Abokin Aikina Book 1 Page 25

 


*ASHIRIN DA BIYAR.*


        _Hankalina a tashe na miƙe da sassarfa na isa toilet na duƙa. Sai ga jini ya ɓalle mini mai uban kauri. Na jima tsugunne ina kallon ikon Allah, sannan na miƙe na fara wanke

jikina na gyara wurin. Jikina babu kuzari na fito ina layi, domin na sare da cewa jinin jikina ne ya tsiyaye kuma mutuwa zan yi. Mukhtar na tayar daga baccin da yake shararawa har da minshari, na nuna masa jinin da ya bi ƙafafuwana zuwa toile cikin sanyin murya na ce da shi,_

         "Mutuwa zan yi."


    "Ban gane ba! Mutuwa kuma me ya faru yanzu?"


       _Sai da na goge hawayen da ke gangaro mini a kan fuska sannan na ce da shi,_

      "Jinina ya gama tsiyayewa, don Allah ka yafe mini ka ce ni ma na yafe wa kowa."

          _Ina ƙare maganar na miƙe na fara ƙoƙarin gyara ɗakin, shiru ya yi yana ta kallona. Sannan ya tashi ya fice daga ɗakin, ko da ya dawo har na gama gyaran har na canza kaya, na koma falo na kwanta kan kujera. Ya shigo falon tare da wanda ya ba mu maganin idanuwansu a kaina._

       _Tambaya ta ya fara yi me nake ji, na yi masa bayanin jinin da na zubar da rashin ƙarfin da nake jin jikina. Tare suka fice ya ce na bari a kawo mini magunguna, da na sha zan ji sauƙi, shiru na yi kawai ina goge hawayena da ke bin gefen fuskata. Saboda na yi da-na-sanin biye musu na zubar da cikina, don da na mutu sanadin hakan ni ce da laifin ba su ba. Kuma ni Allah zai ƙona domin babu ɗa'a ga abokin halitta a wurin saɓa wa mahalacci._


     'Me ma ya sa na amince wai?'


     _Tambayar da na jefi kaina da ita kenan a zuciya, na yi ta saƙe-saƙen illar zubar da ciki da haɗarin da ke cikin shi. Mukhtar ya dawo mini da magunguna na sha tare da maltina da madara, sannan ya ɗauki Ummu Salma ya fice da ita ban san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba._

      _Bayan 'yan kwanaki ina shan magungunan da abubuwan da ke ƙara jini, cikin ikon Allah na ji sauƙi garas kamar ban taɓa ciwo ba. Mukhtar ya sanar da ni za a yi mini allurar planning saboda gudun na koma samun wani cikin kafin a yaye Ummu Salma._

         _Ban ja da tsauri ba na amince, saboda ko ni ba na so na samu wani cikin a lokacin. Duba da yadda na sha wuyar cikin da zubar da shi, kuma alƙawarin na yi wa kaina ko sau dubu zan haifu ba zan sake zubar da cikina ba._


****

      _A lokacin da na yaye Ummu Salma ta iya tafiya ko'ina tana zuwa da gudu, sannan da bakinta ta iya faɗin Mama da Baba har ma da wasu sunayen 'yan gidan tana kamawa. Jamila ma ta iya sunanta raɗam kamar yadda ta laƙaba mata kiran "Jayiya."_  

      _Watarana da yammaci na shiga gidan su Mukhtar, na bar Ummu Salma wurin Jamila da ke yi mini shara. Ana tsaka da hira a ɗakin matar Baban Mukhtar, sai ga ƙanen shi ya zo yana sanar da ni ya dawo. Na miƙe zan fito wata ƙanwar shi ta ce da ni,_

     "Da kin yi zamanki tun da Jamila tana can sai ta tarbar miki shi."

        _Murmushi kawai na yi na fito, saboda surutun da duk suke yi a kan aikin da Jamilar take taya ni ya dawo kunnena. Kuma na san gatse ne ta yi mini saboda haushin jan ta jikina da nake yi. Ina ƙoƙarin shiga gidan na haɗu da Ummu Salma za ta fito da Cheezee a hannu tana nuna mini tare da faɗin,_ 

  

    "Abba! Jayiya!"


      _Cikin sauri na faɗa gidan, sai ga shi ya fito daga kitchen ɗina da leda a hannun shi. Murmushin rashin gaskiya ya fara yi mini sannan ya shige ɗaki, Da mamaki fal raina na tsaya bakin ƙofar kitchen ɗin, ina kallon Jamila da ke ta faman gyara wa kuloli zama._

      _Shiru na yi na rasa me zan ce, don jikina ya ba ni akwai wata a ƙasa. Amma ban ga abin da zai sa na tabbatar da abin da nake zargi ba. Na bar wurin ba tare da na ce da ita komai ba, zuciyata tana ƙuna na nufi murhuna da ke a tsakar gidan na fara tuƙa tuwo. Ta gefen ido na hango Jamila ta fice gidan sum-sum! Sai ga shi ya fito daga ɗaki yana shan lemu ya yi tsaye kaina. Ban kalle shi ba balle na tanka shi, da ya gaji da tsayuwar shi ya ce da ni,_

        "Idan zuwan yarinyar nan zai kawo mana matsala, kawai ta daina zuwa gidan nan gaskiya."


     "Matsalarku ce kai da ita, don ni ba ka ji na ce komai ba balle ka zo da wannan zance."


     "Yanayinki ya nuna abin da kike nufi da ganin na fito kitchen ɗin, to wuƙa na ɗauko domin na yanka lemun da na zo da shi. Ashe ma an yanka shi tun daga can ban sani ba sai da na buɗe na gani."


     "Haka kam!" 


       _Amsar da na ba shi kenan, ina tuƙa tuwon da sauri saboda tsabar gaskiyar da ta yi mini yawa. Daren ranar haka muka kwana ba tare da na bi ta kan shi ba, don shi ma a lokacin ya daina ƙulafucin da yake yi mini wurin neman haƙƙinsa._

     _An kwana biyu Jamila ba ta zo gidan ba, na aika aka kira mini ita muka shiga ɗaki, fuskata a haɗe na ce da ita,_


       "Me ya sa kika daina zuwa gidan nan?"


   "Babu komai."


_Abin da ta faɗa kenan tana wasa da gefen hujabinta, na sauke ajiyar zuciya sannan na kira sunanta cikin sanyin murya na ce,_  

       "Jamila ki sanar da ni abin da ke tsakaninki da Abban Ummu Salma. Saboda jikina ya ba ni akwai wani abu da kuke ƙoƙarin ɓoye mini ke da shi. Bayan ni ina yi miki kallon ƙanwata kuma ina zaune da ke tsakani da Allah kuma da zuciya ɗaya, Allah ya sani duk abin da zai same ki wanda ba alheri ba ba na fatar shi. Sannan ina murna da farincikinki kowane iri ne saboda matsayin da nake jin ki a raina tamkar amana kike a wurina, don akwai gidaje da yawa cikin unguwar nan ba ki je ko'ina ba sai gidan nan kuma wurina. Ki faɗa mini idan akwai abin da yake yi miki wanda bai dace ba sai na sani, domin na yi wa abin tufƙar hanci tun kafin ya yi tsaurin da ba za a iya shawo kan matsalar ba."


     _Shiru ta yi mini kafin ta fara rantsuwa a kan babu abin da ke tsakaninsu, kuma ita bai taɓa yi mata komai wanda bai dace ba. Ganin ba za ta faɗa ba ya sa na sallame ta ta yi gida. Amma zuciyata ta kasa natsuwa da su, kuma ko kaɗan ba na so na ci zarafinta a kan abin da ba ni da tabbas a kan shi._

      _Ta dawo da zuwanta gidan amma ba kullum kamar yadda ta saba ba, ni ma ba na wani sake mata fuska sai dai ta yi ta wasa da Ummu Salma, ko kuma ta goya ta har ta yi bacci. A cikin lokacin ne ta fara amaye-amaye, don duk ta zo gidan kafin ta tafi sai ta yi aman da ya kai biyu zuwa uku._

      _Tun ba na bi ta kai har na fara yi mata magana, a kan idan ba ta da lafiya ta je asibiti a duba ta ya fi zama da ciwo kullum. Ban san ya aka yi ba wata safiya ta zo tana sanar da ni za su je Katsina, wurin dangin Mahaifiyarta. Na yi mata fatan a dawo lafiya da ƙyar ta bar gidan Ummu Salma tana kukan sai ta fita da ita._

       _Sun yi wata ɗaya da kwanaki kafin su dawo, lokacin da ta dawo na gan ta fess da ita alamun ziyarar da suka je ta amshe ta. Sai dai tun zuwan da ta yi sau ɗaya ba ta sake zuwa wurina ba, sai da aka kwashi kwanaki sannan ta zo gidan, muna tsaka da gaisawa Kakarta ta shigo da faɗa tun a soron gidan._


     "Ina take baƙar 'yar iska munafuka, wadda ba ta san ciwon kanta ba, wallahi muddin ba ki daina zuwa gidan nan ba,  sai an sabauta miki rayuwa a kan baƙin kwaɗayi irin naku ke da uwarki."


     _Gabaɗaya muka fito tsakar gidan, Kakar ta ci gaba da zagin ta tana ƙoƙarin kai mata duka da wata ƙatuwar sandar da ke hannunta. Zagayen gidan suka fara yi kafin ta yi nasarar kora ta tana ci gaba da bala'i, ta inda take shiga ba tan take fita ba har ta fice ba ta daina masifa ba._

      _Shiru kawai na yi ina tunanin abin da maganganunta suke nufi, saboda iya sanina ko ƙannen Mukhtar maza ba su zuwa gidan su zauna. Balle na ce maza suke zama gidan shi ya sa Kakarta take gudun a lalace ta._

      _Duk da korar da Kakar take yi mata bai hana ta zuwa jefi-jefi muna gaisawa ba, amma ni ma da kaina na zaunar da ita na nuna mata cewa; Ta daina zuwa kamar yadda Kakarta ta gindaya mata doka, ni kuma duk abin da Allah ya hore mini ko ba ta zo ba zan aika mata. Saboda har raina ina jin daɗin yadda take ƙaunar Ummu Salma, amma tun da abin ya zo da haka dole na yi ƙoƙarin ɗora ta a kan abin da Kakarta take so. Da haka ta daina zuwa sai ranar da kakar ba ta nan ta leƙo mu gaisa tsaitsaye, sannan ta miƙa wa Ummu Salma abin da ta zo mata da shi ta fice._


      _Wata safiya bayan Mukhtar ya fita Mamarta ta zo gidan, mun gaisa a mutumce ta ce da ni wurina ta zo. Zama na gyara ina murmushi ta ce da ni,_ 

      "Na ji duk abin da Inna Huse ta yi, kuma Jamila ta sanar da ni yadda kuka yi da ita. Ubangiji ya saka miki da alheri Allah ya bar zumunci."

 

       _Cike da jin daɗi nake ta faɗin amin amin. Sannan ta yi shiru na ɗan lokacin kafin ta sake cewa,_

       "Don Allah akwai wani taimakon da nake so ki yi mana Maman Salma."

      "Kamar wane fa?"

    "Yawwa! Ai kin san Nura mai son Jamila ko? To zancen auren ne ya ƙi fitowa da gaske sai ja baya yake yi. Ga mutane suna son shigowa amma shi ya ƙi gaba ya ƙi yin baya, don haka nake so ki kira mini shi don Allah ki yi masa magana a kan matsalar. Saboda na gaji da ganin ta a gabana, idan bai tashi ba sai a tsayar da wanda ya shirya, tun da abin na shi ya zama rainin hankali da shiririta."


       _Ban yi tunanin komai ba na karɓi lambarsa gare ta na danna masa kira. Babu wani jinkiri ya ɗauka tare da yin sallama. Na amsa masa sannan na sanar da shi wace ce ni, tare da maƙasudin da ya sa na kira shi a fakaice ba tare da na nuna masa Mamar Jamila ce ta saka ni ba. Buɗar bakin shi ya ce da ni,_


      "E kam! Idan ma ban shirya ba ai sai ki yi mata auren gida a matsayinki na uwar ɗakinta. Don haka idan kun matsu ina jiran goron ɗaurin auren domin ya ƙarasa ɓarnar da ya aikata."


     _Sororo na yi da waya a hannu, domin tun da ya gama faɗin maganar cikin ɗaga murya ya katse kiran, da sanyin jiki na sauke wayar daga kunnena. Sannan na yi mata bayanin abin da ya ce ba tare da na gano inda zancen shi ya dosa ba. Jikinta yana rawa ta miƙe tana yi mini godiya ta fice gidan, yanayinta da maganganun Nuran suka ƙara cukurkuɗe mini kwanya._


      'Shin me yake nufi da jefa mini wannan magana? Kuma me ya sa Mamar Jamila ta shiga tashin hankalin da na gani kwance a kan fuskarta.'


     _Tambayoyin da na yi wa kaina kenan, waɗanda ban san amsar su ba sai daga baya, a lokacin da na ji abin da ya hasko mini ma'anarsu da inda suka dosa._


Ni dai kam ban gane komai ba😼 wanda ya sani ya sanar da ni plss🙁

No comments

Powered by Blogger.