Saran Boye 16-20
(ALLAH ya bar ƙauna Umm da Addah😅😘🤗)
Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*
_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.
Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.
Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.
*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*
_____________________________
*_SAUDIA_*
.............Kai kawo taketa faman yi a falon nasu dake wadace da sanyin ac da ƙamshi kai kace safa da marwa take gudanarwa. Ta canja sosai, dan komai na jikinta ya ƙara girma da cika. Daman can duk tafi su Nu'aymah girman jiki kasancewar ta ɗakko jikin Addah. Yanzu kuma darajar aure saita sake bata damar buɗewa tamkar ba ƴar shekara goma sha takwas ba.
Tabbas tana samun ci da sha da sutura duk irin wadda ta buƙata, sai dai a watanni tara kenan da aurenta da Yah Abdallah babu wata rana da zata ware ta dangantata da farin cikinta. Idan har ta samu kulawarsa to na wasu awoyine da zai biya buƙatarsa. Baya son zaman gidan sam, ita kanta har mamaki take da al'ajabin ina yake zuwa bayan makaranta da harkar kasuwancinsa?.
Duk yanda taso fahimta ko gano hakan ya gagara, babu kalar dabaru da maman Aaida bata koya mataba duk kuma ta bisu daki-daki amma ta gaza samun haske. A yanzu haka wata ƙura ta fahimta baibaye da ita game da mijin nata shine dalilin kaiwa da kawowar tata.
Tun daga randa Abdallah ya fara kusantarta ba'a cikin hayyacinsa ba a washe gari ya haɗata da wasu ƙwayoyin magani guda biyu. Daga haka kuma duk sanda zai kusanceta sai ya batasu ta sha. Tun bata taɓa kawo komai a ranta game dasu ba harta fara zargar wani abu. Ba komai ya kawo mata zarginba kuma sai haihuwa da akullum maman Aaida ke kawaɗaita mata ta sanadinta zata iya samun soyayyar Abdallah, tunda sunyi dukkan wasu dabaru yaƙi hawa network. Da farko Adawiya batason ta haihu yanzu, amma da taji wannan magana daga maman Aaida sai taji ƙwaɗayin hakan itama dan tana masifar son Yah Ab. To amma sai me? Har yanzu babu ciki babu alamarsa a gareta, har zuwa asibiti tayi a ɓoye aka dubata Doctor ya tabbatar mata inhar bata daina sha maganin hana ɗaukar cikiba bazata taɓa samun ciki ba.
Wannan magana ta daki zuciyarta, dan a ɗan hasashenta ta fahimci kenan maganin da Yah Ab ke bata kullum na hana ɗaukar cikine? Duk da zuciyarta taƙi aminta da hakan sai taji tana ƙwaɗayin dubawa ta tabbatar. Wannan shine dalilin kai kawonta tana nazarin hanyar data dace tabi wajen binciken maganin a ɗakinsa batare daya saniba ko ya ganta. Saboda haka taƙi zuwa makaranta yau ta zauna gadin fitarsa. Sai dai kuma har yanzu bataji ko motsin alamar zai fitoba balle tayi tunanin fitar tasama kamar yasan mi take shirin yi....
(Humm muje zuwa baby Adawiya😉😂).
Dr Yoohan ya bama matar da yazo kano dominta dukkan gudumawar data dace har ALLAH ya bashi nasarar dai-daita komai da taimakon Dr Aysha. Sai dai fa Dr Sa'ad yasha masifa dan tabbas harda sakacinsa. Ba komai ya sashi sakacinba kuma sai kasancewar matar talakace, hasalima Dr Yoohan shine ya biya mata kuɗin aikin dukda kuma shine yayi aikin. Ya kuma bama marayun ƴaƴanta wasu ƴan kuɗaɗe tare da buƙatar takardun makarantar babban yayansu dake riƙe da gidan da ƴar sana'arsa ta saida ruwa a cikin kasuwa. ALLAH ya taimakesa tun mahaifinsu nada rai ya haɗa diploma ɗinsa da ƙyar da siɗin goshi. Wannan alkairi nasa a garesu ya sakasu cigaba da jera masa addu'oin fatan alkairi da nasara a rayuwarsa. Tare da fatan ALLAH yasa yanada rabo cikin addinin islama.
Tunda Dr Sa'ad yaga Dr Yoohan ya wuce sai ya fara sakaci da kula da matar yanda ya kamata saboda takaicin ƴarta data bijire masa tun farko. Da farko shine zaima matar aiki akan matsalarta, ya buƙaci kuɗaɗe masu nauyi daga wajensu na aikin amma suka tabbatar masa basu dasu. Sunta roƙonsa ya taimakesu ko rabi su bada kafin ta warke sai su cika ya nuna bazai iyaba, sai kuma ya koma ta bayan fage ya nema yarinyar matar akan inhar zata bashi kanta shiko zaima mahaifiyarsu aiki ƙyau bama sai sun biyaba. Itako tace bazata aminceba, dan ran mahaifiyarsu a hannun ALLAH ya ke, sun kuma dogara da shi.
Wannan shine farkon matsalar. Lokacin da Dr Sa'ad ke bibiyar yarinyarnan saiko karaf a kunnen Dr Aysha, hakanne yasa ta koma a ɓoye ta kira Dr Yoohan da roƙon ya taimaki yaran inhar yanada halin yin hakan. Da yake tasan yana Abuja yana hutun kwanaki uku. Sanin ƙyaƙyƙyawan halin Dr Aysha ya saka Dr Yoohan yarda ya baro Abuja ta mota ya nufo kano. Da taimakonta sukaima matar dukkan hidima, ya tafi yabar amanar kulawarta a hannunta ita da Dr Sa'ad. dan Dr Aysha ta ɓoyema Yoohan sunansa dan kare masa mutuncinsa.
Da Dr Sa'ad ya fahimci Dr Aysha ta ɓoyema Dr Yoohan sunansa da ainahin gaskiya sai yay shirin ɓata aikin da akaima matar saboda jin zafin rashin haɗin kai da bai samuba na yarinyarta. Dr Aysha dake taimaka musu kuma data fahimci hakan ta tabbatar masa saita sanarma Dr Yoohan ɗin komai. Wannan shine yay masifar tada hankalinsa kafin ta sanarɗin shi ya kira ya sanar.
Yunwa da gajiya taima Dr Yoohan rumusu zuwa yanzun, haka ya fito a matuƙar wahale Dr Aysha biye dashi tana masa bayani akan nasarorin da suka samu game da sauran aikin da yayi a wancan zuwan kafin yima wannan matar aiki. Sosai yaji farin ciki a ransa, dan haka ya biye mata suka shiga zagaya ɓangarorin da marasa lafiyar suke yana dubasu.
Duk inda ya gitta addu'a ake binsa da shi, duk da wasu da an masa addu'ar zakaji sunce. Arne ne fa. Jin hakan kansa wasu jikinsu yay sanyi. Wasu kuma suce dan arne ne baza'a masa addu'a ba bisa ga ƙyautatawarsa?.
To shidai baimasan sunayiba, dan farincikine shimfiɗe a ransa ganin nasara na kuma ziyartar aikinsa a koda yaushe. Amma duk da wannan farin ciki sam babu fara'a kota sisin kwabo a fuskarnan tasa saboda halittarsace haka rashin fara'ar.
Suna kammala zagayawa ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa. Ganin yaci a wanni uku a cikin uku da rabi na hutunsa ya sauke ɓoyayyen ajiyar zuciya. Bashi da tabbacin samun jirgi mai komawa Lagos yanzu, dan haka ya yanke shawarar nufar Abuja a mota kawai, sauran patients ɗinsa kuma sai dai Richard ya dubasu.
Da wannan tunanin yayma su Doctor Aysha sallama ya fito batare da ko office ɗinsa yay tunanin shiga ba. Amma duk da haka sai da Doctors ɗin dake matuƙar yinsa suka firfito suka gaishesa, sannan suka yo masa rakkiya zuwa wajen guards ɗinsa da basuyi tunanin fitowar tasa ba a yanzun. Dan Solomon suke ta bama labarin abubuwan da suka faru game da kama Nu'aymah da aka turosu yi.
Cike da farin ciki Solomon ke wata shegiyar dariya, ya ƙyalƙyale da ita yana faɗin, “Inason kafin kuje abuja da ita kuci ubanta a hanya ta ƙarasa da ƙafa ɗaya. Kai bama nason taje da numfashi gaba ɗaya. ku kaita da rabin rai yanda oga zai ƙarasata da kun isa, dan bana fatan kafin mu dawo Abuja boss yaji koda ɓurɓushin labarin abinda ya farune. Kunsansa ɗan hana ruwa gudu ne. Shi a dole masoyin ƙ..........”
Da sauri Solomon ya haɗiye sauran maganarsa jin ƙamshin turaren Dr Yoohan ya cika wajen. Yay azamar juyawa kamar yanda suma sauran duk suka juya a tsorace.
Ganin yana maganane da Doctors ɗin da sukai masa rakkiya ya sakasu sauke ajiyar zuciya. Dan sun tabbata baiji komaiba.
Dr Yoohan yay sallama da abokan aikinsa kafin ya shiga motar da aka buɗe masa yana nai ɗaga musu hannu hamar yanda suke ɗaga masa. A haka motocin suka fito daga cikin asibitin.
“Sir! Zamu koma airport ne?”. Cewar Solomon fuskarsa ɗauke da murmushin jin daɗin kama Nu'aymah da har yanzu ya gaza barin fuskarsa.
Shiru Yoohan ya musu tamkar bai jiba, yama maida hankalinsa kan files ɗin daya fiddo a jikkarsa yana dubawa. Sake maimaitawa Solo yayi.
Nanma sai da yaja wasu sakanni kafin yace, “Police station”.
Ji kake ƙiyyyyy!!! Driver ya taka wani uban birki a firgice, tare da haɗa baki shi da Solomon waje. faɗin, “Police station kuma sir?!”.
(🙄🙄😏An yanka ta tashi ko masu gadi?).
Idanu ya zuba musu na wasu sakanni fuska a matuƙar ɗaure. Sai kuma ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda ya keyi. Ganin gaba ɗaya wutar kansu ta ɗauke a fusace ya sake kallonsu “Kona canja yaren da nai maganar da shi ne bakuji wannan ba?”.
Da sauri suka shiga bashi haƙuri, driver ya ƙarama mota gudu zufa na keto masa ta ko ina a sassan jikinsa. Kai kace motar babu ac. kallo ɗaya zaka fahimci tsagwaron tashin hankali da ɓacin rai tattare da su. Driver bashi da wata hanyar daya wuce ya ɗauki hanyar police station ɗin da suka bar Nu'aymah. Acan kuma ƙasan ransu shi da Solomon tunanin mafita sukeyi.
Sunci rabin tafiya wani dabara yazoma Solo a rai, dan haka ya ɗauka wayarsa ya rubuta text ya turama Madam Chioma. Mintuna uku ba'ayi cikakkuba sai ga kiranta ya shigo wayar Yoohan.
Idanunsa ya ɗago daga abinda yakeyi ya kalli fuskar wayar. Duk da yaga sunan Mom ɓaro-ɓaro a jiki sai ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda ya keyi. Kiran ya yanke wani ya sake shigowa. Yanzun kam maimakon kallon wanene sai ya lumshe idanunsa ma, sai da sukai kusan sakan goma a rufe sannan ya buɗesu akan su Solomon dake a gaba suna addu'a da fatan ya ɗaga wayar kafin su isa station ɗin.
Lip ɗinsa na ƙasa yaɗan lasa da harshe ya sake maida idanunsa ya lumshe bayan ya kife wayar alamar dai bazai ɗaga ɗinba..
“S...S sir ana kiran wayarka fa”. Solomon ya faɗa da rawar baki.
Tamkar yayi magana da dutse, dan Yoohan yi yay kamarma bai jisa ba, kuma sarai yaji miya faɗa ɗin.
A haka suka iso station ɗin, bai fitaba sai da yaja wasu mintuna, ta cikin motar ya gama ƙarema station ɗin kallo har su Solomon da suka fita suka buɗe masa. Solomon yay ƙasa da kansa ganin banzan kallon da Dr Yoohan ɗin ke masa. Batare da yace da shi uffanba ya zuro ƙafafunsa ƙasa ya fito. Gaba yay suka take masa baya kowanne zuciya babu daɗi.
Duk da ƴan sandan basusan wanene shi ɗinba shigarsa da waɗanda suka rufa masa baya ya sanar dasu ogan gayunne gaba ɗaya. Suda ya kamata ya fara gaidawa sai gasu suke masa tarba cikin tsantsar girmamawa kai kace wani babbane a cikinsu.
Ransa dake a ɓace da guards ɗinsa ya sakashi ɗaga musu hannu kawai batare da ya cire ko baƙin glasess ɗin idonsaba ya buƙaci a kaisa office ɗin d.p.o. Guards ɗinsa zasu magana da nuna masa sunada power ɗin shiga kai tsaye basai an nema masa isoba yay saurin ɗaga musu hannu suma cikin fushi. Tsitt sukayi kuwa kowa kai a ƙasa.
Maida dubansa yay ga ƴan sanda ya sake sanar musu su nema masa iso office ɗin d.p.o. Babu musu suka amsa masa cike da girmamawa, yayinda ɗaya a cikinsu ya nufi Office ɗin d.p.o ɗin domin sanar masa.
“Ranka ya daɗe yace ka shiga”. Ɗan sandan ya faɗa da harshen hausa yana ɗan risinawa. Ko motsi Yoohan baiyiba. bai kuma nuna yaji mi ɗan sandan ya ceba. Wani cikinsu dake acan gefe daya fahimci Yoohan baya jin hausa yay saurin sake maimaita abinda ɗan uwansu ya faɗa da turanci. Sai lokacin ne Yoohan ɗin ya motsa tare da ɗaga musu hannu.
Da sauri Solomon ya buɗe masa ƙofar office ɗin ya shiga. D.p.o yay azamar ajiye biron hannunsa yana mai miƙewa cike da tsagwaron mamakin ganin wanda baiyi zato ko tsammani ba. Shi kansa Yoohan ɗin tsaye yayi kawai yana kallonsa, a ransa yana raya ashe papa yayi amfani da wanda ya sanine shiyyasa ya nuna ƙarfin ikonsa.......
D.p.o ya katse tunaninsa da faɗin, “Oh God! Dr Yoohan!”. Hannu Yoohan ya saka ya zare glasess ɗin idonsa, batare da ya amsa d.p.o ba ya zuba masa idanu kawai kamar mai nazari. Har inda yake d.p.o ya ƙaraso shi, ya nuna masa kujera cike da girmamawa yana faɗin Please Sir ka zauna, ka taimakeni ka zauna”.
Kamar bazai zauna ɗinba, sai kuma miya tuna oho masa sai ya zauna a kujerar da d.p.o ya gyara masa tare da harɗe ƙafafu ya ɗora glasess ɗinsa saman table ɗin.
D.p.o daya koma tamkar ya mance da matsayinsa da kansa ya buɗe fridge ya ɗakko ruwa da lemo da kofi ya ajiye saman table ɗin. Abin mamaki duk ya wani rikice.
Nu'aymah na zaune a office ɗin ta cusa kanta cikin ƙafafunta dake mata wani irin ciwo taji takun shigowar mutum office ɗin. Yanda taji D.p.o na magana ba ƙaramin takaici ya bataba. A ranta rayawa take ‘Shin sai yaushene wai ƙasarnan tamu zata gyarune? Sai yaushene jami'an tsaronmu da duk wasu ma'aikatunmu zasu daina fifita masu hannu da shuni akan talaka? Ta taso gidan da Alhmdllh akwai arziƙi da wadatar zuci, akwai kuma kima da daraja na babban gidan. Dan haka duk inda suka tsinci kansu da wuya kiga ba'a girmamasu, sai dai idan ba'asan su ɗin su wanene ba. Ta tabbata wannan d.p.o ɗin inda ace bahaushene da babu yanda za'ai ya kasajin kunyar tura yaransa har gidansu ɗakkota, koda kuwa za'ace an basa kuɗin toshiyar baki. To amma yanda akema talaka na sosa mata zuciya da ruhi. A yanzu haka shigowarta station ɗin nan taga abubuwa kala-kala da suka sosa zuciyarta duk kuma an yisune akan talaka’. Batare data saniba tsaki ya kufce mata, cikin zafin zuciya da takaicin d.p.o ta ɗago dan taga wane shashasha ne yazo ake masa wannan tarbar tamkar wani IG ko gomnan kanon ma gaba ɗaya.
Akan bayansa ta sauke idanunta, dan ya juya mata bayane bata ganin fuskarsa, ta zuba ma bayan nasa harara duk da bawai ta gane wanene ba.
Yoohan da baisan Nu'aymah nayiba ya kalli d.p.o fuska babu walwala yace, “Inason ka saki yarinyar da papa yasa aka kawo nan”. “Sir amma.....” hannu Yoohan ya ɗaga ma d.p.o da sauri. “Emanuel! Haka kawai nake buƙatar ayi”.
“Za'ayi yanda kakeso sir, sai dai nima ka saurareni ko kaɗanne Please ”. Shiru Yoohan ɗin yayi alamar ya bashi dama. D.p.o daya fahimci hakan sai ya gyara zama, cikin kwantar da murya yace, “Ka taimakeni ka kira Pastor ka sanar masa kaine ka bada umarnin a saketa kar yaga kamar na saɓama umarninsa rayuwata ta shiga garari.
Lumshe idanu Yoohan yayi, wani irin takaici da ƙunci na daɗa faɗaɗa a cikin ransa. Yanajin zafi da matuƙar damuwa idan yaga yanda mutanensu ke masifar tsoron papa. Yakan rasa minene dalilin hakan? Dan kawai yana pastor ne ko me? Kodai akwai wani abu da bai saniba game da mahaifin nasa ne? K........’
“Please sir!”. Maganar d.p.o ta katse masa tunani. Maimakon ya amsa zai kira Papa, sai yace, “Ina yarinyar take?”. Da hannu D.p.o yay masa nuni da Nu'aymah dake bayansu ta sake duƙar da kanta saboda ƙafarta. Kafin Yoohan yace wani abu d.p.o ya bata umarni akan ta taso. Ko motsi bataiba dan abinda ya dameta shine matsalarta ba tsawarsa ba. Yunƙurawa ɗaya daga cikin yaransa yay a fusace zaije gareta Yoohan ya ɗaga masa hannu. Komawa yay ya tsaya inda yake cike da takaici.
Nu'aymah da duk tana jinsu bata motsaba, sai da ƙafarta ta lafa mata. Ƴar sandan da suka ɗakkota a gidace ta shigo bisa umarnin d.p.o ɗin ta taimaka mata ta miƙe. Miƙewar tata tayi dai-dai da ranƙwafawar Yoohan da ya miƙe yana faɗima d.p.o “Police ɗin da suka ɗakkota su maidata, su kuma bama iyayenta haƙuri da wanketa, inba hakaba Emanuel kaine zaka ɗauki laifin”. Da sauri d.p.o ya ɗaga masa kai zufa na keto masa. Yoohan ya ɗauki glasess ɗinsa ya juyo zai saka a ido. karaf suka sauka akan Nu'aymah dake tsaye tana binsa da wani shegen kallo na fusata, dan ko kaɗan batai tunanin shiɗinne yasa a kawota nan wajenba, saboda sam bata wani gane guards ɗinsa ba, hasalima ta manta da shi da abinda ya faru tsakaninsun.
Nunashi tai da ɗan yatsa babu alamar koda tsoro tattare da ita, “Kai ne dama kasa a kawoni nan wajen?” tai maganar fuskarta ɗauke da murmushin takaici, sai kuma ta haɗe fuska da maida dubanta ga d.p.o. “Yallaɓai ai bani na cancanci zuwa nanba wannan mai suffar ƴan damben ne, dan haka nima yanzu na kawo ƙararsa”.
Kafin d.p.o yace wani abu ta fisge hannunta daga na ƴar sandar ta fice a office ɗin da ɗan sauri duk da tana ɗingishi. Saurin bin bayanta d.p.o da ƴan sandan da ke office ɗin sukai, yayinda Yoohan ya lumshe idanu da saka glasess ɗinsa da ganinta ya hanashi sakawa ɗazun shima yabi bayansu.
Isowar su d.p.o yayi dai-dai da furucin Nu'aymah dake tsaye gaban ƴan sandan dake wajen kanta . “Yallaɓai na kawo ƙara”.
A tare suka kalleta, ɗaya a cikinsu yace, “ƙarar wa? A kanmi kuma?”. Juyawa tai inda su d.p.o ke tsaye cike da al'ajabi da mamakinta, dai-dai kuwa da fitowar Dr Yoohan daga lungun da office ɗin d.p.o yake ta nunasa da faɗin, “Ƙarar wannan mai siffar ƴan damben na kawo”............✍
😂Wagga ɗiya kina da tsaurin ido aradu😚🚶🏻.
Barka da juma'a😘😍🤗.
17
Cak qwaqwalwarta ta tsaya da aiki na wucin gadi,komai yayi mata dif tamkar qwaqwalwar tata bata taba wani aiki ba,ta daina fahimtar komai sai maganganun umma luba dake mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,sun dade suna maimaita kansu kafin tasoma fahimtar abinda takeson gaya mata
"Taje ta bada fansar kanta da budurcinta wa yariman qasar kaisa na tsahon shekara daya" a dunqule idan ta fahimta kamar hakan umma luba take nufi ko?,ta jefi kanta da tambayar,saita daga idanunta dasuke walainiya ta xubawa umma luba su,shin tasan ma'anar abinda take fada kuwa?,anya hankalinta daya?,a cikin hayyacinta ma take?,bataga alamun wasa saman fuskarta ba face tsantsar gaskiya dason isar da saqo bare tace wasa take mata,karon farko data motsa labbanta
"Ban gane ba umma,ban gane abinda kike nufi ba" murmushi tasakar mata dukka bisa qoqarinta na kwantar mata da hankali
"Kin gane maigado saidai kicemin kin rude,kuma tabbas koma wacece da bata zaci samun irin wannan damar ba ta sameta sama taka dole rudani ya shigeta,kije kiyi tunani kawai nan da jibi,saboda kwanaki biyar yarage mana muje mukai duk wadda muka samu" wani abu ya tsaya mata iya wuya,ta fahimta takuma fuskanta,wato bazasu akayi suyi farautar yara marasa galihu irinta,musamman idan akayi katari da masoya abun duniya masu kwadayi shikenan kaya ya tsinke a gindin kaba?,duk haqurinta duk sanyinta ba zata lamunci a qasqanta mutunci da darajarta ba,lallai ya kamata idanma umma luba tana da wani tunani na daban a kanta ta warware matashi,don a gaba bata fata hakanan bata sha'awar ta sake soko wata magana makamanciyar wannan a tsakaninsu iya zamansu,koda tanason aure koda lokacin da zatayi aure yayi ita ya kamata ta zaba bawai a zabeta ba,bare a yanzu da qaramar qwaqwalwarta take cunkushe da matsaloli,gajeriyar rayuwarta take quntace take kuma takure,a gaba daya tunaninta da abinda idanunta suke gabe mata shine,aure gaba dayanshi matsala ne,babu komai cikinsa face jefa kai cikin damuwa da matsaloli,me yasa ma zata yarda anan kusa da qananun shekarunta ta fada matsala kwatankwacin matsalolin da taga umma katti da sauran matan da babanta yake aurowa suke fadawa?,shi yasa ko daya bata sha'awarsa,koda ya zame mata dole tana duban nisan zangon da zata qara diba kafiin ta fada komarsa
"Aure a nawa qaramin tunanin ana yinsa ne a sanda namiji da mace sukaga juna suna so,suka kuma amince da juna,shi namijin zai tattako koya tura wakilansa zuwa gidansu yarinya su nema masa aurenta,baya ga haka babu wani sharadi da ake gina aure a kansa na cewa bayan lokaci kaza akwai wani abu kaza dazai faru,yakan zama tarayya tahar mutuwa a yadda nake ganin yana faruwa a mafi yawancin gidaje,kiyi haquri umma luba,ni bazanyi aure ba,koda zanyi aure toba yanzu zanyi ba,ki nemo musu wata,nasan da yawa zasu amince,zan wuce gida sai Allah yakaimu gobe" da mamaki take duban bilkisu,ashe yarinyar ta iya magana har haka,ashe tana da zurfin tunani da hankali?,koda ba'a gaya mata ba iya zamanta da bilkisu ita zata bada shaidar ta iya talaucinta,hakanan ba makwadaiciya bace,amma bata taba zaton zata bijirewa wannan tayin ba.
Ganin da gaske bilkisun tafiyar xatayi,kuma idan har tatafin wata qatotuwar dama ce mai gwabi da zata subuce mata,wadda samu ko maida kamarta saitaci wuya,wala'alla ma cikin abokan aikinta wata takawo tata kuma a karbeta ta rasa dukkan wata dama matsayi da daukaka da zata samu a masarautar kaisa,zumbur tamiqe tana qwalawa bikisu kira wadda batakai ga fita ba,gabanta tasha tana dubanta cikin kwantar da murya da karyar dakai
"Haba maigado,haba,qauna ce fa tasa na zabeki na tsallake dubbai,ya kamata ki dinga sara kina duban bakin gatari,a yadda kikeson 'yan uwanki na zaci zaki iya sadaukar da farincikinki saboda tasu rayuwar ta inganta?,kin gwammace ku dawwama a haka bilkisu bayan ga dama da kika samu ta fidda kowa daga qangin da yake ciki?,shekara daya tak fa rayuwarki zata inganta,me za'a gutsira daga jikinki?" Idanunta masu maiqo tazubawa umma luban tana dubanta ganin yadda ta haqiqance,itadin ba tsararta bace hakanan basu saba 'yar tankiya ba,inda sun saba din da taji amsa dai dai da ita,datace bata amsa yadda ya kamata,tana tsammanin a yadda idanun al'umma suka rufe kowa ya tasa kudi gaba fiye da mutuncinsa itama bikisun haka take?
"Kiyi haquri umma luba kamar yadda nace miki dafarko bazan iya ba,don Allah ki duba cikin dubban ki zaba wata,nasan za'a dace" daga haka tarabeta tafice daga gidan,tanajin iska na dibanta,hakanan maganar na ratsata fiye da yadda ta tsammata,sai taji tun daga kan hanya kamar zazzabinta daya sauka yana niyyar dawowa,maganganun sukaci gaba da juyin waina a tanda cikin qwaqwalwarta,ta rasa ma wanne zata kama.
Tsaka da haka taji kamar ana ambatar sunanta a sanda take qoqarin shigewa gidansu,yanayin yadda sautin ke fita saitaji kamar tasan me kiran,don haka ta tsaya cak ba tare data waiwayo ba,hakan yabashi damar qarasowa gabanta,abubakar saddiq ne,sanye cikin shadda dinkin tazarce,kansa babu hula,kana masa kallon farko zakasan yana ji da gayu da samartaka,jifanta yayi da murmushi saita janye idanunta daga kanshi,hakanan yake mata kwarjini,tasamu da qyar ta tattara lafuzan gaisuwa saman lebunanta ta aika masa,ya amsa idanunshi kan labban nata dake masifar burgeshi,ya fuskanci bayan kyau yari yar tana da wani qasaita da izza wadda wala'alla itadin batasan tana dashi ba,miskilancinta yana burgeshi,hakanan yanayin dakiya da basarwarta.
"Kwana biyu baki ganni ba,amma koki cigiyata ko?" Yafada yana dan fidda murmushi gami da shafar sumarshi,maganar tasa ta sake tarwatsa tunanin dake fareti a kwanyarta,saitayi kaman zata kalleshi bisa mamakin furucinsa saikuma ta basar,ta nemeshi akan me?,idanma tasan inda yake din ya cancanci ta nemeshi?,yasake sakin murmushi ganin yadda tasake basarwa
"Koda yake bakisan inda nake ba ko?,kuma baki sha'awar amsar numberta ba kosau daya,koda kin saninma nasan masu suna bilkisu da sarauta,da wuya anemi din,to gashi na sake kawo kaina a karo nabiyu,kuma sai naga kamar sauri kike,ko zaki aramin minti goma cikin mintunanki muyi magana?" Da sauri ta girgiza mishi kai alamun a'ah,duk da hakanan take ganin qimarsa,amma a yanzun bata sha'awar dogon magana,dan shuru yayi alamun baiji dadi ba,amma saiya dage kafadunsa
"Ohk,ba damuwa,asake samin wani lokacin saina dawo muga juna....,ko a bani phone num saina kira ko?"
Kafin tabashi amsa babanta yafito daga cikin gidan,tunda taganshi tasan komai zai baci ne,don haka tabude bakinta dasauri tace
"Sai jibi in sha Allahu,babu damuwa" yasaki murmushi,don ba qaramin dadin amsar jibin data bashi yaji ba
"Allah yakaimu,na gode qwarai". Kafin ta amsa ya iso garesu,don haka saita wuce zuwa cikin gida kawai tabarshi da sadiq,koma meye ita bata sha'awar yafaru a gabanta.
Ko kadan a cikin ranta bata ji ta daina zuwa aiki gidan umman luban ba,a nata ganin komai yana da muhallinsa,yadda maganarsu keda muhalli na daban haka aikinta ma,babu abinda zai shafi wani,saidai yadda maganar ta tsaye mata yasanya washegari bata da qwarin jiki dana zuciyar tafiya gidan aikin.
Rashin zuwan nata yasanya umma luba babu abinda bata saqa ba,abu na farko tsoron tawaye daga wajen bilkisun kamar yadda ta raya,don haka wata washegarin ta yanke gwara ta fuskanci fulani da maganar,wala'alla asamu wata mafitar.
Kamar kowanne lokaci idan zatayi ganawar sirri da amintattun nata,waje ne kebantacce wanda yake cike da sirri da aminci,fulanin aysha ce daga tsaye cikin shigar alfarma dake nuna xallar mulki da sarauta,yayin da umma luba ke zube a gabanta,kanta a qasa bayan ta kammala dukkan bayananta.
Tattaki fulani aysha tayi tana nazarin maganar da umma luban tazo mata da ita,tasan tunda lubabatun takasa sukuni kan lamarin babu ko tantama yarinyar ta cika mace,takuma cika dukkan sharuddan data gindaya musu kafin fararwarsu aikin,ba shakka ba umma luba kadai datasan yarinyar ba,har ita kanta tacika da mamakin yadda za'a samu wasu ko wata cikin qasarsu da zata iya bijirewa wannan tarin alkhairi dasu a nasu ganin suke ganin kamar alfarma ce sukayiwa koma wacce diya ce,eh mana alfarma,tunda banda wannan dalilin da ko cikin mafarkinta bata taba hasashe ko hango azeez din yana nema ko auren daya daga cikin yaran talakawansu ba,azeez din mai tsada ne,saboda haka dole komai dazai rabeshi yazama mai tsada mai daraja
"Kin tuntubi mahaifinta?,idan kin tuntubeshi shidin me yace?" Fulani ayshan ta jefa mata tambayar,ta girgixa kanta da sauri
"Tuba nake Allah ya taimakeki,sam sam na manta da wannan,ai Allah yabaki yawan rai ina da yaqinin cewa idan na tuntubeshi ma magana ta qare,yanzu kuwa zan tashi,bazanyi qasa a gwiwa ba zan sami mahaifinta" murmushi fulanin tayi cikin zuciyarta,don idan ka kalli saman fuskarta ba zakaga alamunsa ba,saita soma takawa zuwa saman daya daga cikin kujerun tana dauko wata jaka tana kuma magana da umma luban
"Ki jaddada masa matsayin wanda ake nemawa diyarsa koda shima zaice zaya musa,daga yanzu bana buqatar a sake magana da ita yarinyar,yardar mahaifinta tamkar yarda ce,abunda nake da buqata kawai shine,hoton yarinyar don inason in ganta dakyau,na tantance kuma na tabbatar da dacewarta da yarona" tana kaiwa nan taciro kudade rafar 'yan dubu dubu tana miqawa umma luba,jikinta na rawa cikin sauri ta amshe tana zuba mata godiya kana tataso cikin farinciki tafito daga falon tana cusa kudin cikin zaninta,tana kuma jaddadawa kanta lallai zatayi dukkanin me yiwuwa taga komai yatafi yadda akeso,takuma cimma nasara.
A lokacin da umman luban tazo tana daga daki kwance,taji murya kamar tata,amma sanin cewa babu wani abu da zai kawota gidan saitaci gaba da kwanciyarta tana jan istigfari cikin ranta kamar yadda tasaba yi a yawancin lokuta idan bata da abunda zatayi,ita daya ce cikin dakin tana sanya ran gobe tawuce wajen aikinta,dukka qannenta sun tafu islamiyya,Allah yasanya weekend ne gobe take saka ran zuwa har makarantar boko.
A falon amarya ladidi tasauka,lokacin yana zaune saman daya daga cikin kujerun falon,gama sa'insarsu da ita kenan akan shinkafa,tace haram tabashi abincinta yaci,tunda rabonshi da kawo cefane yau kwanaki uku kenan,yayi barazanar da muzuran duka a banza ladidi ta dauke kanta,yunwa ce kawai ke sadakarshi,gashi babu ko sisi cikin aljihunsa,yasan ko giyar wake yasha bazai tunkari katti tabashi abinci ba,don tunda ya qara auren nan taja masa layi,irin layin da bata taba ja masa ba,ta tattarashi dukka ta barwa ladidi shi,ta yaranta kawai da sana'arta take.
Ya sake shafa cikinsa yana tsinewa talauci karo na babu adadi,sam a rayuwarsa bai taba kawowa zai tsunduma cikin talauci irin na wannan qarnin dana yafa ba,dai dai lokacin da ladidi ta dage labule suka shigo tare da umma luba
"Baquwa ce takeson magana dakai" ladidi tafada tana wucewa uwar dakanta don adana miyarta data gama soyawa,yabi kwanon da ita kanta ladidin da kallo yana hadiyar yawu kamae tsohon maye,don tuni qamshin miyar yagama cika mishi ciki yasake tada mishi yunwarsa.
Gaisuwar da umma luba keta faman rattabo masa tadawo da hankalinsa,saiya maida hankalinsa gareta yana amsawa cikin yanayin nuna rashin sanin mutum,saita taqaita masa wahalar dakai ta gayamishi wacece ita
"Uwar dakin maigado ce,gidan da take aiki" gyara zamanshi yayi gabanshi nadan faduwa,yayin da wani sashe na zuciyarsa yacika da fatan Allah yasa kudin aikinta takawo mata ganin kwana biyu bata je ba ya amsa ya kalmashesu ya rage radadi na kwana biyu
"Au.....to....to,madallah,ina fata lafiya daiko?" Murmushi tayi tana gyara zamanta
"Lafiya lumi,sai alkhairi dake tafe dani" jin haka yasa yasake tattara nutsuwarshi yana dubanta,tadan karkace ta zaro rafa daya ta dubu dubu cikin irin wadda fulani aisha ta mata kyautarta ta aje gefan malam bilya,bin kudin yayi da kallo a mamakance cikin ranshi yana qissima abubuwa da yawa
"Kadda ace kudin aikin nata takawo mata,to amma maigado na karbar maqudan kudi haka masu yawa amma bata taba jin qaina ba?,kodai yau Allah ne ya toni asirinta?"
"Wadan nan....dama wasu masu tarin yawa zasu zama mallakinka matuqar ka aminta da maganar da nake tafe da ita" mamakin jin zai mallaki kudin suka kamashi,saiya dafe kudin yana sake gyatta zamanshi
"Wacce magana ce wannan baiwar Allah?".
Ba tare data boye mishi komai ba tayi masa bayani filla filla,ta shaida masa yadda sukayi da bilkisu a gidanta,sannan ta rufe bayanin nata da gaya masa irin tarin maqudan kudaden da zai samu da alkhairi iri daban daban.
Ba malam bilya bs,hatta ladidi dake daki wadda dama fakare tayi batasan sadda tafito zuwa falon ba tana rarraba idanu tare da qissima yadda zata sake kame mijinta malam bilya matuqar hakan ta kasance
"Kan ubancan!,amma ban taba sanin baqincikin maigado ya ta'azzara har haka ba da tuni na jima da nema mata maganin samun salama,ashe yarinyar nan bata qaunata duk ban sani ba sai yau?" Yafada yana duban ladidi wadda tasamu waje daura dashi tazauna itama tana neman muhallin da zata tofa tata
"Ai malam kada kasake kada kabari wannan damar tawuceka,koda a mafarki kasameta aika more ballantana a gaske" ladidi ta tofa din kamar tadda bakinta yaketa motsi tunda tafito
"Niko ladidi idan nabar hakan ta kasance a cikin tababbu marasa rabo ai nine sahun gaba,maigado zataci ubanta,wanne amfani zatamin na tsahon shekara gudan dazai kawomin wannan alkhairin" da sauri umma luba ta dakatar dashi
"A'ah malam,bada zafi zaka mata ba,kayi mata cikin hikima da lallashi wataqila tafi fahimtarka a matsayinka na mahaifinta,kaga babu yadda ban kwatanta mata ba amma taqi,ni kuma qauna ce tasa na zabeta cikin dubbai,inasonta da wannan alkhairin" wuyar rigarsa daya zame yajawo yazauna sosai saman kafadarsa,cikin nuna isa da hura qofofin hanci yace
"Yo yarinyar dana haifa a cikina ma saina tsaya ina lallabata?,ai indai nine na haifi bilkisu to kije kawai ki shaidawa ranki ya dade.....koma ku rankaya tare mu sanar mata na bawa yarima ita,zan mata lallashi nafarko amma idan na fuskanci asara takeson jaza mana tofa bazan mata ta dadi ba....kekam babu abunda zamuce dake sai godiya,don ba qaramin masoyinka bane zaiga alkhairi haka ya rungumo ya nufoka dashi".
Kowannensu cike da farincikin zuwa gabar samun cikar burinsa sukayi sallama,don bata tsaya taga bilkisu ba bare tasan da zuwanta ko suyi magana.
Miqewa malam bilya yayi yana jinsa yau da wani irin nauyi sanda yake cusa rafar kudinsa a aljihunsa,ganin yasoma haramar ficewa sai ladidin ta lanqwasa murya
"Malam,bakaci abinci ba zaka fice" harara ya watsa mata
"Ki riqe kayanki mana kici ko zaki qara kumari,an gaya miki ni matsiyaci ne?,ni nan da kike gani duk inda nayi arxiqi bibiyata yake a jinina ne"
"Kayi haquri malam....karka watsamin qasa a ido mana,ta yaya zaka iya shawo kan yarinyar nan bayan kasan cewa mace sai mace 'yaruwarta,nina gama tsara yadda zamusha kanta amma naga kana da niyyar botsarewa" jin ta ambaci kalmar shawo kan bilkisu yasan kuma ladidin akwai hikima saiya sassauto,yana wani ciccin magani murya ciki ciki yace
"To yanzu ya za'ayi?" Tamiqe da hanzari tana cewa
"Kasan kwananta wajen nawa kamar bata da lafiya,kuma gidan nan kasan cewa ba wani cikakken abinci gareshi ba,yanzu haka qila tana kwance bataci komai ba,bari na zuba maka abincin saina tasota itama na zuba mata tazauna kunaci tare kana janta da hira harka sako mata zancan" dariya yasaki
"Yauwa ladita,ladi ga tsiya ga dadi" ya qarashe maganar yana komawa mazaunin daya tashi dazu,yayin da itama tasaki dariyar tana wucewa zuwa uwar dakanta,tasamu farantai biyu tayi zubin shinkafa da miya da salad harda nama tafito falon dasu,ta ajesu dukkaninsu a gabanshi kana tafice don kiran bilkisu.
Cikin mamaki ta amsa sallamar jin muryar wadda yau tashigo dakinsu,matar da tunda tazo gidan ko ta qofar dakin nasu bata taba wucewa ba bare tayi batan kan shigowa koda me yake faruwa kuwa cikin gidan.
Tilas tamiqe tazauna ganin murmushi saman fuskar mama amarya makar yadda yaran gidan suke gaya mata,saita qaraso tadan tsaya daga gefan bilkisun
"Sannu maigado,jikinne dai?" Wani mamakin yasake kamata,saita daure ta gyada kai harda qarin bayani
"Alhmdlh nasamu sauqi ma"
"Masha Allah,naji dadi,babankune sai haquri,baya kyautawa wallahi sam,koda baka da kudin hidima da iyalinka amma ai aqalla ka jasu a jikinka ko?,yanzu gashican duka yadamu,yanason miki sannu amma yana nauyin wai bai siya miki magani ba tunda kika kwanta"
"Baban namu!" Tayi subutar bakin fada cikin muryar dake nuna zallar mamaki idanunta kan ladidi,don iya abinda hankalinta zai iya tunawa bata taba ganin alhini saman fuskarsa don daya daga cikinsu bashi da lafiya ba,kai ta gyada tana murmushi
"Shi dinfa,shi matsalarsa idan baida kudi saiya watsar da kowa maimakon yayi bayanin bashi dashi ne,yanzuma shine ya aikoni yace kizo yana son ganin jikin naki" kusan daskarewa tayi,don bata ma gane ba saida ladidin tasake gaya mata,sannan tamiqe jiki ba qwari ta ciro mayafinta dake rataye jikin qofa cikin mutuwar jiki tabiyo bayan ladidi,don hakanan kawai jikinta ya bata dukka abinda yake faruwa ba gaske bane bogine,akwai wani abu aboye a qasa,don ruwa baya tsami banza,dabi'ar data zama jini da tsoka tsahon shekaru sama da ashirin ba qaramin abu bane zai sauyata cikin gaggawa haka ba,amma kome meye zataji zata gani,don kusan tafi kowa karantar halayyar baban nata cikin yaranshi,saboda dogon zama da sukayi tare dakuma baiwar fikira da Allah yayi mata na saurin fahimtar abu.
*S R B*
18
*_Zafafa biyar na kudine,kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,gamai buqatar mallakar nashi saiya tuntubi wadan nan numbers din_*
0903 234 5899
Ko
09033181070
18
Sanda suka shiga dakin tuni ya soma nisa wajen kai lomar abincinsa,bakinsa cike da shinkafa yake nuna masa inda ya aje daya plate din yana cewa
"Qaraso nan maigado,sannu,Allah yayi miki halin juriya irin na maimunatu na" duk da tazauna a inda ya nuna matan amma bata dubi abincin dake wajen ba,don sam ko kusa ko alama ko amafarki bata taba kawowa a ranta nata bane
"Gani baba" ta fada kanta a duqe kamar yadda suka saba yawancin lokutta,saboda tsananin rashin sabo da rashin jansu a jiki
"Yaya jikin naki?" Sai data masa duban mamaki kana tasake maida kanta qasa ta amsa
"Da sauqi alhmdlh,na warware"
"To madalla,madalla" soma yunqurin miqewa tayi,ya dakatar da ita da sauri
"A'ah,zauna mana ga abinci nan kici,kya tashi bayan ke aka zubowa?" Duban abincin tayi tadubi baban nata,yasan cewa tambayoyine fal a bakinta,amma kasancewarta bamai yawan surutu ba sautari kana gane tana da abun fada ne da hanyar duban abu da idanu
"Zauna kici maza,keda ba isashshiyar lafiya gareki ba" mama ladi tasaka baki,saita koma tazauna cikin matuqar sanyin jiki tajanyo abincin gabanta.
Tsananin rashin sabo da mamaki suka sanyata kasa kai koda loma daya bakinta,sai faman juya abincin kawai take da cokali tana sauraren hirarrakin da baban nata yaketa soko mata,wadda ta kasa bashi cikakkiyar amsar koda abu daya,saboda jinta take gaba daya banbarakwai,har zuwa lokacin daya kammala cin nashi abincin,saita aje cokalin itama tamiqe
"Zauna mana me gado,wai saurin me kikeyi?,magana zamuyi ai" yafadi dai dai sanda mama ladi ta jiye mata ruwan randarta mai sanyi a kofin silba a gabanta tadora da cewa
"Shine ai,kamar ana cizonki".
Shuru ne ya ratsa dakin na wasu mintuna yana kama zaren maganar farawarsa zuwa qarewarsa,sa'annan yaja wata gyaran murya mai kauri kafin yasoma magana
"Wato maigado haka Allah yake lamarinsa,saika haifi yara rututu amma a cikinsu sai Allah ya daukaka darajar wani,yayi masa nasibin da kaf cikin yaran naka babu maishi,wani al'amarine ya tunkaromu na alheri wanda dukkaninmu alherin xaibi ya shafi kowa da kowa haula da zuri'a,amincewarki kawai muke nema harni mahaifinki".
Yana fadin hakan taji gabanta ya yanke yafadi,tasoma ambatar sunan Allah tana addu'ar rabbi yasa ba abinda zuciyarta take raya mata bane,idan kuwa shine ta tabbatar da cewa ta kade daga ita har ganyenta
"Gidan sarautar garin nan suke neman izinin hada zuri'a dani ni malam bilya na shekara daya,wanda acikin shekarar zasu azurtani na zama daya daga cikin jerin alhazawan da ake zance,nasan ke yarinya ce mai biyayya,ba zaki taba cewa komai ba akai,saboda haka tunima na bayar da aiken cewa nabasu ke!" Kamar saukar ruwan sama da tsawa haka taji maganar tashi,ba tare data shirya ba wasu hawaye masu dumi suka soma layi tun daga cikin idanunta zuwa saman kuncinta. Lahaula wala quwwata illa billah!. Ta sani dama tasan xa'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,tasan cewa matuqar wannan batun yashiga kunnuwan mahaifinta to magana ta riga data qare.
Dukkaninsu sunga hawayen dake zirya a fuskarta,hakan yasanya mama ladi gyara zama gami da dora nata sharhin
"Duk ɗa nagari burinsa shine ya farantawa iyayensa yacika burinsu,kuma alhmdlh kedin kin samu shaida a wajen mahaifinki,don kaf ƴaƴansa babu wanda yake naci da damuwa dayimin zancanshi shida mahaifiyarsa irinki,shi yasa muke da kyakkyawan fata dakuma zaton ba zaki watsa mana qasa a idanunmu ba,don ke kanki basai an gaya miki ba cewa babbar masarauta ce take nemawa babban yaro kuma magaji a wajenta aure,kinga wannan bama lamari bane da za'a ce an tsaya ana jayayya akai ko tantama ba" duk da hawayen dake idanunta hakan bai hanata duban umma ladi ba,ba abun mamaki bane donta fadi hakan,saboda sama taka ta ganta,batasan cinta shanta ba bare sutturarta,ba'a maganar lafiya da ilimi harta kawo wannan minzalin,idan akwai wanda zata zarga shine mahaifinta,da har ya amshi wannan wasan yaran hannu bibbiyu yake da muradin wanzar dashi,ba tare daya tuna cewa diyarsa bace ita jininsa ce,dukiya ta rufe masa ido,koda baisan komai na dawainiyarta ba,baison ciwo da zafinta ba amma ai tsatsonsa ce
"Kayi haquri baba,karka bada aurena ta wannan sigar don Allah,hanyar da duk wani mutumin qwarai yaji zaiyi Allah wadai da ita,idan ka matsu ne na matsa daga gabanka,kana iya neman wanda zai aureni saboda Allah,ya riqeni saboda Allah,yaqaunaceni saboda Allah,yakuma zauna dani saboda Allah,wanda zaiga girma da mutuncinka martaba dakuma qimarka,ka duba maganata don Allah" ta qarashe fada cikin rauni,duk da cewa tafada ne koda wani abu zai iya taba ranshi ya waiwaya yadubi abinda yakamata,tasanshi sarai akwai kafiya da tsaiwa kan maganar da yakega tayi masa kuma itace dai dai,ba kasafai ake sauko dashi daga dokin naƙi ba idan yahau.
Cikin hargagi da kaurara murya yace
"Ke bilkisu!,naji duk abinda kikace da uwardakinki,nasan kuma dama ra'ayinki kenan,to ba yardarki nake nema ba,hakanan ba shawartarki nake ba,na yanke hukunci ne a matsayina na mahaifinki wanda yake da iko dake,ki yarda kokar ki yarda wannan ya rage naki,tashi ki fita ki bani waje".
Wani irin duhu duhu da hajijiya take gani,haka ta dinga laluben hanya,a daddafe takai kanta dakinsu,tazube tana sakin wani marayan kuka,karo na barkatai tasake fadawa cikin halin bege da fatan inama ace anty zuhra tana nan,inama ace anty zuhra zata dawo kafin mai afkuwa ta afku,tasan idan da tana nan zatayi dukkan maiyiwuwa ta hana faruwar lamarin,duk da matsananciyar ƴar tsamar dake tsakaninta da mahaifin nata.
Ranar za'a iya cewa ba ita kadai ba,hatta da ƴan ƙannenta babu wanda ya runtsa,ta kasa boye tashin hankalinta sam,kuka tayi mai yawa wanda ya qara yawan zazzabin da tayi tunanin yatafi kenan ashe yana labe,yasamu mafaka kuwa yasake rafketa.
************
Washegari bayan duka qannenta sun wuce makarantar Allo,tana kwance a daki ita daya,tanaji tana gani makarantar data ci burin taje yau hakanan tabi ruwa,don bata da ƙwarin jikin da zata iya niƙar uwar tafiyar data saba.
Mama ladi ce tayi sallama tashigo dakin dauke da kofin silba da faranti mai dauke da kunu da wainar gero
"Sannu maigado,tashi kisanyawa cikinki wani abun kinji,su iyaye haquri ake dasu ana musu biyayya don a wanye qalau" hakanan ta qaraci babatunta ta fice,batako daga kai ta dubeta ba bare ta tanka mata,kamar ta sanya qafa ta shure abincin haka gaji,abun sam babu Allah a ciki,yau da qyar tasamu ta hadawa qannenta abinda sukaci da safe suka wuce makaranta,babu wanda yadamu da basu koda danyar qwayar gero,amma ita din yanzu gashi ana bibiyarta da abincin har shimfidar kwananta.
Umma katti ce ta bankada labulen dakin tashigo,fuskarnan a dinke tsaf kamar hadarin kaka,wanu kallo takewa bikisun sannan tace
"Wai me yake hadaki da waccar matar da naga daga jiya zuwa yau sai wani haba haba takeyi dake?,ko wani sabon munfurcin da tuggun xa'a hada baki dake a qullamin?,to idanma hakane ina mai gargadinki dajan kunneki ahir dinki,kuma shima munafukin uban naku wanda nasan da saninsa ake shirya komai zanje yanzu nasameshi,don ba'a siya sai dana gama dawainiya daku daci daku sannan azo za'amin wannan iyayin ba ehe" daga haka tajuya tafice tana mita.
Batasan ya suka ƙarke ba,amma ga mamakinta da daddare itama saigata da nata abincin tana mata magana cikin lallama,inda ta dangwarar da wancan da wanda mama ladin tasake kawo mata a nan ta dangwarar da natan itama.
********* ***********
Kashingide take saman lallausan carfet din dake madaidaicin falon alfarmar tana amsa wayar sumaira,wadda ke karatu a qasar kano jami'ar bayero,tana hannun yayarta uswa dake aure a masarautar kanon.
Yanayin yadda take amsa wayar kawai ya isa ya nuna maka zallar yadda qaunar 'ya'yan nata,wanda dama hakan aqidartace,halayyarta ce son ƴaƴa
"ƙarshen watan nan muke sanya ran zuwa ma ammi,mu duka harda anty uswa,su irfan zasu samu hutu" cikin jin dadi tace
"Allah ya kawominku lafiya,dama inason ganinku gaba dayanku" daga nan sukayi sallama kana ta maida kanta ga umma luba dake duƙe gefe tana jiranta
"Uhmm,ina saurare" gyara zama tayi tana fidda murmushi
"Ai Allah yabaki yawan rai,Allah ya dafa miki tuni an wuce wajen,don mahaifinta ma yace yabaku,ai babu mai iya ja daku,ya amince yabaku ita" murmushi fulani tasaki,sannan tatashi tazauna sosai
"Dakyau,aikinki yana kyau lubabatu,tun zuwanki nafarko naji dukka hankalina ya karkata kan naki zaben da kikayi,saboda na tabbatar ayadda kika kasa zama kikazo kika shaidamin komai yarinyar ta hau mixanin da nakeso,hakan yayi". Farinciki ya cika zuciyar umma luba,tana ganin kakarta gab take da yanke saqa cikin masarautar kaisa
"Allah yabaki yawan rai,godiya nake,na gode da yabon dana samu daga gareki,yanzun Allah ya taimakeki kina da buqatar ganin yarinyar ne a kawota?" Hannu ta daga mata kana tace
"Bani nake buqatar na ganta ba,inajin yarima shi yafi cancanta ya ganta,idan tayi masa shikenan sauran ayyukan sun gama kammaluwa,abinda kawai yarage sai daurin aure,dakuma biki daga can nasu bangaren,don a nan bangaren namu,bana fatan koda ƙadangaren gidan nan yasan da maganar balle jama'a" cikin girmamawa ta rusunar dakai
"Baki da wata matsala Allah ya taimakeki,yadda kika dama haka kowa zaisha,tauraruwar mai martaba,hasken masarautar kaisa....in shaidawa yarinyar su shirya tafiya can ƙasar da yarima yake kenan?" Kai ta girgiza
"Eh....su shirya cikin satin nan zan sama muku visa keda ita da mahaifinta da mahaifiyarta"
"Angama ranki yadade,Allah yasa ki gama lafiya,godiya nake,nizan koma don nasamu zarafin isar da saqonki" ta furta cikin zumudi da farinciki,don nata manta qasar ba,bata kuma manta irin dadi da kashe ƙwarƙwatar idanu da sukayi ba,duk da cewa dubiya sukaje amma sukam fes haka suka dinga jinsu,kamar wancan karon wannan karonma sai data wanke umma luba da kudi,ba tare data damu da cewa kwanaki kadan ta bata wasu masu yawa ba.
Zuciyarta fes,ranta fari qal,babu tunanin komai a ranta,saima hasaso yadda komai zai tafi dai dai take,yanxu abinda yarage shine tasoma nema musu visa kamar yadda ta gayawa umma luba,wayarta dake aje gefanta tadauka tasoma neman wata number,saikuma ta tsaya saboda wani ɗan gajeran tunani da tayi,tasauya akalar kiran nata zuwa layin azeez,tana kiran tana mita can qasan ranta ita daya,tunda sukayi maganar da ita bai sake tada zancan ba,iyakaci idan yakira suka gaisa sukayi maganar data shafesu shikenan,kamar ma bai damu ba ko nashi da interest akan zancan,itakam babu abinda zai dakatar da ita,tasan gata ne zata masa,don ta yadda yake sharewa kuwa tasani da zarar taga matar a gefanshi zai ware ya manta komai.
Yanzun kam dole tasoma samunshi da maganar,tasan halin miskilancinsa,sai suje yaqi ganinsu harsu dawo suyi zuwan banza,wannan kadanne daga aikinsa.
Dai dai lokacin da azeez din suke zaune a wani wajen kebantaccen wajen shaqatawa,wajene da za'ace yana da tsarki akan sauran guraren shan iska dake mexico city.
Komai nashi farine da ratsin baqi dan kadan,kamar yadda na lura kusan dabi'arsa ce son farin abu,farin wando ne a jikinsa mai azabar kyau wanda ya zarce gwiwarsa amma baikai idon sahu ba,sai shirt me gajeran hannu,v neck wadda tafidda qirar halittarsa,kallo daya zaka yiwa dantsensa kasan yana daga qarfe,qafafunsa rufaffun takalma ne hightop suma farare qal dasu kamar ba'a taba sanyasu ba,sai kanshi dake saye da p_cap fara mai adon baqi a jiki,wadda ya jawota ne sosai tarufe fiye da rabin fuskarsa dake duqe kacokam kan farar laptop dake saman cinyarsa,yana latsata a nutse da hannunsa dake dare da baqin agogo rolex na fata wanda yazauna sosai a hannun nashi.
Saboda shi abokan nashi suka shirya wannan fitar bisa amincewarsa bayan ya tabbatar da tsarkin wajen,amma idan kaga yadda yayi shakulaton bangaro da hirar tasu saika zaci shidin bare ne a cikinsu ba tare suke ba,duk da irin shewa da suke bugawa irin ta zaratan samari da jini ke yawo a jikinsu,hakanan duniya ke gara musu yadda ya kamata.
Suma basu wani damu ba,tunda idan da sabo sun saba da halayyar azeez,ba kasafai zaka sameshi yana hira ba,ba qaramar sa'a ka taka ba duk sanda kuwa ka sameshi yana hirar,ba kowacce irin hira ke burgeshi ba,hakanan ba'a kowanne yanayi yake zama ya bata lokacinsa wajen yin hirar ba,koda yazauna a cikinsu zaka sameshi da waya ko tab a hannu yana wani abun daya shafeshi.
Iska da yanayin gurin daya mishi ma shine yazaunar dashi har tsahon wannan lokacin,baya ga haka da saidai kawai su taddashi gida yawuce abinsa.
A sannan wata budurwa ta iso,duk da cewa shigar doguwar riga tayi amma kuma hakan bai hana wasu daga sassan jikinta fitowa ba,yalolon mayafin data yafa dinma iyakarsa wuya,qafarta sanye da hill shoes,kallo daya zaka mata ka bata sunan 'YAR DUNIYA,saboda dukka yanayinta ya nuna hakan.
Kai tsaye gaban kamal ta tsaya,cikin nuna tsantsar rashin kunya da rashin tarbiyya tadubeshi
"Ka gama guje gujen naka?" Saiya dubi sashen da azeez yake,saidai da alama baima kosan da zuwan nata ba,baya fatan yasan da zuwan nata,don har yau kusan idanun azeez na kanshi,kuma sharudan daya gindaya masa suna nan,duk da yayi niyyar bijirewa amma mommynsa tace yayi haquri ya karba haka,suci gaba da zama tare,saboda akwai wani target nasu kan azeez din,matuqar yabari misunderstanding yasake shiga tsakaninsu to target dinsu zai samu matsala
"Pls lisma,kije zan sameki a gida,ko wani wajen" zare glasses din idanunta tayi tana cuna baki
"Baka isa kasake yaudarata ba ai,kayi na farko kuma kayi na qarshe,bari na gaya maka kamal,ni gaba nake dakai na rantse da Allah akan bariki da iskanci" tafada tana dan daga murya da alama temper dinta tasoma hawa.
Ganin haka cikin wadanda suka san tsakaninsu da lisma din suka soma bata baki,gamida lallabarta taje din kamar yadda yace,sun mata alqawari zai sameta kamar yadda yace.
Kusan duk abinda ake a kunneshi amma saika rantse baya wajen,ko baisan da zuwan nata ba,yana sauraren komai,yana tunanin ba sabgarsa bace ko abinda yashafeshi,hasalima yana ganin zubewar qimarsa ce kamarshi ya tsaya wani maida magana ta hadashi da watsatstsun 'ya'ya irin wadan nan,saidai kalaman data sake fada suka ja hankalinsa harta daga kai yana dubanta fushinsa yanason motsawa
"Ku rabu dani naci uwa da uban dan iska,maqaryaci macuci mayaudari kuma maha'inci,jinin asara haihuwar iska" idanunsa ya lumshe na wasu sakanni kana yabudesu,yamiqe cak yana aje laptop dinshi daga inda yatashin yana kuma qoqarin controlling anger dinsa kafin ya isa gareta,saidai hakan bata samu ba saboda maganganun data ci gaba da fadi.
"Getout of there!" Yafada cikin wata kakkausar murya data ja hankalinsu dukka harda masu bata haqurin,waiwayowa tayi tana neman wanda ya bata wannan umarnin kai tsaye kamar ubanta ta yagashi shima,saidai suna hada ido saqon ya isa qwaqwalwarta,wannan ba kalar wanda ake iya yagawa bane,kwarjininsa kadai yana karya lagon koma waye kai,maimakon magana saita maida glasses dinta ta rabashi sum sum tawuce daga wajen bayan ta kalli kamal taja masa qwafa alamun zancan bai mutu ba.
Idanunsa qur bisa kamal wanda kallon yariman ya rudashi,baison yadda yake zubawa mara gaskiya idanu haka,ran azeez ke tafasa sosai,saboda yanajin xagin datawa kamal din kamar da familynsu gaba daya take,kusan laifin kamal yafi nata yawa a wajensa,tunda yasan cewa idan babu qira meye zaici gawayi?,idan bai kulata ba ina taga fuska da qwarin gwiwar zuwa ta tsaya haka a gabanshi tana gaya masa wadan nan muggan kalaman.
Akwai magana da yawa a bakinsa,amma saidai baison yace komai da zai tozartashi cikin bainar jama'a masu yawa,tunda dai jininsa ne,hakanan bugu da qari ammi ta masa magana kan yadinga controlling fushinsa akan kamal,tunda dan uwanshine,uwa uba kuma akwai 'yar tsama sosai tsakaninta da momi mahaifiyarshi,so kada tadinga ganin kamar ita ke sanya azeez din yana yiwa kamal din wasu abubuwan.
ƙoƙari yayi yasoma hadiyr fushinsa,harya isa inda ya aje system dinsa ya dauketa yakashe sannan yasoma takawa don ficewa a wajen,tunda sukaga hakan sunsan tafiya zaiyi,don haka babu wanda ya tsaidashi.
Yana gab da ficewar wayarshi tadauki tsuwwa,daya duba yaga ammi ce saiya qi dagawa,harsai daya isa motarshi yabude yazauna asit dinsa kana yabi kiran nata.
"Kana lafiya ko?,jiya banga kiranka ba"
"Lafiya qalau ammi,jiya duka wayar tawa a kashe take,muna da test ne,dana gama karatu sai kawai nabarta a kashe saida muka fito,sanda muka fito kuma dare yayi anan babu damar kira"
"To ma sha Allah....kan maganar nan ta aurenka.....yanzu haka nasa an samo maka yarinyar,ina tunanin cikin satin nan zan turo maka ita ka ganta,idan tayi maka shikenan,inaso ne ayi komai a gama within two to three weaks".
Dayaji ta bagarar da zancan tun wancan lokacin ya zaci tabar maganar ne,sam ya manta shaf da batun,don har yashiga sabgoginsa,bashi data cewa kuma bashi da damar musu,tunda yasakar mata ragamar komai kuma tayi din bai isa ya canza ba,cewarsa a'ah kamar ya taso da wani case ko wata matsalar ne tsakaninsa da ammin,gwara ya amsa koda baiso,koda babu abinda zata amfana masa,amma ko daya baya da buqatar zuwan yarinyar,koma ya take ba matsalarshi bace shi
"No ammi....basai tazo ba,kawai ku qyaleta" sai tadan bata fuska kamar yana gabanta kana tace
"Kamar yaya?,dama an taba aure ba tare da anga juna ba?" Shuru yadanyi na wasu daqiqu sannan yace
"Ba wani matsala bace,itadinma bata ganni ba tace ta amince" kai ta girgiza
"Akwao banbamci tsakaninka da ita,saidai kuma idan akwai wani abu daka shirya kake kuma boyemin....ko kuma kana da wadda kake da muradi daban da kakeso ayi hadin da ita" shima kai ya girgiza kamar tana wajen
"Ba haka bane ammi,indai ke tayi miki nima na tabbata zatayimin,sannan bawai abu bane na dindin ba bare ace ana buqatar dogon nazari ko zabe,it was just like a game...babu damuwa" sai datayi shuru sa'an nan tace
"Is ohk,amma zan amshi koda pic dinta ne na maka sending ta email dinka saika duba" bayason yafiya mata musu,saboda tana da wani girma da daraja a idanunsa,hakanan tafi qarfin komai kamar yadda tafi gaban komai,don haka yace
"Alright ammi,na gode" ƙaramin murmushi tasaki
"Anything for you" tafadi,daga haka suka kashe wayoyinsu.
Sauke wayar yayi daga kunnenshi yana sauke ajiyar zuciya,kana ya waiwaya yana duban almustapha daya shigo motar sanda yake gab da gama wayarshi,mutum nabiyu rak a rayuwarsa da yasan abinda yake gudana,saidai shidin bai bayyana masa cewa shekara daya ne rak zaman nasu ba,tun kafin mustapha yayi magana azeez yarigashi
"She prepared anything" murmushi yayi yana dukan kafadarsa
"Dan gata" ganin yanason maida maganar wasa saiya saki qaramin tsaki yana fitowa daga sit dinsa ya zagaya zuwa inda mustaphan ke zaune yabude murfin motar yana cewa
"Kaimu gida da Allah" yana dariya mustaphan yafito saukayi exchanging seat,ya tada motar suka fice daga gurin,yayin da azeez yayi relax a kujerar motar kawai yanason yayi emptying qwaqwalwarsa daga kowanne irin tunani.
19
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*
*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*
*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_______________________________
*_kina buqatar kayan qwalama da kwadayi da kuma maqulashe😋😋,abubuwan motsa baki masu kyau tsafta da kuma inganci?_*
*_Garxaya ki nemi MRS SCHOOL TREATS_*
*_nasan zakuce to me kenan?_*
*_RUGUNTSUMIN GAMAYYAR WAJEN SAMAR MUKU DA KAYAN MAQULASHE IRI DABAN DABAN,DA SUKA HADA DA_*
*tuwon madara mai kwakwa da marar kwakwa*
*da kuma*
*Gullisuwa*
*_dukka na zallar madara mara algus_*🤗
*_cikin nagartacce tsafatatacce_kuma ingantaccen package mai kyau_*
*SIYAN DAYA KO SARI*
_Kar kuyi sanya,maza ku nemeta a tudun wada,hayin buba GUSAU_
_ko kuma akan numbar waya 08069706638_
*_SUNA AIKAWA KOWANNE GARI DA IZININ ALLAH CIKIN AMINCI_*
*_biyan buƙatar abokan hulda shine burinmu_*🤝🏽🤝🏽
19
Wani irin farinciki ne yake ratsashi tun sanda umma luba ta gama gabatar da saqon fulani aisha,bakinsa ya kasa rufuwa,lallai arxiqin daya dade yana mafarkin samu yanxu yasameshi,maganar hausawa gaskiya ce da sukance DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE,yaushi malam bilya akewa albishiri din cewa za'a rushe gidanshi yazabi kalar irin ginin da yakeso ayi masa,yakuma zabi sana'ar da yake da sha'awar yi,hakanan yazabi irin motar da yakeso yadinga hawa,rawa ne kawai bai taka ba gaban umma luban,amma koda tatafi bai iya daurewa ba sai daya taka din,mama ladi tana tayashi,cikin ranta tana godewa Allah daya sanya batayi gaggawar barin gidan ba,ashe da ita za'aci arziqi,sai daya gama sa'an nan yasoma tambayar mama ladin
"Ina mai gadon take ne,kiramin ita na shaida mata tashirya,sati uku ya rage mata a gidan nan"
"Anya ko tana cikin gidan nan,tun sassafe naji karakainarta da yara tana shirin fita makaranta" idanu ya fidda waje
"Ai bataji ba kenan?,bata yarda da hanata zuwa makarantar da nayi ba?,zamu gamu,nida itane,har makarantar zanje yanzu kuwa" ya fada yana shura takalmansa yafice daga gidan cikin hanzari zuwa makarantar tasu,don yanajin kamar bilkisun nason jawo masa wata asara ce dashi kuma bazai iya jurarta ba.
Kwanakin gaba daya tunda take zuwa makarantar kusan babu abinda take tsinanawa banda kwanciya,koda yaushe zaka sameta kife da fuskarta saman tebur,tashin hankalin da take ji yana fuskanto rayuwarta jikinta ya bata ba qarami bane,ta yaya ya akayi mahaifinta ya aminta da wannan bahagon tunanin?,me yasa ya amincewa wannan wasan yaran saboda dukiya kawai?.
Hakanan tasamu kanta da yawan duban sashen da bilkisun ke zaune,duk da bamai yawan magana bace amma koda tana zaune ne shuru to zaka sameta da littafi a gabanta tana dubawa,koda ba zatayi hira da kowa ba,duk da basa shiri,babu wata magana mai dadi dake hadasu,amma saita tsinci kanta da rashin jin dadin sauyawar bilkisu,ko ba komai a baya sukanyi compatition a aji wajen bada amsa a subjects da dama idan malami yayi tambaya,sukanyi rige rigen miqa classwork tsakanin ita da ita,duk da talura badon ita bilkisun takeyi ba,amma rashin ganin hakan kwana biyu duka sai taji babu dadi.
Kasa shuru tayi ganin kusan awa guda bata motsa daga yadda take ba,ta tabo hanan dake gefanta
"Wai meke damun bilkisu kwana biyu" cikin mamaki hanan tadubi afnan din,don tunda suke bata taba jin takirayi sunanta ba saboda takun saqarsu,kai ta girgiza
"Oho mata,waya sanmata ne" idanunta kan bilkisun dake duqe saman benci
"Kamar tana cikin damuwa" sake daga kai hanan tayi daga kwafar note din da take ta dubeta
"Meye damuwarki a ciki ke idan hakanne" kafada ta daga
"Nima ban sani ba" daga haka tabar zancan,saidai batasan me yasa idanunta suka kasa sauka daga nahiyar da take ba,har zuwa lokacin da aka aiko kiran bilkisun daga office din principal.
Tayi mamakin kiran,don tunda take bata taba yin wani laifi ba cikin makarantar ballantana tace ko wani abun tayi akeson ganinta,hakanan tamiqe tana gyara hijabinta cikin kasala da mutuwar jiki taja qafafunta tafice.
Ba jimawa afra tafita fitsari,sai gata tadawo tana qunshe dariya,hanan ta dubeta
"Lafiyarki ke kuma?"
"Wallahi wani abun tausayi nagani kuma abun dariya,mutuniyar billy ana can ana sharbar kuka a office din principal,babanta yazo yacireta daga makaranta,aure zai mata,aurenma na dole,ke kinga baban nata kuwa?,kamar wani mai tallan agwaluma,ke wallahi me yanke flowers din gidanmu yafishi kyan gani,kuma kina gani kinsan babanta ne wallahi" dariya duka wadanda ke role din suka fashe dashi,ga mamakinsu afnan kallonsu kawai tayi ba tare datace komai ba,tausayin bilkisun taji ya saukar mata,ashe da gaske ne ita din ba diyar kowa bace?,ashe abinda yake damunta kenan cikin kwanakin nan?,shiko me yasa zai cireta daga makaranta,duk qoqarinta da himmarta nazuwa makaranta,kaf ajinsu itace take daukan na daya kowanne tearm,afnan din ke mara mata baya ata biyu,ko ya gaji da biyan kudin makarantar tasune?,tunda a yadda afra ta siffantashi tabbas ba qaramin namiji bane mai irin wannan qaramin qarfin dazai iya biyan kudin makarantarsu
"Wai bakiji mutuniyarki bane?" Hanan ta tabo afnan tana fada dariya tana cinta,wani kallo tayi mata sannan tace
"Naji mana,amma banga abun dariyar bane,tunda dai macace 'yaruwarmu,muma xamu iya fadawa irin qaddararta" shuru kowannensu yayi da mamaki suna duban afanan din
"Kuna mamakine?,bilkisu bata taba yi mana laifin komai ba,inda ace za'a titsiyemu da bulala ace mu fadi abinda ta taba yi mana duk cikinmu babu mai amsa,saimu da muke cusguna mata ma amma bata taba tsayawa ta biye mana ba...."
Shigowar bilkisun ajin yakatse sauran maganar tata,kallo daya zaka mata kasan tasha kuka bana kadan ba,tawuce seat dinta tazauna gamida maida kanta yadda yake dazun.
Har duka periods din suka qare aka tashi daga makarantar bata dago kanta ba,saida kusan kowa a ajin yafice yabarta kana ta hada jakarta da qyar tawuce itama.
Duk da uwar ranar da ake qwalawa ko kadan zafinta bai dameta ba,qunci da baqincikin dake cikin zuciyarta yafi ranar zafi da quna a gangar jiki da zuciyarta,da mahaifinta za'a gama hannu a tarwatsa rayuwarta?,wadanne irin azzaluman masu sarautane su?,wadanda basu damu da buqatar kowa ba saita qashin kansu,dama duka qarya ce da shaci fadin mutane da suke cewa
"Masarautar kaisa badai adalci ba,dukka mai neman adalci to kansa tsaye yanufeta" gashi ita yau adalcin take nema xalla daga garesu amma sun gaza dubanta,indai da gaske ne daga masarautar kaisa akeson shirya mata wannan abun,indai da gaske ne afnan jinin masarautar kaisa ce iya dabi'u da halayenta kawai sun isa su gaya mata cewa lallai sudin mutane ne masu dagawa zalunci da takura,inama ace wanda yamutu yana dawowa yau ummanta tazo taga halin data tafi tabarta a ciki,inama ace wanda yayi nisa yanajin kira anty zuhriyya tazo taga yanayin datake shirin afkawa ta tsamota,tasamo mata adalci da nutsuwar ruhi.
Tafiya kawai take ba tare da tasan inda take jefa qafarta ba,bata ankara ba tajita tsamo tsamo cikin wani ruwa,sai a sannan ta maida hankalinta,ta duba dakyau sai taga ashe kwatace,dai dai sanda motar dake dauke da afanan take dosowa wajen.
Tun daga nesa taga kamar bilkisun,a hankali ta bada umarnin ya gangara gefan titin,tana tsaiwa motar tabude murfin da kanta kana tafito tana qarasowa inda bilkisun ke tsamo qafafunta tana son ci gaba da tafiya ba tare data damu da tsaiwa tayi ratse koda a fanfunan gefan hanya bane ta gyara jikinta.
Riqotan da akayi ya sanyata tsaiwa
"Bilkisu bilyamin" taji an furta a hankali,yadda aka kira sunan yasanya tagene daya daga cikin 'yan makaranta ko ajinsune,saita waiwaya don taga waye,mamaki ya cikaya ganin afnan abdallah mu'az kaisa tsaye tana dubanta cikin alhini da mamaki
"Ya akayi kika fada kwata bilkisu,me yasa bakihau mota kin koma gida ba bayan baki da lafiya" kai ta kada
"Ba komai,yanzu zan isa gida" tasan ta fadane kawai,amma ko ba'a gaya mata ba tasan akwai tazara tsakanin unguwarsu da unguwar da makarantar tasu take
"Ki tsaya ki wanke jikinki,karki dinga tafiya ana kallonki" bata tsaya jin amsar bilkisun ba tayi magana daga cikin motar,saiga drivern yafito cikin hanzari hannunsa dauke da ruwan roba manya guda biyu.
Baki tasake yadda taga afnan din ta balle ruwan roban takama gefan unifoarm din nata cikin rashin damuwa tana tittilewa a jiki tana wanke ruwan kwatar,saita kai hannu da sauri ta riqeta
"Zubamin zan wanke dakaina" murmushi ta sakar mata,bata musa din ba taci gaba da xuba matan tana wankewa,lokaci lokaci tana satar kallon bilkisun,harga Allah tausayi take bata,ta tsani kalmar auren dole,koda a littafine take karantawa tota aje littafin kenan,saboda bata manta dauki ba dadin da aka dinga yi cikin gidansu ba lokacin da maimartaba yaso baiwa arifa yayarta tabiyu wani ba,yadda arifan tashiga tashin hankali qwarai harsu kansu saida suka tayata shiga damuwa,daga baya dai Allah ya warware da yake wani baya auren matar wani.
Tas tawanke,ta kama inda zai matsu ta matse kana ta yarfe
"Na gode" tafada a sanyaye tana duban afnan,tare da mamakin meya sauyata haka?,don ko amafarkinta bata taba tsammanin afnan din nada tausayi da sauqin kai ba
"Ba komai,kishiga mota saimu saukeki a hanya" motar takalla kana ta kalli afnan,tana qoqarin hadiye wani abu dake taso mata,hala afnan tana cikin masarautar kaisa ne amma batasan dukkan abinda ke faruwa ba,da zata iya data gaya mata cewa a yanzun ta tsani dukkan wani abu daya shafi masarautarsu,saidai ko Allah ma yace kada laifin wasu mutane yasa ka kasa yi musu adalci,babu ruwan afnan cikin batun,don ga alamu sun suna batasan ma meke faruwa ba,wala'alla data sani ko kallon tsiya ba zata mata ba bare na arziqi,a yadda suke da ita abaya na rashin jituwa a tsakaninsu
"Ki barshi,zan iya qarasawa ai,kada na bata muku mota da danshi,kinga a jiqe nake,na gode sosai" saita soma takawa,tausayinta takeji sosai,ba zata iya barinta tawuce ba,saitasha gabanta
"Don girman Allah kishigo mu saukeki,bakyau maida alkhairi" ta kashe mata jiki,tilas tabita tabude mata murfin motar,sai data soma shiga sannan itama afnan din tashiga.
Wani sassanyan sanyi ne yasoma ratsa kowanne loko da saqo na jikin bilkisu yana busar da gumin da ada ta hada saboda tafiya a zafin rana data soma,sanyin da rabonta data jisa tun lokaci anty zuhriyya na rayuwa a kusa da ita,duk da yanayin da take ciki sanyin ya mata dadi,saita lumshe idanunta kawai tana jin yadda motar ke tafiya wani suuuuu kamar ba saman kwalta suke tafiya ba,kai kace a iska ko a sama suke tafiya.
"Kiyi haquri xan miki shishshigi bilkisu,duk da ina zaune aka gayamin,ban sani ba gaske ne koba gaske bane,amma indai da gaskene auren da bakiso za'a miki,kizo na kaiki wajen abbana,na tabbatar da cewa zai hana faruwar hakan,don tun daga cikin gidansa zuwa al'ummar qasarsa ya haramta auren dole tun daga kan yayata arifa" idanunta tabude akan afnan,ashe haifaffiyar sarkin kaisa din ce ita,hakan na nufin ita din 'yaruwa ce ga yarima wanda akeson bata?,uwa daya ko uba daya ko uwa daya uba daya?,rashin sani yafi dare duhu,batasan daga can zancan yataso ba take da yunqurin kaita don samun adalci,akwai adalci da gaske irin wannan a masarautar amma ya kasa biyowa ta kanta?,waishin ins matsalar take ne?
"Karki damu,babu damuwa,na gode da kulawa" abinda tace mata kenan,don koda ace ba daga gidan tushen matsalarta take ba bazata iya kai mahaifinta qara kan zai aurar da ita ga wani ba komai lalacewar mahaifin nata.
Basu sauketa a hanya ba kamar yadda da farko afnan ta fada ba sai da suka danganata da bakin layin
"Na gode" tasake maimaitawa tana duban afnan din,itama ita take kallo cikin murmushi tace mata
"Babu komai" koda sukayi gaba da kallo tadinga bin unguwar tasu,tana ganin tarin banbance babance qarara,wane sashe na zuciyarta yana sake cika da tausayin bilkisun,da kuma ganin kuskurenta qarara na sanya 'yar tsama ga innocent mutum kamar bilkisun,wadda bata taba taka mata ba bare ta zubar mata.
**************
Cikin irin kebantattun lokutta da take warewa ne domin iyalinta,tana zaune a falonta na musamman,sanye take da doguwar riga mai hade da hula na wani irin yadi mai sulbi da taushi,afnan ce kanta saman cinyarta,hannunta riqe da wayarta,saidai hankalinta bai kan wayar tata gaba daya,ta ta'allaqashi ne wajen bawa amminta labarin bilkisu,da abinda ta fuskanta daga rayuwarta duk da bata taba bude baki anyi magana makamanciyar haka da ita ba,har sai da fulani aysha ta soma gajiya dajin labarukan autar tata afnan tace da ita
"Baki da sauran abunyi mata ai afnan,tunda tace babu komai tagode" cikin shagwaba irin ta wadanda suke auta a wajen iyayensu tace
"Toni ammi tausayi take bani wallahi,da bama shiri amma yanxu tausayinta nake"
"Ai shikenan,saikiyitayi,daga min cinya hakanan na huta" tana dagawar jakadiya tayi sallama bakin qofar falon tana jiran abata izini tashigo,saita dubi afnan
"Idan kin fita ki mata ixini" amsawa tayi dato tana gyara yafen mayafinta,kana ta wuce jakadiya kuma tashigo.
"Allah yabaki yawan rai....an shaidawa ubabatu kuna son ganinta,gata kuma ta iso"
"Anyi mata izini tashigo"
"An gama Allah ya taimakeki" daga haka tajuya tafice,cikin qiftawa da bismillah umma luba ta bayyana cikin falon.
Babu jinkiri fulani aisha tasoma zayyana mata dalilin kiran
"Da farko munason ki shaida musu a sanda zasu tashi zuwa gidan zama nawucin gadi kafin a kammala musu ginin gidansu kafin lokacin da za'a daura auren....zamu dauketa zuwa gidan da za'a kebeta...inason ayi mata horo na musamman,ayi mata gyara na amare na musamman irin gyaran da aka jima ba'a yiwa wata diya ba,duk da cewa xabinmu ce zuwa wani lokaci amma ko babu komai zatayi tarayya da jininmu ne,sabida haka inason a sauyata amantar da ita wacece ita,a dabi'anceta da dabi'a ta gidan sarauta,halayyarsu yanayin maganarsu da sauransu saboda yarima yaji dadin zama da ita ba tare da yana tuna wani abu na daban ba,ko yaji damuwa cikin ranshi,bayan wannan inason ayi mata training na yadda zata kula kanta,babu buqatar takoyi yadda zata zauna dashi,don iya aikinta kawai zataje tayi,kula da komai nashi yana da masu yi masa shi,bana buqatarma takoya din saboda wasu dalilai nawa dana barwa kaina sani,abu na iko,inason ki shaida musu,su lissafa dukkan adadin dukiyar da sukeso a matsayin dukiyar auren 'yarsu,ko nawa ne zamu biya,su fadi ko nawa suke da buqata daga nan har zuwa ranar rabuwarsu,bisa sharadin idan an rabun,zasu manta cewa 'yarsu ta taba auren mai suna abdul'azeez,yariman masarautar kaisa,munason rabuwa tahar abada,ta rayu takuma ci gaba da rayuwa babu shi ko digo cikin tunaninta,wannan shine babban bangare kuma babban sharadi na tafiyar alaqarmu,samun akasin hakan kuma dai dai yake da faruwar kowanne abu...." Saita tsagaita tana maida numfashi
"Wannan sharadin kusan shine abu na farko dana fara shaidawa mahaifinta,yakuma yarda yayi na'am da hakan dari bisa dari" kaita gyada cikin nutsuwa sannan tadora
"Ko a mafarki bama buqatar su hado diyarsu da wani abu,itadin kawai zallarta muke da buqata....abu na qarshe shine,za'a daura aurensu cikin masarautar mali cikin ahalina ba'a qasar kaisa ba,daga nan zamu dauketa zuwa muhallin da zata zauna na tsahon shekara daya,ba zata bar wajen ba harsai sanda kwanakin suka cika"
"Allah yabaki yawan rai an gama,wannan saqo zai isa kunnensu da izinin Allah" kai tasake jinjinawa
"Da kyau,ina da buqatar hotonta wanda zai turawa yarima don yaga irin zabinmu....jibi zata bar gidansu zuwa gidan da muka tanadar mata tazauna,zamu aika da mai hoton can,inason a zaman ya kasance kina daya daga cikin masu kula da ita,har zuwa lokacin da zasu wuce mali,tukuicinki kuma kizauna ki zaba dukkan abinda kikeso a duniyar nan,matuqar mun mallakeshi xamu bakishi"
"Godiya nake Allah ya taimakeki,wannan karamcin naki da bashi da kwatankwanci bakina yayi kadan yayi miki godiya,kalmomin bakina sun qare fulani". Umma luba ta fada cikin rudewa da zallar farinciki.
Ƙarfe biyu da rabi na dare ne amma saika tsammaci tsakiyar rana ce tarwai saboda yadda idanunta suke a bushe kuma a soye raqayau,babu digon wani abu mai suna bacci tattare da ita,bata jin koda alamarsa duk kuwa da yadda ya qware wajen iya sata.
Ji take kamar zata zauce a duk lokacin data tuna kalaman da mahaifinta ya gama rattaba mata daxu bayan sallar isha'i,YA SAIDA ITA,YAYI CINIKINTA wannan itace kalma mafi sauqi daya kamata mahafinta ya gaya mata akan hanyar dayabi ta dogon sharhi kan buqataun masarauta akanta
Jin zantukan nashi take tamkar a shirin film ko kuma a qagaggun labari na hikayoyi,wadan nan sharuddan da dokoki dukkansu sunfi kama dana matar da za'a siyeta a matsayin baiwa ba 'ya ba,ta ina zata fara?. Ta ina lamarin zai yiwu?. Saita waiwaya tana duban qannenta dake kwance suna bacci ba tare da sunsan gagarumin tashin hankalin dake fuskantarsu ba. Ta ina zata soma barin wadan nan bayin Allahn da yafi kyau a kirasu da marayu?. Ta yaya zasu iya jurewa rashinta?. Wa zata barwa su?. Umma katti?,mama ladi?,koko mahaifinsu da yafi kowa rashin damuwa da rayuwarsu,wanda asanda take masa bayaninsu ma cewa yayi basu da wata damuwa tunda zasu samu sauyin muhalli,zasu kuma samu ci sha da suttura maikyau.
Wani abu dake mata yawo saman kwanyarta kamar ana mata tafiyar tsutsa haka tadinga ji,ta dinga kaikawo tana tafiya tsakanin qannen nata daga bango zuwa bango na dakin. Ji take kamar ta zura da gudu tabar gidan...tabar qasarma gaba daya,da sauri ta juya tafice daga dakin,saita tsinci kanta tayi hanyar soro tana muradin ficewa.
Sanda tabude qofar gidan babu abinda yasoma mata maraba sai zallar duhun dare,wanda ya cukudu da haushin karnuka daya cuka anguwar tasu
"Wa kika barwa su?" Daga qasan zuciyarta aka jefa mata tambayar data sanyata tsaiwa cak
"La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim". Tasamu kanta da furtawa sau babu adadi,wanda wannan ya taka rawa wajen sanyayar jikinta,tamaida qofar ta kulleta kamar yadda take,kana ta janyo qafafunta zuwa cikin gidan.
Maimakon tanufi dakinsu kai tsaye saita durfafi bakin famfonsu gadan gadan,ta kunnashi kana ta duqa gami da tara hannayenta,saita bige da alwala.
Bata damu da neman abun salla ba,hakanan saman dandaryar sumuntin dakin ta tada sallar,sallar data jata har zuwa lokacin da akayi kiran assalatu,ta bada farali wanda daga wannan bata kuma sanin abinda ke faruwa ba,gwanin iya sata ya saceta duk da yadda take kokawa dashi da nuna mishi nata maraba da ziyararshi.
A kallon farko zaka san cewa babu wani abu da yayi kama da sukuni tattare da ita,duk wata wulgawar da yaran zasuyi binsu take da kallon zallar tausayi,bata ankata ba tuni mahaifinta yagama gaya musu cewa zai aurar da yaayarsu,wanda hakan yayi masifar dugunzuma hankulansu gaba daya,tana zaune tana saqa da warwara sai ganin yara tayi sun sata a gaba gamida zagayeta,gabanta na faduwa tana fatan ba abinda take hasahe bane ta tambayesu lafiya
"Aure wai zakiyi yaaya inji baaba,kema aure zakiyi ki tafi kibarmu mudaina ganinki yaaya?" Hauwa ce tajefa mata tambayar cikin matuqar mutuwar jiki dakuma saddaqarwa.
Da idanu ta dinga binsu da kallo dai dai da dai dai,tana jera kalaman da zata gaya musu,saidai yanayin dake saman fuskar kowannensu ya sagar mata da gwiwar kowanne yunquri nata,tausayinsu yasake ninkuwa cikin zuciyarta,qwarin gwiwarta da karsashin data tattaro suka baje,ta rasa abin cewa,sai kawai ta sanya musu kukan data jima tana boyewa,karo na farko a rayuwarta,karon farko data nuna gazawarta a gabansu,abinda komai girman nauyi da tsanani bata taba bari gazawarta ta bayyana koda saman fuskarta ba,saboda tasani itace kadai qwarin gwiwarsu,itace kadai hope dinsu,batason tayi abinda zata kashe musu fata da burinsu da dukka suka aza wuyanta.
No. 20
..............Aiko ALLAH ya amsa masa, dan cikin amincinsa Yoohan na komawa gida bai rufa awa ɗaya ba wani irin barci mai daɗi da saka kwanciyar hankali yay awan gaba da shi. Sai ga Yoohan da ya kwanta tun kusan shida na yamma bai farkaba sai goma na safiyar washe gari.
Wannan al'amari ya bama Yoohan da su Papa mamaki, suka shiga masa tambaya akan yaya akai yay barci jiya?. Bai ɓoye musu komaiba ya basu labarin haɗuwarsa da mutumin da bai sani ba, bai kuma san inda zai sake samunsa ba a yanzun. Duk da sunji daɗin hakan sai suka nuna rashin damuwarsu da sanin wanene mutumin ko inda zasu samesa, saboda kawai sun fahimci musulmi ne. Yoohan ɗin kuma ya koma inda suka haɗu da mutumin har kusan sau huɗu bai samu koda mai kama da motarsaba ma balle shi ɗin. Haka ya haƙura badan yasoba ya koma makaranta.
Wannan shine dalilin samun sauƙi sosai daga matsalar Yoohan, ya koma yana barcinsa lafiya lau kamar kowa, sai dai lokaci-lokaci abin nasa kan buga, idan kuma ya juyo yana tsintar kansane cikin mawuyacin hali na baƙin rai da fushi da tsangwamar kansa. Dama gashi dalilin hakane sanadin maidashi mutum mara fara'a da son hayaniya.
To a yanzu gashi al'amarin nasa ya sake motsawa, duk da yakan jima baiyiba ma. Yau kwanakinsa uku kenan da dawowa ƙasar, amma ko barcin mintuna goma ya kasa ɗaukarsa. Yanda yake ganin rana haka yake ganin dare. Ya mugun fita hayyacinsa a kwana ukun nan, ya daina magana da kowa, abincima ya masa yajin aiki sai abinda ba'a rasaba yake ɗanci idan yaji yana neman halaka a banza.
★★★★
Cikin murya mai cike da lallashi papa ke kiran sunan Yoohan ta jikin Window da suke a tsaye shi da Madam Chioma. Duk da yana jinsu bai fasa wurgi da abinda duk yaci karo ba a ɗakin, har wani sashe na gilas ɗin dake zagaye da ɗakin ya tsage, dan ya jefa ƙarfe ne ya bigi gilas ɗin dake a matsayin bango ɗakin.
Sai da ya jigata dan kasan sannan ya zube a ƙara yana wani irin sauke ajiyar zuciya mai ƙarfin daban tsoro.. Duk da hankalinsu ya ɗan kwanta ganin yabar jefe-jefen basu daina kiran sunansa da roƙon ya buɗe musu ƙofarba cike da lallashi. Shi kuma yayi banza dasu tamkar baisan da zaman nasu a wajenba.
Papa ne ya tuna da extra keys ɗin sashen nasa, dan haka yabar wajen Window da sauri zuwa bedroom ɗinsa. Mintuna ƙalilan sai gashi ya dawo cike da farin cikin samo keys ɗin. Hakama Madam Chioma saboda daɗin da taji har kiss taima papa tare da rungumesa. Zagayawa sukayi domin buɗe ƙofar, sai dai kuma key ɗin yaƙi shiga alamar yabar wani key ɗin a ciki. Ransu duk a jagule suke bin ƙofar da kallo, madam Chioma har hawayenta sun dawo kwarara.
Solomon ne ya kawo shawarar bin ƙofar can baya dake sada mutum da ɗakin motsa jikinsa kai tsaye. Su ruɗewama ta sakasu mantawa da ƙofar. Da sauri suka zagaya tacan, cikin amincin ALLAH kuwa suna gwada key ɗin da suketa kokwanton ba nata bane sai gashi ya buɗe musu.
Har rige-rigen isa garesa kuwa sukeyi. Duk da yana jinsu bai motsa ba, sai da sukasha fama, dan Yoohan akwai taurin kai dama, da ƙyar ya yarda suka tadashi zuwa ɗakinsa. Madam Chioma da kanta ta shiga toilet ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi sosai. Kafin ta dawo inda papa ke rungume da shi yanata faman lallashinsa da masa magana mai daɗin gaske, wadda ko ba'a faɗaba da alama tana tasiri ga Yoohan ɗin.
Zama tai kusa dasu itama, ta miƙa hannu ta riƙo na Yoohan ɗin tana murmushin jin daɗin ganin ya nutsu, matsawa tai jikinsa sosai zata rungumesa kamar yanda papa yay masa, sai ya ƙwace hannunsa ya miƙe zumbur. Cike da basar da abinda ya fahimci zatayin ya nufi toilet yana ɗingishi, dan da alama yaji ciwo a ƙafar tasa ne.
Duk binsa da kallo sukai ita da papa, yayinda ranta ya sosu sosai akan yanda Yoohan ɗin keyi mata a duk lokacin da ta nufi yimasa makamancin waɗan nan abubuwan. Tarasa dalilinsa na yimata hakan, ‘shi kodai ya fara tunanin.......’ sai kuma ta kasa ƙarasawa ta girgiza kanta alamar ba haka bane. Dariyar papa ta sakata saurin kallonsa. Ya ɗage mata gira da matsowa shi ya rungumeta yana faɗin, “Ɗanki fushi yakeyi dake yau, kinga yamaƙi yarda ki rungumesa. ni zo na rungumeki”.
Fuskarta a yatsine taɗan turesa, cike da salon yaudara ta matsa baya da juya masa keya irin maganarsa ta ƙara mata haushin nan. Shiko ya sake matsowa jikinta ya rungumeta ta baya yana dariya ƙasa-ƙasa. “Wasa nake miki Momyn Yoohan, shima nasan yanayin da yake cikine kawai ya sakashi aikata miki hakan”.
Duk da haushin da take ciki sai maganar papan taɗan sanyaya mata rai, dan ita ada tunaninta ba haka yake kawo mata ba. Juyowa tai idanunta cike da ƙwalla, muryarta na rawa tace, “Darling! Anya kuwa bazamu nema mutumin nan daya taɓa yimasa maganiba shekarun baya da suka wuce sannan muna farko-farkon zuwa Abuja?”.
Papa dake kallonta ya ɗan ɓata fuska yana nazarin maganarta, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya amsa mata. “Shawaranki mai ƙyaune momyn Yoohan, sai dai kuma a ina zamu samesa? Shi kansa Yoohan ɗin bana tunanin zaima iya ganesa idan ya gansa ai”.
Kafin ta samu damar bama papa amsa Yoohan ya fito daga toilet ɗaure da towel, dan duk zatonsa sun fita. Turus yaja ya tsaya yana kallonsu fuska a turɓune.
Ahankali madam Chioma ta sauke idanunta akan buɗaɗɗen jikin yaron nata dake ɗauke da wata lafiyayyar farar fata mai santsi da ɗaukar idanun mai kallonsa. Basai an faɗaba a kallo ɗaya zaka fahimci shi ɗin ya tashi cikin kulawar rayuwa da jin daɗi, dan sam babu alamar rama tattare da shi......
Jikinsa ya fara ja da baya yana ƙara tamke fuska, hakan yasa Mom saurin tashi tsaye har tana neman faɗuwa, da yarensu tace, “Ina zaka kuma yaro na? Kaga zo na shafa maka man ma da kaina idan bazaka iya b.....”
Kafin takai ƙarshen maganarta harya maida ƙifar bayin ya rufe, jingina yay a jikinta ya lumshe idanu zuciyarsa na ƙara ƙarfin bugu. Duk da yanda take buga ƙofar a hankali tana kiran sunansa bai motsa ba, sai ma wani haushi dake sake ziyartarsa. Sam bayason wannan halin da Mom take masa, a ganinsa bai daceba, yakamata tasan da ba yanzu bane, yanzu fa ya girma, shekararsa talatin har da biyu a duniya, miyasa bazata daina masa kallo kamar ɗan shekara goma ko ƙasa da hakaba?. bawai yana saka abinda take masan a wani mizani daban bane, dan yasan soyayyar da suke masa mai yawa ita da papa ne ya jawo hakan, amma ya kamata ta fahimci yanzu ya wuce ta dinga masa wasu abubuwan kanta tsaye ai......
A hankali ya buɗe kumburarrun idanunsa dake cike da barcin da baisan ranar yinsaba, ya sake lumshesu yana sauraren yanda Papa ke lallaɓa Mom akan su fita su bashi waje ya shirya, idan yaso saisu dawo daga baya.
Badan madam Chioma taso hakanba ta yarda suka fita ɗin ranta na mata ƙuna.
Yoohan najin sun fita shima ya fito, dan dama a gajiye yake da tsayuwar saboda ƙafarsa wani bala'in zogi take masa. Sai da ya leƙo ya tabbatar babu kowa sannan ya fito. Bai kalli ko inda Mirror ɗinsa yake ba balle ai tunanin shafa mai ya nufi wajen kayansa kawai. Dogon wando ash mai taushi da farar t-shirt data kama jikinsa ya saka. Ya taka zuwa gaban gadon yana cije baki, zama yay yana mai kallon ƙafarsa data ɗan kumbura dai-dai idon sawu. Hannu yasa ya taɓa wajen yana yamutsa fuska, duk da zafin da yaji haka ya daure ya kama ƙafar yaja da ƙarfi. Siririyar ƙarar azaba ya saki tare da sakin ƙafar itama.
Har rige-rigen shigowa ake tsakanin papa da Mom da Richard da yazo gidan yanzu babu jimawa. Sai Solomon da Miracle dake ƙoƙarin shigowa falon suma Joy biye dasu tare da masu aiki dake ɗauke da abincin Yoohan ɗin.
Yanda sukagansa a kan gadon ya saka hankalinsu sake tashi, suka zagayesa da tambayoyin yaya akai?. Duk da surutun nasu haushi yake sake bashi sai ya tashi zaune, ganin Rich tare da su ya sakashi miƙa masa ƙafarsa. Kallon ƙafar Richard yayi da ƙyau, kafin ya jawo stool ɗin mirror ya zauna yana tambayarsa garin yaya yaji ciwon?.
Bai tanka masa ba, dan haka Rich ɗin ya kama ƙafar kawai ya hau ja masa. “Jesus!!!” ya faɗa da muryar nan tasa mai amo data haɗu da damuwa a yanzun. Saurin zama Momy tai a kusa da shi ta amshe filon daya damƙe ta maye gurbin filon. Caraf kuwa ya kama hannunta ya damƙe cikin nasa da masifar ƙarfi, dan har sai da ta saki ƙara itama.
Yanda jikinsa ke rawa zufa na fito masa sai duk tausayinsa ya sake kamasu, Miracle tai saurin zama ɗaya gefensa tare da kwanciya a jikinsa tana hawaye. Sai da Rich ya tabbatar ƙafar tayi yanda ya kamata sannan ya barsa. Sai faman jera masa sorry sukeyi.
Duk da yaji mutum kwance a jikinsa bai motsaba sai da zafin ƙafar ya daina sosai, a lokacin ƙamshin turaren Miracle dana Momy suka tabbatar masa sune nanuƙe da shi. A hankali yasa hannu ya ɗaga Miracle dake lafe a jikin nasa, kafin itama Mom da tunda ta farga da Mira take zuba mata wani kallon ƙasan ido na gargaɗi, shi dai ya zare hannunsa daga cikin nata, jan jikinsa yay baya ya haye gadon sosai batare da yace uffanba duk da sannun da suketa faman yimasa har yanzun.
Cike da kulawa Rich ya basu shawarar ya kamata su fita abar Yoohan ɗin ya huta, dan ya kula da yanda Yoohan ya sake cika tamkar zai fashe, hakan kuma yanada nasaba da zamansu a ɗakin, dan shi ɗin shaidane akan yanda Yoohan yay mugun tsanar jin kowanne kalar motsi a kusa da shi idan har yana cikin wannan yanayin.
Papa da ya gamsu da shawarar Rich ɗin sai ya tarkatasu suka fice duk da uwar gayyar Mom bataso hakanba ita. Bin bayansu Richard yay shima dan yana buƙatar ɗakko wani abun da yake son gwadawa Yoohan ɗin ko zai aminta wannan karon yasha.
Yoohan na zaune yanda suka barshi idanu a lumshe Richard ya dawo ɗauke da ƙaramin tray mai ƙyau. Duk da Yoohan na jinsa bai buɗe idanu ba balle ya motsa, Rich ya jawo ƙaramin table glass dake gaban sofa zuwa gaba gadon. Trayn dake ɗauke da kwalbar barasa da kofuna biyu, sai ƙanƙara a wani bowl ya ɗaura a kai yana kallon Yoohan ɗin. “Mr-x!”. Ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe kwalbar barasan.
Buɗe idanu Yoohan yayi a hankali batare da ya amsama Rich ɗinba. Rich ya ɗan murmusa, dan bai damu da rashin amsawarba, barasan ya zuba rabin kofi, ya ɗiba ƙanƙara ya zuba a ciki yana murmushi. Ɗagowa yay ya miƙama Yoohan dake kallonsa ta ƙasan ido kofin.
Ɗauke kai Yoohan yayi fuskarsa na nuna ƙarin ɓacin rai, dan yasan Rich ɗin yafi kowa sanin shi baya shan giya...........
“X-Man! inhar bazaka yarda na maka allurar da zata taimakeka kayi barci ba to ka daure kasha wannan, na tabbatar ita zata saka ka barcin koda na awa ɗaya ne. Kai fa likitane, kasan illar wannan matsalar da yanda take maida rayuwar mai fuskantarta a ƙarshe. Idan kana tunanin ƙin shan giya ne dan karta shiga maka rayuwar aiki yanzu ai ba'akan aikin kake ba, sannan don neman lafiyarka ne”.
Shiru kamar Yoohan bazai kulasa ba, dan har Rich ɗin ya fidda tsammanin samun kulawarma. Sai ya tsinkayi sautin tsakin Yoohan ɗin a hankali. Kallonsa Yoohan ɗin yake cikin ido da jajayen idanunsa dake a kumbure, murya a daƙile yace, “Rich! a wajenka ya kamata mutane su ƙara sanin halina akan idan nace bazanyi abuba bazan taɓa yinsa ɗinba, dan haka karka sake tunanin zansha barasa koda ba yau ba”.
Yanda yay maganar cikin kaushin murya ya saka Rich saurin cemasa “I'm very sorry”. Batare da Yoohan ɗin ya sake cewa komai ba ya maida idanunsa ya lumshe duk da yasan barcin ba ɗaukarsa zaiyi ba.
Haka suka cigaba da zama a cikin ɗakin shiru, Richard da ya sha barasar da Yoohan yaƙi sha har ya fara barci a gefen sa, shiko idanunsa biyu amma suna a lumshe. Lokaci-lokaci hawaye kan ziraro masa ta gefen ido. Yana sauraren yanda Momy da Papa keta faman zaryar leƙowa ɗakin, sai dai ɗauka suke ko Rich ɗin yaci nasara yasha giyar barci ya ɗaukesa, shiyyasa hankakinsu yaɗan kwanta suketa faman jin daɗin yanda duk shigowar da sukeyi suna samun Yoohan ɗinne a kwance.
Wajen misalin goma na dare Yoohan ya gaji da kwanciyar, tashi yay ya sauka daga gadon yana bin Rich dake barcinsa hankali kwance da kallo, bayi ya shiga ya watso ruwa. Bai jimaba ya fito sanye da bathrobe. a bakin gadon ya zauna tare da jingina da fuskar gadon. Ya kai hannu zai kashe fitilar gefen gadon idanunsa suka sauka akan farar envelope, cak ya tsaya yana kallon rubutun jiki, janyewa yay kamar zai share, sai kuma yasa hannu ya ɗauka tare da buɗewa ya zaro takardar dake a ciki.
Rubutun bashi da wani yawa sosai, amma a tsare yake gwanin sha'awa, sannan yanda aka tsara kalaman cikin rubutun da harshen turanci sunyi matuƙar jan hankalinsa har yana ɗan lumshe ido. Sai da ya maimaita takardar sau biyu sannan ya ninketa ya maida cikin envelope ɗin ya jawo drawer ya ajiyeta yana juya abinda ta ƙunsa a cikin ransa.......
________________________
*_SAUDIA_*
Duk da fushi da zuciyarsa keyi ga duk zuri'ar gidan tasu hakan bai hanashin jin ɗokin zuwan hajjo da Ahmad ba, dan baisan harda Nu'aymah a tafiyarba. shiri yay tsaf ya wuce airport domin tarbosu batare da ya saurari Adawiya da tace zata bishi ba, dan tana wanka ma ya siɗaɗe ya fice daga gidan.
Cikin sa'a kuwa yana isa airport ɗin jirginsu Nu'aymah na taɓa ƙasa. Lumshe idanu tayi tana karanto addu'oi da fatan cika alƙawarin da taima iyayenta akan kama kanta batare da wata fitina ta ɓullo ba. Hajjo na lura da duk motsinta, amma sai batace da ita komaiba har sukabi ayarin masu fita. Sanye take cikin wando blue na jeans da farar rigar fakistan da tsahonta yake har gwiwar ta, an ma rigar ado da blue ɗin duwatsu manya da ƙanana, sai farin veil da ta naɗa a kanta wanda ya sake fidda ƙuruciyarta da ƙyawun da ALLAH ya bata. Farar ƙafarta da kalar wandon ya haska tana sanye cikin blue ɗin takalmi da yay masifar mata ƙyau dan bata da babbar ƙafa sam. Sai ƙaramar jakarta itama dai blue ɗince.
Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta tai lokacin da suke ƙoƙarin sakkowa daga jirgin, ta ɗan yamutse fuska tana sauke hannun a hankali da kai dubanta can ɗan nesa dasu. Wani irin bugawa ƙirjinta yayi saboda hango Abdallah dake tsaye jikin motarsa sanye cikin ƙananun kaya da sukai masa ƙyau, ya ƙara ƙiba da ƙwarjini a idanun mai kallo kamar ba azumi ake ba. A take wata kasala ta saukar mata, tafiyarta ta sake raunana fiye da farko. Dan sai da Hajjo ta kama hannunta ta ida sauka da ita ma.
Abdallah da ya yunƙuro saboda hango Ahmad dake a gabansu da yay yaja ya tsaya cak lokacin da idanunsa suka sauka akan Nu'aymah da bai zato ko tsammaanin gani ba.. Wata irin hajijiya-hajijiya ya faraji tana neman ɗibarsa a wajen, ya kasa motsi balle ɗauke ido daga kallonta har suka ƙaraso inda yake.
Hajjo datai tamkar bataga halin da suka shiga ba ta mangare masa ƙeya tana faɗin, “Kurwata kur dan gidanku”. Firgigit yay da sauke nannauyan ajiyar zuciya, sai dai ya kasa ɗauke idanun nasa daga kan Nu'aymah da ta ɗauke kanta gefe tamkarma batasan da zamansa ba a wajen. Hannu yakai ya shafa inda Hajjo ta tallaresa kafin ya janye idanunsa da ƙyar ya maida kan hajjon data wani ƙyaɓe fusaka tana zuba masa harara.
“Yanzu dan ALLAH daga zuwanki mina miki zaki tallemin kai?”. Ya faɗa yana ɓata fuska da kallon Hajjon. Watsar dashi tai taƙi magana, saima hannun Nu'aymah data kamo suna shirin barin wajen.
Dariya Ahmad yayi, ya matsa ya rungume Abdallah, “Oh Yaya kaifa kai da Hajjo sai a slow, manta da batunta kayi tani da ƙanwarmu kawai”. Murmushi Abdallah yay tare da rungume Ahmad ɗin shima. Kafin su saki juna kowanne fuskarsa da murmushi jin daɗi. Abdallah ya sake kai dubansa ga Nu'aymah sannan ya kalli Ahmad.
Kai Ahmad ya ɗan jinjina yana murmushi, amma baice komaiba sai ƙyafta idanu da yayma Abdallahn. Ab ya kaɗa kansa kawai da nunama Ahmad hanya alamar suje to.
Nu'aymah da Hajjo na baya, yayinda Ab da Ahmad ke gaba. Hajjo ce kawai ke magana a motar Ahmad na tayata, dan mafi yawan maganar tata duk tsiya takema Abdallah, shi kuma Ahmad ɗin na karesa.
Abdallah kam rabin hankalin na'a tuƙi ne rabi akan Nu'aymah da a yanzuma ta ɗauke kanta tamkar bata gansa ba. A haka suka iso madaidaicin gidan nasa mai ƙyau da tsari. Sai da ya faka motar inda ta dace kafin su fita shi da Ahmad, Ahmad ya buɗe na Hajjo, ya taimaka mata ta fito, Nu'aymah kuma ta buɗe da kanta ta fito tana kallon gidan dama anguwar gaba ɗaya, a baɗini kuwa zuciyarta har wani zallo take saboda ganin Yah Ab ɗinta, duk yanda tai tunanin zata daure sai ganinsa ya canja dukan ƙudirin nata lokaci guda. Sai dai kamar yanda ya fiske itama haka tai ƙoƙarin fiskewar.
Abdallah ne a gaba lokacin da zasu shiga gidan, Ahmad da Hajjo biye da shi, sai Nu'aymah a ƙarshe tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki domin samun sassauci daga abinda takeji akan ganin Abdallahn.
Falon tsaf yake ko ina a gyare, ga ƙamshi mai daɗi yana tashi da sanyin ac. Sallamar Abdallahn da karaɗin Hajjo ya saka Adawiya data cika da haushin tafiyar Abdallah batare da ta saniba ta fito. Sam idanunta basu kai a kan Nu'aymah ba, dan haka ta daka tsalle cike da ihun murna ta ɗane Hajjo, saurin riƙota Ahmad yayi yana faɗin, “Ke malama karki ƙarasata ki jamin tsiya wajen su Baba malam”. Sakin Hajjon tai tana dariya ta juyo ta rungume Ahmad ɗin shima tana tsale.
“Wannan matar taka bata da man kai sam Yah Abdallah ”. Ahmad ya faɗa yana janye Adawiya daga jikinsa. Murmushi yaƙe Abdallah yayi yana kama hannun Hajjo ya zaunar a kujera. Hakan yay dai-dai da ɗagowar Adawiya zataima hajjo magana idanunta suka faɗa akan Nu'aymah dake tsaye gefe tana kallonsu.
“What?!!!!” Adawiya ta faɗa da sauri tana waro idanu waje, a take ta sarƙe da yawu kuwa ta hau tari.
Karan farko Nu'aymah ta saki wani lallausan murmushi da har ya bayyana fararen haƙoranta waje, ta taho da wani irin ɗoki ta rungume Adawiya dake tari tamkar zata amayo harshenta.
Dakatawa Abdallah da Ahmad da suka miƙe saboda ƙwarewar Adawiyar sukai. Nu'aymah ta ƙanƙame Adawiya jikinta tana matso ƙwallar da suka taru mata a ido akan dalili biyu. Ganin Abdallah, da kuma kewar Adawiyan.
Da wani irin sauri Adawiya tasa hannu biyu ta tura Nu'aymah, jikinta na wani irin rawar tashin hankali............✍
🤔Tofa, hajiya Adawiya yaya dai?🤗🚶🏻.
Barka da juma'a😍😘😍🤗
Leave a Comment