Sanadin Zane 1-2


 

       1️⃣🫦2️⃣

    

Monday aka ce tushen aiki 


12:40pm 


Fitowa yayi Yana tafiyar kasaita Wanda ke nuni da jinin dake gudana a jiyoyinsa na cikakkiyar sarki ne watoh shi jinin sarauta ne ta ko wace fuska .... agogo ya duba kafin ya shiga motarsa domin aid dinsa sun shirya jiran fitowarsa kawai ake daga meeting zashi lunch....kafin ma ya karaso an bude me motar tsakiya ya shiga sai aka kulle 


A mugun gajiye yake hakan yasa ya jingina da kujera ya lumshe Ido Yana Jin kewar gida na lullub'eshi yau dai zaiyi kokarin ganin ya Gama abinda ya kawo su ya koma gida ya gaji da kasar Nan 


        *Bilkebab minna niger state* 


         Babban eatry ne da tayi suna a garin minna, wuri ne na manya mutane irin yan siyasa da kuma manyan gomnati sai kuma masoya da suka amsa sunansu masoya watoh ba ko wani saurayi zai iya Kai budurwarsa Nan 


         

          Convoy ne na motorci wanda kallo daya zaka musu kasan babba ne ke ciki domin harda na security 


       Tsaye take ta bawa gate din baya sai bincika jakarta take da alamun dai da abinda take nima tayi zurfi hankalinta yayi nisa 


     Horn ake kamar za a tada gari amma bata motsa ba bare su sa ran zata matsa tun suna yi a hankali har suka fara matseshi continuesly sai piiiiiiiiii piiiiiiii kake ji ba gaugautawa 

 


Motarsa ne a tsakiya daman ya kishigid'a ne ya lumshe ido saboda gajiyar dake jikinsa sai ga wanan azabben horn din a firgice ya bude idanunsa yana mamaki dan duk wani wanda ke karkashinsa Kuma ko yasansa toh an San da da rashin son hayaniya baya ko kad'an baya san hayaniyar 


      Driver dake motar gaba kallon wanda ke gefensa yayi yace"wanan ai rainin hankaline Ya za ayi ta tsaya a hanya ana horn taki matsawa 


Bude motar driver yayi da niyyar zai je ya turata dan a zuciye yake wallahi yasan tana jinsa ta sharesa 


    Daidai lokacin data sauke ajiyar zuciya ta d'au jakar materials dinta tayi cikin gidan abincin ko juyawa batayi ba dan bata ma san sunai ba wallahi 


Har dan dagawa yayi daga zaune da yake yana kallon bayanta yana mamakin nata kalan iskanci dan wanan horn din ko kurma ce ita zata ji,a ranshi yace"Nigerians"


              Gyara parking sukayi security suka fito suna kalle kalle supervising the environment kafin suka bada umurnin ya fito 

Wow nace domin ya kai duk inda ake bukatar namiji ya kai ga jiki ga height wanda kallo daya zaka masa ka gano sarautar dake gudana a cikin jininsa dukda ba wata shiri yayi da zai nuna hakan ba but izza da dattakonsa ya nuna waye shi,


      Ciki sukayi Yana tafiya kamar dai baya son Yi Kamar wani Mara lafiya 


      Ciki ya shiga aid dinsa na kokarin sa a Kori mutane Dake ciki ya d'aga musu hanun tunda yasan shi ba Dan kasa bane kuskurene a nimi nunawa mutane ikonsa ba tare da sun San shi din ko waye bane hakan sai jawo Masa rainin Amma dukda Haka Saida suka Samar me kebetancen wuri ya zauna shi kadai sanan ya d'au menu Yana dubawa 


      A inda ta zauna da friend dinta tana facing dinsa ne tunda ya shigo ta zuba me Ido tana kallonsa har Saida kawarta ta tab'ata tana tambayarta da hannu


    Girgiza Mata Kai tayi alamun ba komai tana kallonsa isah daya kawo su na kallonta dan da k'yar ta yarda ta Zo Saida kawarta Amina ta roketa a waya kafin ta zo Allah ya gani yana son fannah har cikin ransa ko ya take Yana sonta da kaunarta but sai wulakanci take Masa 


        Idanunsu na had'uwa ta sakar me murmushi daya kusan narka me zuciya dan Saida ya dafe Yana lumshe idanunsa 


    D'auko jakar material dinta tayi ta fito da wani board Yana da dan girma but ba sosai ba 

Ta fito da paint dinta 


Gyara Zama isah yayi a tunaninsa shi za a Zana Dan a wautansa shi take kallo tun d'azu, da yike shima Yana facing dinta ne


Amina ce ta Kuma tab'ata sai ta harareta 


Shiko ya d'au takkadarta da suke comunicating da ita 


     Ya rubuta mata are you ok honey you are smiling "


    Amsa tayi ta karanta sai ta ajiye ta Fara hada paints dinta 


       A Haka waiter ya kawo musu abinci aka ajiye musu a gabansu Amma Bata ma kalli abinci ba,Amina ko tuni ta Fara ci tana dambe da kaza 


      Shiko isah Abu goma da ashirin ne ya damesa gashi su ba Daman ayi hira dasu gashi ko tashi basayi ita Amina hankalinta na Kan abinci itako sai zanenta take hankali kwance sai duk yaji ba Dadi be ma iya tab'a abincinsa ba 


    Ganin Yana blocking views dinta sai kaiwa ta Kai hanun kansa ta tura gefe hakan yasa ya juya Yana kalle kalle saidai hankalinshi be Kai kan yarima ba 


      Haka kawai ta ji a ranta Yana da sarauta dan ko cin abincinsa abin kallone ci yake kamar baya son ci Kai inda da dama toh fah da yace a basa a Baki 


        Cikin kankanin lokaci ta Gama zanesa a position din da yake zaune wallahi Kamar a busa me Rai yayi magana sabar kwarewa dan sak shi ne


Ajiyewa tayi a gefe sanan ta d'auko wata board daman daga kasuwa ta fito siyo kayan paint ta biyo Nan wanan karon lumshe Ido tayi tana imagining dinsa a kujeran sarauta data lumshe sai ta bude ta cigaba Aiko ta zanesa zaune akan wani kayatancen royal chair irin na sarakai har sanda ce a hanunsa ga rawaninsa abin birgewa baground tasa me shegen kyau ba kamar dayar da exactly baground din gidan abincin tayisa ba Kuma da suit din jikinsa paint dinta is real wanan baiwa ce daga Allah and wanan shine abinda takeyi taji tana farin ciki 


Koda ta d'ago ta gan har sun Gama cin abinci Amina ma ta cinye ta kalli aminan Dan yunwa takeji 


Amina ko sai cire nama take a hakora tana Wasa da halshe 


     Cikin yarensu na kurame cike da matsifa ta Fara yiwa Amina matsifa harda tafi da yike da karfi takeyi sai ya kalli direction din da take Yana mamaki how could a lady be lousy like this 


       Sosai suke fad'a isah ba damar rabawa Dan shi be ma iya yin yaren kuramen ba saidai suyi rubutu ya dade da sanin fannah tana da fad'a ga zafin zuciya 


     Dan har plate ta d'auka zata fasawa Amina akai Allah ya Kare yayi saurin tarewa 


     Mikewa tayi cike da haushi ta kwashi pain work din da tayi ta rubuta fannah art work in Italian hand writing sai phone number ta 


     Tana zuwa security Dake tsaye Dan nisa dashi suka hanata karasawa 


Murmushi tayi sai ta ajiyewa security din board din ta juya tana komawa table dinsu Jakarta ta kwashe ta bar wurin Har ta Kai exit sai Kuma ta koma gun security din ta 
Maman Nur 

No comments

Powered by Blogger.