Auren Kwangila Complete Hausa Novel
001
Safa da marwa yai tayi a tsakar falon, hannuwanshi goye a bayanshi.
Kallo daya zaka yimashi kasan yana cikin tsananin damuwar da yake Neman mafita.
Tsaki yasake ja a karo na ba adadi.
"Kai impossible wlh!" Yafada cikin qaraji.
"Wlh bazai ta6a yiwuwaba... Bankrupt? Ni? Ni? The whole Alhaji Shamsu bankrupt kema barazana? No, bazai yiwuba, dole insamu mafita, dolene!"
Ya kai zancen yana kaiwa bango naushi.
Qara kai dubanshi yayi ga agogo, 5:55pm.
Tsaki yaja don lokacin be mashi gudu, cigaba yayi da parade dinshi har saida agogon yabuga 6 dot.
Hannu na kyarma ya dauki wayarshi dake kan center table yashiga Neman lambar, har zufa yake don bala'i.
Saida takusan tsinkewa sannan aka Daga.
"Hello sir" muryar wata ta doki kunnenshi.
"Hi Helen...so what's up, komai yayi daidai" ya tambaya yana dan Waro idanu kamar mai jin tsoro.
"Yes sir, at last ya Baka appointment..."
"Really?!.. Oh am grateful, thank you thank you Helen" yafada yana katseta.
"It ok Sir, Saidai fa sai ranar Monday kuma yace 8 dot zai ganka kuma kasan baison sa6a..."
Qara katseta yayi da "ohh don't worry, Tun seven ma zanzo, thanks zan maki kyauta idan komai yatafi successfully"
"Alright sir, bye and thanks"
"Ni keda godiya" yafada yana latse wayar.
Zubewa yayi kan cushion din bayanshi yana sauke ajiyar zuciya.
"Wuhh! Allah na godema, atleast nafara jiyo qamshin nasara"
"Don Monday, duka duka yau Friday, ay ko nanda sati yace injira zan jira indai zan samu nasara, Nidai Allah ka dorani akanshi kabani sa'a, bari in rama sallolina, Haba tension ba dadi"
Haka yayi gaba yana 'yan sabbatunshi, sai lokacin yasamu kwanciyar hankalin yin sallolinshi na azahar da la'asar.
*********************************
"Ok.. Insha Allah... No you don't have to worry ai munada cika alqawari insha Allah... Sosaima and I bet you zakuji dadin mu'amala damu...hhhh mu keda godiya.... Alright bye thanks for patronizing us"
Katse wayar tayi tana sauke ajiyar zuciya.
"E be like say wannan satin sai munfi shiga chakwakiya" tafada tana kallon wata budurwa dake gabanta riqeda wani qaton littafi da Biro.
Murmushi budurwar tayi tace " wallahi kau ma'am, nima naga alama "
"Hmm yanzufa sufee's family mukayi waya dasu Wai suna buqatar snacks na birthdayn autarsu, kuma this coming Friday, sati daya kenan, ga order din bikin sir Wilson, Wanda ko farawama bamuyiba"
"Aikaudai don yanzu haka bamu gama na ordern savannah hotel ba" inji budurwa tana kada kai.
"Wuhh! Ba damuwa ai, kin gane maryam, kawai yawan ma'aikata zamuyi yadda komai zai tafi fast and smoothly, kinsan an sanmu da cika alqawari banaso mu 6ata wannan image din namu"
Maryam tace "hakane ma'am, hakanma yakamata Ayi"
"So kije kiyi Duk yadda ya dace, ni zan tsara komai zan turomiki anjima ta email..."
Ringing din wayarta ya katseta.
Dauka tayi tana duba mai kiranta.
Da hannu tayima maryam nuni da tana iya tafiya, Dan russunawa tayi sannan tajuya tafice tareda janyo kofar.
Daga wayar tayi cikin fara'a
"Assalamu alaikum"
"Wa alaiki salam, jewel" aka amsa ta dayan bangaren ciki fara'a.
Cikin jindadin yanayinda taji muryarshi tace "Na'am sweet daddy, ina wuni?"
"Lfy jewel, ya kike? Ya aiki"
Marairaicewa tayi tana cewa "as usual dad, ganinan kamar inyi kolo saboda gajiya"
Dariya yayi yace " maganinki ai, ba yadda banyi dakeba akan kiyi White collar job kina zaune cikin AC babu wahalar komai abiyaki Duk wata da albashi mai tsoka kinqi, yanzu ai ga irinta nan"
Itama dariyar tayi tana jujjuyawa saman kujera don inda sabo tasaba da qorafin daddy.
"Yanzu daddy ya lbr?" Ta tambaya trying to switch the topic.
"Akwai lbr shalele, mai dadi kuwa" yafada cikin zumudi.
"Haba?!" Itama ta tambaya cikin zumudi.
"Wlh, kawai ki qaraso kisha labari" yafada yana yar dariya.
"Aikau yanzu zaka ganni Dama nayi closing"
"To saikin zo shalele"
Kit ta katse wayar tana murmushi.
Saurin tashi tayi tana tattara komatsanta, ta qosa taje taji meya chanza mood din daddynta, yau dasafe ko magana beson yi sbd damuwa, dakyar ta tausashi ta tattausan kalamai sannan tasamu yayi break, Amma yanzu shine hardasu dariya, lallai addu'arta ya qarbu.
Rataye jakar tayi ta gyara rolling din gyalenta ta feshe kanta da turarenta mai sanyin qamshi sannan tafita.
Bakwana tayi da ma'aikatanta kamar ba itace boss dinsu ba sannan ta hau motarta ta kama hanyar gida...✍
Ummin fasihu ce
Leave a Comment