Abokin Aikina Book 1 Page 20




*LAMBA ASHIRIN.*


      Shiru na yi na ɗan lokaci dafe da kaina da ke ta sarawa, sannan na miƙe su Ummu Salma suka fara kuka tare da roƙo na don Allah kada na buge shi.

       Ban bi ta kansu ba balle ta kan Haidar da ke kulle cikin ɗakinsu. Ɗakina na nufa yaraf na zauna bakin gado saboda jirin da ke kwasa ta, mintuna a tsakani na miƙe na ɗoro arwala. Sallah na gabatarwar tare da ɗaga hannuwana sama ina roƙon Allah shiriya zuwa ga 'ya'yana. Ruwan hawaye yana zarya a kan dandamalin fuskata cikin ƙanƙan da kai tare da tawassuli da haƙurin da nake yi a gidan Mukhtar. 

       Ummu Salma ta shigo ɗauke da kula ta ajiye gefena, tana ƙoƙarin ficewa cikin sanyin murya na ce da ita, 

       "Kira mini Haidar ku zo tare."

       "To" Ta faɗa sannan ta fice jim kaɗan ta dawo riƙe da hannun Haidar yana tirjiya tana janyo shi, Iman ta yi hanzarin zuwa inda nake tana matsar hawaye ta ce,

       "Don Allah Mama ki yafe masa Abbanmu ya dake shi sosai."

          Kallo na bi fuskar shi tare da tsuke tawa fuskar na ce,

 "Zo nan!"

      Ya tako yana ɗari-ɗari tare da haɗa hannuwan shi wuri ɗaya yana faɗin,

      "Don Allah! Don Allah Mama wallahi ba zan sake ba." 

        Har ga Allah jikina ya yi sanyi da zancen shi, uwa-uba yanayinsu duka da ya koma kalar tausayi. Wuri na nuna masa da nufin ya zauna, zama ya yi a ɗarare yana tsiyayar hawaye daga idanuwan shi da suka yi jawur saboda kuka. 

   

     "Kana so na mutu?"


        Tambayar da na fara jefa masa kenan ina ƙoƙarin goge hawayen da ke ta ambaliya a cikin idona, kai ya shiga girgizawa tare da faɗin, 

       "Ba na so!"

        "Kana so Allah ya ƙona ka?"

     A nan ma ya girgiza kai, "To idan har kana so na ci gaba da zama tare da ku, to kada ka sake shan taba daga yau har ranar tashin duniya. Domin duk ranar da ka sake shan tabar nan, ina tabbatar maka da cewa a ranar zan mutu, kuma muddin ka sake sha har na mutu kai ma za ka mutu ka je lahira a saka ka wuta. Kana so Allah ya ƙone ka saboda shan taba?"

       Girgiza kai ya shiga yi hawaye yana zarya kan fuskar shi har yana feso mini. Hannuna ya riƙe da hannunsa biyu yana faɗin,

       "Wallahi na yi alƙawari ba zan sake sha ba. Idan kuma na sake ki ce Allah ya kashe ni Mama."

         "Allah ya ba ka ikon dainawa. Kuma ya sa daga wannan shi kenan har abada. Idan kuma ka sake shi kenan da ni da kai duka za mu mutu a rana ɗaya."

      Rungume ni ya yi tare da fashewa da kuka yana faɗin, "Ba na so ki mutu don Allah kada ki mutu."

      Daga haka na cire shi jikina saboda warin tabar da nake ji yana tashi a hannunwansa. Wanka na ce ya je ya yi kuma dukansu su yi shirin zuwa islamiya. Sannan na fito ɗakin ba tare da na bi ta kan abincin da Ummu Salma ta kawo mini ba.

      Ɗakin Mukhtar na nufa, na ga ƙofar a rufe alamun ya fita. Sannan na dawo na yi wanka zuciyata a cunkushe da zallar nadamar auren Mukhtar a raina. Cike da takaicin haihuwar 'ya'yana ga wanda bai cancanta ba. 

      'Ashe ba namiji kaɗai ya dace ya nemar wa yaran shi uwa tagari ba har da mace.' 

        Zancen zucin da na yi kenan a zuciyata cike da tausayin matan da ke zumuɗin yin auren. Saboda da sun san tarin ƙalubalen da ke cikin auren, maimakon murna kuka za su yi. 

      Shigowar su Ummu Salma ya katse mini tunanin da na lula, saboda ko kayan da na fitar daga wardrobe ina riƙe da su ban saka ba. "Allah ya tsare na ce musu, tare da Addu'ar kariyar da nake yi musu koyaushe." 

      Har sun fita Haidar ya dawo ya durƙusa gabana tare da haɗa hannuwansa wuri ɗaya yana faɗin, "Ki yafe mini Mama. Na yi miki alƙawarin ba zan sake ba daga wannan."

        "Na yafe maka Haidar, tashi ka je Allah ya yi muku albarka dukanku."

       Ya fice yana yi mini bye-bye ina yi masa tare da murmushin jin daɗin farincikin Allah ya mallaka mini yarana, ba don iyawata ba kuma ba don na fi kowa ba. 

      "Alhmdulillah!"

    Ita ce kalmar da na faɗa sannan na miƙe na saka kayana, abincin na janyo na cakula kaɗan na ture. Sannan na fito falo mintuna kaɗan na fara jin ƙarnin taba yana tashi.

      Na miƙe na nufi ƙofar ɗakin inda hayaƙin da ke fitowa ta kusufar makullin ɗakin Mukhtar, haksn ya tabbatar mini da yana ciki. Tura ƙofar na yi babu shiri na ja baya ina toshe hanci, saboda gabaɗaya ɗakin ya turnuƙe babu abin da ke fitowa sai hayaƙin tabar. 

      Tari na fara yi ina kaɗe hayaƙin a fuskata har ya lafa, sannan na yi ƙarfin halin faɗin,

 "Idan ka gama ina son magana da kai."

        Da hanzari na koma falon na zauna ina sauke numfashi a wahale, don na kasa sabawa da warin tabar duk tsawon lokacin da muka ɗauka da shi. Bai fito ba tsawon lokaci sannan ya fito yana zuba ƙamshin turare, tare da haɗe fuska ya yi tsaye nesa da ni, fuskata babu yabo babu fallasa na ce da shi,

      "Zama za ka yi, don maganar ba ta tsaye ba ce."

     Ya zauna yana shan ƙamshi tare da faɗin, "Sauri nake yi akwai inda zan je. Idan maganar mai tsayi ce ki bari na dawo kawai."

      "Yanzu ya dace mu yi maganar, don haka yana da kyau ka san illar da ke cikin shan tabar da kake yanzu. Domin idan can baya ka yi babu yara, yanzu da suka fara mallakar hankalin kansu yana da kyau a ce ka daina. Saboda ci gaba da sha zai iya gurɓata mini tarbiyar da nake ƙoƙarin ɗora su a..."

       "Me kike nufi? Kina zaton ni na koya masa shan tabar? Ko kuma ni na ce ya zo ya ɗauka ya sha!?"

      Tambayar da ya jefo mini kenan a fusace, wanda alamu ya tabbatar ba za mu kwashe ta daɗi ni da shi ba. Saboda ba ƙaramar danna nake yi wa zuciyata ba, dalilin da ya sa ban zo da zafi ba saboda ina so ya fahimci abin da nake son nuna masa.

      "Ban ce ka ba shi ba, amma tabbas kai ka koya masa. Saboda kai ya ga kana sha shi ya sa shi ma ya fara gwadawa, domin ƙaramar ƙwaƙwalwarsa ba ta hango masa illar abin, saboda ganin  kana sha tunaninsa zai ba shi babu matsala a ciki. Don da akwai illa a ciki matsayinka na babba ba za ka dinga sha ba."


     "Oh! Kenan dai ni kaɗai suke ganin ina sha shi ya sa ya koya?" 

    

      "Kai ne dai kusa da shi, don haka ka taimaki yaran nan ka daina sha a gidan nan ko da ba za ka fasa sha duka ba. Sannan ka yi ƙoƙarin nisanta tabar a inda ka san za su gan ta su ɗauka. Saboda tarbiyya daga gida take farawa, kuma Iyaye su ne makaranta ta farko da suke bai wa 'ya'yansu karatun da zai fi shiga kansu."

     "Za a yi yadda kika ce!"

       Yana ƙare faɗar hakan ya miƙe ya fice da sauri saboda kiran da ake yi masa a waya, tun a lokacin da muka fara magana yana ƙin ɗauka. Ya bar ni zaune ina bin ƙofar da kallo, tare da sauraron maganar da ya yi a wayar kafin ya fita gidan.


     "Ga ni nan zuwa yanzu ki jira ni."


     Tagumi na yi ina goge hawayen da ban san lokacin da suka gangaro kan fuskata ba.

        'Habi ba ta san matsalar zama da irin wannan mijin naki ba, saboda labari ya zo mini har gida a kan riƙaƙƙen ɗan iska ne kuma ɗan shaye-shaye. Duk zaman da za ki yi da shi ba za ki taɓa samun farinciki ba sai kayan takaici da za ki yi ta kwasa kina jibga wa kanki. Amma tun da ta kafe a kan ba ta yarda a sake ki ba, to ki je ki ci gaba da zaman na zare hannuna a cikin sakin da nake nemar miki wurin shi. Don haka zancen zuwa kotun ma na ajiye ki je ki ci gaba da zaman haƙurin har Allah ya kawo miki ƙarshen shi.' 

   

     Maganar Baba Ali ce ta faɗo mini a rai, ranar da muka yi wani zama a lokacin da rikicinmu da Mukhtar ya yi tsananin da Baba Ali ya ce; na baro gidan Mukhtar na dawo Kebbi shi zai karɓar mini takardata a hannun shi, ko ta arziƙi ko ta tsiya idan ya ƙi bi ta lalama. Saboda ƙazafin da ya jefe ni da shi tun kafin na san MD kuma tun kafin na fara aiki a ma'aikatarsu.

       Daren ranar ma na yi shi ne da ƙunci tare da kai wa Allah kukana a kan ya kawo mini sauyi da mafita ta alheri.

       Da safiyar ranar Talatar, mai adaidaitan har gida ya ɗauke mu kamar yadda muka yi ajanda. 

      Fuskata a sake na shiga ma'aikatar saboda tuno abin da MD ya yi wa Sara, ban damu da kallon da mutane suke yi mini ba saboda na yi amanna da cewa, fiye da rabinsu ba za su yarda da ƙazafin da Sara ta jefo mini ba. Duba da yadda ban da sakewa da kowa daga matan har mazan, idan aka cire Amina da gaisuwar mutuncin da nake yi da kowa.


     Aikina na yi cikin natsuwa har ana gaf da tashi, sannan Amina ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi ta zauna. Kallo na bi ta da shi ina 'yar dariya saboda tuno damben da muka sha ni da Fatima matar MD. 

    "Hajiyata! Me ya sa a cikin labaran da za ki ba ni ba ki sanar da ni kin iya faɗa da dambe ba?"

    Baki na rufe ina ƙumshe dariya saboda ba ƙaramar dariya maganar ta ba ni ba. "Ai faɗa zuwa yake yi, kamar yadda dambe yake afkuwa bagatatan ba tare da an shirya masa ba. Wataƙila hakan ce ta hana ni sako su a labarin, sai da suka zo da kansu kika gani domin ki tabbatar da komai zuwa yake yi a lokacin da aka rubuta. Yanzu dai na ga fuskar ki da yalwa, me ke faruwa ne? Ba ni na sha tun kafin ta sarare a iska."

       "Hmmmmm!" Ajiyar zuciyar da ta sauke kenan sannan ta ce, "Yau dai Mama ta amsa gaisuwata. Saboda 'yarta ta zo jiya kuma a gabanta na koma gidan, ko ɗakina ban shiga ba sai da na je wurin Mama domin ta san dawowata. Saboda wani lokaci faɗa masa take yi ta ce ban dawo gidan ba sai gaf da magriba. Dalilin hakan na tsiro zuwa wurinta idan na dawo domin ta san lokacin da na dawo ta daina haɗa ni da shi."


    "Ma sha Allah! In Sha Allah da sannu za ki ga komai ya zama tarihi. Saboda ko Bature ya ce; No condition is permanent. Babu abin da yake tabbace idan ba ƙudura da irada ta Ubangiji ba. Wanda yake kum-fa-kun ne da ya ce a yi komai zai tabbata babu jinkiri."

        "Na yarda da zancenki, kuma in Sha Allah zan ci gaba da haƙuri. Fatana kawai ta gane da wuri saboda ta daina ɗaukar zunubin da take loda wa kanta." Zancen da ta yi kenan bayan ta sauke ajiyar zuciya. Sannan ta ce, 

        "Yanzu nake ji, wai jiya Basiru ya ɗebo wa MD 'yansanda a kan ya mari matar shi. Shi kuma MD an ce ya maka Sara kotu, a kan ƙazafin da ta yi muku."


      "Subhanallah! Abin duka bai yi daɗi ba. Gaskiya da bai biye shirmen su ba. Saboda suna yi ne duka don haushin korar da ya yi wa Basirun. Da ya bar su don ko ba komai shi sama yake da su, kuma ya fi su mutunci a idon mutane, bai dace ya biye su girmansa ya zube a banza ba saboda hakan."

         "Ni ko sai na ga ya kyauta, saboda sun yi ne kawai don su ci zarafin shi. Amma nuna musu da ya yi ya fi su hauka, hakan zai rage wa iskancinsu kaifi. Don na tabbatar da ba su da kuɗin ɗaukar lauyan da zai ƙaryata abin da Sara ta faɗa a idon mutane."

        Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na ce, "Ba za ki gane ba Amina. Wani abin fa kana da ikon ɗaukar mataki kake haƙura, saboda illar da abin zai haifar maka ya fi amfanin shi ya yawa. Domin fallasuwar wannan abin zai taɓa ƙimar MD sosai wallahi, kuma ba zai gano hakan ba har sai an gama shari'ar tsegumi zai fara tashi a tsakanin mutanensa da bai yi tsammani ba. Amma idan ya haƙura ya ƙyale shi kenan komai zai wuce waɗanda suka sani ma za su manta. Saɓanin fallasar da za ta janyo labarin ya fantsama ta yadda goge tarihin zai yi wahala a zukatan mutane."


        "Lalle kin fi ni gaskiya Maman Haidar. Don haka ya dace ki yi wannan gudunmawar domin ki datakar da shi ko za a dace ya haƙura ya janye." 

      Shiru na yi ina nazarin maganar, saboda duk abin da zai haɗa ni magana da shi personally ba na so, amma idan aiki ya haɗa ko ɗar ba zan ji ba saboda babu yadda zan yi.  

      "Ba na son duk wani abu da zai haɗa ni da shi Amina."

        "To ki tura masa saƙo!"

Shiru na yi na ɗan lokaci, sannan na janyo wayata ba don ina so ba na tura masa saƙo kamar haka;

       

         'Ka yi haƙuri ka janye ƙarar da na ji ka saka. Saboda babu alfanu idan sirrin ya fallasu a idon waɗanda ba su san da shi ba. Maimakon kankare laifin, sai ka ƙara ɓanɓaro mana yamaɗiɗin mutane, garin neman gira za a rasa ido. Ba na jin kaina, amma ina jin takaicin ƙimarka ta taɓu ta sanadina.'


         Amina na bai wa ta karanta, sannan ta dawo mini da wayar tana faɗin.

     "Sannu gwanar hikima da azanci. Allah ya ba ki iya tsara magana da hangen nesa. Ina ma kaso mafi rinjaye na mutanen duniya haka suke. Da an samu rangwamen cakwalkwalin cakwakiyar da ya baibaye mutane a wannan lokacin da muke ciki. Ubangiji ya kawo miki mafita a cikin rayuwarki."





Amin Amina. Tare da sauran masu Matsala irin taku da ma wadda ta fi.👏🏻


No comments

Powered by Blogger.