Auren Gado Complete Hausa Novel


1⃣&2⃣

 A kwance yake abakin wani tafkeken beach , yana kallon duk matan dake kaida kawowa a wurin cikin fitinannun bikini da kuma lafta laftan sun glasses, wani irin ya mutse fuskar shi yakeyi domin kamar kashi haka yake ganin su, ba Abinda ya dameshi, bayajin mace zata iya burgeshi just like that saboda shigar banza,  
Kallon shi nayi dakyau, gayen ba laifi chocolate ne shi duk da banga idanun shi ba saboda suna boye a cikin sun glass, Amma nasan zasu kasance masu kyau da tsari, lips dinshi kuwa I can clearly see them suna sheki very soft and shinny, he is behaving like jinin sarauta Amma I don't know yet who is he? Gefen shi system dinshi ne tareda wayoyin shi guda biyu, daya tayi kara ya dauka cikin sauri domin ganin sunan dake jikin screen din wayar, "heartbeat, Hmmm no wonder mata basa burgeshi duk da yawon da sukeyi a gabanshi necked, sai dai me, yanda yake zuba shagwaba tareda maganar da yakeyi yasa mamaki ya cikani domin daga gani bada mace yake magana ba, is he a gay??? 

"Yaya please, wai kai are you really serious you are getting married??,
Banajin maganar dayan side d'in saidai Amsar shi, "of cos yaya dole inzo Auren ka nine fa best friend best brother and ur best partner in life, am coming insha Allahu, but kasan halin momy kuma I don't want problem shiyasa nake zama na a bangkok, is alright am on my way don't worry heartbeat, just for you. 
Datse call din yayi ya mike, a lokacin na kalleshi da tsarin jikinshi daba riga sai guntun wando kawai ga six packs dinshi da suka fito gwanin burgewa alamar yana gyming, tareda kulada lafiyar jikinshi sosai, zare sunglass din yayi, na kalle sexy eyes da lashes dinshi kamar na mace zaro zaro, he is really handsome, one look zakiyi mai ki afka soyayyar shi indai zaki kalli wa'innan killer eyes dinshi, gashi ya iya juyasu, kamar wani karuwar namiji, cikin takun kasaita ya zura beautiful sleepers dinshi na maza ya kwashi kayanshi tareda key ya nufi can gefe inda ya parker open jeep dinshi, ya zube su tareda zama yajata a guje yabar wurin,. 

Wani D'an madai daicin gidane a cikin jerin gidajen dake cikin unguwannin dake shahararriyar Unguwar ta 
  Phetchaburi Road, Makkasan,
 Ratchathevi, Bangkok 10400 Thailand. unguwa ce ta wanda ya tada Kafada da Abubuwan duniya, duk da gidan da ya shiga ba wani kato bane amma kana ganin shi kasan ya gaji da haduwa, maid dinshi ne yayi saurin taron shi da gorar ruwa tareda towel, karba kawai yayi ya nufi bathroom, ya dauki Kusan hour guda kafin yafito kamar zai canjo fata, 
Yana fitowa daure da guntun towel ya tsaya Turus tareda zubawa dakin ido yana mamakin ta, tayi mai dai dai tareda kashe shi da idanu, he just hate that character a wurin mace, shi so yake rana daya Allah ya hadashi da mace mai kunya, that is, tagama siyemai zuciya, but this kind of girls dake rayuwa a irin wannan garin wai in the name of study, Ahh he really hate them, karuwai kawai, 
Ganin kallon rainin wayau Dayake watsa mata yasa ta zaburo tareda matsowa cikin rangwada, doguwar riga ce har kasa she cover all her body but akwai gyara a al' amarin ta, duk da kyakykyawa ce gata a dire, kuma fara tas bai hana kagano idanun ta sun bude,. 
"Hey dear tafada cikin kashe murya, wani irin kallon don't touch me ya mata tayi saurin daga hannun ta sama tareda cewa "is ok I won't dear, but please  just once give me chance to prove myself. 
"Dont even try to suffer ur self, nafada miki fauzy am not interested, just back up. " am ready to follow you I promise zanyi duk y'anda kakeso am ready to change for you, nafada ma dady na kai nakeso zamu koma kano tare dakai please na horu ka soni don Allah, "Look don't even try, bazan Auri sauran wasu ba  infact am not ready for marriage now shiyasa dana gama school naki komawa gida saboda nasan Abinda zai faru, don haka kifita a rayuwa ta banason naci. Kuka tasa mai tareda  dukawa kasa, "I swear bantaba bari wani yasanni ba kawai romance ne kuma kasan is a normal thing ai, kana ganin saboda kai nakasa komawa gida kullum cikin karya nake musu please  karka tarwatsa min Rayuwa kaine cikon numfashi na, tausayin ta yaji sosai domin ta dade tana wahala a kanshi tun baya kulata har yafara D'an sauraran ta, "Oh come on, kinsan natsani kuka ko, ki shirya am going tomorrow mutafi nija am going for good, if you are ready..... "Of cos dear am ready, tafada tana dariya mai hade da tausayin kanta, goge hawaye tayi tafita cikin sauri domin ganin ta tattara duk Abinda zata bukata. 
"Ahhh yafada tareda dafe kai, this girl is headache I swear, 
Shiryawa yayi cikin guntun wando da black singlet yafito gwanin burgewa  sai tsadadden agogon shi da kuma dankwalelen zoben dake karawa hannun shi tsari da kyau wa'inda baya taba rabuwa dasu, infact ko shopping zaiyi agogo ne first a tsarin shi he just love watches saboda suna karamai tsari da kwarjini, 

 Abincin shi ya zauna yafaraci wa'inda duk ganye ne sai crabs roasted ones, saida ya dauki lokaci kafin ya kammala ya sanya tissue ya goge bakinshi ya mike, duk al'adar Chinese ta gama ratsa shi abincin su harshen su al adunsu, wainda zasuyi matukar wahalar dashi a nija,. 
Saida yayi clearing komai a daren, about visa da sauransu, karfe uku na Asuba jirgin su ya daga wanda zai kasance long journey duk da a jirgine, tafiyace ta Kusan awoyi,  tana zaune a gefen shi ta zuba mai ido sai faman danna system dinshi yakeyi like ba wata halittar dake existing a kusa dashi, 

She don't bloody care tunda yace su koma nija tasan komai zaizo cikin sauki,  
Saida  ya dauki lokaci kafin ya rufe ya saka headphones ya rufe idanun shi yana farin cikin zaije wurin yayan shi wanda yafi kowa daraja a duniya a wurin shi yana mashi so mai girma yana kaunar shi fiyeda kanshi, 
Duk da su marayu ne ubansu ya mutu tun yana D'an karami, baiyi lacking komai ba, domin baban su gawurtaccen D'an siyasa ne kuma D'an kasuwa wanda yanada share a manyan campanonin dake ciki da wajen kasar mu harma da ketare, subiyu ne kacal wurin mahaifiyar su, yayan shi Ahmed sai shi Ibrahim khalel wanda khalel din  ne yafi amfani dashi, 
Gatan da yake dashi baya faduwa haka kudi ba matsala bane a rayuwar su domin mahaifiyar su itama ba azaune takeba tana aiki da first bank tareda matsayi mai girma, 
Akwai banbancin hali a tareda shi da d'an uwanshi, domin shi mai zuciya ne, shikuma Ahmed yanada sanyin hali da hakuri,  shakuwa ce mai girma da tausayi a tsakanin Y'an Uwan biyu sukan iyawa juna sadaukarwa ta kowacce hanya, tun suna yara balle kuma yanzu, kowa yasan how they love each other, don haka ko ginin su a hade yake basu taba raba gida ba duk da sunfi karfin hakan, katoton gidan mahaifin su suka kara fadadawa tareda buga plat biyu nasu tangama tangama sai na mahaifiyar su wanda a ciki ma akwai part part dinsu, domin bataso suyi mata nisa, mace ce mai tsananin zafi da kuma rashin hakuri gashi bata son sunan talaka bare kuma talauci batason rashin Aji a rayuwar ta don haka kullum burinta ta fantama, bakaramin shiri takeyi a Auren ya'yan taba tunkafin su tashiyi ma, saidai kash ansamu akasi domin Ahmed ya kaucewa tsarin ta ta hanyar dakko Y'ar talaka tulus, wanda bakaramin daga akasha ba kafin ta Amince da zancen Auren bayan dogayen sharuddan data gindaya bayan Amincewar ta. To muje dai zuwa yanzu zamu fara,. Karfe goma jirgin nasu ya sauka a babban filin jirgin na Aminu kano, wanda sukaci karo da motoci birjik a jere na taron su, tuni fauzy ta matso "you see kamar jira akeyi indawo kaga irin motocin da sukazo daukana please ka yarda muje gidanku after two days sai intafi gida. "Hmm yafada tareda watsa mata kallon you lost ur mind, kafin ya ce "al adar Chinese ce wannan ba ta bahaushe ba don haka go home zanyi inviting dinki to my brother wedding ok,. "Ok tafada cikin farin ciki, ta nufi masu taron ta wainda kana ganin motocin kasan itama Y'ar gidan wani kwallon barawon kasar muce,. 

Hango yayan shi da yayi yasa ya tafi da sauri cikin farin ciki ya rungume shi, Ahmed din ma kyakkywa ne suna matukar Kama saidai shi fari ne while Khaleel chocolate ne, "my yaya kai kadai kazo were is mommy? 
"Long story muje ko, yafada yana karbar jakarshi karama tareda bawa driver umarnin kwaso kayan da yazo dasu yakai boot, saida suka zauna yace "Am sorry yaya sai jiya nayi placing odar na kayan matar ka zasuzo tunda by air ne kafin bikin insha Allahu nasan zakaso su. 
Rungume shi yayi cikeda farin ciki tareda cewa "tank you my kani,  but please karka bari momy tasani kawai zamu Ajiye mata ne a dakina har akawo ta. "Why?  Cos momy batason ta infact bakaramin yaki akayi ba kafin ta Amince ayi komai. "Mommy mommy bazata canja ba, so why she hate her? "Because she is poor. Saurin kallon shi yayi "so brother is your foult kasan momy tunfarko ai why ka dakko poor girl uhm? 
"Because I love her so much I love Naziya a lot khaleel, she is innocent and young she is very cute I can't help it, bazan iya Auren wata ba in har aka hanani zama da ita. Rungume shi yayi cikeda so da kuma tausayin D'an Uwan nashi yace "is ok am here you know I will support you, don't mind mommy, but her name is unique. "Yeah she is also unique brother, yafada yana lumshe idanun shi tareda jin soyayyar ta mai zafi har wasu irin madarar ruwan hawaye ne suka taru a idanun shi,. 
 
A cikin fitacciyar unguwar ta sulaiman crescent suka yada Zango cikin wani tafkeken gini na kece raini, tsarin gidan kamar a turai, ya fito tareda shakar iskar kayan marmarin dake   zagaye da ginin gidan, 
 Harabar gidan shake yake da motoci different product da kuma runfuna na Alfarma dake karkashin bishiyoyin kwakwa ta ko ina irin na gargajiya da masu kudi keyi,. 

Kallon shi Ahmed yayi tundaga kasa har sama "bazaka canja character dinka bako yawo daguntayen kaya imagine tundaga bangkok kazo da three quarter da t shirt baka ko jin sanyi? "Kamar ka mantani ko yaya nifa I hate heat wallahi shiyasa nake wuni a beach., zaka hadu da momy muje ciki,. 


A tafkeken katon falon an tsara shi fiyeda tunanin mai karatu kujeru Kusan set uku ya mamaye amma da sauran fili kowane set da center carpet dinshi masu laushi da nutse kafafu, standing art tangama tangama ta koina bayan na jikin gini wainda suka zama kamar decoration a falon, 
A tsaye take tanata kai da kawo kamar Y'ar sintiri tana jiran fevourite son d'inta, ya iso, ta hana masu aiki sukuni sun kalkale but parts dinshi yafi sau uku da safen nan,  dishes kuwa kamar a hotel saboda d'oki, 
Macece hakima kamar  Aisha D'an kano margayiya taci Abuja style cikin tsadadden leshin ta wanda yafi karfin dari a jikin ta, da glashin ta na kara karfin idanu, wanda yakara fito da haiba da hutun ta harma da masu gidan ranar data tada Kafada a ciki, 

Sallamar su yasa tamike cikeda fara'a tana "Oyoyo my happiness welcome back dear tafada tana rungume shi tareda bubbuga bayan shi, "tank you mommy munsame ku lafiya?  "Alhmdulillah tafada tareda dagowa tana "ai dai tunda kadawo yanzu zanji saukin lamura na at least inada inda zancika burina, ka huta ka dage ka dakko min Y'ar gidan bayero ko buhari, ka huce min takaici. Tafada tana watsawa Ahmed harara, dukar da kanshi yayi tareda daukar Karamar jakar D'an Uwan nashi yayi ciki da ita, zama tayi a set daya tareda janyoshi tana faman korafi tun bai hutaba, " hope zaka dakko Y'ar gidan mutanen arziki kai ba Y'ar matsiyata ba?  "Mommy mommy mommy please meyasa kike hakane?  Nifa am here because of my brother, kinsan banason korafi kibarshi ya Auri choice dinshi koda cripple ce tunda shi zai zauna da ita please allow him to be happy I beg of you. "Shikenan tunda kaima kabi bayan shi, amma promise me zaka share min hawaye kaji? "Ok I promise bari inje in huta am tired, fresh up akawo maka abinci a ciki ko? "Yes please kinsan me nakeso ai ko? "Sosai karka damu na shirya maka komai.  
A zaune yasamu brother dinshi yana dafe da kanshi ya zauna tareda dafashi cikeda tausayi "relaxed bro am here komai zaiyi normal kaji, Aunty what ma sunan ta? "Naziya, yafada fuskar shi na washewa domin sunan ta kawai nabashi farin ciki, "get ready zamuje unguwar su anjima kaganta kaji. "Ok my heartbeat. "Stop that name kafin my Naziya taji tayi kishi fa. "Oh no yaya zata shiga tsakanin mu ne, to nima zanbi bayan mommy fa. Rungume shi yayi tareda cewa "no no no tasan da zaman ka, tundaga lokacin da muka fara haduwa, da ita, ka huta zanfada maka komai game da ita kafin muje gidan,. 


Karfe biyu ya farka daga baccin gajiyar da yayi yaga Ahmed zaune ya na baza kamshi cikin D'an datsesiyar getzner  tana maiko, tashi yayi "yaya har kayi wanka?  What is the time now? Agogon shi ya nuna mai ya zabura yana holy shit, ya diro a lumtsumemiyar katifar shi, yayi bathroom domin baiyi Azahar ba, cikin sauri sauri ya zura jallabiya ya tada sallah, domin duk abinda yake yi baya son wasa da ibadar shi amma idan ka kalleshi zaka dauka rayuwar duniya tafi komai ratsa shi amma yarone mai   riko da Addini bisa ga  goyon yayan kwarai da yazamo mai tamkar uba. 
Saida ya idar ya bude jakar shi tareda ciro kananan kaya. 
"Wait gidan kawu zamuje a mandawari  kasan halin shi ka sa manyan kaya nasa an shirya maka new ones a wardrp dinka na nan dana can side d'in. 
"What?  Kasan nifa banason zafi ga garin nan da zafin tsiya kuma insa kayan da zasu hanani sakewa, "wait yaya ba an gama zuba komai ba a part dinmu why muke nan har yanzu? "Bisaga umarni na khaleel bazan yarda a saka Y'ar talakawa cikin ginin da na narkarda dukiyar mijina datawa ba, a kawo min gayyar  k'uma da kudin cizoba ta zo nan ya isheta zama tunda bazata iya zama  a katon giniba, domin ko dakin generator dinmu yafi gidan ubanta girma,. Saurin kaucewa khaleel yayi domin inda sabo sun saba,  ya nufi katon wardrp din yaga kaya shake saida yayi murmushi saboda yasan aikin yayan nashi ne, 
Fito da Kala daya yayi irin na jikin shi ya nufi hanyar bathroom domin ya canja saboda mommy dake dakin, 
Tana zazzaga complain, fitowa yayi tareda rungume ta yana baza kamshi shima kanshi da yasha askin matasan zamani ya na sheki ya sha gyara ya ce" mommy please enough of your complains kibar yayana yasamu farin cikin shi mana,. "Oh wato kuna tunanin bansan what is best for him ba ko?  Bayan na kawo mai yammata Kala Kala Yaran kawaye na masu ilimi amma ya nace sai Y'ar talakawa mtsww, ka kara Abinci kafin kutafi gidan kawun naku kafin yazo yana baza min fitinar shi shima yace na hanaku zuwa ku gaidashi, ta fita tana kasaita, "Hmmmm Sorry brother kariga kasan halin momy. "Is ok eat muje ko? 

Hour guda ta kaisu gidan na kawun nasu Alhaji modu mai gwal wanda D'an kasuwa ne sosai a harkar gwalagwalai, mutum ne a tsaye akan zumuncin shi domin baida wasa yanada mata biyu da yara sunkai goma, shikadai Hajiya balkisu ke shakka domin yafita fitina kuma shima yanada kudi shiyasa take ragamishi domin sau tari yakan yimata Abu tace yaci Arzikin Aljihun shi. 
Sunada kanni biyu mata bayan mahaifin su khaleel  shine babba sai Alhaji modu din, su Y'an Asalin garin maiduguri ne iyayen su ne suka kawosu babban birnin na kano, sunginu suma duka domin ba talaka a cikin su har matan ma domin suna gidajen kusoshin kasar mu, 
  

Y'an mata ne birjik a gidan wainda kowaccen su nada burin samun daya daga cikin wa'innan zaratan mazan saidai sam su Hankalin su baya kan kannin nasu infact basa burin Auren zumunci ma, itama Hajiya balkisu bata ra'ayi domin batason ya'yan ta suyi Aure inda bazata iya juya Suruka ba,, 
Domin tasan Y'an Uwan mijinta duk ba wai mutunci sukeda shiba wanketa zasuyi akan ya'yan su, 
Sun samu tar bar bangirma daga uwar gidan Kawu modun kafin ya dawo, 
Sundauki lokaci a gidan har kawun nasu yazo, wanda yayi farin ciki sosai ya musu nasiha tareda basu shawarori, "yanzu tunda kadawo khaleel saika tallafawa D'an Uwan ka domin yayi matukar kokari wajen tafiya da campanoni da kuma masana'antun ku, sai kuci gaba da tafiyar da kasuwancin ku cikin tsari, Sannan naje munyi magana da uban Naziya, Auren naku nan da sati biyu aka tsayar don haka ka je ka karasa shirin ka  "na kammala komai kawu ni ta wajena. "Toh masha Allah, sai mu jira lokaci Allah ya tabbatar da Alkhairi, Amma dattijon nata mutumin Arziki ne baidamu da Abin duniya ba gaskiya karka damu da shirmen mata wannan gidan irin shi ya kamaci namiji ya nemi Aure. Wani irin dad'i yaji tareda sauke Ajiyar zuciya, saida suka yi magrib kafin su bar gidan, suna hanya yana bashi labarin Naziya,........ πŸ–Š


No comments

Powered by Blogger.