Daudar Gora Book 2 page 5

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (05)




........Tun a jiyan Doctor Afif yaso fahimtar da Tajwar Eshaan haƙuri da wannan zama saboda jikinsa har yanzu bawai ya kasance yanda ake bukata bane ba. Hasalima ana shirye-shiryen masa aikin da ya rage ne daga nan zuwa kwana biyu. Kallonsa kawai Tajwar Eshaan yay har ya kammala masa bayanin cike da girmamawa kai a rissine. Bai ce da shi komai ba tsahon lokaci, sai daga baya ya ɗan girgiza kansa kawai iya amsar kenan. Dole doctor Afif ɗin ya haƙura gudun shiga hurumin daba nasa ba. 


        Kamar yanda ya saba komansa kafin faruwar al'amarin haka ya gudanar a yau ma duk da rashin ƙarfin jiki dana ciwon dake sukarsa kaɗan-kaɗan. Sai dai kasancewar jarumin jarumai gwanin juriya da shanye kowane irin al'amari cike da ƙarfin hali ya shirya cikin ƙasaitaccen shirinsa mai firgitar da duk wanda ya ɗaura idanunsa a kansa shi ɗin wanene. Shirine da ya bayyanar da tsantsar ƙyawun da ALLAH ya bashi da cikar kamalar mulki mai tafiya da kwarjinin kasancewar sa cikakken mutum mai matuƙar zama barazana ga kowa. Ƙamshinsa matuƙar narka da zuciyar mai shaƙa yake a kowane motsinsa. Ya cika ɗawusun da al'ummar ƙasar sa ke kiransa wajen iya ado da zauna masa a jiki koma ya zarce. Dan tabbas ko'a cikin dubu baya boyuwa da lalube ma cankosa ake kasancewarsa ɗaya ƙwallin ƙwal Shahan-shan Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed da babu wani mai irin matsayinsa a ƙasar ruman da kewaye kaf.

          A lokaci ɗaya gaba ɗayan masarautar ta ɗauki tsitt kasancewar fitowarsa a zahirinsa cikin takun dake tabbatar ma ga duk wanda bai san wannan fuska a zahiri ba shi ɗinne dai da suke cike da ƙishirwar son gani. Cikin karkarwar jiki data zukata hadimai ke faman zubewa bisa kafafunsu zukatansu na neman wantsalowa ta bakunansu duk da a kallo ɗaya da suke masa basa sake iya daga kai yin gigin kallo na biyu. Baga hadiman kawai ba hatta da masu faɗa ajin masarautar ma wutar kawunansu gaba ɗaya ta gama ɗaukewa dan al'ajabi. Domin kuwa tun fitowarsa hadimansu ƴan leƙen asiri har ci da goshi suke wajen isar da tsegumi ga iyayen gidan nasu kan fitowar Shahan-shan Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed yau a zahirinsa ga kowa babu shamaki.....


      ★A yanda dokin ya cika bargar da haniniya da fisge-fisge ya matuƙar tada hankalin masu kula da su. Iya kokari yi suke na ganin sun dakatar da shi daga ballewa saboda saninsa amma hakan ya gagara. Da yay wata irin mahaukaciyar girgiza sai ga zaratan mazan su biyar a ƙasa wanwar. Darewa a ka dingayi duk inda ya keta a cikin masarautar, yayinda hankalin mafi yawan hadimai ya tashi sanin babu mai iya dakatar da shi sai mai shi......


       Cak ya tsaya daga yunƙurin shiga motar da aka tanada domin zuwansa falon da zaiyi zaman tattaunawa da yan jaridar duk da kuwa a cikin masarautar ne. Ko'a cikin barci yaji takun waɗan nan kofatan bazai iya manta mai su ba. A zabure jami'ai Da Gazi dake zagaye da shi suka zabura domin dakatar da ingarman farin doki da ko ga mai kallo ya san ya wuce tara irin ta gaba-da-gaba. Amma domin kare shugabansu a gare su tunkararsa dole ne koda tasu lafiyar bazata samu kariya ba. Ai girgiza ɗaya yay ya zubar da kusan uku da suka tunkaresa, wasu na ƙoƙarin sake tunkararsa yay wata irin turjiya, ya kwafuci ƙasa ya sake ƙwafuta yay girgiza mai haɗe da haniniya sai gashi gaban Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. 

       Dole kowa ya dakata wajen ya ɗauki shiru na wucin gadi duk suna kallon ikon ALLAH. A hankali ya kai tattausan hannunsa a fuskar dokin ya shafa, haniniya ya sakeyi da ƙwafutar ƙasa ya girgiza jikinsa. Wannan al'amari ya matuƙar ƙayatar ga duk wanda ke wajen, duk da kuwa ba'a yau suka saba ganin irin haka ga dokin ba a duk lokacin da ya kasance tare da Tajwar Eshaan ɗin..

        Cikin muryarsa mai tausasawa da tarin nutsuwa ya kema dokin magana yana shafasa a hankali fuskarsa da ƴar sakewa kaɗan sai dai ba murmushi ya ke ba. Hasalima sai mai lurane zai fahimci sassaucin fuskar tasa a zahiri. Ya kwashe tsahon mintuna huɗu da dokin, hakan ya bama duk wanda ke a wajen damar cigaba da satar kallonsa, wanda kuma aka kaima gulma na ƙoƙarin tururuwar fitowa da leƙe a maƙe. Cike da ƙasaitarsa ya damƙa dokin a hannun Sayeed Fayzul-haq, shi kuma ya shige motar da ke buɗe har yanzu. Da sauri hadimin ya maida ya rufe murfin kansa a rissine. Da ga haka motocin suka nufi inda za'ai zaman.


       ★Isar da saƙon shigowarsa katafaren falon ya saka duk wani mahaluki mai numfashi yin ƙasa da kansa. Daddaɗan ƙamshinsa shine abu mafi ɗaukar hankali a garesu da saka nutsuwar zuciya. Yayinda takun sawayensa masu tabbatar da ƙasaitarsa ke ɗauka da sauka da bugun zukatansu. A zahiri da baɗininsu cike suke da ɗokin kasancewa a tare da shi koda bazasuga fuskar tasa ba. Duk da kasancewar sa Shahan-shan mafi ƙarancin shekaru a cikin duk Shahan-shan da suka gabata a daular ruman kwarjininsa na razanar da su, dan ko makaho ya laluba zai bada amsar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed cikin jerin jaruman maza zaratan gaske koda basu ganin ainahin zahirinsa kuwa.

       A hankali ya kai zaune saman kujerar da aka tanada dominsa cikin nutsuwarsa da sanyin da rashin ƙarfin jiki ya haddasa masa. Kallo ya dinga binsu da shi cike da nazarinsu kafin ya lumshe idanu da buɗewa yana jan ƙaramar iska ya fesar. Su Miran Jasim da ke biye da shi bayan an kai musu labarin fitowarsa babu shamakin da ke ɓoye zahirinsa suma duk zaman sukayi ransu yana ƙuna matuƙa, wasu kam ransu fari ƙal da abinda Tajwar Eshaan ɗin yayi. Kasancewar sun tsara abin a yanda sukazo bisa jagorancin wakilai ɗai-ɗai daga kowace jiha sai zaman ya kasance a tsare. Ko sau ɗaya a cikinsu babu wanda ya gwada iya ɗaga kansa ɗan kwarjininsa ya gama mamayesu tun kan su gansa, sai dai tabbatar da kammalawar zamansa ya sakasu sake gurfana gaishesa. An amsa musu da yawun Shahan-shan batare da shi yako motsa ba daga zaman ƙasaitar da yayi har sai da falon yay shiru.

       Umarnin da aka basu na shiryawa ya saka su miƙewa musamman masu gyara camaras da tabbatar da abin ɗaukar maganarsu ya zauna yanda ya kamata a inda aka jerasu reras gabansa kaɗan. Kaɗan ya rage zukatan wasu su wantsalo da gasken gaske. Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed a zahirinsa, wannan fuskar da suka jima da mafarki da kulafucin son gani a bayyane ce a zahiri babu shamaki yau. Duk da kowa yay masa kallo ɗaya baya sake maimaitawa a ransu ayyanawa suke dole ya dinga kasancewa a ɓoye kam duk da cewa hakan al'adarsu ce, dan zasu iya cewa shine na farko a tarihi cikin duk Shahan-shan da suka gabata daya bayyana fuskarsa a zahiri. Abune da bai taɓa faruwa ba. Mafi yawancin al'ummar ƙasar ruman ƙyawawane duniya ma ta shaida hakan, sai dai fa a yau kam sunga inda ƙyawu yake na zahiri, ƙyawu irin wanda ko'a ƙasar ruman ɗin zasu ambacesa da ƙyawu ɗan gaske da ba'a iya ɗauke ido a kallo ɗaya ga mai shi...

       Wannan firgici ba'a iya falon kawai ya kasance ba. A duk lungu da saƙo na ƙasar ruman ne dan tunda aka ɗora Camara ga Tajwar Eshaan komai ya koma live ga masu kallo da saurare kamar yanda ya bada umarni..

        A karan farko ya motsa pink lips ɗinsa da kyar ya fara magana a hankali. “Inama duk wanda ya kasance anan fatan alkairi da godiyar amsa wannan gayyatar. Tare da duk al'ummar ƙasata baki ɗaya. Kakannina, Iyayena yau ga ɗanku. Yayuna ga ƙaninku, ƙannena ga Yayanku, ƴaƴana ga Abbun ku ba'a matsayin shugaban ku kawai ba. Zaune nake anan da suna Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ba Shahan-shan ka ɗai ba. Zaune nake domin baku haƙuri, zaune nake anan domin roƙonku alfarmar zama lafiya, zaune nake anan domin baku damar bin hanyar data dace kubi dan ganin kun miƙani a duk inda kuka aminta da a tuhumeni bisa duk laifukan da kuke kallon nayisu gareku. Na yarda kuma na amince zan zama mai amsawa in har na aikata koda zai kasance ƙarshen numfashina kenan. Bakuma zan zargeku ba. Kuje, kuje daga yau na baku damar yanke hukunci, zan kasance mai jiranku. Zan kuma kasance mai biyayya ga shari'a, zan kuma damƙa wannan mulkin ga duk wanda kuke buƙata na biku da fatan alherin ya kasance alkairi ga ƙasar ruman baki ɗaya a bayana. Fatan alheri a gareku baki ɗaya, da roƙon afuwar gazawata akan ku. Nagode nagode da fatan alherin da kuka min a baya da ma wanda wasunku ke min har a yau👏”.

      

      Tabbas da akwai camara da zata iya ɗaukar ƙasar ruman baki ɗayanta a wannan lokaci da ansha kallon mamaki, da ansha kallon yanda komai ya tsaya cak tamkar ana juya ƙasar da na'urar remote. Kalmomi ne da gaba ɗaya bazasu gaza ɗari da hamsin ba, amma sun shiga al'umma fiye da zamansu guda dubu. Sunzo a wata siga da babu wanda ya taɓa zato ko tsammanin fitarsu daga bakin da suka fita. Abu na gaba mamakin ganin fuskar wanda ya ambatasu ga wasu mutane da ruɗani ya riska. Dole su kira al'amarin da ruɗani kasancewar sanin wannan fuskar a fuskar da basu taɓa zato ko tsammani ba. 

       Motsin gaɓɓai basu fara bayyana ba a zahiri sai da ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ta gushe daga allunan talabijin ɗinsu. A take amon sautika ya fara tashi a sigar furuci daban-daban wanda ya hargitse ƙasar baki ɗaya tako ina, har zuwa dare kuma babu alamar lafawarsa, dan tako ina sharhine ke kai kawo ga masu fashin baƙi akan kalaman Tajwar Eshaan ɗin, ata wani gefen kuwa wasu videos masu ban mamaki suke faman kaikawo a yanar gizo daga talakawan ƙasar game da fuskar da suka gani yau matsayin Shahan-shan ɗinsu. Sai dai abin farin cikin kowane furuci kan fitane da alkairansa batare da sun san shi ɗin wanene ba. Yayinda wasu kuma ke nuna irin shock da suka tsinci kansu na ganin fuskar a matsayin Shahan-shan ɗinsu.........✍️







   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

No comments

Powered by Blogger.