Sanadin Zane 7-8    🅿️7️⃣🫦8️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


       Cikin kankanin lokaci ta cinye ta saki wani katuwar gyatsa 


Kawu ya yatmusa fuska yace"shegiya kurma ba abinda aka sani sai abincin


Kallonshi tayi tana harararsa Kamar taji maganarsa yace"da yike ta rainani Ni in nayi magana tana ji,na rasa wanan matsifa ta wanan yariyar shi shaida ne kwata-kwata Bata ji amma wani lokaci Yana da kokonto a lamarinta Dan shegen matsifar son zuwa gun DJ ne da ita in ta gan ana rawa zata Fara takawa 


       Tafi da yaji tanayi yasa ya kalleta sai ya gan alama takewa hafsat da Kar ta bashi indomie 


Yace"yariya kinyi karya me Shiga tsakanin Mata da miji ai sai Allah bare ke kurmar banza "


Hafsat tace"Kai dai ka bar magana kasan tana iya karanta laben mutum in akayi sa'a ta gano me kace sai kuyi tashin hankali tunda ka girma ne baka San ka girma kayi ta biye Mata Kuna tashin hankali yariya na rainaka toh ka sani duk Randa data kashe ka ba lallai in maka takaba tunda har ta Kai ga tana d'aukar ice wata Rana tayi sanadinka saidai inyi matsa mudu biyar a bika da sadaka Dan Kai ka jawowa kanka Amma aure zanyi"


     Tashiwa zaune yayi yace"da kuwa kin kafurta hafsat ke kin Isa aiko sakin ki nayi ba ma mutuwa Baki Isa kiyi sure ba sai kin min idda saidai in Zaki ja da fadar Allah"


Hafsat ta shiga ciki ta watsa ruwa ta fito da taburma ta zauna tana kallon kawu daya kurawa kurma Ido 


Tace"Wai lafiya kake Mata wanan kallon "


Yace"hafsat watoh kullum in na kalli kurma sai nayiwa Allah tasbihi da Kuma mamakin kasancewarta a ahalin nan kin dai San Yar kanwata ce Amma wallahi wani lokaci sai inyi ta Jin kamar da wata a kasa Dan yariya gata dai kamar balarabiya ni kyaunta ma firgitani uake shiyasa Kika gan na dage Ina ta zuba hanun jari a kanta,kudina kanta yake karewa dan wallahi bazan bawa talaka ita ba kinji rantsuwar musulmi,duk inda akayi ranan da aka halliceta ranan sa'a ne ki dubeta fah watoh shi Allah ba ruwansa da ya Mata kyau yayi Mata diri ya Mata tsayi sai kawai yayi ta kurma,Allahu Akbar Allah buhayi gagara misali Kuma uwarta a balaguro ta sameta can uwa duniya Cameroon 


    Hafsat tace"Ni kaina Ina tausayin wanan baiwar tasa"


Kawu yace"Kuma ita Bata tausayin kanta ba '


    Jibrin ne ya shigo da sallama da niyyar ya ci abinci sai ya gan murhu a jike kwalawa ummi Kira yayi ta fito ta zauna kofar d'akinta yace"ummi Ina abinci na"


Ummi tace"banyi ba sai Kuma gobe so Nike kowa ya kwana da yunwa duk uban wahalal da naci wajen had'a wutar fannah ta kashesa sanadin kabiru baxan kashe kaina ba 


      Ai jibrin Fara buga kafa yayi Yana yi Kamar zaiyi kuka Yana cewa"kawu ka gan abinda ka jawo yanzu me kake so inci 


Kawu yace"gani har sai ka nimi abinci kawai dai in kwanta kayi ta datseni kana ci in Banda iskanci godai godai da Kai kana kukan yunwa ko da yike ban gan laifinka ba laifin uwarka ce da ta muku wanan b'arnan,shekaru baya ba abinda ba a Gaya Mata ba karta auri mahaifinki tace tsam soyayya ya rufe Mata Ido ai tare zasuyi arziki,lokacin wani alhaji Allah ya jikan musulmi alhaji mato ya sota taki tace sai mahaifinki gashi dai har ya mutu beyi arzikin ba an haifeshi Yana fama ya mutu Yana fama yanzu da a ce alhaji mato ta aura ai da Kuna da gado Amma taki mahaifinku ko tabarma ya bar muku 


    Jibrin ya samu wuri ya zauna yayi tagumi ji yake kamar ya rufe kurma da ko a jikinta zanenta na jaraba take hankali kwance kawai Dan kawu ya cinye Mata abinci sai ta kashe wuta a zuciye ya mike zai Kai Mata duka saidai kafin ma ya Kai kawu yace"karka kuskura dan da ka tab'a min ita gara ka lakada min duka wallahi insurance kake gani zaune itace co'operative Dina duk wata kudina kanta yake karewa ka sani. so kake ka daketa in Shiga uku wani Abu na samunta wallahi haukacewa zanyi 


         Komawa yayi ya zauna ita Bata ma San sunai ba Dan Bata ji me ake ba 


Kawu yace"in Banda duniya ta lalace Kai baka Isa ciyar da kanka ba ka wani Zo niman abinci toh mu gan sauki ni kabiru 


       Ummi dai Bata ce musu komai ba....jibrin na zaune Yana kukan zuci Dan beds juriyar yunwa 


         Zane kurma keyi hankali kwance kawu yace"hafsat


    Ba tare da ta kalleshi ba tace"Ina ji "


Yace"Yana gan kina ta wani Jin kanki bàyan kai kikayi laifi kin fita Baki sanar min bance komai ba Amma kike wani Shan kamshi 


        Tace"ka fadi me zaka fad'a Dan Allah"


      Yace"kamar yariyar Nan ta dusashe ko?na gan kamar tayi baki,ko za a canza Mata cream ne"


        Hafsat ta me wani muguwar kallo tace"a hakane ta dusashe sai ka b'ata Mata skin dinta hankalinta zai kwanta kabiru a cikin wata biyu an canza Mata cream yafi guda biyar yariyar nan tana fa da haskenta Mai kyau Dan ko wani nature sai haka Kuma sai Mai ake canza Mata da yike itama doguwar burine da ita sai biye maka take"


Yace"nifa bance ta bleaching ba Wanda dai za gyara haskenta tayi ta haskakawa 


Hafsat tace"da haka' ake kawai ga bleaching din ai....in so kake a canza kawu kudi Dan so uku Ina siyowa kana kin biya"


        Yace"kashh hafsat daga magana sai a tada tsohon bashi a bar magana"


Kwafa tayi,ummi tace"jibrin sai Ina Fahad ne shiru dai har yanzu Kira min shi inji ko lafiya"


Kawu yace"Ina da lafiya tunda yace"ba zai nimi aikin kwarai ba kullum yawo da jaka kamar wanzami yanzu duk dadewar Nan sai ya dawo da abinda bazai fi dubu biyu ka tambayeshi na Kati ya karanta ma coc......."


    Be karasa ba Fahad yayi sallama shiru yayi Yana gyara Zama yana washe Baki yace"Ashe kana tafe yanzu Nike cewa a Kira a ji ko lafiya baka dawo ba ummika tace Kai ba yaro bane shine Nike fahimtar da ita duniya fah ta canza ba kamar da ba....da da duniya ke kwance kamar lagwani waye yasan wani sata yara,yanzu ko duniya a tsaye take kyam cike da iskanci da rashin kunya har a biyo ka gida a saceka Allah yasa mu dace dai"


Fahad yace"Amin kawu "


Kawu ya sake kishingid'a yace"toh an dai dace ko Dan wallahi Allah dai yayi zamu sake ganawa yunwa be kasheni ba da baka dawo ka sameni ba ka ganni nan toh yunwa ce take cina na kasa bambamce Baki da fari "


         Fahad ya kalli ummi ta amsa cike da fara'a yace"ba ayi girki bane"


Kawu yace"karka tsaya binciken tarihi ka motsa kawai mu samu abinda zamu ci"


Fiti da taliya biyu yayi a jakarss ya ajiye 


     Jibrin ya mike ya d'au abacan anty hafsat yasa gawayi ya Fara Hira wuta 


Yace"Bari kurma ta dafa Mana"


Kawu yace"lah lah lah Kai ka gan kalar girkine ita ah'ah Kar muyi wasan da ba dariya so kake tayi Baki a maidani baya 


          Jibrin ya Fara kunkuni kawu yace"fad'a inji in banci ubanka ba


   Fahad na murmushi yace"baza ayi Haka ba ai sai in dafa Mana 


      Kawu yayi me kallon kasa kasa

      Jibrin yace"Zan dafa Yaya 


Fahad ya mike zai shiga d'aki yace"anty hafsat ya gida d'azu na Aiko ki bada Wana sakon ance Baki Nan badai maitumbi Kika je ba "


    Kafin hafsat dake washe Baki tayi magana kawu yace"wane ita ai yanzu maitumbi yafi karfinta d'ari biyar ne da kudin Moto daga Nan,fuel ya Kara kudi masu Keke ke shanawa"


    Dariya ne ya subucewa ummi har shi Fahad din 


    Tace"ba Nan naje ba Nan Tunga na tafi yiwa wata Mai jego design


Fahad yace toh Allah bada sa'a 


Shigewar Fahad ba jimawa sai ga sa'adatu ta shigo da kuka 


Kawu ya zabura Yana cewa Yaya Yaya da wanan Daren badai yaji kikayi ba 


Sa'a na kuka tace"ummi wallahi na gaji da auren alhaji Ashe dama ba shi da lafiya ya aureni ku duba fa watan goma da aure Amma a ce dudu befi so biyar mukayi ba "


    Ummi data rikece tace sako ki yayi ne?"


   Kawu yace"ban Gane ba kukayi me so biyar "


Kuka ta fashe dashi Fahad dake jinsu ya fito ya dakawa sa'a tsawa yace"miye haka miyasa Baki da kunya ne wace irin magana ne wanan kikeyi 


Kawu ya d'aga me hanun yace"Bari tayi magana"ya maida kallonsa ga sa'a itama kurma kallonta take 


Yace"ki fayyace min komai ki farfasa min komai,ki budemin komai inda Zan fahimta"


    Sa'a tace"kawu tunda mukayi aure wallahi befi so biyar ya kusanceni ba ko haihuwar ummita wallahi rabone kullum Nike korafi Ina ta Jin kunya sanar daku shine yau Dan nayi Masa magana yace"shi haka' yake in baxan iya Zama ba in tafi 


Kawu yace"da fatan dai kin taho da Kira Baki bar Masa ba"


Tace"eh Yana pake kofar gida 


Kawu yace"kin kyauta yanzu dai a takaice bashi da lafiya ne ko?"


      Tace"wallahi kawu lafiyarsa kalau tunda in ya so dan kansa yanayi 


Kawu yace"toh me take cikin dare saidai kuyi bacci 


Nan ko kunya ne ya rufeta ya daka Mata tsawa yace"bani amsa 


Tace"kowa baccinsa yake"


Kawu ya jinjina Kai yace"yayi Ina ruwan casbi sarkin lazumi dan mugunta sai ya barki kina kwasar takaici toh gone zanji dalili ?"Maman Nur 

No comments

Powered by Blogger.