Abokin Aikina Book 1 Page 27


ASHIRIN DA BAKWAI.*


         Da safe ban fita aiki ba har sai da na gyara zaman kujeruna, kasancewar falon babba ne na yi gefen ɗakina da su duka.

Sannan na sa aka kafa mini plasma TV ta a bango, daidai tsakiyar kujeruna. Saboda ba na son a zo yi wa amarya jere a nemi kawo mini rainin hankali, ko kuma shi ya faɗa mini abin da ba zan ji daɗi ba a samu matsala.

       Ranar sai ƙarfe sha ɗaya na je ma'aikatarmu, na duƙufa aiki sosai ba tare da na biye surutun Amina ba. Lokacin da aka tashi ma ban yi jinkirin komai ba na nufo gida, saboda tunanin yaran da ke raina. Domin fargabar da nake ciki a kan kada ya hana su yin girki kamar yadda ya yi jiya, cikin sa'a na taradda Ummu Salma kitchen tana aikin abincin. 

     Sannu da zuwan da suke yi mini kawai na amsa, sannan na yi wanka a gurguje na fito. Iman na ce ta zo ta raka ni mu je gidan Maman Taufiƙ. Haidar ya fara rigimar sai ya bi ni na ce da su kowa ya yi zamansa na fasa ba zan je ba.

       Abincin Ummu Salma ta kawo mana muka baje a tsakiyar kujerun muka fara ci muna hira. Mukhtar ya shigo da manyan ledodi a hannunsa ya yi ɗakin shi yana muƙu-muƙu, sai da ya fito sannan ya fara faɗin ina abincin shi. 

      Kallo ma bai ishe ni ba balle na tanka masa, Ummu Salma ce ta miƙe ta ɗauko masa kular abincin ta miƙa masa. Karɓa kawai ya yi ya nufi ɗakinsa, na bi bayansa da harara saboda haushin auren da ya jajiibo wa kansa nake ji. 


***

      Abu kamar wasa, cikin kwana biyu Mukhtar ya shiga fafutukar auren shi gadan-gadan. Domin kuwa na ji labarin ya kai wa amaryarsa lefe daidai gwargwadon ƙarfinsa. Mafarin na sani ma, yara ya shigo wa da lemuna ya bai wa kowa gora ɗaya, sannan ya ba su biskuit guda huɗu ya ce a kawo mini. 

       Muna falo ni da su muna kallo Sajida ta kira ni a waya, cikin muryar damuwa ta ce da ni, "Aunty ke ya ba ki kayan?" 

       "Waɗanni irin kaya Sajida?"

      Tambayar da na mayar mata kenan don ban gane inda zancenta ya dosa ba, "Kayan faɗar kishiya mana, saboda na ga ya yi wa amaryar lefe ma sha Allah tamkar wata budurwa." 

      Ƙirjina na ji ya buga dam-dam!  Sai da na dafe saitin zuciyata saboda luguden da take yi mini, sannan na yi murmushin ƙarfin hali na ce da ita, 

"Ma sha Allah! Ki ce da ke aka kai lefen? To Allah ya tabbatar da alherin da ke ciki."

      "Amin Aunty!  E, da ni aka je. Amma ke kala nawa ya ba ki? Don na ga ita kala goma sha biyu ne bayan tarkacen da ke ciki." 

        "Allah ya sa ta kashe lafiya. Sai dai ni bai ba ni komai ba Sajida, amma kuma hakan ba zai hana ni saka sabuwar sutura a ranar bikin ba."

      Ajiyar zuciya ta fara saukewa sannan ta ce, "Allah dai ya kyauta Aunty. Wallahi idan kika ga matar sai haushi ya nemi kashe ki. Ni na rasa me ya gani a jikinta yake wannan rawar jikin auren. Ki yi haƙuri Aunty in Sha Allah babu inda auren nan zai je, don kina zaune za ki ga haƙƙinki ya fita a kan duk wanda ya zalunce ki."

        "Kada ki damu Sajida, Allah yana tare da ni koyaushe. Na gode sosai da ƙaunar da kike nuna mini a kowane lokaci."


      Daga haka muka yi sallama ta kashe wayar, shiru na yi ina nazarin maganganunta.

      'Waton dai tukuicin kai lefen ne ya ba mu muka laƙume ba tare da na sani ba.'

      Haka kawai na tsinci kaina cikin damuwar da ta janyo mini zubar ruwan hawaye, waɗanda ban shirya wa zuwan su ba. 


'Ashe ma Bazawara ce!'


      Zancen da na yi kenan a zuciyata ina kuma maimatawa a cikin raina.

      Murmushin takaici na yi tare da jin haushin Ummata, wadda ta janyo mini ganin irin wannan ranar baƙincikin a gidan Mukhtar. Don da a ce ta bar ni na yi abin da nake so, da tuni ba wannan zancen ake yi ba. Da rayuwata ta yi farin da zan hango haskenta gaba da bayana.


     "Babu komai akwai Allah!" 


      Maganar da na yi kenan a zuci ba tare da na san ta fito fili ba. Gaba su Ummu Salma suka saka ni da tambayoyi.

"Me ya faru Mama?"

"Me Sajidar ta faɗa ne?"

      "Babu komai ku jira na je gidan Maman Taufiƙ na dawo yanzun nan!"

       Daga haka na koma ɗaki na janyo hijabina, waya a kunnena na fice muna magana da Firdausi.


 "E da gaske ne mana! Satin nan ma za a kawo amaryar." 

       Amsar tambayar da ta yi mini kenan daga bakina, kafin ta gama jimami ta samu sukunin cewa, 

       "Anya Mukhtar kansa ɗaya kuwa?" 


  Murmushi na yi mai sauti sannan na ce da ita,

  "Me kika gani?"

         "Yo idan ba don Allah yana son tona masa asiri ba, me zai sa ya rikito aure yanzu? Bayan ke ɗin ma bai iya sauke haƙƙinki ba amma yake neman ɗebo wa kansa masifa."

      "Ya ji ya gani ne! Kuma kika sani ko ya samu lafiya ni ce bai bari na gane ba?"

       "Shi dai ya sani, namu kallo ne kawai! Amma don Allah kada ki nuna masa komai a kan auren nan. Ki bar shi da kan shi zai yi regretting ɗin me ya sa ya aikata."

        "Na bar shi ai! Tuni na zamo 'yar kallo."


    Daga haka muka yi sallama na shige gidan Maman Taufiƙ zuciyata babu daɗi, don daman can ƙofar gidan na tsaya saboda ba na so na shiga gidan ba mu gama maganar ba.

          Zama na yi a kan ɗaya daga cikin kujerun falonta, bayan ta amsa mini sallama ta yi mini jagora har cikin falon, sannan ta fice. Lemun Coca-Cola a ɗan ƙaramin tire ta ajiye gabana, sannan ta zauna tana faɗin,

         "Oyoyo Maman Haidar! Yau na so shiga gidanki Amini ya kawo mini aikin kajin da ya hana ni fitar."

          "Ni ma yanzu wani uzuri ya shigo da ni, wurin mai hajarki nake so ki kai ni na zaɓo kaya. Sannan ki yi mini jagora wurin mai ɗinkinki ya rantsama mini ɗinki mai kyau, irin na gani na faɗa da tsokanar magana."

        Da dariya na ƙare maganar saboda ƙoƙarin kore damuwar da nake ciki a kan fuskata. 

"Wai don Allah da gaske auren nan zai yi?"

          Tambayar da ta yi mini kenan bayan ta shiga natsuwarta.

 "Tun ranar ai na faɗa miki, yanzu haka a cikin satin nan za a yi auren idan Allah ya ara mana numfashi."


         "Hmmmmm! Ikon Allah!"


Abin da ta faɗa kenan sannan ta janyo wayarta ta yi kira, mintuna a tsakani bayan an ɗauki wayar ta ce, 

            "Hajiya Ruƙayya Wada, kaya nake so ki turo mini yanzu na zaɓa. Ki haɗo da sarƙoƙi da takalma half shoe's masu kyau kalar ya yi." 

      Tana ƙare maganar ta ajiye wayar tare da rungume hannu ta ce,

      "Jarumtarki tana burge ni Maman Haidar. Ina ma zan iya kwatanta ko da rabinta idan Amini ya tashi aure? Amma har ga Allah na san ba zan iya ba."


          "Za ki iya! Matuƙar kika saka kanki."


    Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi sannan ta ce, "Mu bar maganar! Wane shiri kika yi wa kanki a matsayinki na Uwargida?"


      "Shiri kuma?" 

      "E"  Ta ba ni amsa, cikin rashin sanin inda zancenta ya dosa na ce, 

     "Wane iri fa?"

             "Gyaran babbar hedkwatar mana! Don ke ma kin san ba zai yiyu amarya ta zo ta same ki a haka babu wani canji ba. Saboda ita kanta sai ta yi gyara sosai kafin ta shigo, to ke ma me zai hana ki yi gyaran da za ki mayar da tsohuwar shimfiɗarki sabuwa dal?"


        "Zan yi! Yanzu haka ma ina kan yi."

Amsar da na ba ta kenan, don ba na so ta fara nuna mini ban iya komai ba a kan tattalin miji kamar yadda ta saba. 

       "Kin yi farar dabara, bari na ƙaro miki wasu zafafan da aka kawo mini daga Maiduguri jiya. Don mazan nan idan babu sabon service kullum idanuwansu suna kan leƙe-leƙen wasu matan. Amma idan kina gyara jikinki komai cif-cif, da wuya su yi miki kallon raini balle su nemi ɗauko miki wata masifar a waje."


       Ta miƙe ta kawo mini kayan mata kala-kala, tun daga kan shu'umar humra har wani ɗan matsin da ta tabbatar mini yana mayar da tsohuwa yarinya. Sannan turaren tsugunno da na jiki, bayan tsimin da ƙamshinsa kaɗai zai sa mutum ya ji sha'awar shan sa. 

        Leda na zuba su duka, na ce da ita sai na je gida zan sha, ta matsa mini na sha tsimin a nan saboda ya yi saurin kama jikina. Domin akwai buƙatar na sha shi kamar sau uku kafin bikin, domin ya haɗe mini jiki ta yadda idan na karɓi girki zai rasa bambance wace ce amarya a tsakaninmu. 

         Kasa musa mata na yi, saboda ba na so ta gano ba na so, kaɗan na kurɓa na rufe gorar swan ɗin da ta cika mini ita taf! Hira muka ci gaba da yi a kan amfanin kayan mayen, tare da yi mini bayanin yadda suke yi mata aiki sosai har aka kawo kayan.

         Kala biyu na zaɓa masu kyau shadda da lesi, sannan na zaɓar wa su Ummu Salma atamfa ɗaya da shadda gizna, wadda ba ta kai kuɗin tawa ba yadi bakwai su uku. Saboda na san estimate ɗin abin da suke ci don na fara koyon ɗinki tun kafin na yi aure. Yanzu ma ina da experience sosai a kan abin da ya shafi ɗinkin duk da ba na yin sa.

          Gyale, takalmi da jaka na samu mahaɗin shaddar da lesin. Sannan na zaɓar mana sarƙoƙi nawa set biyu su Ummu Salma ɗaiɗaya. Na ɗaukar wa Haidar 'yan kanti ɗaya shi ma ya yi kala biyu kamar yadda su Ummu Salma za su yi. Maman Taufiƙ ta kira mai kayan aka haɗa lissafin kuɗin dubu saba'in da uku cif. Shiru na yi ina nazarin kuɗin a raina, saboda ba na so na yi abin da zai ƙure  mini maneji. 

        Kamar Maman Taufiƙ ta fahimce ni ta ce, "Kayanta akwai tsada, amma kuma quality ne za ki ji daɗinsu sosai."


       "A ido ma kayan kowa ya gani zai san sun ci kuɗinsu. Amma akwai uzurorin da ke gabana, zan rage kala ɗaiɗaya mu ji nawa kudiyn za su kama."

          "Kada ki rage ki bar su kawai, ba ta da matsala duk lokacin da kika samu dama da ƙire-ƙire ma za ki biya ta ba sai duka ba."

          "Gaskiya na ji daɗi Maman Taufiƙ! Saboda a yanzu samun masu haƙurin bashi 'yan kaɗan ne a wannan lokacin da muke ciki."

          Ta yi murmushi mai sauti sannan ta ce, "Ai Maman Marwan ba ta da matsala ko kaɗan, kuma ta iya hulɗa da mutane sosai. Duk masu sayen kayanta sun san da hakan, shi ya sa ba na iya sayen kaya a wurin kowa sai wurinta. Ga quality, ga sauƙin kai, kuma babu matsi balle a dame ka da aiken kawo kuɗi wata ya ƙare. Tana ɗaga ƙafa musamman idan ta san kana cikin masu biya babu taurin bashi."

         "Ai kuwa in Sha Allah za ta same ni mai cika alƙawari, don ni ma ba na son bashi sai ta kama dole. Ki ce ta turo account yanzu na tura mata 20k ɗin da nake da ita ƙasa, idan aka yi biya zan ƙara mata wani abu in Sha Allah!"


       A haka muka kai ƙarshe ta turo da account na yi mata transfer, sannan Maman Taufiƙ ta kira mini mai ɗinkinta ya zo muka ba shi kayan, Bayan mun zaɓi wanda zai yi mana a wayarsa. Shi ma na ba shi 10k deposit ta account ɗinsa, ya tafi bayan ya yi mana alƙawarin zai haɗa ɗinkin a cikin kwana uku.

       Sauran kayan na saka a leda na yi gida, zuciyata cike da nishaɗin. Ko babu komai zan yi wa Mukhtar barazana tare da gayyar danginsa da zugar mutanen amarya.

       Yaran ma da na sanar da su suka shiga tsalle suna murnar sun yi sababbin kaya. Ummu Salma kaɗai ce na hango damuwa a kan fuskarta, hakan ya sa na tattara kayan na mayar a leda na bai wa Iman ta kai ɗakinmu. Sannan na zaunar da ita na gyara zamana na ce, 

        "Damuwar me ce na gani a kan fuskarki?"

        Hawaye ta goge sannan ta ce, "Wai da gaske Abbanmu aure zai yi?"


        "E gaske ne! Me ya faru?"


    Amsar da na ba ta kenan ina haɗe fuska, domin ba na so ta ɗora wa kanta takaicin auren. Ta hana kanta sukuni a banza a kan abin da ko ni ban da ikon hanawa balle ita. 


        "Wace ce zai aura?"


      "Ko ma wace ce, idan ta zo ai za mu gan ta. Don haka idan ma damuwa kike yi a kan auren nan da Abbanku zai yi ki daina tun wuri, saboda babu wanda ya isa ya sauya abin da Allah ya ƙaddara. Shi ya ke sa a yi, kuma shi yake hanawa, idan ya nufa babu wata damuwar da zai sauya abin da aka rubuta. Idan kuma bai ƙaddara ba, duk yadda aka kai ƙololuwar son abin sai an bar shi dole."


       "To Allah ya sa tana da kirki."


        "Ko tsiya take yawo a jikinta babu abin da ya shalle mu, don ba a kanmu za ta zauna ba."

            Amsar da na ba ta kenan raina a ɓace, saboda maganganunta sun dawo mini da jin zafin auren sabo. Cikin tsananin ɓacin rai na fara nuna su da hannu na ce, 

        "Duk wanda ya yi gangancin shiga shirgin amaryar nan, sai na saɓa masa. Ku tsaya inda Allah ya ajiye ku, hakan sai ya fi mini alheri da ku shiga hurumin da ba naku ba. Sannan ku yi nesa da duk abin da zai sa a ga laifinku, don ta wannan hanyar ne kawai za mu tattara komatsan matsalar duka mu wurgar gefe, domin a zauna lafiya mu huta da hayaniya."

        Yanayin fuskokinsu ya tabbatar mini da maganganuna da kashedin da na yi musu, sun shiga kansu da kyau sun zauna. Na miƙe da ledar kayan da Maman Taufiƙ ta ba ni na yi ɗaki, zuciyata sai zafi take yi mini a kan tsananin kishin auren da nake ji a raina.

        Ina ɗakin na jiyo sallamar Taufiƙ yana faɗin,

     "Ku bai wa Mamarku in ji Mamata."


        Haidar ya shigo da leda baƙa ya miƙo mini, tun kafin na karɓa na ji ƙamshin naman kaji. Na karɓa na ce ya yi masa godiya, ya ce da ni ai ya wuce, na buɗe ledar na ɗauki yanka ɗaya na miƙa masa sauran na ce su je su raba.

        Duk ƙaunata da naman kaji, haka na ajiye shi a kan bed side na kwanta ina ta ƙuncin rai. Saboda tunanin lefen da ya yi bai faɗa mini ba balle ya nuna mini na gani, sannan ni bai ba ni ko falle ɗaya ba balle na rage takaicin da yake ƙoƙarin cusa mini. 

           Wayata da ke ruri ta katse mini tunanin da nake yi, da hanzari na ɗauka ina sauraron abin da Ummata take cewa, 

         "Yanzu Zaituna Mukhtar zai yi aure amma ba ki sanar da mu ba?"


       "Ki yi haƙuri!"


    Abin da na iya cewa kenan bayan na sauke ajiyar zuciya mai fito da feshin iska 'Huuuuuu!'

           "Shi kenan! Allah ya ba ku zaman lafiya. Zuwa gobe zan aiko miki da sababbin kujeru, idan an zo za a ɗauki naki a kawo mini."


         "Na gode sosai Allah ya ƙara buɗi."


Iya maganar da na yi kenan ta kashe wayar, hawaye ya dinga fareti daga kwarmin idona zuwa gefe da gefen fuskata. Motsin shigowar yaran ya sa na yi jarumtar gogewa tare da gyara kwanciyata, don ba na so su gano damuwar da nake ciki balle hakan ya saka su rashin walwala.

Kishiya akwai zafi. Amma idan an saka haƙuri da juriya komai zai zamo kamar ba komai ba.🥲


No comments

Powered by Blogger.