Gidan Aro 4

 


*04*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
K’aran da wayarsa tai ne ya sanyasa k’ok’arin zame jikinsa daga nata, Safeenah kam da alama bama taji sautin wayar ba har saida taji Mu’azzam na k’ok’arin cire hannuwanta daga rik’on da tai masa.Ta d’ago tana dubansa idanunsa naga fuskar wayarsa yana ganin mai kiran nasa, caraf itama ta sauk’e idanunta kan screen d’in wayar tasa.. Sunan Assad data gani ya sanya gabanta wani irin fad’uwa.. Tasan Assad amininsa ne sannan abokin aikinsa ne a CID Office.

Haka kurum taji wayar da Assad Ke masa nada alak’a da case d’in mutuwar Ikram..


“Excuse me, I’ve to take this call..” ya fad’i yana mik’ewa tsaye, lokaci guda ya tura dogon k’ofar glass da ya raba d’akin da balcony ya shige yana amsa kiran Assad.. Cikin sauri Safeenah tabi bayansa cikin sand’a ta d’an lab’e ta kasa kunnuwa tana san sauraron wayar tasa..


Mu’azzam yaci gaba da fad’in “What do you mean Negative...?”


Daga d’aya b’angaren Assad yace “You heard me right, negative..”


Lumshe idanunsa yai kad’an kafin ya soma fad’i cikin b’acin rai “Assad kana so na koyar dakai aikinka ne.. you need to get ya act together, I have no time to babysit you..”


“Mai kake so nayi  Mu’azzam. Ka bani location without going through the details.. Naje wajen and guess what.. Wannan location d’in is an open waje, nothing suspicious.. Ba kowa babu komai a wajen.. Ban San mai zanyi a wajen ba..”


Girgiza kai Mu’azzam yai cikin rashin yarda yace “No.. There must be something in that particular location,.. Danger ne ya bani location d’in nasan haka kawai bazai bani ba dole akwai dalili.. Look around, babu wani daba da mutane ke zama wajen, babu wani shago kodai wani abu..?”


Assad yai shiru yana duban wajen da babu ko alamun mutane kafin ya fuzar da huci yace  “He played you.. Wasa dakai kawai yayi Mu’azzam.. There’s nothing suspicious here.. Ga Maleeka ma ta taho tare muke da ita.. But we couldn’t find anything..”


“Damn it..!” Ya furta yana jin zuciyarsa na masa wane irin k’una, idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa shine a raina masa hankali.. Fuzar da huci yai kad’an kafin yace “I’ll give him what he’s asking .. I’ll play his games.. Ka gane ku bar location d’in zamuyi magana..” 


Assad ya amsa masa da fad’in “Copy sir..” Yai maganan yana sarawa kaman Mu’azzam d’in na ganinsa..


Safeenah tana jin ya ida wayar tai saurin komawa mazauninta dikda cewa ba wai ta fahimci mai yake cewa bane cikin wayar amma kam ta tsinci wasu kalmomi kuma Ta fahimci bincike yake... 


Saida ya tsaya ya ida abinda zaiyi cikin wayar tasa kafin ya dawo cikin d’akin, Safeenah tana ganinsa ta mik’e tsaye, fuska fal damuwa take fad’in “Are you leaving now..?”


K’arasowa yai kusanta hannayensa saman waist d’insa, ya d’an fuzar da fuci kad’an yana mai duba wristwatch d’insa “I have to.. Aiki na jirana..”


Rau rau tai da idanunta tace “But you just got here.. Can’t you stay a little  longer..” Tai maganar cikeda shagwab’a


K’uri ya d’anyi mata kafin yace “Why..? Do you need something..?” Yanda Yai maganar yana bud’e idanunsa Sai ya koma mata Mu’azzam d’insa wanda a baya yake gwaleta a mafi akasarin lokuta.. Idan da Ta barsa ya gwansaleta sam bazata bari yanzu hakan ya kasance ba, shid’in mijinta ne kuma zatayi komai domin taja hankalinsa gareta.. Zatayi what ever it takes ta tabbata ta gina soyayyarta cikin zuciyarsa..


Matsowa ta kumayi kusansa.. A hankali ta isa ta d’aura kanta saman k’irjinsa, cikin raunanniyar murya tace “I need you here.. Please stay with me kaji..”


D’an kauda kansa gefe yai yana son tureta daga cikin jikinsa amma sai yaji ta sakalo hannayenta saman waist d’insa ta rungumesa sosai tana ci gaba da fad’in “Please stay..”

Tai maganar tana mai d’ago fuskarta idanunsu cikin na juna..


Bai iya tureta daga jikinsa ba sannan bai iya furta koda kalma ba saima samun kansa da yayi yana mai tallafe bayanta da hannunsa kad’an..


Inne Kakarsu mahaifiyar Daddy itace Ke k’ok’arin shigowa d’akin dashike Mu’azzam bai rufe k’ofar d’akin ba sanda zai shigo.. Safeenah tana hango Inne na dosowa d’akin Ta kuma mak’alewa cikin jikinsa dan tasan idan Inne ta gansu a haka zata hura wuta su tare a cen gidansu...


Aiko Inne tana hangosu haka sai bata shigo d’akin ba tayi juyawarta..

Saida suka kwashi mintoci a haka kafin Mu’azzam yai gyaran murya yace “Safeenah, I need to go now.. They are waiting for me..” Yai maganar yana mai cireta cikin jikinsa..


D’ago fuska tai tana dubansa kafin tace “How long will you take..?”


Ya d’an tab’e baki kad’an “I can’t say for sure.. It depends.. Kinsan yanda yanayin aikin namu yake..”


Ta d’an rausayar da idanu kad’an lokaci guda tana mai kuma rau rau da idanun cikeda shagwab’a “My Inspector, nasan yanda yanayin aikin nan naku yake, very dangerous..Sannan kana bada mahimmanci sosai ma aikinka... Please promise me you’ll take care of yourself.. Always..”


Yanda tai maganar sosai ya sanyashi jin sanyi can k’asar zuciyarsa, ya saki murmushi kad’an yana mai tallafo fuskarta da tafukan hannayensa, a hankali yake furta a hankali ya jinjina mata kai kafin yace “Zan iya tafiya..”


Wani irin dad’i da mamaki ne ya cika zuciyar Safeenah Wai Mu’azzam ne yake mata magana softly haka ba tareda ya gwansaleta ba harma tambayarta yake zai iya tafiya.. Dad’i ya mamaye zuciyar Safeenah tabbas lokaci k’ank’ani zata d’iba ta dasa soyayyarta mai tsafta cikin zuciyar Mu’azzam..

Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Zan duba Mamy first daga nan zan shige..”


Ta jinjina masa kai a hankali tana sakin murmushi.. Hannunsa guda dafe da b’angaren fuskarta yaje furta “You take care..”


Ta jinjina masa kai a hankali su duka biyun suna masu sakar ma juna murmushi kafin Mu’azzam ya fice..


Yana ficewa Safeenah ta fad’a kan gado tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali.. Ta janyo pillow Ta kwanta ciki tana shafe fuskarta yanda Mu’azzam ya d’aura hannunsa.. Ta lumshe idanunta a hankali tana jin bazata tab’a bari wani abu ya datse mata wannan farin ciki da take ciki ba.. Zata kare aurensu no matter the cost.. 

Tana tsaka da tinanin wayarta dake gefen bedside Ta soma ruri.. Tai saurin d’agowa tana duban mai kira, lamba ce Babu suna..

Batasan dalili ba amma ta tsinci kanta da fad’uwan gaba... A hankali ta d’aga wayar tana mai k’arawa a kunnenta..


Lokaci guda ta mik’e tsaye sanda take receiving wayar “Barrister Ameer..Ina ka samu sabuwar layina..?”


Daga d’aya b’angaren mutumin data kirada Barr Ameer murmusawa yai kad’an kafin yace “Ba damuwa bace sanin yanda na samu sabuwar layinki... Kawai na kira ne na miki murnan aure tinda ba’a gayyace mu biki ba..”


Murmushin da yafi kama yak’e ta d’anyi kafin tai masa godiya Ta muka rok’esa da kar ya sake kiran layinta bata san duk wani abinda zai haifar da zargi tsakaninta da mijinta... Barr Ameer yace babu komai kawai dai dama ya kira ne ya mata murna tinda Allah bai k’addara shid’in zai aureta ba dukda tsananin k’aunarta da yake..


Barr Ameer Dikko yaso Safeenah sosai tun tana makaranta a Salford, da aure yaso Safeenah bada wani shashanci ba, tun Safeenah bata kulasa har saida yayi amfani da dabaru nasu na lauyoyi wajen iya tsara zance da kuma tsananin nacinsa da soyayyar da yake mata har dai ta soma kulasa, bata b’oye masa d’anuwanta Mu’azzam take so ba dukda kuwa cewa a lokacin bata gaban Mu’azzam d’in.. Barr bai karaya ba yace zai gwara luck d’insa.. A haka dai har Safeenah ta d’an basa dama cikin rayuwarta sabo ya shiga tsakaninsu sosai dukda cewa ita ba irin son da yake mata take masa ba, zuciyarta na Mu’azzam ne batajin zata iya had’a soyayyarsa da wani cikin zuciyarta, Barr Ameer yasan da haka amma bai damu ba a cewarsa nasa sa’an yake gwadawa.. Koda aka saka aurenta da Mu’azzam kuwa tuni tai cutting ties da Barr, ta yanke duk wata alak’arta dashi, dan sabida shi ma da nacinsa Ta canza layinta..


Bazata tab’a mancewa da  furucin da Barr yai mata ba wata rana suna firan Mu’azzam shida Ita, tana sanar dashi irin soyayyar da take wa Mu’azzam d’in, Barr yace ‘Na saka a raina zaki zauna a gidan Mu’azzam ne na d’an wani lokaci tamkar dai kina a GIDAN ARO ko bajima ko na dad’e bazan tab’a cire rai ba, nasan watarana zaki dawo gareni..’ Batama d’auki maganar tasa da mahimmanci ba dan tasan irin son da takewa Mu’azzam zata iya shanye duk wani miskilancinsa ta tabbata aurensu ya d’ore har k’arshen rayuwarsu..

A hankali ta sauk’e ajiyan zuciya tana mai kuma kwanciya saman gado..Mu’azzam kaw a parlor  ya hangi Inne Kakarsu da Daddy harma da Mommy, yanda yaga Mommy da Daddy sun gurfana ya tabbatar masa assembly Inne take, shi sam bai zaton ma bata koma Adamawa ba, hango Musaddiq da yayi duk’e gaban Innen ya sanyasa k’ok’arin janye jiki da niyyan ficewa ba tareda wani yayi noticing d’insa ba dan yasan fitinar Kakarsu..


Yana cikin sand’uwa zai fice ya sinkayo muryarta da girma ya d’an kama tana fad’in “Kai Kai Dansanda ina zakaje..? Zo nan kaima akwai namu da kai.. Bari na gama da wannan shashashan d’anuwan Naka..” Ta k’arashe tana dungure kan Musaddiq da yai zaman rak’umi gabanta, ya kuwa cika yayi fam kaman zai fashe...


Dan dole Mu’azzam ya dawo ya tsaya daga bayan parlorn can wajen staircase..


Inne Dattijuwa da sam bazaka bata shekarun da take ba sabida kyaun k’ira da Allah yayi mata, ta dubi Musaddiq dake duk’e gabanta k’iris ya rage bai fashe ba Ta kuma dungurinsa tana fad’in “Sokon banza, ai bansan shashashancinka kawai kake a nan ba.. Mu dik zuri’armu babu mashayi baza’a fara samu cikin jikokina ba.. Kana jina Gida zan tafi dakai cen Fufore kaje kayi noma da kiwo naga alama gata ne yai maka yawa a nan shiyasa ka sangarce..”


Musaddiq ya d’ago yana mata wani irin duba, Ta kuma dungure masa kai tana fad’in “Daina kallo na da wannan jajayen idanun naka.. Sabida azaban shan kayan maye jibi dik yanda kayi duhu ka lalace..”


Mommy ta k’walolo idanu waje jin Inne tace zata tafi da Musaddiq Fufore yaje yayi noma da kiwo, ta dubi Daddy tana jiran taji mai zaice amma shiru baice komai ba...


Musaddiq ma ganin iyayensa ba suce komai ba ya sanyasa soma girgiza kai yana fad’in “No.. No way.. Gaskiya bazan koma Gidan Gona ba..Ai dai kinsan ina makaranta Inne..”


Ta kuma Kai masa bugu a kafad’arsa yana karewa, lokaci guda take furta “Rufe mun baki shashasha.. Yo makarantarka har wani makaranta ne, inji kaje can k’asar wajen ka gama yawon shashashancin Naka babu abinda ka tsinana, na tabbata nan d’inma ba abun arziki kake ba.. Idan ba an rabaka da shashashan abokan naka dake nan ba bazakayi hankali ba.. Ni tuntuni nasan cewa shashashancinka yakai har ruwan kwalba kake sha da ban Barka ka girma a bariki ba..” Ta dubi Daddy da kansa Ke kife k’asa tace “Kana jina Marwan, yaron nan zamu tafi tare.. Kayi magana da D’anuwaka Salmanu tinda shike kula da Gidan Gonar, ya samar wa Gidado aiki a nan Gidan Gonar.. Ya dinga kula da shanun dake gidan gonar..”


Musaddiq baki sake yake dubanta shaye da tsananin mamaki.. Katseta yayi da fad’in “Amma Inne kinsan ni ba karatun kula da Dabbobi nayi ba koh..I’m not a Vet Dr..”


Carbinta da ko yaushe yake nad’e hannunta wannan karon ta warb’a masa tana fad’in “Rufe mun baki idan bakayi karatun kula da dabbobi ba ai ka gada kiwo...  Ubanka ma ya gada.. Gidan Gonan da Kakanka ya mutu ya bari arzikinsa kake ci..”


Ta d’ago tana kuma duban Daddy “Kana jina ka kira Salmanu ka sanar dashi tun kafin mu koma Adamawa..”


Jinjina mata Kai Daddy yai yace “Za’ayi yanda kikace Insha Allah Inne..”


Mik’ewa ta soma k’ok’arin yi ta dubi Mu’azzam tace “Kai kuma shige muje..”


Cikin rashin yarda da batun Musaddiq Ke fad’in “Haba Daddy.. You can’t be serious.. Daddy this is unfair.. Dan Allah kar ka bari hakan ta kasance..” Ya d’ago ya dubi Mu’azzam dake k’ok’arin bin bayanta yace “Officer dan Allah ka mata magana, you’re her favorite zata saurareka..” Ya k’arashe yana bin bayan Mu’azzam d’in cikin gudu gudu...


Saitin kunnensa Mu’azzam Ke fad’i a hankali “Hakan yafi idan dai halinda zakaci gaba dayi kenan a nan..”


Musaddiq ya girgiza masa kai yace “Wllhi na daina..”


“Proof it then..” Mu’azzam ya fad’I yana mai bin bayan Inne..


Cikin sauri Musaddiq ya take masu baya..


Suna ficewa Mommy Ta dubi Daddy tace “Yanzu bazakace komai ba.. Haka zaka zuba ido Ta tafi dashi..”


“Mai kike so nace Hajara.? Nace mata ba haka ba.. Ko kin mance cewa matar nan mahaifiyata ce.. Sannan idan hakan shi zaisa d’anki ya dawo cikin hayyacinsa I’d welcome the idea d’ari bisa d’ari.. If he stays here babu wani abinda zai tab’uka ma rayuwarsa..”


Shiru Mommy tai tana mai kwantar da kai, hawaye ya ciko idanunta, k’ok’arin saita kanta tai sanda Daddy yaci gaba da fad’in “He’ll be better off there, tinda a nan dai kina gani yanda muke tare tare dashi, idan aka canza masa environment d’in na d’an wani lokaci k’ila Allah yasa hakan ya zamto sanadin shiriyarsa... Muyi masa addu’a kawai da fatan hakan ya zamto alkhairi..”


Mommy dai bata ce komai sai mik’ewa da tai ta haura sama tana tinanin hukuncin cikin ranta.. Ita tanadinta shine Nuratu ta fice mata daga gida tayi nesa da ita da ahalinta ba Wai d’aya daga cikin yaranta yai nesa da Ita ba..


Daddy ya bita da kallo yana mai kwantar da kansa cikin kujera had’ida lumshe idanunsa kad’an..Inne na gaba Mu’azzam da Musaddiq na biye da ita, Musaddiq naci gaba da magiyan cewa ta janye k’udirin ta..


“Kai Gidado (Kaman yanda take kiran Musaddiq d’in) bari kaji na fad’a maka.. Ko Marwan Ubanka bai isa ya hanaka komawa Gidan Gona ba.. Na riga na gama magana ehe, bazan zauna inaji Ina gani ka zame mun zakka ba.. Banyi shirin sallameka ba.”


Musaddiq ya dubi Mu’azzam da yai kaman bashi a wajen a hankali kaman mai rad’a yake furta “Aren’t you gonna say anything.. Talk to her please.. She can’t do this to me... I mean she’s turning my life into a nightmare.”


Bai Kai aya ba yaji sauk’ar ‘ya’yan carbi a k’eyarsa, yai saurin sosawa yana d’an sakin k’ara.. Kunnensa ta kamo dikda ratan tsawo dake tsakaninsu.. Nanma k’ara Musaddiq ya saki yana k’ok’arin k’watan kunnensa..


Inne Ta dage k’arfinta ta matse kunnen tana fad’in “Ni na gayyaceka d’akina..? Maza a k’ara gaba.. Fita ka bani waje jarababbe..” Ta k’arashe tana turasa waje..


Dik tsimewan da Mu’azzam yake saida yaji dariyar Inne da Musaddiq ya taso masa.. Ya sunkuyar da kansa gajeriyar murmushi saman fuskarsa..

Inne na hankalce dashi sannan sosai taji dad’in ya d’an saki ransa dan zata iya cewa tinda tazo bataga murmushinsa ba.. Abubuwa da dama Sun faru dashi d’in.. Ga mutuwar k’anwarsa bayan jinyar da mahaifiyarsa Ke ciki...


Musaddiq na ficewa Inne ta K’araso ta zauna bakin gado, tai nuniwa Mu’azzam da kujerar dake fuskantar gadon “Modibbo zauna kaji muyi magana.”


Ba musu Mu’azzam ya k’arasa ya zauna yana “Inne na zata kin tsufa a Adamawa..”


Ta tab’e baki kad’an tace “Ina zanje bayan ban kai maka Matarka d’akinka ba..”


Ba zata yaji maganan nata ya d’ago yana dubanta, dan shi harga Allah ya mance da wani maganan tariyar Safeenah..


“Kana jina.. Yau d’in zuwa dare.. Kokuma a barshi gobe yarinyar nan ta tare a d’akinta.. Zaman baida wani amfani..”


D’an tura yatsunsa yai kad’an cikin sumarsa kafin yace “Inne Wai dama da dai an barshi sai zuwa gaba kad’an..”


Shiru tai tana dubansa cikeda tausyawa, ta jinjina kanta a hankali kafin tace “Idan kace haka zan iya fahimtarka Modibbo.. Nasan har yanzu alhinin rashin ‘yaruwarka na tareda kai.. Amma idan kana tareda Matarka sai ta d’ebe maka wani kewan ka fahimta..”


D’an shafe fuskarsa yai kad’an kafin yace “Inne ai akwai abubuwan da nake so su daidaita kafin nan.. Kinga yanzu babu Ikram dama itace take taimaka wa Aunty Hajara  da jinyar Mamy na.. Aunty Hajara bazata iya kulada Mamy ita kad’ai ba dukda dai dama akwai ma’aikatan jinya da ake hayansu masu taimakawa.. Inaso idan al’amarin suka daidaita Sai mu tare mu koma cen gidan..”


Katsesa tai da fad’in “Ni nan zanyi jinyar Nuratu.. Dama wannan karon nace zan d’auketa mu koma gida a jarabba jinyar gargajiya tinda na asibitin Allah bai nufa za’a dace ba.. Nayi magana da Baban naku dikda shima naga yafi son zamanta a nan amma haka dole zaku hak’ura a jarabba na gargajiyan.. Sannan zatafi samun kulawa a wajena sama da nan d’in..Watak’ila maganinta na gida bamu sani ba..”


Shiru yai kaman mai nazari, harga Allah baison mahaifiyarsa tayi nesa dashi musamman duba da yanayin jinyar da take ciki.. Amma baida wani zab’i idan hakan shine Alkhairi.. Zaifi kowa son mahaifiyarsa ta sami lafiya.. Kaman kuma yanda Inne tace zatafi samun kulawa wajen Kakar tasa dukda kuwa cewa bai tab’a ganin gazawar Mommy ba sannan har kullum fatan alkhairi ne tsakaninsa da ita.. Ko dan mutuncin iyayen Safeenah Daddy da Mommy da yanda suka rik’esu amana shida ‘yaruwarsa da kuma mahaifiyarsu dake cikin tsananin jinya baiji zai iya wulak’anta Safeenah, koda ace baya sonta zaiyi hak’urin zama da Ita.. Mommy da Daddy sun cancanci ya rik’e masu d’iya da amana..Alk’awari ne da ya d’aukar ma kansa..


Muryar Inne ya sinkayo tana ci gaba da fad’in “Jinya yak’i ci yak’i cinyewa.. Idan ban b’ata lissafi ba yau a k’alla kusan shekaru shabiyar kenan Nuratu na fama da jinyar nan, ni ban tab’a gani ko jin had’arin mota irin nasu ba..”


Mu’azzam ya d’ago yana dubanta  “.. Ina makarantar Kwana a lokacin, aka sanar dani Mamy ta auri Uncle Marwan saidai a hanyarsu Ta tafiya Abuja daga Adamawa sunyi accident.. She survived the accident amma tana cikin critical condition.. Condition d’in da bata fice daga ciki ba har rana mai kaman Ta yau.. Ance motar da Mamy na take ciki kowa ya mutu ita kad’aice tayi rai a ciki..”


Ya k’arashe cikin yanayi na ban tausayi.


Sauk’e ajiyan zuciya Inne tai tana mai d’an goge hawayen da ya mak’ale mata cikeda tausayin Mu’azzam d’in..“Modibbo ina k’aunar Mahaifiyarka tamkar d’iyar dana haifa a cikina wannan dalili yasa na umarce d’anuwan mahaifinka da ya aureta bayan da muka rasa mahaifinka... Ina tsananin k’aunarta kuma bana so ta bar cikin ahalinmu.. Nuratu yarinyar kirki ce mai tsananin biyayya.. Da ita da Baffanka Marwan sunyi min biyayya kuma Sun cika min burina sun amince da auren juna.. Saidai bansan wannan aure haka zai kasance ba.. Bansan a hanyar zuwa GIDAN Baffanka Nuratu zata had’u da wannan mummunan tsautsayi ba.. Ance had’arin motar bama irin wacce aka saba gani bane.. A samar bishiya aka tsinci motar da mahaifiyarka ciki... Mu’azzam inaji kaman alhakin ciwon mahaifiyarka a kaina yake.. Watak’ila da banyi masu umarni da su auri juna ba itada Marwan da yanzu lafiyarta lau.. Bazan daina jin zafin abun nan ba har na koma ga mahaliccina..” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka.


Cikin sauri Mu’azzam ya taso ya duk’a gabanta, ya kamo hannayenta ya dunk’ule cikin nasa “Inne none of this is your fault.. Ki daina d’aura ma kanki alhakin ciwon Mamy, wannan wani abu ne da Allah ya K’addara.. Mutum baya shige k’addarar Sa a rayuwa.. Wani baya iya yi ma wani abin cutarwa ko na amfanarwa face Allah ya k’addari faruwar hakan,.. Baki nufi Mamy da komai ba face Alkhairi. Had’ari kuma ko ta auri Uncle ko bata auresa ba tuni Allah ya rubuta hakan zai faru.. Ki daina d’aura laifi ma kanki kinji Inne..” Ya k’arashe yana mai goge hawayen fuskar Kakar tasa da ‘yan yatsunsa..Ta Shafa sumarsa murmushi saman fuskart “Allah shi maka albarka Modibbo na.. Ubangiji ya maka jagora a duk abinda kasa gabanka.. Allah tsare mun kai ya kareka daga sharrin mai sharri..”


Sumbatar hannayenta dake rik’e cikin nasa yai yana furta “Ameen Inne na.. Allah ya bar mun ke..” Ya k’arashe yana mai d’aura kansa saman cinyarta.. 

Dik zafin da zuciyarsa Ke ciki idan yana tareda Kakar tasa Sai ya dinga jin wani sanyi can k’asar zuciyarsa, har wani shagwab’a yake mata, ga wanda yasan zafin sa a waje idan ya gansa da Innensa sosai zaiji mamaki..


No comments

Powered by Blogger.