Gidan Aro 1

 

 


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM _Abuja, Nigeria_


National Police Headquarters.

_Criminal Investigation Department (CID)_
Cikin k’warewa da sanin makamar aikinta budurwar mai kimanin shekaru 29 taci gaba da kwararo bayanai tana mai nuni da Farin allo wanda hasken k’wan wutan projector ya haskesa, Ko ba’a fad’a maka ba zaka fahimci cewa cikin d’akin gudanar da binciken manya manyan laifuka suke musamman irin laifin da ya shafi kisan kai, fyad’e, Garkuwa da mutane da sauransu..


Hoton wani matashi ne na’urar Ta hasko, kwance yake a k’asa tamkar bai numfashi, ga dukkan alamu babu rai tattareda shi.. Ko ina na wajen a kewaye ne da Doguwar igiya mai launin ruwan d’orawa, jikin igiyan an rubuta _Restricted Area_ da manyan bak’ak’e...


Budurwar ta k’urama hoton idanu Wanda ya bayyana Babba gabansu kasancewar da na’uarar projector ake hasko hoton.. Ta matso sosai tana mai rage girman idanunta tana kallon hoton, a hankali take furta “Da hannun hagu ya rik’e bindigar, direction d’in da bindigar Ta kalla bai kamata harsashi ya samu k’irjinsa direct ba, ya kamata harsashin ya huda ribs d’insa kafin ya ratsa cikin k’irjinsa indai har da hannun da aka sami bindigar a ciki yayi harbin..”


Wani matashi mai kimanin shekaru 32 ya taso yana k’arasowa kusanta wanda shima d’aya ne daga cikin ‘yansanda masu gudanar da bincike da suke zaune a madaidaicin Zauren gudanar da binciken.. Hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa, idanunsa naga hoton yake furta “Well done Agent Maleeka.. But wani hanzari ba gudu ba.. Baki tunanin idan mutumin nan ya kasance bahago zai iya karkata hannunsa har harsashin ta iso daidai tsakiyar k’irjinsa ta hudasa..?”


Karkatowa Maleeka tai tana duban wanda Yai maganar kafin ta d’an tab’e baki tace “Bani da tabbaci Inspector Assad.. Amma hakan nake tunani..”


Bata Kai aya ba wata murya ta katsesu da fad’in “Oh shut up.!”


Gaba d’aya suka juyo suna dubansa, kusan tun shigowarsu d’akin kansa a k’asa yana aikin murza zoben dake mak’ale yatsarsa guda wanda yin hakan kusan d’abi’arsa ce musamman idan yana nazarin bincike..


Ya d’ago kai yana dubansu, kallon da yake sanyata daburcewa ta rasa mai take ciki, tunaninta duk su sakwarkwace shi ya jefata dashi kafin yace “Tunani kikeyi.? Ko kuwa kin tabbatar..?”


Kasa furta komai tai sai yin k’asa da idanunta da tai 


Hannayensa biyu sakale cikin aljihun wandon jeans d’insa, yana tsaye gabanta yana iya hango tsakiyan kanta sabida ratan tsawo dake tsakaninsu.. Cikin muryarsa da yake tsakanin kashe mata jiki lak’was wanda yake sanyata losing kanta gaba d’aya ya soma furta “We are investigating a murder  here, in case you forgot.. There’s nothing like you thought, everything here must be known.. You must Know.. I want results and  not assumptions.. Kin fahimta..” Ya k’arashe yana kwanto da fuskarsa kusan nata, idanunsa da suke matuk’ar furgitata dab kusan nata...


A hankali take jinjina kai cikin yanayi na d’an daburcewa “I..I’m sorry Inspector, Sir..”


“I don’t need your apology.. Just do your work correctly.. Or else, you’ll be kicked out of this team..!”


Yanda yake maganar cikin tsananin zafin rai zaka fahimci ransa a matuk’ar b’ace yake..


Mutumin dake tsaye gefen Maleeka ya d’an girgiza kai kad’an kafin yace “But..”


Katsesa yai da fad’in “What do you mean but.?.. You know me quite well Assad, you know I hate incompetence.. And I easily get irritated by people like her around.”


Assad ya d’an shafi kansa dan yasan Wanene abokin nasa da kuma yanayin da yake ciki “MU’AZZAM.. will you please calm down.. I was only asking you to go easy on her..”


“Oh really..! Da gaske Assad..  Am I really being too strict?.. Let me remind you idan ka mance.. Mutuwar k’anwata muke bincike a nan Assad.. K’anwata was found dead tareda wannan d’an ta’addan.. And you’re asking me to go easy on her... My sister Assad.. My only Sister.. An kasheta in a cold blooded murder.. Someone murdered her Assad.. Sannan na kasa aiwatar da komai domin wad’anda suka kasheta su biya abinda suka aikata.. Tell me, a haka ne kake ce min na natsu.. A haka ne kake ce min I should calm down and go easy on her Assad.!” Ya k’arashe cikin tsananin d’aga murya gashin jikinsa na kuma mimmik’ewa 


D’akin yai shiru sai hucin fitar numfashin Mu’azzam kakeji.. Cikin rarrabewar kalma yake ci gaba da furta “If she’s not competent enough to work with this team, the door is widely open..”


Cikin zafin nama Assad ya katse sa da fad’in “But the man who killed your sister is dead too.. He committed suicide after he killed your sister Mu’azzam..!”


Ya k’arasa jikin k’aton allon ya shiga nunawa yana fad’in “Look.. Look here, look at the suspect, ya kashe kanshi bayan ya kasheta.. Bindiga d’aya yayi amfani dashi.. Ga finger prints d’insa a jikin bindigar an samu.. Duk iyaka binciken da za’ayi anyi Mu’azzam but still babu wani abinda yake canzawa.. Until now we couldn’t figure anything out sabida bamuda wani dalili Ko hujja...Amsa  d’aya muke samu a k’arshe shine mutumin nan kashe kansa yayi bayan ya kashe Ikram.. Sannan inaga ya kamata mu saki mutumin nan dake tsare cikin interrogation, babu amfanin detaining d’insa a nan..”


Wani irin duba yake ma Assad da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja, lokaci guda yake jinjina kai kafin ya mik’a hannu saman Table dake gefensa ya d’auko k’aramar bindiga piston.. Cikin tsananin huci yake furta “I’ll proof to y’all that that man didn’t kill himself.. Someone killed him..” Yai maganar yana pointing Assad da bindigar zuciyarsa na kuma tafarfasa..


Maleeka kame baki tai idanu a warwaje take duban Assad da Mu’azzam..


“Sir.. What are you doing.. Please don’t..” Maleeka tai maganar cikeda tsoro..


Ko kallo bata ishi Mu’azzam ba balle ya amsata.. Pointing bindigar yai daidai saitin k’irjin Assad, yana kallonsa yana huci kaman mai shirin d’ana harsashi..


Lokaci guda ya karkato da bindigar saitin ya juyo da Ita saitin nasa k’irjin, bindigar tana rik’e ne cikin left hand d’insa kasancewarsa left handed, shid’in bahago ne.. Bai daina sakin huci ba yana rik’e da bindigar idanunsa tar akan fuskar Assad.


Maleeka Ta kuma zaro idanu waje ganin Mu’azzam yayi pointing kansa da bindiga, cikin tsananin daburcewa take girgiza kai tana k’ok’arin rintse idanunta, dan gani take kaman d’ana ma kansa harsashi yake da niyya 


D’aya mutumin dake zaune saman kujeransa wanda shine cikon na hud’unsu a cikin d’akin wanda ya d’an fisu gaba d’aya a haife dan shi zai kusan shekaru 39 sai sannan ya taso ya k’araso yanda suke a tsartsaye..


Ya isa jikin board d’in yana nuna hannun mutumin yanda ya rik’e bindigar ya d’ana ma kansa harshashi cikin hoton, kafin ya kaikaito yana duban Mu’azzam dake rik’e da bindiga yayi pointing kansa daidai yanda wannan mutumin yayi.. A hankali ya saki murmushi yana ma jinjina kafin tunani da jajircewa a aiki irin na Mu’azzam.. Rik’e bindigar da yayi so yake ya masu proving cewa mutumin nan baiyi committing suicide ba kaman yanda ya bayyana masu cikin hoton.. Wani ne ya kashesa sannan ya saka bindigar cikin hannunsa dan idan ba haka ba babu yanda za’ayi ya harbi kansa a wannan position d’in...


Tafe hannunsa mutumin ya shigayi yana furta “Impressive.. Bravo Officer MA Gamji..” Yai maganar yana mai tafe hannayensa lokaci guda yake duban Mu’azzam..


Assad ya kai dubansa ga hoton yana yanda mutumin ya rik’e bindigar sannan yakai dubansa ga Mu’azzam, ko shakka babu wannan rik’on bindigar saka masa akayi sannan ya tabbata bashi ya harbi kansa ba..


Jinina Kai Assad yai murmushi saman fuskarsa yake duban aminin nasa.. Lokaci guda ya k’araso gabansa kafin ya d’aga hannu yana sara masa alamun jinjina.


Officer Maleeka ma wani irin murmushi ne taji ya kufce mata cikeda jin dad’i dan har Ta fara tunanin idan basu samu komai out of this case ba watsi za’ayi da binciken and bazata samu lokacin da take so Ta samu dan Ta kasance da Mu’azzam ba.. Sabida son kasancewa taredashi ne yasa tayi yanda tayi akayi assigning nata to case d’in...


A hankali mutumin ya zare bindigar daga hannun Mu’azzam yana mai furta “Weldon Mu’azzam har na fara tunanin idan bamu samu komai ba anything can happen.. Za’a iya rufe case d’in...”


Sai sannan Mu’azzam ya dubesa ya sara masa kafin yace “Believe me Yusuf babu  wanda ya isa ya rufe case d’in nan until I get to the bottom of everything.. Is a promise, Alk’awari ne da na d’aukarwa mahaifiyata dake cikin tsananin jinya wacce batasan d’iyarta Ta mutu ba.. Wacce duk randa ta farka daga wannan jinya nata zata farka ne ta tadda babu d’iyarta.. Babu Ikram..” Ya k’arashe wane irin gumi na karyo masa tin daga cikin sumarsa har zuwa karan hancinsa da ya dace da kyakkyawan fuskarsa...


Lokaci guda yaci gaba da furta “Yanzu da duk muka fahimci abu guda nida ku.. I’m goin to make that imbecile talk..!” Daga haka cikin sauri ya juya ya fice daga cikin d’akin..


Assad yabi bayansa yana kiran sunansa inaa Ko zarafin tsayawa bai samu ba balle ya amsa sa..


Yana isowa ya bud’e k’ofan interrogation d’in ya shige ciki saidai yana shigewa ya maida k’ofar ya danna mata lock yanda Assad Bazai iya shigowa ba...


Girgiza kai kurum Assad yayi dan yasan waye abokin nasa idan ransa ya b’aci..


Wani mutumi ne zaune saman kujera nan cikin interrogation d’in, Mu’azzam ya d’ibi lokaci yana dubansa cikin tsananin tsimewa..


Murmushi ne saman fuskar mutumin, yana murmushin yana shafa hab’arsa, cikin muryarsa da yafi kama da ta ‘yantadda yake furta “Officer MA Gamji, you’re not going to get anything from me.. zaifi kyau idan ka sakeni nayi tafiyata dan idan ba haka ba zan iya shigar da k’ara an ajiyeni a police station babu dalili..”


Cikin takunsa irinta cikakkun mazaje da suka sha training suka k’oshi ya soma takowa, hannayensa dafe da belt d’in wandonsa.. Saida ya k’araso har gaban mutumin kafin ya zauna a kujera mai fuskantar mutumin.. Zoben dake hannunsa ya cire ya wainata saman table d’in da ya raba tsakaninsu da mutumin, saida yayi hakan kusan sau uku k’afarsa d’aya bisa d’aya kaman bazai ce komai ba, har lokacin idanunsa naga zobensa da yake faman wainata saman table..


Mutumin ya kuma murmusawa kafin yace “Mr Officer, if you think you’re goin to get something from me you’re quite mistaken..” Cak ya katse maganar nasa sakamakon ganin hoton da ya aje masa saman table d’in..


“Im gonna ask you for the last time.. Tell me everything you know about this guy..!” Mu’azzam ya k’arashe yana mai matso da fsukarsa dab kusan na mutumin yatsarsa manuniya na saman hoton yana nuna hoton da Ita....


K’uri mutumin yai yana dubansa kafin ya saki murmushi kad’an yace “You won’t get anything from me, Mr Officer..?”


Wani irin zabura Mu’azzam yayi saida yai fatali da table d’in da ya raba tsakaninsu da mutumin.. Ya finciko wuyan mutumin ya matse ya had’uda da garu yana mai ci gaba da sakin huci “I am not playing games with you.. Now tell me.. Ka fad’a mun mai ka Sani akanshi..? Wanene shi..?”


Mutumin da yaji matsa idanunsa sun firfito waje yana neman hanyar da zai shak’i iskan numfashi ya fitar da k’yar yake jinjina kai ma Mu’azzam alamun ya sakar masa wuya zai fad’i abinda ya Sani...


Jifa dashi Mu’azzam yai yana yarfe hannunsa kafin ya isa gabansa ya d’an duk’a kad’an “Tell me..” Ya fad’i idanunsa akan mutumin..


Da k’yar mutumin ya d’an iya mik’ewa ya zauna dirshan a k’asa kafin ya soma fad’in “Baida kowa.. D’an ta’adda ne.. Baida kowa a garin nan, sannan bansan daga Ina yake ba.. Amma nasan a nan yake running businesses d’insa..”


Cikin zak’ewa Mu’azzam yace “Ya akai kasan d’anta’adda ne...?”


“Sabida ni kad’ai yake zama yayi min firan da bai wuce mintoci....”


Ya jinjina kai kafin yace “What was his business..?”


Girgiza kai mutumin yai kafin yace “Komai ma business d’insa ne as far as wannan kasuwancin ta’addanci ne...Iyakacin abinda zan iya fad’a maka kenan..”


Mu’azzam ya kuma gyara tsugunonsa idanunsa nakan mutumin kaman mai tsoron kar yayi losing sight d’insa kafin yace “Baida kowa.? Baida tak’amammen aboki ko wani abu mai kama da haka.. Tell me..”


“As I  told you , mutumin nan ganinsa kawai muke yazo ya sai sigari yasha ya k’ara gaba.. Amma wata rana naji yana waya kaman da wacce zai aura ne..”


“Wacce zai aura..?” Mu’azzam ya tambaya cikin son jin yaji komai.


Mutumin ya jinjina kai yace “K’warai wacce zai aura.. Dik a wanann daban ni kad’ai yake zama yayi hira dani da bai wuce na tsawon minti uku zuwa biyar.. “


Tura masa kujera Mu’azzam yai yace “Tashi ka zauna sannan ka sanar dani firan taku..”


Saida mutumin ya d’an fuzar da huci kafin yace “Amma Rankaidad’e bazaka bari a ajiyeni a police station ba dan ka gani da idanunka shago na bana sayar da komai, bana sayar da tabar wiwi sannan bana sayar da k’waya.. Karan sigari kawai nake saidawa Rankaidad’e.. Dan Allah ka taimakeni kar a ajiye ni a nan.. Bana komai illegal I promise..”


“Kar ka damu idan muka tabbata baka running wani illegal business na maka alk’awari bazamu ajiye ka a nan ba.. Yanzu ka fad’a mun hiranku na k’arshe da wannan mutumin..”


Saida ya gyara zamansa kafin ya soma fad’in “A satin da ya gabata yazo k’ofan shago na, as usual ya sayi sigari na kyauta masa lighter.. Kaman ko yaushe bai shiga cikin mutanen dake zama a daban k’ofan shago na ba.. Ya koma gefe ya soma zuk’ar sigarinsa.. Ya gama shan sigarinsa yazo wajena karb’an canji dan dama sanda ya sayi sigarin ban basa canji ba dan babu canji, nace masa ya gama sha kafin a samu canji.. Toh tsayuwarsa yana jirana na had’o masa kan canji na basa yai daidai da fara ringing d’in wayarsa..Ya ciro wayar yana amsawa. Cikin maganganun nasa a waya na fahimci da wacce zai aura yake waya.”


Mu’azzam yace “Bakaji wani abu ba gameda budurwar tasa.. Maybe a ina take kokuma wani abu mai kama da haka..?”


“Inspector I told you I was only his smoking buddy.. How would I know all the details..!” 


Murmushi Mu’azzam yai kafin yace “Do you really want us to play this game..? I can assure you I know exactly when to throw my card..” Ya k’arashe yana mai waina zobensa saman table. Lokaci guda yake ci gaba da furta “Nasan baka Sani ba, but I do know a lot of things about you.. I know about your criminal records.. Nasan abubuwan da kake aikatawa wanda zasu kaika jail ka shafe shekaru da Dama.. But If you cooperate with me, zanyi iya k’ok’arina a kotu to make sure anyi reducing sentences d’inka.. So ina shawartanka don’t let me lay my cards first.” Ya k’arashe yana tsaida zoben dake faman wainuwa saman table da yatsarsa guda...


Murmushi mutumin yayi yana mai jinjina kai dan yasan business na drugs da yakeyi zai iya kaisa gidan yari.. Yai k’uri wa Mu’azzam yana dubansa wanda babu alamun tsoro Ko d’ar a tattare dashi.. Kaman bazaice komai ba Sai kuma yace “I need protection..”


Mu’azzam yai masa k’uri yana dubansa kafin yace “So you do know something..?” Yai maganan yana jinjina kansa yana kuma tabbatarwa plan d’insa really works.. Gyara zamansa yai had’ida d’aura k’afa d’aya bisa d’aya still yana fuskantar mutumin yace  “I knew it.. I was right all along..”


K’uri mutumin yai masa gajeriyar murmushi saman fuskarsa “But you  need to guarantee my safety first, Inspector..”


Mu’azzam ya jinjina masa kai yana mai furta “We will give you protection here.. I promise.. Just tell me what you know..”


Ya jinjina kansa a hankali idanunsa akan Mu’azzam sann ya tura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya ciro k’aramar takarda a nannad’e.. Lokaci guda ya mik’a ma Mu’azzam yace “Wannan zai iya amsa maka duka tambayoyin ka.. Duk abinda kake so ka Sani gameda mutumin nan..”


Mu’azzam yasa hannu ya amshi takardan ya warware.. Address ne na wani gida a jiki..


Ya d’ago yana duban mutumin da alaman tambaya..


Jinjina masa kai mutumin yayi yace “Kaje wannan Address d’in zaka sami amsoshin da kake nema...”


Mik’awa tsaye Mu’azzam yayi yana juya address d’in wanda yake a garin SULEJA...


Bai kuma ce ma mutumin komai ba yasa kai ya fice kaman zai kifa da k’asa.. Mutumin na kiransa yana fad’in yaushe za’a sake shi ya tafi gida.. Inaa ko zarafin juyowa Muazzam baiba balle ya amsa Sa.. Yana fitowa ya tadda Assad yana jiransa.. Cikin sauri Assad ya take masa baya yana fad’in Ina zasuje..


Bai tsaya amsa Assad ba har saida suka k’araso yanda motocinsu Ke ajiye.. Ya dubi Assad yace “You drive..”


Assad yace “Destination.?”


Takardan dake hannunsa ya d’an warware ya nuna masa..


“Suleja..?” Assad ya maimaita a hankali kafin ya girgiza kai kad’an yana mai capke d’an makullin da Mu’azzam d’in ya jefo masa..


“Do we have a mission there Inspector.?” Cewar Assad dake k’ok’arin key wa Mota..


“Idan munje zaka gani..” Mu’azzam ya basa amsa yana mai kuma duban takardan dake hannunsa..Maleeka da tin fitowarsu take hangensu, Ta nufo waje cikin sauri amma saidai bata cimmasu ba, cikeda takaici take ciza baki kafin Ta koma cikin building d’in..


**


SULEJA 
Wata matace zaune tsakar gida tana tsintar wake, yara guda biyu maza zaune gefenta saman tabarma suna cin abinci.. D’aya bazai gaza shekaru 12 ba d’ayan kuma bazai gaza 9 ba.. Sai cin abincin suke hannu baka hannu k’warya alamun yunwa taci ta cinyesu...


“SADIYA..! SADIYA..!! Ke SADIYA..!!” Matar Ke fad’i daga nan yanda take zaune tana tsintar wake..


Ganin wacce ta kira d’in bata fito ba ya sanyata yin k’wafa tana mai gyara zamanta saman kujerar had’ida daidaita zaman parantin da waken Ke ciki saman cinyarta “Kar Allah Sa ki fito daga cikin d’akin nan.. Idan yunwa ta azalzaleki zaki fito.. Ke kanki farau ake saka aure a fasa..? Ai ke abinma ki gode ma Allah ne da yanzu kin je kin auri wanda ba’a san danginsa ba.. Wa yasani ma ko d’anta da ne Ko d’an fashi da makami ne, ko kuma ma Dan garkuwa ne da mutane.. Ki gode ma Allah baki da rabon shan wahala ne tinda gashi har shagulgulan bikunku aka fara d’aurin aure kad’ai ya rage aka nemesa aka rasa sa, Allah kad’ai yasan shid’in wane irin mutum ne dan ko danginsa bamu tab’a gani ba sai wannan Kawun nasa.. Da yanzu kin aure shi d’in Allah kad’ai yasan irin masifar da zai janyo miki, ke da gidanki saidai ki rayu ciki tamkar kina a GIDAN ARO ne..” Ta k’arashe tana bushe waken dake cikin parantin...


Tana busar waken take ci gaba da furta “Ni duk bama wannan ba uban bashin da mukaci ne na fitan biki ya tsaya min a wuya da yanda zamu kwashe da d’inbin mutanen dake binmu bashi... Oh Allah dai ya fiddamu..”


Bataji sallamar ba sai Muryar data jiyo tana furta “K’warai kuwa Uwani gwara ki nemo hanya tun wuri dan yau bani fita cikin gidan nan sai kin lale min kud’ad’e na.. Yo Ai ni bani nace kiyi bukin k’arya ba.. Harda cewa d’an gidan Babban k’usa a k’asar Amurka  ‘yarki zata aura.. Toh maza maza idan ma guduma ne ba k’usa ba a fiddo mun kud’ad’ena yanda suka shiga suka fita ehe..” Ta k’arashe tana wane irin jijjiga


Mata mai tsintar waken murmushi ta saki wanda hausawa Ke ce ma kafi kuka ciwo

“Tabawa kece tafe, k’araso k’izauna mana, ga wajen zama..”


“Ank’i a zauna d’in.. Nace bazaa zauna d’in ba.. Yo ni naga wajen zama ne a nan..”


“Haba Tabawa mu shiga daga ciki sai muyi maganar..”


“Bazan shiga ba..!” Tabawa Ta fad’i tana mai fatali da parantin waken da matar Ke tsincewa Ai ko sai cikin abincin da yaran ke mamuk’a... 


Wane irin kuka k’aramin ya fashe yana birgima yana fad’in sai an biyasa abincinsa da aka b’ata...


No comments

Powered by Blogger.