Auren Bare Complete Hausa Novel


001*


_GARIN KANO UNGUWAR SHARAÆŠA_


Yammaci ne mai ɗauke da wani irin lullumi mai daɗin gaske, hadarine yaketa faman haɗowa kota ina garin yay wani irin luf har wani  duhune ke kawo kai, sabida yadda garin yagama gamewa da wannan

hadarin, ƴan matane, guda uku suna tafe kowacce hannunta riƙe da bokiti mai ruwan garai wanda hausawa ke masa laƙabi da ɗan ballasa.

Seda na ƙarasa gabansu sannan idanuna ya ganemin ashe ba kansu ɗaya ba, domin farar cikinsu itace mai ƙiba amman ba canba tana da cikar halitta irin ta ɗiya mace, kallo guda zaka mata kagane ƙarancin shekarunta domin daga gani bazata haura shekaru goma sha shidda a duniya ba, se ragowar biyun suma sunada haske amman dai basu kai wannan ɗin ba, sukam kallo ɗaya zaka musu kagane ƴan biyune sabida yadda suke tsananin kama da juna, waɗanda bazasu haura shekaru goma sha takwas  aduniya ba, kuma kana kallonsu kasan sun girmewa wannan farar sedai kuma daga ganinsu kaga jini ɗaya sabida tsananin kamar dasuke da ita, abin da zata fisu shine girman jiki da cikar halitta gami da hasken fata.

Ɗaya daga cikin ƴan biyun ce ta dubi wannan farar yarinyar tare da cewa "Haba Bebi! bakya ganin yamma tayi sosai yakamata mu koma gida hakan nan dan ALLAH kinsan halin mama da ruɗewa wallahi nasan yanzu haka tana ƙofar gida tana faman zagaye". Takai maganar tana kallon ɗayar wadda batai magana ba tare da cewa "Koba haka ba hassana?" tafaɗa tana kallonta,cafkewa hassanar tai tare da jan tsaki! kaɗan"Bebi kiwa ALLAH ki rabu da bin ƴan bashin nan mutafi gida ai gobe ma ranace, wallahi mu dukke kike jamana ana ƙin sayan awararmu sabida jarabar faɗanki" takai maganar cikin ƙufula. wannan farar yarinyar wadda ita nake tunanin itace bebin ita ta dubesu cikin fitsara kana tace"Nifa karku uzzuramin wallahi saina koma na amsowa mama kuɗinta aini ba baiwar ubansu bace" takai maganar tana huci kamar taci gudu, wadda aka kira da hassana ita tai rau-rau da idanunta"Dan ALLAH bebi kiyi haƙuri mutafi nai miki alƙawari gobe zan karɓi kuɗin da kaina". wani kallo bebi ta watsa musu tare da dire bokitin hannunta batama tsaya jiraba ta arta aguje, ko nauyin jikinta bata ji.

Baki ɗaya baki da hanci su hassana suka saki suna kallon yadda ƙanwar tasu ke gudu amman babu yadda zasuyi sabida halin bebi se ita bata tsoron kowa ko kaɗan bebi bata da kunya ga faɗan tsiya da taurin kai da mita, ganin an soma ruwa kaɗan kaɗan yasa suka ƙara sauri, domin nufar gida sedai cikin zuciyarsu tsorone fall na yadda basu san halin da bebi zata shiga a hanya ba.

Cikin wani irin zafin nama take gudun baki ɗaya tagama jigata kanta harseda takai dai-dai jection ɗin sharaɗa kai da ƙafa, sannan taja ta tsaya ta huta, lokacin ruwan harya soma saukowa, hijabin jikinta ta cire tare da ɗaurawa a ƙugunta, baki ɗaya manyan breast ɗinta waɗanda suka zame mata kaya, masu bata tsananin haushi duk sun fito waje, ta saman rigarta amman haka ta kurmutsa cikin kan dakalin da matasan samarin ke zaune cikin zafin nama da masifa ta dubi ɗan baƙin cikinsu "Kai siba dallah kabani dari biyun awarata idan ba haka ba wallahi zamu kwashi ƴan kallo anan wajan dakai" takai maganar tana riƙo ƙugunta tare da jijjiga jikinta wanda ya baiwa albarkatun kirjinta damar kaɗawa kamar da gayya wanda ita ko kaɗan batai wannan tunanin ba, wanda aka kira da siba ne ya taso daga cikin samarin yana ɗan shafa gemunsa tare da lasar ƙasan lip's ɗinsa kaɗan yana binta da wani mayen kallo, wanda kafin ya furta wani abu ruwan dake zuba kaɗan ya kece da ƙarfi, cikin tsananin zalama yake dubanta"idan har kika bari na taɓa nan" ya nuna saman kirjinta,"Nikuma zan baki ninkin kuɗinki, amman idan kika saka taurin kai na cinye kuɗin inga uban daya isa ya karɓa miki" yakai maganar yana dariya wadda baki  ɗaya mazan wajan suka haɗe baki wajan sakin ta suna mara masa baya kamar da gayya, cikin tsananin ƙufula bebi ta dubeshi "Kai! dakata gaja da kai dawani ƙazamin hannunka mai datti kakeson taɓa min jikina lallai da uwarka ta haifi mai yankakken hannu kuwa" takai maganar tana mayar da hijabinta jikinta, dariya ya saki kana ya kai hannunsa dai dai wajan wuyan hijabinta wanda tunma kafin ya ɗago hannun yaji saukar mari! tas!tas!!tas!!, har sau uku, baki ɗaya idanunta ya juye ya koma kamar banata ba"Dan uwarka dan ubanka shege bunsuru jikina yafi ƙarfin gaja irin........," bata ƙarasaba taji saukar yatsunsa a fuskarta, kafin ta ɗago taji muryar okasha yana magana"Haba baba kafayi kwafsi tayaya zaka bari mace taga weak ɗinka haba dallah wuce kabarta da yawarta" yafaɗa yana watsa mata kallon banza, sam bebi tama kasa furta komai illa maganar siba wadda ke cike da borin kunya ta karaɗe mata kunnenta"hakane fa oka bara nabar wannan wawiyar wadda bata da arabi bare boko ƴar matsiyata masu gidan buhu, ƴan makarantar tallah........." yafaɗa yana bin bayan okashat abokinsa, tsaye suka bar beby wadda tai saƙare kamar doluwa still kuma ruwan yana kuma zuba ajikinta su basu bata  kuɗin bashin taba gashi kuma sun barta da dukan ruwa.

Wata ƙwallar takaici ta saki wadda takejin zuciyarta na mata suya kamar zata faso ta fito abinda tun tasowar ta bata yarda dashi ba kenan kuka! sam bebi bata yarda tai kuka akan abu sabida tsabar kafar kanta tare da yawan faɗanta, jan ƙafafunta tai tare da barin wajan tanajin yadda ruwan sama ke sauka ajikinta.

Kanta tsaye sharaɗa police station ta nufa dukkan kayan jikinta suna ɗigar da ruwa domin sun riga da sun jiƙe jagaf da wani ɗan sanda taci karo ɗan gajere baki, yana ganinta ya washe baki yaga ƴar fara kyakykyawa"A,a madam lafiya na ganki cikin ruwan nan?" yafaɗa yana ɗan matsowa gabanta, da baya taja kaɗan tana ayyana yadda wasu mazan suke hali kamar na kwartaye, kana ta dubeshi"Officer na kawo ƙara ne akan ina son abimin haƙƙina" yadda ta kame kanta tana kora masa bayani seka rantse babbar macece mai hankali, seda ta gama yi masa bayanin duk yadda sukai dasu siba hatta marin daya mata bata ɓoye masa ba sabida tun asalinta ita bamai yawan ƙarya bace, sannan ta ɗora da cewar"idan da hali officer ina son ku ɗauko mota aje na nuna muku har inda yake domin a karɓar min naira ɗari biyuta". takai maganar da iyakar gaskiyarta, wata iriyar dariya officern ya kece da ita, da kallo ya bita yana nazarin ko ta samu taɓin hankali sedai kuma tsaf take babu alamun ƙazanta ko rashin hankali agareta, dai dai ta nutsuwar sa, yay tare da ɗan haɗe ransa kaɗan"Ke yanzu ƙanwata idan banda abinki haka ake kawo ƙara wama yace miki muna aiki da kane?" ya jefa mata tambayar yana kallonta tsaki! taja kaɗan tare da ɗan sharce ruwan daya zubo mata saman fuskarta"Kaga ni daman wajan shugaban wajan nan nazo idan bazaka tai makamin na karbo mana kuɗinmu ba kaban wuri kawai malam ruwa yana faman jiƙani" tafaɗa tana murguɗa masa baki, haɓa officer ya kama sannan yace"To muje naga wasu tsagerun samarin ne base kin shiga cikiba sabida ba kowa ne ze fahimce kiba", babu musu bebi taja  ƙafarta suka jera da officer seda takai har kan dakalin ƴar rumfar dasu siba ke ciki sannan taja ta tsaya tana nunawa officer siba, wanda yaketa faman zaro idanu tamkar yay ma sarki ƙarya.

"Officer wannan ne kadai san bayanin dana maka tun acan ko?" tafaɗa tana makawa siba harara, da kallo officer yabi siba tare da ce masa "Kai kuwa abokina tayaya zakaci kuɗinta na sana,arta kaƙi bata abin kuma yakai ga cin zarafi harda mari?" yafaɗa cikin sigar tambaya, duk ruwan da ake bai hana siba sharce gumi ba wato duk jarabar yarinyar nan da ake faɗa masa bai taɓa tabbatarwa ba se yau, inda yasan akan ɗari biyunta zata kaishi ƙara ai da tuni anwuce wajan ya bata abinta, basar da tunanin yay kana ya ɗago  "Officer ai min aikin gafara Bebi kiyi haƙuri insha ALLAHU hakan baze kuma faruwa ba, gama 500 nan wallahi ki riƙe duka" yafaɗa cikin sauri kana ya zaro sabuwar ɗari biyar daga pocket ɗinsa wanda daman can iya shege ne yasa ya hanatan, wani watsatstsen kallo ta watsa masa tare da murguɗa bakinta gaba"Ni ai bana buƙatar kuɗin ƴan tasha haƙƙina kaɗai zaka bani na kama gabana nasan inda dare yay min" tafaɗa tare da kauda kanta gefe, mamakine ya kama ƴan wajan harshi kansa officer sannan ya dube ta,"Haba ke kuwa an miki alkhairi ai kya amsa ko?"........wawan kallo ta masa tare da cewa"officer na gode da taimako kaga siba bani ɗari biyu ta nai gaba bana son ɓata lokaci". a wajan okashatu siba ya amshi ɗari biyun ya bata hannunsa na rawa, bata tsaya kallon kowa na wajan ba bare taiwa officer godiya taja jikinta tabar wajan, har taje titi ruwan bai bar dukantaba.....................




DOWNLOAD HERE

No comments

Powered by Blogger.