Abokin Aikina Book 1 Page 17

 


*LAMBA SHA BAKWAI.*


         Shiru na ji ya ratsa tsakani bayan maganar Mukhtar, sannan na ji muryar Kawu Sale yana faɗin, "Yanzu ke Habi tun da ya gano laifin shi, yana da kyau a ƙara ba shi wata dama. Idan har ya kiyaye abubuwan da ke janyo musu  rikici shi kenan matsala ta kau, saboda haka ki zubar da komai a daina

bitar abin da ya wuce. Kai kuma tsakani da Allah matuƙar ba ka gyara halinka ba, to duk abin da ya ƙara tasowa a gaba kada ka ga laifin kowa kai ka janyo. Abu na ƙarshe kuma ka daina zargi, domin muddin ka tsayu a kan zargin matarka to ba za ka taɓa jin daɗin zama da ita ba. A wani ƙaulin Malamai ma an tabbatar da cewa zargi yana ɓata aure."

         "Ni a wurina komai ya wuce Kawu, amma maganar gaskiya aikin nan da take zuwa, ko kaɗan ban da natsuwa da shi. Saboda mutumin nan babu komai a ran shi face buƙatar kashe mata aure domin ya aure ta."

        Maganar shi nan take ta saka idona  rufewa, ta yadda ban san lokacin da na yi wuf na faɗa ɗakin ba. Cikin ƙunar zuciya na fara nuna shi da hannu ina cewa, 

        "Kai dai baƙin munafuki ne ƙarshen bugun lamba. To wallahi ko za ka mutu ba zan fasa zuwa aik..."

          "Yi mana shiru Zaituna!" Babu shiri na gantsara saboda tsawar Baba Sale da carbin da ya watsa mini a jiki, na durƙushe ƙasa ina sosa wurin tare da aika wa Mukhtar harara ta gefen ido. Kafin Baba Sale ya ci gaba da magana cikin fushi tamkar ya dake ni.

       "Me ya kawo ki nan balle ki saka mana baki? Ko kin ji an kira ki da za ki zo kina yi wa mutane hauka? Wannan rashin mutuncin naki yana daga cikin abin da ke ƙara lalata muku zaman lafi..."


       "Wallahi ko a gaban yara haka take yi mini ba ta shayin komai. Na sha faɗa mata duk abin da za ta yi mini zan jure matuƙar ba gaban wasu ko 'ya'yana ba. Domin yanzu silar hakan har yaran sun fara yi da ni a tsakaninsu. Ko yau da safe ina jin Haidar yana faɗin; shi ya gaji da kukan da nake saka Mamarsu, Idan ban bari ba shi ma zai rama mata a kaina. Ka ga a nan ta yi ƙoƙarin cusa musu ƙiyayyata tun kafin su mallaki hanka...'" 

       "Wannan kuma ba laifinta ba ne kai ka janyo. Don a irin halinka babu abin da 'ya'yanku ba za su yi ba, matuƙar aka biye doron da kake ajiye tsarin gidanka a kan shi. Yana da kyau ka fahimci matsalar taki ce duka ba ta mutum guda ba, yadda kake da laifi ita ma tana da shi. Don haka ku taru ku gyara dukanku ko don tarbiyyar yaranku. Ke kuma ki ji tsoron Allah ki daina cin zarafin mijinki don komai lalacewar shi miji miji ne, kuma yana sama da ke ko babu auratayya balle aure ya haɗa da 'ya'ya a tsakani."


      Zancen Mukhtar da Ummata kenan a  lokacin da ya so goga mini laifi,  ta yi hanzarin toshe komai ta hanyar ankarad da shi domin ya hankalta. 

       Daga ni har shi suka rufe mu da faɗa, a kan mu zauna lafiya mu daina raba wa kanmu abin faɗa. Da nufin a bar wanda aka yi baya a matsayin ya wuce a fuskanci gaba, sannan batun aikina ma ba a hana ni zuwa ba kamar yadda yake da buƙata. Sai dai sun tunantar da ni abubuwan da baƙinciki ya sa nake ƙoƙarin aikatawa, ba don na manta da hukuncin laifi ba a musulunce ko a al'ada ba.

        

         Sannan aka tashi zaman sasancin da zummar da dare zan koma gidan shi, bayan an saka ni dole sai da na ba shi haƙuri ba don na so ba. 

      Ina gunguni na fito ɗakin saboda ko kaɗan hukuncin bai yi wa zuciyata daɗi ba. Domin ni a rayuwata ban da wani buri a lokacin; face  ya tsinke igiyon aurensa da suka yi mini mugun ɗaurin talala a jiki. Saboda ina so na kasance free babu aure ko da zan mori sauran rayuwar da ta rage mini a duniya. Domin na  yi nagartacciyar ibada irin wadda zan samu natsuwar zuciya, saboda ina so na daina aikata alfashar da nake yi a ƙoƙarin kaucewa zinar zahiri.  

       Inna Kulu ta dinga ba ni haƙuri domin na rungumi ƙaddarata har zuwa lokacin da Allah zai kawo mini ƙarshenta. Sauraron ta kawai nake yi, amma ba don babu abin da take faɗa mini zai yi tasiri a zuciya ba, matuƙar ba za ta goya mini bayan rabuwa da auren Mukhtar ba.

     Ƙarfe huɗu da minti goma na rana, bayan na gama sallar Asr ina kan sallaya da carbi a hannuna ina ja. Na jiyo sallamar Amina a tsakar gidan. Tana tambayar inda nake tare da yi wa su Umma bayanin ni ta zo dubawa, har da yi musu ya jikina suka amsa mata tamkar da gaske ciwon nake yi. Inna Kulu ta fara shigowa ɗakin sannan Amina a bayanta har inda nake zaune. 

      Murmushi muka yi wa juna ni da Amina sannan ta zauna tana faɗin, "Kai matar nan, ashe ma ciwon da sauƙi MD ya tsorata mu da cewa ciwon ya sa aka dawo da ke gida. Wataƙila ma lamɓo ne kawai gidan kika yi marmari, shi ya sa kika dawo don ki saka su Umma aiki." 

       Murmushi na yi mata da jajayen idanuwana, waɗanda har lokacin ba su gama washewa ba a kan kukan da na sha. Baki har kunne na ce da ita, "Ciwon kaina ne ya motsa, ban san lokacin da aka kawo ni gidan nan ba. Amma yanzu Alhmdulillah da sauƙi komai ya lafa."

        "Allah ya ƙara lafiya, amma ki daina cin abin da ke tayar miki da ulcer, sannan ki dinga shan magani saboda ki samu ta lafa miki ki huta."

       "In Sha Allah!"


     Dukanmu muka bi ƙofa da kallo saboda shigowar Inna Kulu da kula. Gaban Amina ta ajiye tana faɗin, "Ku ci awara tun kafin ta yi sanyi."

        Bayan fitar Inna Kulu Amina ta miƙe tana faɗin, "Bari na fara yin sallah don ba na son na ci na kasa motsin kirki. Tun da kin tayar mana da hankali a wurin aiki ana ta jimamin ciwonki, MD ma yau bai zauna ba tun da ya zo da safe ya fita har na baro wurin bai dawo ba."

      "Uhumm!" Kawai na ce ta fice na ci gaba da jan carbina, har ta dawo na tashi na ba ta sallayar. Kafin ta gama na zuba mana awarar a plate ɗaya, tare da ruwa a kofuna.

       Bayan ta gama muka fara cin awarar ta sha kayan haɗi da daddaɗan yaji, domin sana'ar Inna Kulun ce kuma sosai take samun rufin asiri da ita. Shiru ya ratsa tsakani, kafin Amina ta kawar da shirun da cewa,

         "Da zumuɗi na tashi yau domin na zo na ji cigaban labarina, abin haushi sai ga shi na tsinci zancen ciwonki a bakin MD. Bayan na yi ta rangadin zuwa offishinki ina ganin shi a kulle, a zuwa na ƙarshe ne da na gan shi zai fita nake tambayar shi ko kin zo; ya ce da ni kin turo masa saƙo ba kya samun damar zuwa ciwonki ya tashi kina gida. Da ƙyar na samu na kammala aikina na nufi gidanki, ganin gidan a rufe ya sa na kira lambarki ba ta shiga. Dole na  na sake neman shi na sanar da shi ba kya gidan,  ya sanar da ni kin ce kina gidanku wurin Umma Bafarawa Estate. Adaidaita na ƙara samu na yi gida, sai da na kammala ƙananun ayukana sannan na ƙara shiri zan fito." 

      Ƙasake ta yi tana lagudar awarar da ke hannunta wanda a take na gano akwai abin da ya faru kafin ta fito gidan. Hakan ya sa na samu kuzarin faɗin, "Ai da kin yi haƙuri gobe ma zan shiga aikin. Kin ga sai mu ɗan samu abin da zai sauwaƙa kafin a tashi."

       "Hmm! Ai ba zan iya haƙurin ba wallahi, in da na samu wayarki da ba zan shiga damuwar da na shiga ba. Saboda ina tunanin a wane hali kike ciki duba da  yanayin da kika baro wurin aikin jiya, kamar akwai wani abu maras daɗi da ya faru da ke. Hakan ya ƙara tayar mini da hankali ga shi matsalar da na samu ban san gidan da zan faɗa a kawo ni ba. Kuma ina da tabbacin MD ma bai san gidan ba shi ya sa ban neme shi ba." 

       "Ya aka yi kika gano gidan yanzu?"

        "Tambaya muka fara yi ni da mai adaidaitan da muka zo unguwar, har na yi katarin ganin Haidar tare da wasu yara a daidai wani shago. Da hanzari na kira shi yana gani na ya nufo ni yana gaishe ni, a nan yake yi mana kwatance na ce ya shigo ya kawo mu kawai."

             

     Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce, "Allah Sarki Amina, na gode sosai da ƙoƙarinki. Allah ya bar zumunci."

         "Amin" ta ce sannan ta yi hanzarin fiddo wayarta a jaka saboda kiran da ake yi mata. "Ga ni nan zuwa yanzu." Abin da ta faɗa kenan fuskarta a haɗe bayan ta gama sauraron abin da aka ce cikin wayar. Mere na ga ta yi tare da hurar hanci tana lasar maiƙon da ke hannunta. Ban ce da ita komai don na san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. 

          "Na rasa me na tare wa Mama da ko kaɗan ba ta ƙaunar farincikina. Yanzu fa ba ta ji kunyar kai ƙara ta wurin shi ba. Kuma shi ya bar ni fitar nan amma ƙiri-ƙiri ta so hana ni fitowa, saboda girkin da zan gama wahala a hana ni kwana da miji."

        Ta ƙare maganar fuskarta a cure, hakan ya tona mini asirin takaicin da take ƙumsa dangane da baƙar dokar Mama. Wadda mijinta ya mayar tamkar faɗar Allah da ta faɗa sai ya aiwatar ko ba ya so, duk da san kuskure ne yake aikata wa matar shi, bayan alaƙar zumuncin da ke tsakaninsu mai ƙarfi. Domin Mama uwar miji ce gare ta kuma Gwaggonta, saboda Yaya take ga Mahaifin Aminar uwa ɗaya uba ɗaya. 


       Amina ta so zama na ɗora mata labarin, amma dole na dinga nuna mata rashin dacewar zaman tun da gobe zan fito aiki. Sannan na ba ta haƙuri sosai tare da nuna mata alfanun juriya a kan cutarwar da Mamar take yi mata da gangan, matuƙar tana son ganin ribar a gaba. Cikin nasara na ci kanta ta miƙe tana saɓa jakarta a kafaɗa tana faɗin,        

          "To ni zan tafi Allah ya ƙara sauƙi. Amma don Allah ki ƙoƙarta ki fito goben."


        Har bakin titi muka raka ta ni da su Ummu Salma, tare da ba ta tabbacin zan fito gobe ta tsumaye ni. Ta tafi muna ɗaga wa juna hannu na juyo ina goge ƙwallar tausayin kanmu ni da ita, duk da na fi ta matsala amma har zuciyata ina jin tausayin ta a raina. Saboda ba ta da ƙarfin zuciyar shanye damuwa, saɓanin ni da na zamo turmin tsakar gida sha luguden mahassada. Domin duk wani sara da sukan da aka yi mini bai hana ni kirkiza ba, balle damuwar hakan ta bayyana a jikina. Dalilin hakan ya sa wasu da yawa suke hawa kan batutuwan Mukhtar su zauna.  Saboda na kasa zama abin tausayi a kan fuskokin mutane, ta yadda za a gano matsalar da nake ciki ta hanyar rama ko lalacewar da ido zai tabbatar da lalle ina shan wahala a gidan shi.


        Da dare misalin ƙarfe tara da rabi na dare, Umma da Inna Kulu suka kai ni gidan Mukhtar. Da motar wani Baban ƙawata kuma maƙocin Kawu Sale kuma abokin shi. Bayan sun gama jan kunnena sosai a kan na yi haƙuri na zauna lafiya da mijina, sai dai ni ko kaɗan ban ɗauki shawarar zama da shi a yadda suke so ba. Don ya gama sire mini kuma mutuncin shi ya daɗe da zubewa a idona. Saboda ba na jin zai iya dawo da martabar shi gare ni ko da zai mallaka mini ƙasar Nigeriya da abin da ke cikinta.  

         Ko da muka je mun tarad da shi, suka ƙara haɗa mu duka suka yi mana nasiha tare da saka mu neman yafiyar juna. Bayan sun tafi na saka yarana suka kwanta na tofe su da addu'o'in bacci sannan na rufo musu ɗaki. 

           Ɗakina na nufa na yi sabon wanka don jin daɗin kaina, sannan na kwanta tare da janyo wayata. Messages na shiga dubawa ta inbox da saƙonnin da ake ta turo mini daga waɗanda nake mutunci da su a wurin aikinmu. inda ake ta yi mini ya jiki tare da fatar samun sauƙi, saboda tun an karɓo mini jakata a hannun su Ummita, ban sake kunna wayar ba sai a lokacin. Shi ya sa ban san da shigowar saƙonnin ba. Amsa na shiga bai wa mutanen har na  zo kan saƙon MD, haka ƙawa na tsinci kaina da yin guntun tsaki ba tare da na shirya ba. Saboda har lokacin ban daina jin haushin abin da ya yi mini ba, wanda nake ji a raina tamkar ya datse ganin walwalar fuskata har abada. Domin na ci alwashin ko kallo don ya zama dole na gan shi, amma da ina da iko da hana kaina ganin shi saboda tsabar takaicin shi da nake ji. 

       Bubbugar da na ji ana yi wa ƙofar ɗakina ya sa na yi kasaƙe ina sauraron muryar Mukhtar da ke ta faɗin, "Ki buɗe magana za mu yi." Tsaki kawai na ja sannan kashe wayar tare da juya kwanciyata, yawan bugun da yake yi wa ƙofar ya sa na miƙe a fusace na buɗe ƙofar tare da tare hanya, ƙugu na riƙe fuskata a cure na ce,

         "Malam lafiya?"

         "Lafiyar ce ta kawo hakan!"

Amsar da ya ba ni kenan ya ratsa ta gefena ya shigo ɗakin. Zama ya yi a kan gadona yana murmushin shi da ke nuna mini alamun wata sabuwar yaudara ta kawo shi ɗakina. Domin ba na kawo ƙarshen zuwan shi ɗakin cikin lalama ba tare da tashin hankali ya ingizo ƙeyar shi ba. 

       "Zo ki zauna." 


       Abin da ya faɗa kenan yana nuna mini kan gadon a kusa da shi, kallon banza na aika masa tare da sakin guntun tsaki na rungume hannuna a ƙirji ina kallon gefe. Tasowa ya yi kai-tsaye na ɗauka fita zai yi kawai na ji ya rufe ɗakin da key yana ƙoƙarin tuɓe kayan shi. 

        Kallon mamaki na bi shi da shi tare yin dariyar takaici saboda na san ƙarshen wasar. Domin fankam-fankam ba shi ne kilishi ba, an sha yin ruwa ƙasa tana shanyewa. Idan ba yaudarar kan shi yake so ya yi ba ya san ba zai iya ba komai ba a nan fagen, amma don ya nuna mini shi ma jan wuya ne ya zo mini da ɗanyen kan da babu inda zai ƙare sai rabuwa baram-baram ni da shi.

Shin wane shiri ne Mukhtar yake yi wa Zaituna? Domin alamu ya nuna shi ma wannan karon zai zo da sabon salo.🤔


No comments

Powered by Blogger.