Abokin Aikina Book 1 Page 16

 


LAMBA SHA SHIDA.*


        Daga nan ɗakin da nake ina jiyo sautinsu ita da Inna Kulu tar-tar a cikin kunnuwana. "Haba Kulu! Shi kenan kullum abu ɗaya za a dinga yi? Har yaushe Zaituna za ta gano abin da nake lurar da ita? To ni kam a wannan

karon, wallahi zan fitar da wuyan hannuna a cikin duk abin da ya shafe ta. Ta je ta yi duk abin da take so tun da ta isa da kanta da rayuwarta, amma wallahi ba zan zauna da ita cikin gidan nan ina ganin wulgawar ta ba. Don duk lokacin da na tuna ta kashe aurenta ta bar 'ya'yanta a wulaƙance sai na ji baƙinciki."

         "Ki yi haƙuri Habi, tun da dai hannunka ba ya ruɓewa ka yanke shi ka jefar." Zancen Inna Kulu kenan cikin tausasa murya a ƙoƙarin ta na tausar Ummata, daga mugun fushin da ta shiga tana ta feso hayaƙin maganganu masu nuni da zallar ɓacin ran da ta shiga, sannan kuma masu kama da yi mini baki a fakaice. 

         "To ke Kulu sau nawa mutum ya sa aka cire masa hannun aka jefar? Ai sai dai idan ba ta kama ba. Don haka ta tashi ta koma gidan mijinta yanzu tun muna shaida juna. Idan kuma zaman gidan take so ni zan bar mata gidan ta zauna, amma ba za mu jeru ni da ita ba"


         "Ba za ta zauna gidan nan ba, sai dai ta koma gidan Alhaji Ali tun da daman can shi yake ɗaure mata ƙugu tana iskanci." 

        Maganar Kawu Sale kenan da na tsinkayo muryar shi a sama alamun shi ma ya ɗauki zafi da ni. 

        Hawayena na share sannan na miƙe ina gyara zaman mayafin da ke jikina, na rataya jakar hannuna, na ja ta kayana na fito ɗakin.

      Ƙofar fita gidan na nufa ina sharɓen kuka ba tare da na ce da su ƙanzil ba, "Wallahi muddin kika fita gidan nan a yanzu sai na tsine miki albarka, matuƙar ba gidan Mukhtar za ki koma ki rungumi 'ya'yanki ba."

        Turus na yi babu shiri na ja na tsaya, domin a raina babu zancen komawa gidan Mukhtar har abada. Inna Kulu ta zo har inda nake ta karɓi jakata tare da riƙo hannuna muka koma ɗakinta. 

       Nasiha ta fara yi mini cikin kwantar da murya, tana ƙoƙarin fahimtar da ni muhimmancin yi wa Umma biyayya, da gudun lalacewar tarbiyyar 'ya'yana da take yi. Wanda abu ne a bayyane ko ni na sani Mukhtar ba zai iya ɗora su a kan tarbiyyar da na ba su ba. Domin zai iya dawo da hannun agogo baya kamar yadda na sha yaƙi da shi a kansu, kafin komai ya daidaita ya daina mayar mini da 'ya'ya kishiyoyi. Saboda duk wani aikin da ya dace mata ta yi wa mijinta idan aka cire kwanciyar aure, to shi yake saka su ba tare da ni ya damu da ni balle ya ce na yi masa. A kan haka mun yi faɗa ya fi a ƙirga da ƙyar na samu ya daina, saboda ƙaƙƙarfar iyakar da na yi masa da yarana.        

        Da wannan tunatarwar Inna Kulu ta samu kaina na rage kukan da nake yi, saboda matuƙar na ce zan tsallake na watsar masa da su, to babu makawa sai ya dawo da bara bana. Idan kuma hakan ta faru to babu amfanin nema wa kaina 'yanci bayan na wargaza tarbiyyar yarana.  

       "A ce.. ya kawo.. su idan.. na... tashi mu koma.. tare da su..." 

       Maganar da na faɗa kenan cikin ajiyar zuciya da shesshekar kuka. Domin jikina ya yi sanyi ƙalau musamman da na tuno lokacin da ya rufe su a ɗaki suna kuka, ba tare da ya damu da rarrashin su ba balle ya nuna musu tausayi irin na Uba.

      "Tun da sassafe yau ya kira Ummarki yana sanar da ita ba ki kwana gidan ba, shi ma bai san ba ki nan ba har sai da ya zo yi miki ina kwana sannan ya gano ba ki gidan."

          Murmushin takaici na yi sannan na ce, "Idan har da gaske ya san ban kwana gidan ba, to dole ne a ce yana sane na fita ko kuma a kan idon shi. Idan kuma har bai san ba na gidan ba har sai da ya zo yi mini ina kwana kamar yadda ya ce. To bai da masaniyar lokacin da na fita balle ya san gidan na kwana ko ba gidan ba. Abu na ƙarshe kuma ni rabon ina kwana ta haɗa ni da shi; na yi masa ko shi ya yi mini an fi shekara uku ko huɗu. Domin ko sallar asubu ba ya tayar da mu daga ni har yaran, balle zuwa ya ga tashin mu idan safiya ta waye."


     Ajiyar zuciya Inna Kulu ta sauke sannan ta ce, "Ni wannan zama naku Zaituna, ban taɓa ganin irin shi ba sai gare ku. A ce ko kaɗan babu jituwa tsakanin mace da mijinta; to ya ya za ku fahimci juna balle ku nemo hanyar gyara domin ku gyara zamantakew...?"

         "Ita ma ai tana da matsala, babbar matsalar Zaituna a rayuwa bai wuce kafiya ba. Da tana bin shawarar da muke ba ta da tuni ta zauna lafiya mu ma ta bar mu mun huta. Amma duk abin da kika ce ta yi sai ta nuna miki ta fi iyawa. To zama da Mukhtar ya zama dole ko don 'ya'yanta, tun da tun farko ba ta bayyana mana matsalar shi da wuri ba. Balle a taro tun kafin ta yi tsanani, har sai da komai ya lalace sannan ta faɗa bayan ta fara tara zuri'a da shi."

      Maganar Umma kenan da muka ji a sama ba tare da mun ji shigowar ta ɗakin ba, sai da ta ja numfashi sannan ta sake cewa, 

     "Na sani Mukhtar bai yi mata halacci ba mu ma bai yi mana ba, amma babbar matsalar shi ne yaran da ke tsakaninsu. Mahaifiyar shi ba ta duniya balle a miƙa mata yaran, domin ta san yadda za ta yi da su, shi kuma ba ɗa ba ne balle a ce za a bar masa su hannun shi. Sannan kaf dangin shi babu mai zuciyar riƙa masa 'ya'ya tsakani da Allah balle a kai musu su karɓa, saboda zuri'arsu kaf babu haɗin kan taimakon juna balle a share wa ɗan'uwa kuka. Babbar matsalar ita ce a cikin gidan ma tarbiyyar yaran za ta fara gurɓacewa ba sai an je nesa ba. Domin idan kin manta na tuna miki, sau nawa suna neman 'ya'yanki da lalata Allah yana tsarewa kafin ki baro gidan?"

       Ta ƙare maganar a fusace cikin ɗaga murya, saboda fuskarta ta nuna kai wa ƙoluwar ɓacin rai. Kafin na ba ta amsa ta ƙara da cewa,

        "Lokacin da kika daka yaji kika zo gidan nan, watanki biyu ana faɗi-tashi da yaran, nawa Mukhtar ya kawo mana domin mu ciyar da su ko a yi musu wata lalura? To a haka kike so na kawo ki gidan nan ke da yaranki ya bar mu ciyar da ku da sauran laluro, shi ya rungume hannun shi ya zuba mana ido? To ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa. Sawunki a likkafa ki ɗauki jakarki ki koma tun kafin wankin hula ya kai ki dare, baƙincikin ɗa namiji ba a kanki aka fara ba kuma ba za a ƙare kanki ba. Kula da tarbiyyar yaranki ya fi miki alkhairi da neman wani matsugunnin da kike yi. Saboda inda kika sani kin raina shi, shi kuma inda za ki je an raina ki."


      Tana ƙare faɗar hakan ta fice, mintuna a tsakani na ji tana magana a waya. "A kawo yaran nan idan ta tashi ta koma tare da su. To idan sun dawo a kawo mata su."


       Daga ni har Inna Kulu babu wanda ya yi motsin kirki balle mu samu kuzarin cigaba da bitar maganganun. Domin har zuciyata na gamsu da zancenta ɗari bisa ɗari, saboda ta tunanar da ni wasu abubuwan da na manta a baya. Hakan ya sa na yi ammana da Mukhtar ne ƙaddarata a cikin duniya, wanda ban da ikon gyara ƙaddarar ta dawo mini daidai yadda nake so; har sai ranar da Allah ya kawo mini sassauci da mafita a cikin rayuwata da ta 'ya'yana.  

       Inna Kulu ta tashi ta fice, mintina a tsakani ta dawo ɗauke da kofin kunu da ƙosai a ƙaramin faratin silba. Gabana ta ajiye tana faɗin,

       "Ɗauki ki karya sannan ki bar wa Allah lamarinki, in Sha Allah za ki ga haske a gaba muddin kika cusa wa zuciyarki dangana, kuma kika bi abin da Mahaifiyarki take so."

        Ban musa ba na sauko daga kan gadon na fara shan kunun, domin shi kaɗai nake jin zai iya shiga cikina. Ko shi saboda yunwar da nake ji maƙoshina har ya fara bushewa.


      Kasancewar yaran sun je makaranta, bai kawo su ba har sai da aka gama sallar juma'a. Sannan suka shigo da gudu suna ihun murna tare da ƙwala mini kira, tarbon su na yi fuskata ɗauke da mayalwacin murmushi. Jikina suka faɗo dukansu suka rungume ni, ni ma na rungume su ƙam-ƙam. Nan take damuwa ta ziyarce ni har ta bayyana kan fuskata.

        Saboda kukan da Ummu Salma da Iman suke yi. Jan su na yi muka ƙarasa cikin ɗakin ina faɗin, 

     "Ya isa, ku daina kukan haka."


      Haidar riƙe da hannuna ya ce, "Mama wai da gaske kin ce ba za ki sake zama gidan Abbanmu ba?"

      Kallo na ƙura wa fuskar shi kafin na ce, "Wa ya faɗa maka?"

        "Abbanmu ne ya ce dama mun daina kuka don kin ce ba za ki sake zama da mu gidan ba, shi ya sa da dare kika tafiyar ki kika bar mu."

Amsar da Ummu Salma ta yi hanzarin ba da ni kenan tun kafin Haidar ya faɗa.

            Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce, "Ko ma dai mene ne ina tare da ku abadan in Sha Allah! Ku je ku gayar da Umma." Har sun fice Iman ta dawo tana goge hawaye ta ce, "Abbanmu yana wurin Umma da Baba Sale suna magana." 

       Zumbur na miƙe saboda na san sharri da ƙage irin na Mukhtar, abu kaɗan zai iya juya shi zuwa babba. Balle ganin da ya yi mini tare da MD komai zai iya faɗa domin ya jaza mini wani sabon tashin hankali na daban.

           "Wallahi Umma da idona na gan ta tare da shi a ƙofar wani gida, kuma a gabana ta shiga motar shi suka tafi tare da 'yansan..."

        "Ban katsi hanzarinka ba Mukhtar! Amma mutumin nan ya faɗa mini duk abin da ya faru a lokacin da ya kawo ta gidan nan. Asali ma ban da shi; da tuni an cutar mana da ita saboda sakacinka. Kada ka ga ina zuba maka ido kana zaluntar mini yarinya ka ɗauka ba na son ta. Wallahi duk girman mutuncin da kake gani ina yi maka albarcin 'ya'yanka kake ci. Domin ni ba ki yi mini halacci ba kuma ba ka yi wa Zaituna adalci ba. Saboda ta nuna maka ƙauna kuma ta yi maka rufin asirin da a tara mata dubu ba za su iya yi maka irin shi ba. Mutumin da kake aibatawa kuma, mahaifiyar shi ya kai asibiti a daidai lokacin da taƙadarun suka biyo ta.  Saboda ciwon asma gare ta wanda tashin shi cikin daren ya yi sanadin ceton Zaituna. Domin ba don ta ya fito ba, kuma ita ma ba wurin shi ta je ba, amma idan har ba ka yarda da zancen ba; kana da damar ɗaukar mataki daidai da laifin da kake ganin ta yi maka."


       Maganganun da na ji kenan a lokacin da na durfafi ɗakin Kawu Sale, saboda a can ne mahaɗarmu a duk lokacin da aka zo sansancin rikicinmu ni da shi.

       Hawayen daɗi na goge a fuskata na sha jinin jikina a bakin ƙofar, saboda ba ƙaramin farinciki zancen Ummata ya saka ni ba.

 'Ashe har yanzu Umma tana so na.' 


        Zancen zucin da na yi kenan kafin na ji ɗaci ya ziyarci kan harshena, a sanadiyyar muryar Baba Sale da na ji yana faɗin, "Ke Habi ba haka ake sulhu ba, yadda ya kawo ƙara ya dace ki tsaya a saurari ta bakin..."

         "Babu abin da zan tsaya sauraro daga gare shi Sale, don magana ta gaskiya kai kanka ka san Zaituna ta sha wahalar auren shi. Kuma ba wai mun rasa inda za ta zauna ba ne ko abincin da za mu ba ta, balle ya zargi neman kai muke yi da ita shi ya sa muke tauye ta zama da shi koyaushe. Don haka idan har ya gaji babu dole ba sai ya yi ta ɗora mata ƙazafi ba, ya sake ta kawai gari da yawa maye ba zai ci kan shi ba wallahi. Amma ba ita ba ni kaina na gaji da matsalolin shi, idan bai gyara ba a wannan karon; to zan bai wa Babanta Ali dama ya raba auren kowa ya huta. Don daman can ni na hana da yanzu duk mai sha ta sha komai ya zama labari. Miji goma ai ba Uba goma ba ne."


       Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi tamkar an sauke mini ƙaton dutsi a saman kaina, domin yau kaɗai Umma ta tabbatar mini da lalle ita ce ta haife ni. Saɓanin baya da nake tantamar hakan a duk lokacin da ta ɗauki gaskiya ta miƙa wa Mukhtar. Ko idan ta kawar da kai ga duk matsalolin shi idan na rattaba mata, a matsayin kare kaina daga wani laifin da ya ƙaƙaba mini ban ji ban gani ba, ko faɗan da take yi mini a kan boren da nake yi wa auren lokaci bayan lokaci.


     "Wallahi Umma ban san ta fita ba, sai bayan na farka tsakar dare na ga ƙofar gidanmu a buɗe. Kuma na yi ta kiran lambarta ban samu ba, haka ma sai da na biyo sawunta kafin na sake rufe gidan. Ke ce kawai ban yi tunanin kira ba sai da safe gudun na tayar miki da hankalin."

        "Ai da zafi-zafi ake bugun ƙarfe ba sai ya huce ba, domin da ka kira ni a lokacin dole mu fita neman ta mu da muka san zafinta. Saɓanin kai da rashin  ganin ta bai hana ka komawa gidanka ka rufe ba, saboda ba ka da asara ko mutuwa ta yi akwai mata da yawa a gari har waɗanda suka fi ta." 

        Cikin kakkausan sauti na ji Umma ta ba shi amsa mai harshen damo. Babu shiri na maka wa ƙofar harara saboda maganar da na ji yana faɗi daga bakin shi cike da yaudara da daɗin baki,

        "Yanzu dai don Allah Umma ku yi haƙuri, in Sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba. Domin Wallahi gabana har  faɗuwa yake yi a duk lokacin da na ji ana zancen sakin nan. Saboda ko maƙiyina ba na fatar ya saki matar shi balle ni na aikata. Kada Allah ya nuna mini ranar da zan furta wannan mummunar kalmar daga bakina zuwa ga Zaituna."



No comments

Powered by Blogger.