Abokin Aikina Book 1 Page 22

 


*ASHIRIN DA BIYU.*


        Dariya na sha sosai har ta nemi ƙulle mini ciki, saboda maganganun Maman Taufiƙ sun saka ni dariya ba tare da na shirya ba. Fuskarta na kalla bayan na gama dariyar, hadarin da fuskar ta ɗoro tare da ƙwafar da na ga ta yi, alamunta ya nuna mini har lokacin kishin matar bai daina cizon ranta ba.

        "To ke Maman Taufiƙ, ai ita ce ke son shi idan na fahimci labarin da kyau. Da kin bari an yi auren, wataƙila da yanzu har mu maƙotanki mun je hajji. Saboda bauta ce kawai za ta zo yi miki tun da kin fi ta power a wurin Baban Taufiƙ." 

        "Hmmmmm! Ba za ki gane ba!" 

        Zancen da ta yi kenan tana haɗe fuska tamkar ta yi kuka, kafin ta cire tagumin da ta rafka hannu bibbiyu ta sake cewa, 

         "Kin san me? Ko da za ta kwanta ƙasa na dinga taka ta da ƙafafuwana saboda biyayya, ba zan taɓa cire takaicin ta a raina ba. Wai ko ki san yadda nake kishin Amini kuwa? Ke ni fa da dai a ce ya haɗa ni sharing ɗinsa da wata, gara kawai ni na haƙura na bar wa kowace ce shi. Na fi son haka da a ce na zauna baƙinciki ya kashe ni."

      "Ba fa za ki mutu ba! Matuƙar ba ke ce kika ƙwallafa wa kanki hakan ba. Saboda duk abin da kika gani daman can muƙaddari ne daga Allah, don haka ki daina zafafa kishinki gudun ki saka kanki matsala a banza."

     Na yi maganar cike da burin saka mata ƙwarin gwiwa a zuciya, sai dai ko kaɗan zancen bai yi tasiri ba. Domin idonta a rufe ta ce da ni,

      "Ni fa komai za ki faɗa in dai a kan zancen kishiya ne, to ba zan fahimta ba balle na gane.  Don haka mu bar zancen kawai raina suya yake yi sosai wallahi." 

        Shiru ya ratsa tsakani sannan na sauke  ajiyar zuciya, bayan na dawo daga zuzzurfan tunanin da na lula, a kan tashin hankalin da za ta shiga a lokacin da ta ji Baban Taufiƙ yana neman aure, domin da idanuwana na gan shi da wata bazawara a bayan layinmu suna taɗi.   

       Saboda kusa da gidan su bazawarar nake zuwa kitso, da tunani fal raina na shiga gidan a lokacin, bayan zancen zucin da nake yi. Ina ta jefa wa kaina tambayoyin da ba amsa, a kan miye haɗin shi da ita? Duk da yanayinsu ya bayyana mini zahirin abin da ya haɗa sun. Amma ban gasgata ba sai lokacin da bazawarar ta shigo gidan ana tsaka da yi mini kitso, mai kitson tana 'yar dariya ta ce da ita,

     'Har ya tafi?' Ita ko bakinta har kunne ta zauna tana faɗin, 

      'Ya tafi! Ai mutumin ya san kansa, sosai yake da qualitys ɗin da nake so, kuma nake fatar samun su a wurin namijin da nake muradin ya zama mijina. Yanzu haka duk da ba mu jima tare ba, amma ya nuna mini shi ba ya son a ja lokaci. Idan na shirya wata biyu masu zuwa a yi komai a gama.'

     'Caɓji! Lalle wannan da zafinsa ya zo.'

       

      Haka na yi ta tuno hirar bazawarar da mai kitsona, wadda har suka ci suka cinye ban ce da su ƙanzil ba. Saboda ba na so na katse musu zancen, sannan kuma ba zan iya shiga sabgar da ba a kasa ta da ni ba.

      'Yanzu idan ta ji wannan batun ya za ta yi?'

      Tambayar da na jefi kaina da ita kenan, wadda ban samu amsarta a zuciyata ba na fara jiyo sallamar da su Ummu Salma suke ta rafkawa.

       Tare muka amsa musu ni da Maman Taufiƙ, sai da aka ba su umurni sannan suka shigo. Gayar da ita suka fara yi ni ma suka gaishe ni, na miƙa musu makulli  suka fice suna faɗin sai na zo.

       Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce da ita, "Wallahi kin sa jikina ya yi sanyi Maman Taufiƙ. Saboda har raina, ba na jin daɗin zafin kishin nan naki, da ina da iko da na rage miki shi ko da kaɗan ne. Domin ina jin tsoron abin da zai faru a lokacin da ƙaddarar aure ta haɗa Baban Taufiƙ da wata."

         "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Don girman Allah ki daina ambatar wannan magana, kada tsautsayi ya sa 'yan amin su amsa ki janyo mini masifa. To idan ma wannan ne in Sha Allah babu shi babu aure nan gaba, saboda ni kaɗai na ishe shi rayuwar duniya, kuma ni kaɗai yake da buri zama da ni. Baya hangen kowace mace balle ya yi mata kallon daraja, saboda Allah ya karɓi addu'ar da nake yi masa koyaushe. A kan duk matan duniya, fuskarsu ta koma ta akuyoyi a idonsa, balle ya ga kyawunsu ya ƙyasa ya ɗauko mini jangwam!"

           "Hmmm! Kin fi ƙarfina Maman Taufiƙ! Ni zan tafi don babu amfanin duk wata maganar da zan ƙara yi a kan hakan. Saboda kin fi ƙarfina, amma duk da haka, na yi alƙawarin zan dinga yi miki addu'a a kan wannan kishin balbal, domin ina da burin Allah ya rage miki shi ki samu sukunin zuciya ko don ki ji daɗin fuskantar rayuwa."

         Zancen da na yi mata kenan a lokacin da na miƙe, fuskarta a haɗe ta rako ni tana faɗin, "Ban ji daɗin wannan zuwan ba, domin kin fama mini mikin da na daɗe ina jinyar zuciyata kafin ya warke."

          "Kwantar da hankalinki, in Sha Allah sai kin daɗe ba ki gan ni cikin gidan nan ba. Sai dai kuma hakan ba shi zai hana ni yi miki fatan shiriya daga wannan azababben kishin naki ba."

       Ina gama faɗin hakan na fice gidan, ta raka ni da faɗin, "Kishi halas ne! Ke da ba kya yi kuma ai kin hutar da kanki daga ladar da ake samu."


        Dariya na ƙumshe gudun ta ga damata, sai da na shiga gida sannan na tuntsure da dariyar tamkar wata zautacciya, 'Waton shi ma zazzafan kishin miji ibada ne da ake samun lada a ciki idan an yi?' Tambayar da na yi wa kaina kenan ina dariya. 

        "Wallahi sai dai kada na samu wannan lada, da dai a ce na yi kishin Mukhtar irin haka. Cabɗijam! Da sake!"

      Maganar da na yi kenan a fili lokacin da nake shiga falon, kiran sallar magrib da na ji an fara yi ya sa na ce da yaran,

 "Oya a tashi a yi sallah."

          Sannan na shige ɗakina na faɗa toilet. Har na gama sallah tunanin hira ta da Maman Taufiƙ nake yi, ban tashi daga kan sallayar ba sai da aka yi Isha. Na daɗe ina yi wa Maman Taufiƙ addu'a tamkar damuwarta ce kaɗai abin da yake damu na. 

     wayata na ɗauka na fito falo inda su Ummu Salma, tare muka ci abinci da su ina duba saƙonnin da ya tarar mini. Waɗanda suke buƙatar amsa ta dole, saƙon MD na fara buɗewa raina  a haɗe tamkar yana gabana. 

        'Na gamsu da hangen nesanki. Kuma in sha Allah na janye ƙarar daga yau. Na gode sosai!'

        

     Mere na yi kaɗan sannan na tura masa 'Ana tare!'  

          Daga haka ban sake bi ta kan shi ba duk da yana online a lokacin. Bugun da ƙirjina yake yi, ya sa na bar WhatsApp na koma facebook. Saboda a duk lokacin da na hango sanarwar da ake yi mini a kan yana online, sai na ji gabana ya ƙire ya faɗi dam-dam!

       

      Bacci ya ci idona, ban san lokacin da Mukhtar ya dawo gidan ba, sai da safiya ta waye muna shirin fita. Sannan na hango shi ya nufo ɗakin su Ummu Salma ya buɗe da makulli ya shiga, jim kaɗan sai ga wani garjejen ƙato ya shigo da bokitin fenti biyu a hannunsa ya shige ɗakin. Mintuna kaɗan wani ya ƙara shigowa da wasu bokitan ya shige.

       Raina ya fara turirin baƙinciki, saboda haushin shigowar mutunen ba tare da Mukhtar ya sanar da ni ba, domin a tunanina ko ba gidan aure ba ne, yana da kyau a sanar wa masu gida wasu gardawa za su shigo, domin su kimtsa. A matsayin su na mata ko ba su da aure, tun da ba maza ne danginsu ba balle a ce duk ɗaya ne.

        Zuciyata ta zo wuya, na dinga ji kamar na shiga na shaƙe wuyan Mukhtar a gaban mutanen, kuma na gasa masa baƙaƙen maganganun da ke cizon raina. Da ƙyar na iya furta 'Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!' A zuciyata, domin na samu sauƙin da nake ji, dangane da ingizanin da take yi, a kan na yi abin da zai rage mini takaicin da aka ƙumsa mini.

      A gurguje muka shirya muka fice gidan, daga ni har yaran babu wanda ya bi ta kan shi, ko mai adaidaitan a kan hanya ya haɗu da mu ya ɗauke mu, saboda gudun na yi jinkirin jiran shi cikin gidan, na aikata aika-aikar da zan raba halina a gaban gardawan.


        Raina a jagule na kammala aikin da na taras ofishina, ko da Amina ta zo ta daɗe ban ce da ita uffan ba bayan gaisuwar da muka yi. Har sai da ta kasa haƙuri ta ce da ni, 

       "Yau dai kamar an sake taɓa mana ke?"

      Shiru na yi mata tsawon lokaci, sannan na sauke ajiyar zuciya tare da fesar da iska a bakina na ce, "Ina muka tsaya a labarin?" 

         "Inda kika shiga ɗaki"

    Amsar da ta ba ni kenan a taƙaice cikin sanyin murya. Na cire gilashin da ke sanye a idona, sannan na gyara zama na ce da ita,


     _"Baƙin tozalin da na yi ya sa na yi salatin da na yi babu shiri. Saboda falona babu komai a ciki face ledar tsakar ɗaki da agogon da ke manne jikin bango, da sassarfa na yi ƙuryar ɗakin, a nan ma sai da jiri ya so kayar da ni. Bango na yi hanzarin kaiwa na jingina bayana ina sauke numfashi da sauri da sauri. Nauyin da ƙafafuwana suka yi mini, ya janyo na kasa ɗaukar kaina a hankali na sulale na yi ƙasa. Zaman dirsham na yi rungume da Ummu Salma da ke baccinta sharkaf ba tare  da ta san wainar da ubanta ke toya mini ba._

         _Na jima ina karanta wasiƙar jaki kafin Mukhtar ya shigo da guntuwar sallamar shi, ban iya ɗaga kai na kalle shi ba balle na samu kuzarin amsa masa sallamar da ya yi. Zama ya yi kusa da ni ya miƙe ƙafa tare da janyo mu jikin shi, na yi hanzarin sakar masa Ummu Salma sannan na miƙe tamkar wadda aka tsikari. Jikina yana rawa tamkar mazari muryata tana harɗewa na ce da shi,_

          "Ina ka kai mini kayana!? Ka yi gaggawar dabon fito mini da su yanzun nan, kamar yadda suka yi ɓatan dabo a cikin gidanka. Domin na tabbatar da ka san yadda aka yi suka salwanta, shi ya sa kake gwara kan mutane ka dinga zagaye-zagayen ƙarya!" 

         _Na ƙare maganar muryata a sama numfashina yana hawa da sauka saboda tsananin ɓacin ran da na shiga. Kansa ya duƙar ƙasa ba tare da ya ce da ni komai ba, mintuna a tsakani na fara jin sharɓen kukan shi. Mamaki fal raina na bi saman kan shi da kallo, domin idan ba kunnuwana ne suke ƙoƙarin yaudarata ba, to tabbas na ji sautin kukan shi. Lallaɓawa ya yi a hankali ya ajiye Ummu Salma, idona a kan shi har ya durƙusa a gabana gwiwa biyu, tare da haɗa hannuwansa wuri ɗaya yana sharɓar kukan da ya saka jikina yin sanyi. Kafin ya samu kuzarin yin magana cikin muryar kuka ya ce,_


        "Ki yi haƙuri ki yafe mini, saboda na san na yi miki laifin da na cancanci duk wani hukunci daga gare ki. Amma don alfarmar Ubangiji da darajar Manzonmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ki yafe mini. Ta wannan hanya ce kaɗai idan kin yafe mini zan iya ba ki labarin dalilin da ya sa na sayar da kayan nan, wanda ko ke kika ji za ki iya ba ni da kanki ki ce na sayar domin daga ni har ke cigaban namu ne. Don haka don Allah ki yafe mini ba don halina ba, saboda matsin da na shiga wurin nemo mafita ya sa na sayar da kayan nan. Kuma na tabbatar da idan kika ji za ki amince da kanki ki ce na je na sayar domin mu rufa wa kanmu asiri."

        _Jikina ya yi sanyi ƙalau! Saboda maganganun shi sun shiga jikina, kuma ratsa zuciyata sosai. Saboda idan akwai abin da ba na iya kaucewa a duniya, shi ne a haɗa ni da Allah a kan abu. Komai hawan da na yi sai na sauko saboda ba na kauce tayin alfarmar da duk aka haɗa ni da roƙon Allah. Sai dai kuma zama da shi ya fice mini a rai, duk da na ƙudurta yafe masa laifin kamar yadda ya roƙa. Tsayuwata na gyara, sannan na sauke hannuna ƙasa daga rungumar da na yi musu a ƙirji, tare da kawar da kaina gefe bayan na riƙe ƙugu na ce da shi,_

      

        "Zan yafe maka kamar yadda ka roƙa, amma sai ka yi mini alƙawarin za ka yi abin da zan nema daga gare ka. Saboda zuciyata ba za ta taɓa yarda da kai a matsayin miji ba, ka sauwaƙe mini kawai cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya sani ba. Ni kuma na yi maka alƙawarin zan yafe maka duk kayan da ka salwanta mini. Don haka ka ba ni takardata yanzun nan gobe idan Allah ya kai mu lafiya na koma inda na fito. Kuma komai za a yi ba zan fasa wannan ƙwan ba balle wani ya ji warinsa, amma fa idan ka sallame ni cikin mutunci ba tare da wani ya ji ko ya sani ba. Domin Wallahi ba zan iya zama da miji irinka ba."

      "Don Allah! Don girman Allah ki yafe mini Zaituna! Wallahi ba zan iya sakinki ba ko da za a ɗora mini wuƙa a wuya." 

       _Ya ƙare maganar tare da riƙo hannuna yana cisgar kuka tamkar zai shiɗe. Ƙwace hannuna na yi sannan na tura shi ya faɗi ta baya, saboda tsabar takaicin da ya ba ni. Amma hakan bai hana shi furta mini  cewa,_


       "Gara kawai ki yi mini duk abin da kike so a matsayin huce haushin laifin da na yi miki, idan ma dukana za ki yi na shirya karɓar hukuncin kowane irin duka daga gare ki, amma ba zan taɓa yafe wa kaina ba muddin na yi abin da kike so. Na fi so na mutu, ko kuma duniya ta Allah-wadai da ni, a kan abin da na yi miki da a ce na sake ki."

       

       

No comments

Powered by Blogger.