Abokin Aikina Book 1 Page 4

 


LAMBA TA HUƊU.*


Kiran sallar zuhur ya sa na miƙe jiri yana kwasa ta na ɗoro arwala. A zaune na yi sallah saboda ƙafafuwana da na jin ba za su iya ɗauka ta ba. Bayan na gama a nan kan sallaya na kwanta ina sharɓar hawaye, ban san lokacin da bacci mai nauyi ya yi awon

gaba da ni ba. Azababben ciwon kai ya farkar da ni babu shiri, saboda luguden da ake yi mini cikin kai ya linka yadda na saba ji, dafe kan na yi ina ta faɗin sunayen Allah a zuci da bakina. Kukan da cikina yake yi ya sa na yunƙura zan miƙe jiri ya kwashe ni na koma na zauna. Shiru na ɗan lokaci ina sauraron daddaƙar da ake yi mini cikin kan, sannan ina jin tashin ƙarar tv'nmu cikin kunnuwana daga nan inda nake, ƙarfin halin miƙewa na yi ina layi na fito daga ɗakin domin na samar wa kaina abin da zan iya ci. Ganin Mukhtar zaune a falon yana kallon waƙar Indiya, hakan ya sa na ji wani tuƙuƙin baƙinciki ya rufe mini zuciyata, don har ga Allah na tsani jin muryar shi ma balle na yi ido biyu da shi. Hakan ya sa duba ɗaya na yi masa na kawar da kai na shige kitchen, duk da raina ya ɓaci da ganin garar da yake ci shi kaɗai ba tare da ya neme ni ba. Duba da yadda ya san ban da lafiya tsawon kwanaki kuma ban ci komai ba.  Sai maganin Chemist da yake siyo mini don bai yarda da zuwa asibiti ba. Ganin yake yi na cika jaye-jayen abin da zan ɗora masa wahala, ko yara ke ciwo sai an yi da ƙyar yake bari a je asibiti. Wani lokaci ma sai mun yi rigima sosai sannan yake jan yaro ya je da shi da kan shi, a ƙoƙarin shi na nuna jin haushin matsin lambar da nake yi masa. Ba zai je da ni ba ko ya ba ni damar zuwa da su ba, sai dai idan sun dawo na ga magungunan da aka siyo ban isa na ce komai ba.

   

   A wannan karon ma tea kawai na iya haɗawa na fito. Ina ƙoƙarin shigewa ɗaki ƙamshin naman da yake ci ya cika mini hanci, amma hakan bai sa na waigo ba balle na yi masa ƙorafi. Zaune na  yi bakin gadon na zuƙe shayin sannan na yi shiru ina nazarin yadda aka yi na rasa wayata. Domin hankalina duka ya dawo kanta saboda ita ce abokiyar hira ta, kuma ita ke ɗebe mini damuwa a duk lokacin da nake cikin ɓacin rai ko kaɗaici. Mintuna kaɗan da shan shayin na jiyo muryar wata tana sallama, kamar na share amma na kasa haƙuri na miƙe ina taku a hankali na fito domin, na ga wake sallamar.  Firdausi ƙawata ce na gani ta nufo ni cikin fara'a tana faɗin "Ashe kina ɗaki?" "E, mu je daga ciki" Sai da ta yi gaba sannan na bi bayanta, bayan na aika wa Mukhtar mugun kallon da nake ji kamar na shaƙe masa wuya, saboda kallon da na ga yana yi muna ta gefen ido. 


"Zaituna kin rame da yawa, har yanzu jikin ne?" Sai da na yi murmushin ƙarfin hali sannan na ce "Jikin ne, tare da baƙincikin Mukhtar da ya addabi zuciyata.."  "Mu yi zancen ciwon, don ita matsalar Mukhtar idan da sabo kin saba da ita. Gaskiya ya dace ki je asibiti a bincika a ji me ke damunki, zama da ciwo cikin gida ana shan magani ba ya kawo waraka. Don wani lokaci ciwo daban maganin da ake sha ma daban.." "MD ya kai ni asibiti, a lokacin da na faɗi na some a wurin aikinmu. Amma masifar Mukhtar ba ta bari na karɓi magungunan ba..." "Ban gane ba!" Sai da na zuƙe majinar kukan da ya zo mini sannan na ce "Shi ya kai ni asibiti daga can wurin aikin, bayan na samu kaina ya ɗauko ni a motar shi ya kawo ni gida. Shi ne fa Mukhtar ya farfasa masa gilassan mota sannan ya tara mana mutane yana jifar mu da miyagun maganganun da babu komai a cikinsu face ƙazafi da zargi..." "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Wai shi Mukhtar me ya sa ba ya hangen nesa kafin ya aiwatar da abu? Meye laifin MD a nan don ya taimaka miki a matsayin shi na babba a wurin aikinku? Wani lokaci rashin fahimta da zargi shi yake kawo duk wata matsala da ke faruwa ke da shi, sannan abin haushin ma Mukhtar ba ya jin maganar kowa kuma ba ya jin shawara ko an ba shi. Tabbas! Zai ji zafi idan ya ga wani ya kawo ki gida a cikin motar shi. Amma kuma yana da kyau ya yi bincike ya ji wane dalili ne ya kawo hakan? Saboda ya fi kowa sanin halinki, abin da za ki iya yi da wanda ba kya iyawa, duk da ba a shaidar mutum amma ana gane zurfin ruwa a cikin ido. Duba da tsawon lokacin da kuka kwashe tare ya dace a ce akwai fahimtar juna tsakaninku. Ni fa wallahi ban ga amfanin irin wannan zaman da kuke yi ba. Idan shi ya hau ke ki sauko mana, duk da na san zuciya ba ta da ƙashi, amma ya dace ku zauna ke da shi ku samu maslaha a cikin zamanku. Yaranku girma suke yi, kuma suna fahimtar duk abin da ke wakana a tsakaninku. Wanda hakan kwata-kwata bai dace ba. To ni zan tafi, amma ki daure ki je Asibiti gaskiya, zama da ciwo da ba zai yiyu ba. Saboda lafiya 'yar tattali ce idan ta suɓuce komai zai iya lalacewa, sannan ki daina saka wa kanki damuwa a kan matsalar shi. Don da lafiyarki ma ya mayar da ke juji balle kin rasa lafiyar da kowa yake tinƙaho? Allah dai ya kyauta..." Cikin matsanancin ɓacin rai kwance a kan fuskarta ta fice, domin a kaf faɗin garin babu wadda ta san matsalata ciki da baya sai Firdausi. Domin akwai abubuwan da ko Ummata ba ta san da su ba, amma ita amincina da ita da zamanta mace mai sirri ya sa ba na shayin sanar da ita damuwata. Tare muka fito tana faɗin "Ki daure ki je asibiti gaskiya" "In Sha Allah" na ce da ita, ko da muka fito Mukhtar ba ya falon. Har ƙofar gida na raka ta, bayan mun ɗan taɓa hira sannan muka yi sallama ta tafi. Ko da na dawo falon na hango Mukhtar yana fitowa daga ɗakin shi, ba ƙaramar jarumta na yi ba wurin tsayawa na fuskance shi na ce "Gobe ina so na je asibiti..." "Ko ba ki faɗa ba ai na ji komai da kunnuwana..." "Daman ina sane da laɓen da kake yi mini idan na yi baƙi. Shi ya sa ba na shayin faɗar komai domin ka ji da kunnuwanka" Shiru ya yi yana kallo na saboda na kamo tashar shi da kyau, domin abu ne wanda na kiyaya gare shi duk lokacin da na yi baƙi sai ya laɓe ya ji me muke faɗa, ko da gidan ya dawo ya fahimci akwai wasu saɗaf-saɗaf yake yi ya laɓe ya dinga sauraron hirar da ake yi. 

      "Yana da kyau da ki koyi ɓoye sirrinki, don ba ke kaɗai ce mai matsala a gidan aure ba..." "Kowa ta shi ya sani, don haka kowa karatun sallah yake yi da kumfan bakin shi. Asibiti nake so ka kai ni gobe, saboda haka na yi maka magana. Domin duk abin da zai sa na haɗa yawu da kai ma ba son shi nake yi ba, matuƙar bai kama dole ba.." amsar da na jefo masa kenan a  ƙufule, shi ma bai bari na dire zancena ba ya ce "To ni gaskiya ban da kuɗin kaiki asibiti. Yanzu haka ko kuɗin da zan je aiki Boɗinga ban da su balle na kai ki asibiti". Shiru kawai na yi ina kallon shi sannan na ce "Ba ka da kuɗi ka ci kaza ɗazu?" "E, wannan daban, don ba ki san yadda aka yi na same ta ba. Amma gaskiya ban da kuɗin kai ki asibiti, wurin aikin ma da wuya idan zan je goben saboda ban da kuɗin mota..." "Ni ina da, kuma ina roƙon Ubangiji ya ƙara mini.." A harzuƙe na tari numfashin shi na yi maganar, sannan na wuce kan kujera na zauna ina nishi saboda zuciyata da ke ta bugawa da sauri da sauri. Raka ni da "Amin" ya yi sannan ya fice abin shi. 

      Kuka na shiga yi ina nazarin rayuwata ta baya da yanzu, da badaƙalar da aka sha farkon auren har zuwa yanzu ba tare da an gama ba. Tiryan-tiryan komai ya shiga dawo mini cikin kwanyar kai. Hawaye ya ɓalle mini tamkar burgaggen famfo mai bori, sai da na gaji da kukan don kaina sannan na miƙe na yi wanka na yi sallah. 


Rashin wayata da rashin jin motsin yarana kusa da ni, ya haifar mini da wata sabuwar damuwar da ta janyo mini Zazzaɓi. Nan take na fara jin sanyi na nemo paracetamol,  ƙwara biyu na afa na dunƙule ina rawar sanyi. Cikin ikon Allah mintuna a tsakani na fara jiɓi a daidai lokacin da na fara jin ihun murnar yarana, wanda hakan yake tabbar mini da alamun sun dawo. Farinciki fal raina na fara ƙoƙarin saukowa daga kan gadon da nufin tarbon su. Sai ga su sun shigo da gudu sun rungume ni suna faɗin "Oyoyo Mama" tsananin daɗi ya sa na maƙalƙale su duka su ukun ina faɗin "Sannun ku da zuwa". Ummu Salma babbar 'yata ta taɓa wuyana ta ce "Mama jikinki da zafi har yanzu ciwon kan kike ji?" Hawayen kuka ya zo mini na yi ƙoƙarin mayar da su ina faɗin "Ai na ji sauƙi, amma gobe zan je asibiti a duba ni..." "Mama duk na girma na zama babba, sai na gina miki ƙatuwar asibiti a cire miki ciwon kan nan ki huta" Abin da Haidar ya faɗa kenan yana share mini hawayen da ban san lokacin da suka zubo kan fuskata ba. Iman na kalla wadda ta yi tagumi tun da suka shigo ba ta ce komai ba tana kallona. Sanyin halinta da na sani ya sa na dafa kanta cikin ƙaunar uwa zuwa 'yarta na ce "Ke kuma me za ki yi mini idan kika girma". Sai da ta share hawayenta sannan ta ce "Zan saka ki farinciki ki daina kuka ba na son ganin hawsyenki..." Kukan da ta fashe da shi ya sa ni ma nawa ya ƙara ambaliya. Hannunta na riƙo cike da jarumta na goge hawayen da ke ta sauko mini kan fuska na ce "Ki daina kuka kin manta za ki zamo likitaa!?" Na ja kalmar ƙarshe cike da jan zaren wasa domin na tsayar da kukanta. Kai ta ɗaga mini alamun "e" Ina murmushin ƙarfin hali na ce "To ai da kin yi mini  allura cikin baki shi kenan ruwan hawayen zai ɗauke" cikin sauri ta rufe bakinta tana dariya ta ce "A baki kuma..?" Kafin na ba ta amsa Haidar ya ce "Ai Mama har cikin ido ana allura ko?" Tambayar shi ta ba ni dariya na ce "Har cikin kunne ma.." Gabaɗaya daga ni har su muka fashe da dariya. Cikin dariyar na kalli Ummu Salma na ce "Ki je ki dafa muku Indomie.." "Umma fa ta ba da abinci a kawo muku ke da Abbanmu. Mu ma ta ba mu namu ta ce mu zo da shi mu ci a nan" Annurin fuskata ya ɗauke a dalilin Abbansu da na ji ta ambata, saboda har ga Allah ba na son maganar Mukhtar da duk abin da ya shafe shi, har cikin zuciyata. 


Haɗe fuska na yi na ce "Oya ku je ku yi shirin sallar magrib ga ta can an fara kira. Kai kuma Haidar ka wuce masallaci kada ka bari a fara sallah ba ka fita gidan nan ba" Suka fice ɗakin cikin sauri na sauke ajiyar zuciya. Raina a jagule na sauko gadon na fito falo, kulolin Ummata da na hango saman table ɗin tsakiyar falona. Hakan ya sa na isa da sassarfa na fara buɗe babbar kulolin da ke gabana. Tuwon masara ne da miyar ganye sai ƙamshin man shanu ke tashi. Sai ɗaya kular da na buɗe na hango ɗanwake maƙil a ciki da man ja a leda tare da yajinsu a leda. Hakan ya tabbatar mini tuwon ne namu su ne da ɗanwake. Wuri na samu na zauna cikin tagumi ina nazarin har yaushe Umma za ta dawo daga rakiyar Mukhtar, duk da abin da yake yi mini ita har kullum girmansa take gani a idonta. 'Shin ta ya ya zan fahimtar da Umma illar ɗaure wa Mukhtar ƙugun da take yi? Kuma har zuwa yaushe zan fita daga wannan ƙangin rayuwar da nake ciki?'

No comments

Powered by Blogger.