Gidan Aro 5

 


05*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*


Ya jima tsaye bakin k’ofa yana dubanta, yana mai tina tattaunawarsu da Inne. A hankali ya soma takowa cikin d’akin har ya k’araso bakin gadon da take kwance.. B’angaren da fuskarta yake duba ya k’arasa, ga duk’a kad’an yana mai k’ura mata idanu.. Su kuma kalan tasu k’addarar kenan.. Da fari mahaifinsa ya rasa sannan mahaifiyarsa ta had’u da tsautsayi na jinya yanzu ga tilon k’anwarsa itama ta tafi.. Tinani yake lokacin ahalinsu ke cike, Daddynsa Mamynsa da kuma ‘yar k’aramar k’anwarsa Ikram.. Ahali mai cikeda Farin ciki da k’aunar juna.. Inama wad’ancan lokutan zasu iya dawowa.. Inama zai bud’e idanunsa yaga mafarki ne duk abubuwan da suke faruwa.. Amma saidai wannan itace gaskiyar, littafin k’addararka a kullum bud’e maka Sabon shafin rayuwa takeyi.. Rayuwar duniyar kenan, duk yanda ka kaiga ganin cewa dad’i kakeji a duniyar nan toh wannan dad’in k’ayadadde ne, aronsa aka baka akwai ranan da zaka wayi gari ka rasa wannan jin dad’in.. Sannan duk yanda ka kaiga ganin wahala kake sha toh wannan wahalan yanada wa’adi akwai ranan da zai k’are.. Duniya ba gidan zama bace gida ce ta jarabawa, dik yanayin daka tsinci kanka ciki a gidan duniya toh kuwa ko shakka babu jarabawa ce kake cikinta.. Gidan duniya gidace da aka baka aronta domin a jarabceka a cikinta, ba gidan Sharholiya bace sannan ba gidan baje koli bane.. Kai d’in tamkar matafiyi ne da aka baka Aron Gida domin ka yada zango na wani d’an lokaci k’ayadadde.. Babu komai a GIDAN ARO face tarin jarabawa da kuma k’alubale na rayuwa.. 


Mu’azzam ya lumshe idanunsa yana mai kamo hannayen mahaifiyarsa wacce ga dai idanunta a bud’e tarau amma wani b’angaren take duba.. Bata um bata um um.. A hankali ya soma furta “Mamy inada babban albishir da zan miki.. A yau d’in na soma gano wani abu gameda mutuwar Ikram.. Kuma na miki alk’awari in sha Allah bazan gajiya ba har sai na samo bakin zaren.. Mamy na Sani addu’arki da albarkanki suna tare dani.. Fatana shine Allah ya baki lafiya ya tashi kafad’unki.. Inada yak’inin cewa wata rana komai zai wuce ya zamto labari.. Wanda sukaci zarafin d’iyarki suka kuma kasheta zasu biya.. Zasu biya abinda suka aikata Mamy.. I won’t rest until I get to the bottom of everything..” Ya k’arashe yana mai sumbatar hannayen nata dake rik’e cikin nasa had’ida lumshe idanunsa siririyar hawaye ta gangaro daga cikin idanunsa guda...


Yana duk’e wajen yaji hannun mutum a kafad’arsa, sanin ko wanene tsaye Kansan ya sanyasa k’ok’arin saita kansa kafin ya mik’e yana goge fuskarsa da duka tafukan hannayensa..

“Sorry Daddy banji shigowarka..” Ya fad’i yana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye.


K’ak’aro murmushi Alhaji Marwan yai kafin ya girgiza kai kad’an yace “Babu komai Mu’azzam..”


Ya kuma duban Mu’azzam d’un  cikeda kulawa kafin ya maidoda dubansan ga mahaifiyar Mu’azzam d’in.. Idanunsu Su duka biyu naga mahaifiyar Mu’azzam d’in Daddy Ke fad’in “D’azu muke magana da Inne cewa tana so Nuratu ta koma Fufore.. Za’a gwada yi mata maganin gida ko Allah zaisa a  dace.. Hajara ta fara mun maganar sai kuma Inne ma tazo da batun.. Toh amma a zahirin gaskiya Mu’azzam ni banyi Na’am da maganin gargajiyan nan ba.. Tinda ga abinda likitoci daga manyan asibitoci na duniya suka fad’i.. Zai matuk’ar wahala ta warke a bisa iya binciken da sukayi..So ina tunani kar aje a shiga bata wasu magunguna da babu dosage ba likita bane yayi prescribing aje a k’ara rikita jikin nata.. Toh amma kuma sai nayi tunanin likitocin nan ba sanin gaibi sukayi ba.. Cuta Allah Ke sakashi kuma shi Ke yayewa, saidai yakan bama wasu daga cikinmu ilimin sanin magani domin kuwa bai halicci cutan ba har saida ya sauk’ar da maganinta.. Ba Lallai sai ta hanyar likitoci wanda sukayi karatun ilimin zamani ba.. Wani dake rayuwa cikin daji ma sai Allah ya basa ilimin sanin magunguna a kumayi amfani dashi idan Allah ya nufa sai a dace...Amma Kai mai kake gani..”


Shiru Mu’azzam ya d’anyi kaman mai nazari kafin yace “Haka ne Daddy..Abinda ka fad’a gaskiya ne.. And duk hukuncin da ka yanke zanyi na’am dashi.. Kaine mijin Mamy, and you’ve every right ka Kai Matarka jinya yanda kakeda tinanin za’a iya dacewa da magani.. Inne ta min maganar d’azu dana shiga wajenta.. Daddy duk hukuncin da kuka yanke yayi.. Fatanmu shine Allah ya Bawa Mamy lafia..”


Murmusawa yai kafin ya d’an bubbuga kafad’ar Mu’azzam yace “Ka kasance d’a mai biyayya a wajena.. Ko Hamma ne yake raye yanzu iyakacin biyayyar da zaka masa a matsayinsa na mahaifinka irinsa kake min Mu’azzam.. Allah Ubangiji ya maka albarka ya dafa maka cikin duk abinda ka saka gabanka...”


Kansa a k’asa kad’an yace “Ameen Daddy..”


“Ya maganar binciken case d’in Ikram..  Ba wani abu da aka samu har yanzu..?”


Mu’azzam ya d’an shafi sumarsa yace “Muna nan Muna bincike  Daddy.. And da zaran mun sami wani haske zamu maka k’aran a Kotu..” 


Jinjina kai Daddy yai yace “Allah ya mana jagora, Allah kuma ya tona asirin duk wanda sukai mana wannan aika aikan..Zan kira Adnan yaje yai mana booking flight zuwa Adamawan within the week.. Zaka samu zuwa kuwa..?”


“Idan Mamy zata tafi ya kamata nima ina wajen.. But I’m not sure idan zan samu damar hakan..”


Daddy ya jinjina kai yace “Hakan yayi, kar ka samu damuwa zamuyi duk abinda ya dace in sha Allah.. Just concentrate on your job kaji koh..Allah ya shige mana gaba..”


Mu’azzam ya amsa da “Ameen Daddy” 

 wayarsa Ta soma ringing, sallama yaima Daddy ya fice yana amsa wayar..


**


SULEJA 
Sabeera na gefenta su duka biyun sunyi jigum jigum kowacce da kalan tagumin data zabga suna sauraro cecekucen dake tashi daga tsakar gidan Tabawa tana fad’in wllhi sai ta d’ebo masu ‘yansanda muddin wa’adin data basu ya cika basu nemo mata kud’ad’enta ba, dan itama kud’ad’en mutane ne da suka turo ta sai masu kaya ta had’a ta baiwa Uwani da shike Tabawa  tana business na pre order irin na online d’in nan, ga mutane masu kaya Sun soma d’aga mata hankali, babu kaya babu kud’i ta tattara kud’in mutane ta bawa Uwani bashi dan tayi hidiman biki, da nufin da zaran Angon Sadiya ya biya kud’d’en events zata maida mata abinta harda k’ari ma tace zata mata, zata biya da interest kenan(K’arin nan kuwa ya zama kud’in ruwa, cin kud’in ruwa kuma haramun ne komin ka’ank’antarsa).

A tak’aice dai itama Tabawa son banzanta ya kaita ya barota, babu uwar kud’i babu riba ga mutane Sun tasota gaba.. Komi zakayi yanada kyau ka tsarkake niyya..


Sabeera ta kuma sauk’e ajiyan a karo na babu adadi, ta canza position d’in taguminta yafi sau abinda yafi “K’awata kodai Police station zamuje ne muyi filing report na missing person Ko Allah zaisa a dace a zak’ulo mana Sagir yanda ya shiga ya fita..”


Ai bata Kai aya ba Sadiya Ta shiga girgiza kai tana kuma goge fuskarta da tuni har ya kumbura sabida kuka “Haba Sabeera idan mukaje police station kuma ai shikenan mun kai kanmu, Tabawa ta samu daman maka k’arar Ummata a sauk’ak’e.. Ni bama wannan ba kin sanni da mugun tsoron duk abinda zai jawo mun tashin hankali.. Duk rawar kan nan nawa da san abin duniyata wllhi Sabeera ina mugun tsoron abinda zai had’ani da ‘yansanda balle har a kulleni.. Bana son ‘yansanda bana k’aunar abinda zai had’ani dasu..Sannan nasan Kema kina fad’a ne kawai dan naji sanyi cikin zuciyata, a gidanku akaji kin rakani police station Ko k’ofa baza’a sake barinki ki fita ba..”


Sabeera ta kuma sauk’e ajiyan zuciya tace “Yanzu ma Mama ce na samu tamin hanya na taho nan dan wllhi Baba cewa yayi ko mai kamanni na aka sake gani na fito daga gidanku Dutse  zai maidani wajen Kakata ya aurar dani a cen.. Dama tin ba yau ba ‘yan Sa idonsa ke kai masa gulman ni kad’aice k’awarki a unguwar nan, kowa bai Barin d’iyarsa tayi abota dake sabida rashin kamun kanki.. Kinsan ‘yan unguwar nan ‘yan unguwar nan da shegen gulma da saka ido, musamman wad’anda yake d’an masu alheri, suke Kai masa gulma tinda shi ba wani yini  yake a nan ba, sai dare yake dawowa... Toh yanzu da batun auren nan ya faru abun Sai ya dad’a worse dan ance ma D’andamfara ne ya rud’eki bayan ya gama abinda zaiyi dake ya gudu ya barku da tulin bashi..”


Sadiya Ta lumshe idanunta wasu hawayen na gangaro mata, Allah shine shaidanta dik kwad’ayinta bata saida mutuncinta ga wani namiji.. Amma saidai a rayuwa fuskar daka bayyana ma mutane da ita zasuyi kwatancenka sannan da ita zasu maka shaida.. Su mutane har kullum abun kushewa suke nema tattare da kai Sai su aibataka ba tareda Sun duba nasu aibun dake tattaredasu ba.. Tabbas Duniyar yanzu kiwon mutane ake bata dabbobi ba..


Sauk’e ajiyan zuciya tai tace “Nasan za’a rina haka, yanzu Ko k’ofa ban isa fita unguwar nan ba wllhi sai kiga har ‘yan yara suna nunani da yatsa, rufin asirin Allah ma makaranta ana strike nasan da na zama abin cecekuce da nunawa ana zancen angona ya gudu ran aurenmu...” Muryarta ya soma rawa sanda taci gaba da fad’in “Maiyasa al’amara suka kasance haka Sabeera.? Maiyasa Sagir zai rud’eni ya yaudareni..? Shin laifi ne dan naso ma kaina abu mai kyau.? Laifi ne dan na zab’awa kaina rayuwa mai inganci..? Sabeera ki dubeni ki gani wllhi ni ba matar k’anan mutane bane, matar manya ce ni.. Idan nace manya Ina nufin masu kud’i masu abun duniya Sabeera..Ni ba yawon banza nake ba kuma duk samarin da nayi k’arya yace na mik’a masa kaina, da yawansu burinsu suyi soyayya da kyakkyawar mace ce irina ni kuma nai masu wayo da dabaru irin tamu ta mata na amshe abin hannunsu, da zaran naga kana neman shige Gona da iri nake sallamarka ai ke shida ce.. Ni abinda nake so kawai shine na auri mai kud’i wanda zanji dad’i a gidansa na fantama na sakata na wala na baje koli na nayi Yawo k’asashen duniya mahaifiyata da ‘yanuwana suji dad’i.. Wannan shine mafarkin Sadiya a duniyar nan Sabeera....” Ta k’arashe guntun hawaye na zubo mata..


Hannayenta Sabeera ta kamo tana mai k’ok’arin k’ak’aro murmushi take fad’in “Kowa yanada ‘yancin da zai mafarkai da burukan da yake so ya cimma a rayuwa.. Amma saidai mukanyi kuskure idan bamu nemi zab’in Allah a ciki ba.. Ba tarin dukiya ba Sadiya, ki nemi farin ciki da kwanciyar hankali a gidan aurenki.. Aure is a lifetime commitment ba abu bane da za’ayisa jeka nayi ka, abu ne da yake buk’atar dogon nazari da bincike..”

Katse ta Sadiya tai da fad’in “Dan Allah ni kiyi shiru kar ki karyar min da zuciya Sabeera, kud’i abin so ne kinji..  Maza kuma dik halinsu d’aya ne, da na auri talaka nayi kuka a bakin murhu wuta yana gasa ni gwara na auri mai kud’in nayi kuka a Dubai a rarrasheni da new brand of car..” Ta k’arashe tana kuma gyara zamanta..


Sabeera Ta murmusa tace “Saidai ba Sady pretty d’in ba.. Mai hali ai bazai fasa ba, yanzu ana tinanin mafita Ke baki daddara da zancen mai kud’in ba.. Koda shike I won’t judge you Sady sannan kuma bazan fasa gaya miki gaskiya ba, Kema Kinsan da hakan, bazan tab’a aibataki ba dan nima k’addara bata wuce kaina ba.. Babu wanda yake wuce k’addararsa a rayuwa kuma baka San da mai zata Zo maka ba, saidai a kullum ana so kayi fatan Allah ya nisantaka da mummunan k’addara...”

Sabeera Ta kuma gyara zamanta tace “Sabida har yanzu baki had’uda true love d’inki bane shisa tinanin nan ya kasa barin kanki.. Bari kiga dik randa Allah ya had’aki da true love d’inki zaki k’aunacesa ba dan abin hannunsa ba.. Dashi ko Babu zakiyi hak’urin zama dashi..”


Tab’e baki Sadiya tai kad’an tace “Babu wani true love Sabeera.. True love kawai nauyin aljihunka ne kin gane..”


“We shall see..” Sabeera ta fad’i tana mai mik’ewa tsaye “Ni zan wuce naga magrib na hararowa kafin ‘yangulma su fara fito da bencinsu..” Ta k’arashe tana yane kanta da mayafin Doguwar rigarta..


Sady Ta mik’e tana fad’in “Ki tsaya na taka miki..”


“A’a wllhi kiyi zamanki kawai, and please ki rage saka damuwar nan haka cikin ranki Allah zai kawo mana mafita kinji koh..”


Jinjina mata kai tai tana fad’in “Toh K’awata na gode sosai sai munyi magana..”


A tsakar gidan ta tadda Umma ta had’a tagumi, ta duk’a kad’an tace “Toh Umma na tafi saida safe..”


Tsaban Umma na cikin tsaka mai wuya ko sallaman Sabeera bataji ba har saida Ashiru ya tab’ata yana fad’in “Umma Anty Sabeera tace miki ta tafi..”


Umma ta nusa tace “Toh Sabeera ki gaida gida koh, mun gode sosai ki gaida Maman taki..”


Sabeera Ta amsa da “Zataji Umma..” Kafin tai ficewarta..


**


K’arfe takwas daidai a Office yai masa, yana rik’e da disposable cups guda biyu wanda coffee ne cikinsu.. 


Danger yana hangosa ya soma murmushi yana shafa hab’arsa dan yasan Mu’azzam d’in dole ya kuma dawowa wajensa..

“Inspector.. Ban tsammaci ganinka da safen nan ba..” Ya fad’i yana duban Mu’azzam d’in..


Saidai ga tsananin mamakinsa shima Mu’azzam d’in murmushin ya sakar masa kafin ya zauna yana mai aje masa disposable cup d’aya na coffee, lokaci guda yake furta “Don’t you think drinking coffee together is much better than smoking cigarette.. Baka so ka zama abokin shan coffee d’ina..? Kaman dai yanda ka zamto abokinsa na shan sigari...” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da furta “After all, they say Smokers are liable to die young..” Ya d’an gyara zamansa yana  tapping table d’in da ya raba tsakaninsu da yatsarsa mai zobe, sautin zoben saman table d’in na fitowa a hankali, lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Da alama zaka d’auki tsawon lokaci a nan sannan zamu jima muna shan coffee tare fiyeda lokacin daka kwashe kana shan sigari taredashi..” Yai maganar yana mai sipping coffee d’insa k’afa d’aya bisa d’aya..


Danger ya dubesa da mamaki ya kuma dubi coffee d’in da ya aje masa gabansa..


Murmusawa kad’an Mu’azzam yai kafin yace “Karka damu ban saka guba a ciki ba, because I want you to live long and spend your declining years in jail..”  Ya k’arashe yana mai kuma sipping coffee d’insa still k’afarsa d’aya na kan d’aya...


Danger ya murmusa kad’an yace “I’m not scared of your empty threats, Mr Inspector... Bakada wani hujja ko dalili k’wakk’wara da zaisa ka ajiyeni a nan..” Yai maganar yana juya cup d’in cikin hannunsa..”


“Ka Sani wad’anda kake karewa bazasu maka haka ba, Dama kad’an suke jira su samu akanka sannan su gama dakai..Sannan ni kuma...” Ya d’anyi fasali kafin ya mik’e daga cikin kujerar ya kawo bakinsa saitin kunnen Danger yace “ Ka rubuta wannan ka ajiye, ni kuma Sai na tabbata ka tafi kurkuku tsawon rayuwarka..” Yana ida fad’in haka ya mik’e ya juya zummar ficewa..


Muryar Danger ya sinkayo yana furta “Gidan Alhaji Kabir Isyaku D’an canji dake Suleja..”Cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba..


Danger yaci gaba da furta “A k’ofar wannan gidan za’a d’aura aurensa, kaman yanda naji ya furta a lokacin da yake waya da budurwar tasa..”


Juyowa Mu’azzam yai yana nanata sunan mutumin da Danger ya ambata, lokaci guda ya tako zuwa gaban Danger hannayensa saman kunkumi “Ya akai kasan duka wad’annan..?”


“Believe me Inspector, iyakacin abinda naji kenan daga cikin wayar nasa.. Sannan Iyakacin abinda na sani kenan gameda wannan mutumin...”


Mu’azzam yai masa K’uri kafin yai alama ma sergeant guda dake tsaye bakin k’ofa, yana k’arasowa ya sara masa.. Umarni Mu’azzam d’in yai masa cewa ya maida danger cikin cell d’insa..


Danger yana tarjewa yana fad’in “Rankaidad’e ai sai ku sakeni nayi tafiyata tinda na fad’i Iyakacin abinda na sani..”


“You’re not off the hook yet..zamuci gaba da shan coffee tare na d’an wani lokaci...” Yai maganar yana mai sakar masa murmushi da gefen bakinsa.. Daga haka bai kuma tsayawa sauraron Danger ba yai ficewarsa ya nufi ofishinsu cikin sassarfa.

A hanya ya had’uda da Yusuf da Assad, suka shige cikin Office yana sanar dasu yanda sukai da Danger.. 

Ana haka Maleeka ta shigo tana fad’in ai mata afuwa na rashin k’arasowarta kan lokaci.. Takaicin da take basa yasa bai Ko kalli yanda take ba..

Yaci gaba da shirya bindigarsa had’ida sanyata gefen suit pocket d’insa, lokaci guda yake fad’iwa Yusuf su tsaya nan zasuje shida Assad, idan suna buk’atan backup zasu sanar dasu..

Yusuf ya amsa yana mai sara masa kafin suka fice, Assad na kashe wa Maleeka idanu alamun tai hak’uri da abokinsa Ta sauk’e idanunta akan wani amma Mu’azzam kam bazata samesa ba..

Harar y’ar wasan da suka saba da Assad ta jefa masa, yabi bayan Mu’azzam yana rik’e dariyarsa.


**


Tin farar safiya Tabawa take abu d’aya a gidan, banda zuba ruwan masifa da bala’i bata komai, ta shiga janyo Habeebu autan su Sadiya tana fad’in kodai a biyata kud’inta kokuma ta tafi dashi.. Sadiya kuka Umma kuka ga Abbansu bai gida ya fita.. 


Tsaban tashin hankali daga ita sai ‘yar T-shirt d’in dake jikinta da zani ta fito ko takalmi babu k’afarta balle d’ankwali.. Ihu kawai take cikin unguwar tana neman a kawo masu d’auki wata mata tayi Garkuwa da k’aninta.. ‘Yan unguwa da suka San cewa su Sady na cikin rikici tsamo tsamo babu wanda yabi takanta Sai kururuwa take tana tsalle hannu aka tana fad’in a taimaketa anyi garkuwa da k’aninta..


Dashike daga can bakin layin sukai parking motarsu hakan yasa suka shigo da k’afa..

Sam bata kula da mutanen ba gudu kawai take hannu aka idanu a rintse tana tsalle tana fad’in a taimaketa, taimako taimako.


Ta karyo kwana kenan a wannan yanayin suma sun nufo layin kenan saiji tayi ta bangaji mutum ta fad’a cikin jikinsa..


Cak ta tsaya ta daina ihun saima k’ok’arin ware idanunta da take..


No comments

Powered by Blogger.