura mata kasancewarta kyakkywa gaske ga tarin illimi . fadila itace Diya ta biyu a gurin iyayenta su uku ne , ahmed  ne babba sai ita sai farida ,  kin amincewa iyayenta sukayi da auren shi a cewarsu bako ne sannan kuma bakin fata. sai da aka kai ruwa rana dasu sannan suka amince  da auren .

 koda yazo daita Nigeria ma bata wani sha wuyan zama cikin family dinsa ba .

kasancewarta mace mai tsananin  son jama'a da son yara cikin lokaci kadan tashaku da sulaiman da  mahamud ya'ya ne ga yayyen aliyu sun shaku matuka da yaran ta daukesu tamkar ya'yan data haifa  acikinta .

suma  kuma suna maseefar kaunarta dan haka suke   kiranta da ummi ,duk abinda suke so itace take musu bata ragesu da komai ba saboda bata da rowa  hakan ne yasa ta sake janyo mata soyayya ta daban a gurin iyayensu.


 shekarata biyar da aure mutuwar mahaifiyar ta risketa ,zuwan datayi indiya ne dazata dawo tazo da kanwarta fadila  ta hada dasu Mahmoud tacigaba da rikonsu .

 sai da fadila ta dauki sama da  shekara takwas  da aure  sannan tasamu cikin murna a wajen wannan family bai faduwa .

    cikinta na da wata tara cif ta haifi NASURUDEEN  daga ita har aliyu suna matukar son DEENI tamkar numfashinsu DEENI yataso cikin gata da kulawar iyayensa, da dangi gabadaya suna nuna masa tsansar  gata da soyayya fiyye da tunanin mai karatu .

shiyasa yataso a shagwabe a sangartacce saboda kaf estate din  kowa yasan da zaman DEENI babbar matsalar da suka fara fuskanta da deeni  , shine rashin magana da bai yi ,da farko fadila  ta dauka ko kurma ne sai daga baya tagane tsabar miskilanci ne kawai yayi masa yawa .

duk tarin ya'yan dake cikin wannan estate din DEENI yafita dabam acikinsu,   bashida aboki  ,.

 gabadaya baya yarda da kowa  koda yaushe  yana tare da umminsa ko farida ko su  Mahmoud tun tasowarsa yake da burin son zama soldier yayinda ummi take bashi goyon baya wajen kiransa soja .

Domin  wani lokacin zai je yatasa hotonta marigayi kakansa dake manne a falonsu gaba yayi ta kallo yana shafa fuskar tsohon yana murmushin ,Sam shi  bashi da fara'a ballanantana sakin fuska   koda yaushe fuska nan tashi a hade take tamkar hadari , .DEENI Nada shekara takwas byn yakare primary school aka sai mishi form din  shiga makarantar sojoji ba'awani samu wata matsala ba yasamu  sakamakon matsayin mahaifinsa da kakansa. sabanin wayanda  basu da gata.

 domin a wanan lokacin idan dai kai bawani  bane  ko dan wani  ba  ko bakada  hanya a military school  ,sunanka sorry.

Domin kuwa  kana ji kana Gani  military school zai gareka shiga  .


    byn wani lokacin farida ta samu miji anan cikin estate din  wanda shima    yakasance "Da"ne ga marigayi  Muhammad bello wato  habibu ubansu daya da aliyu mahaifin ga DEENI   .

duk da fadila ta nuna rashin amincewarta matuka , da nuna wa er'uwartata illar aurenta da Habib   Amman sai taga yarinya ta nuna tana so abunta  ,dan haka ta kyaleta kuma da kunya dai ta fito fili tace batason jinin aliyu ,wanda itama kanta tasan hakan ba mai yiwu bane . itama ba wai shi din ne bataso ba ,halinsa ta tsana , 

Amman shi babban  ma'aikace  gwanati ne,   director of land  and housing & same   na Lagos state gabadaya. yana da mata biyu da yaya bakwai farida ce ta uku . 

Ko alokaci daya auri   farida   takasance mace ce mai tsananin hakuri .

duk da mijin nata Vai kasance mutun  mai adalci ga iyalansa ba. Amman bata taba kawo kararshi ga ummi ba domin tasan halin ummi Sam bata son raini .


Shekarar da aka yiwa sulaiman da mahamud aure shekarace Allah yayiwa mijin ummi rasuwa wato alh aliyu Muhammad bello sunji matuwar farar daya  , mutuwar tayi matukar gigita ummi dan byn ya dawo  daga sallah asuba ne yayi irin kishingide nan yana lazimi  koda ummi taji shiru shiru bai sake fitowa ba Sannan bai nemeta ba  kmr yadda ya saba , wanda aldarsa ce  da zarar gari yayi sha ...yake fitowa ko yakirata a waya    Amman taji shr .

 tashiga dakin nasa  ta tarar dashi kishingide da carbi a hannunsa .

 da fari ta dauka ko bacci yakeyi sai tayi nufin ta tasheshi yakoma kan gado.

  Ammai sai taga alamun rashin motse atare dashi takai hannuta wajen hancinsa da karjinsa a lokacin daya taji baya numfashi.

   take ta zube anan ta sume.

 har a kashare zaman makoki ummi  batasan a wani hali take ba ,dan   bata  cikin haiyacinta' koda ta farfado ma sai da akayi ta hadawa da addu'a Sannan aka samu kanta ta dawo daidai , dan mutuwar ta girgiza har ta kusan zarar daita  .


Byn wani lokacin  su sulaiman suka cigaba da tallafawa ummi da DEENI a lokacin farida na dauke da tsohon ciki  duk da itama ta dan jima bata haihuwa ba, kuma har lokacin ummi bata san er'uwarta tana cikin matsala ba ,sai byn data haihu" lokacin ne ummi taga komai bbu alhalin ga tarin dukiya kmr zai kashe habibu , gashi yasake kara wani sabon  auren matansa sun cike hudu cif .

ummi tayi kuka kmr may  gashi tana cikin danginsu da suke tamkar tsiya madauri daya.

 ba daman tace zata dauki wani mataki akan  haka  .

dan tasan yadda kansu yake a hade .

    dan haka taci kukanta  takoshi ita da er uwarta ahankali take furta kalmar shiyasa tun farko naki amincewa da auren nan naki da habibu ,ba dan komai ba sai dan irin haka  Amman kika nace ,ga  irin abinda nake gudar miki kennan Amman kika kiji , sai kuma ta tsagaita da kukanta ahankali  tace  ba yadda zamuyi da ikon Allah ,sannan ga rabo a tsakani.

 Amman duk da haka sai da ummi tayi masa tatas saboda daman ita bawani sakar masa fuska take ba kuma  yana shakkata.

 kullum ummi acan take wuni har ranar suna    yarinya tace sunan mahaifiyarsu ummi wato muzeenat ,  shima habibu yayi hakan ne saboda ya wanke kansa a wajen ummi,kuma yayi nasara domin  hakan da yayi  yasa ummi taji dadi Sosai aranta har ta dan rage jin zafinsa .

 sannan bakaramin kudi ummi takashewa bby ba. haka ma   ranar suna ummi Tayi rawar Gani sosai .

byn anyi suna ne ummi  tasamu habibu akan dan Allah  ya dinga kula da farida dan ita kadai gareta bata da kowa duk fadin Nigeria sai ita,  idan ma bazai damu ba,  zata bashi Rabin dukiyarta yakara akan nashi  da duk wani  abinda yake so, ita dai burinta kawai ya kular mata da er,uwa ,yayi murmushi kawai hade da ce mata yaji  .


Byn wani lokacin farida ta kuma samun wani ciki wanda tun yana karami take fama da laulayi tun lokacin ummi tadawo da zeenat wajenta ,

a kwana a tashi bbu wuya a gurin Allah har cikin farida ya isa haihuwa gurin haihuwar ne taji jiki sosai .

koda     ta haifi yaron ma  bbu rai sannan itama tace ga garinku .

mutuwar ta shigi habibu matuka yayi kuka tamkar ransa zai fita ,dan shi kansa yasan yayi babbar rashin  da ba zai taba maida irinsa ba.

  yayi rashin mata  mai tsananin kirki da hakuri da sanin darajar miji . Allah sarki ummi   kusan har  tafi habibu jin mutuwar tilon er'uwarta ta ,.

a  wannan Lokacin ne  rikon zeenat ya dawo dindindin  gurin ummi ta dauki soyayyar duniya ta daurawa zeenat tana mugun ji da Yarinyar   tamkar ranta kwata kwata bata son abinda zai rabata da zeenat Sannan kuma   tana debe mata kewar er'uwarta .

lokacin shi  DEENI   na ss1  a NMS, Nigeria military school dake zariya.

   yayinda DEENI Sam ba halinsu daya da ummi ba koda yaushe kagansa fuskar nan tasa  a daure a cunkushi  bbu wani fara'a ga shegen miskilanci tsiya  sai dai mugun kyakkyawa ne na karshe . ajin farko, wato first class ,gashi  da  maseefar  iya sa kaya kallo daya zaka masa ya gigitaka kaji yashiga   ranka farar daya saboda tsabar kyawunsa sai shegen shiga ran mutane domin kusan yan'mata cikin  estate din suna maseefar son sa yayinda yake  girma kyawunsa na sake bayyana hade da miskilancinsa     .


Tunda zeenat ta dawo gidan magana bata taba hadasu ba ko gaisheshi Tayi baya amsawa in dai bayaga idanun ummi ba yana da matsanancin tsafta wanda kusan a wajen ummi yagada .

Cikin haka ya kammala karatunsa na secondary school ya wuce NDA burinsa kennan nason zama cikakken soja itama  ummi kuwa  nasake karfafamasa gwiwa da bashi goyon baya   yana karantar science ne ,wato likitan soja .

bansan yadda zan kwatanta muka  halinsa ba Amman yakasance mutun ne shi mai bambanci ra,ayi.

 byn yakare karatunsa ya fito da mukami second lieutenant star biyu  kennan   .


Zaune zeenat take a falo tana kallon wani serisfilm  a zeeword my let home Tayi zurfi cikin kallon film din gabadaya attention dinta naga kallon ita kadai ce ummi tashiga cikin estate din yin barka taji karar Bell wanda shine kusan karo na hudu da taji ana dannawa. cikin jin haushi ta mike dan bata son abinda zai dagata daga kallon datakeyi , tana bude door din bata tsaya ganin kowaye ba ta juya abinta takoma mazauninta  sallama taji  hade da shigowa ta dago kanta  kennan   da niyar amsa sallama sai taga mutun tsaye kikam  sanye da sabon  kayansu na  sojoji gabadaya zeenat ta gigice hade da rikicewa tsabar tsoro dan ita Allah yayita  da maseefar jin  tsoron soja   take cikinta ya dauki kugi Amman still  idanunta  na kansa ta tsaresa da  kallo .

  in ina tasoma yi wa..wa.. waalai....ya dakatar daita da hannushi, yana zabga mata wata uwar  harara muryasa a kwasashe yace yau ne kika fara ganina  da har zaki wani  tsareni da idanu Kona canza miki ne ?da sauri tasoma girgiza masa kai. Kai tsaye dakin ummi ya nufa tunda bai ganta a parlour ba yasan tana dakinta  tana kallonsa ta kasa dauke idanunta daga garesa har sanda ya dawo fuskar nan tasa a hade yace ke.....dan iskanci kina kallon mutune bazaki iya cewa  ummi bata nan ba   kin wani tsare mutun da idanuwa tamkar na maciji ,dayake bawani manyan idanu gareta , da sauri bakinta na rawa tace dan Allah kayi hakuri mantawa nayi  ko kallonta bai sake yi  ba yaja tsarki yayi hanyar dakinsa  ta tabe baki hade dacewa   jarababbe kawai ai  yadawo kennan, itama taja tsaki ta juya tacigaba da kallonta ..


DOWNLOAD HERE

No comments

Powered by Blogger.