Daudar Gora Book 2 page 4


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔. (04)



.......Kai tsaye ya sauke kumburarrun fararen idanunsa dake a ɗan shanye kanta. “Barkan ki Ammie”. Ya faɗa a hankali fuskarsa da ɗan murmushi kaɗan tamkar an masa dole. 

   “Barka My Niger”. 

  Ta amsashi tata fuskar na sake faɗaɗa da murmushin tsantsar kulawa da soyayyar da take masa. Idanunsa ya lumshe ya sake buɗewa a kanta, dai-dai ta juya gasu Miran Jasim dake tsaye tamkar gunkinan da aka ajiye domin tarihi. Shima a karon farko ya ɗan juya nasa idanun zuwa garesu. Mara gaskiya ko'a ruwa gumi yake, haka kawai sai kaifafan idanun nasa da rauninsu ke a bayyane sukai tasiri garesu. Da ƙyar suka iya ƙoƙarin danne tsarguwarsu da bugun da zukatansu keyi a ƙirazansu. Kasancewarsa mutum mai kaifin tunani da saurin karantar yanayi tuni ya karancesu tsaf, ya risinar da idanun yana ƙoƙarin haɗiye murmushin dake neman suɓuce masa. Cike da basar da yanayin nasu ya marabcesu da sannu da zuwa. Sun saita kansu da ƙyar wajen amsawa fuskokinsu na ƙoƙarin bayyana damuwarsu mai ɗauke da tsantsar kulawa da takaici. 

   Malikat Bushirat da gaba ɗaya hankalinta ke kan Tajwar Eshaan ba fahimtar yanayin nasu tai ba ta sake juyowa garesu tana murmushi mai faɗi da amsa gaisuwar ya jiki da sukai masa sai dai bai amsa ba ya basar kamar bai jiba. 

   “Ai jinkin nasa Alhamdullah, duk da dai doctors ɗin sunce sai sun masa aiki nan da wasu kwanaki. A yanzu haka suna kan bashi magani dafin gubar na tattare kanta waje guda dan ta macizan dai anci nasarar daƙileta.”

    Zancen nata ya matuƙar dukansu a zuciya, sai dai ta wani gefen ya sakasu a farin ciki. Amma sai suka danne komai wajen nuna jimami da tsantsar takaici da damuwa. Tare da aibanta Iffah da tabbatar da sai sun saka dukan zuri'arta a nadama Bama ita kawai ba. Babban burinsu kawai ALLAH ya basa lafiya ya koma karagar mulki. Kalamansu sun sake tunzura fushin malikat Bushirat a bayyane, sai dai kuma batace komai ba kamar yanda shima Tajwar Eshaan ɗin bai tanka ba, hasalima tun fara zancen nasu ya ɗan kai dubansa ga likitansa dake a ɗakin shima, dan ƙa'idar zaman nasu a ɗakin sai da shi. Da idanu ya masa magana. Doctor Afif ya jinjina kansa da takowa gaban gadon ya janye ɗan tabir ɗin da aka saƙala ta samansa ya ɗaura lap-top ɗin da yake sarrafawa. Gefe ya maida shi ya kife fuskar laptop ɗin. Daga haka ya kwantar masa da gadon kaɗan da remote, shi kuma ya ɗan gyara kwanciyarsa ya maida idanunsa ya lumshe. Bai sake buɗesu ba balle ya tanka duk maganganunsu, duk da kuwa yana jinsu sarai....


    ★★.... ★....


  “Anya kuwa matsiyacin yaron nan ba akwai abinda yake ɓoyewa ba kuwa?”.

  Miran Arshaan ne ya faɗa cikin tashin hankali da kaikawo. Barowarsu daga sashen Tajwar Eshaan kenan, Malikat Bushirat ta nufi sashenta suma suka nufi na Miran Jasim dan akwai tazara a tsakaninsu da ita. 

   Miran Jasim da shima irin abinda ke ran Miran Arshaan ɗin ne a zuciyarsa ya taune lips da masifar ƙarfi. “Akhi nima inajin hakan a raina, sai dai na kasa ɗaura dukan motsinsa a mizanin daya dace. Kaima kasan yaron nan hatsabibin kansa ne fiye da mahaifinsa, dole ne mu koma wajen Barbushi zuwa safiyar gobe dan muna buƙatar ganawa ta gaggawa da shi”.

     “Wannan shine dai-dai. Amma tilas tafiyarmu ta kasance tare da babban shiri, dan muna buƙatar gusar da yarintar can itama kafin mudawo garesa”.

   “Babu damuwa, dan yanda nake jina ko a yanzu akace nikam a shirye nake. Amma asubancin ma yayi”.


   Kamar yanda suka faɗa hakance ta kasance. Sai dai a daren sun gana da ɗaya daga cikin Doctors ɗin dake kula da Tajwar Eshaan ɗin, sun kuma jima suna tattaunawa da babu wanda yasan akan minene. Da safen suka sami damar sake shiga duba Tajwar Eshaan bisa jagorancin Malikat Bushirat da suka sake maƙalewa, sai dai sun samu ma yana barci. Dole sukai sallama da Malikat Bushirat ɗin dan ita a sashen take yini ma yanzu. Duk da sun so jin abinda ke bakinta basu sami damar ba. Dan mace ce mai zurfin cikin tsiya da zamu iya cewa Tajwar Eshaan ya gada a gareta ga miskilanci......


     ★★...... ★.....


   A safiyar basu sami damar barin masarautar ba zuwa ga Barbushi kamar yanda sukaso saboda zuwan baƙi. Sarakunan ƙasar ruman gaba ɗaya ne suka sake zuwa domin ƙara duba jikin Tajwar Eshaan. Inda wannan dubiya ta bama al'ummar ƙasar ruman damar sanin yanayin jikin Shahan-shan ɗin. Dan Alhamdullah har fitowa yay falon da akai musu masauki. Yayi zaman kusan mintuna talatin da su, lokacin da yake miƙewa domin komawa kunnensa ya riski matsananciyar hayaniyar da ke ɗan tashi sama-sama kamar daga wajen masarautar. Da farko baiyi mamaki ba, dan tunanisa har yanzu waccan zanga-zangar ba'a dainata ba. Sai dai ya ɗan dakata daga yunƙurin barin falon ya kai dubansa Sayeed Fayzul-haq daya jagorancin shigowar sarakunan garesa. Cikin sauri ya matso garesa kansa a risine cike da girmamawa. 

    “Amincin da kariyar UBANGIJI su cigaba da gadinka ya adalin shugabanmu ko ana bukatar wani abu ne?”.

    Shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya nisa a hankali tare da ɗan lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kansa. A kan lips ɗinsa ya furta, “Akwai abinda ke faruwa ne bayan wanda na sani?”.

      “A sani na dai babu wani sabon abu, sai dai idan akan waccan hayaniyar ne ƴan jarida ne ke cike da nacin son sanin yanayin jikinka kamar yanda al'ummar ƙasar ruman ke ƙulafuci suma. Duk da kullum cikin jeren zuwa suke ƙofar masarauta dama, amma yau ganin baƙi suke tunanin zasu sami abinda suke so shine suka taru fiye da kullum. Shine jami'ai ke ƙoƙarin hana dukkan hanƙoramsu ta hanyar sake tsaurara tsaro”.

    “A tara taron manema labarai zanyi magana da su zuwa gobe Insha ALLAH”.

     A firgice, a razane, a kuma ɗimauce Sayeed Fayzul-haq ya ɗago batare da ya farga da abinda yay ɗin ba. Dan wata irin saukar tarnatsa kalaman Tajwar Eshaan ɗin da suka fita a bazata sukai a cikin kunensa. Tabbas bashi kaɗai ba ga duk wanda zaiji dolene al'amarin ya firgitar da shi, dan abune da bai taɓa faruwa ba kai tsaye kamar haka a ƙasar ruman. Koda Shahan-shan nada buƙatar ganawa da manema labarai sai dai ya wakilta waninsa bisa umarninsa ya tattauna da su da yawunsa. Amma duk da Tajwar Eshaan ɗin bai fito yace shine zai tattauna da su ɗin ba a yanzu Sayeed Fayzul-haq ya girgiza ƙwarai matuƙa.

     A cikin abinda bai wuce awa guda ba wannan saƙo na Tajwar Eshaan ya shiga karaɗe lungu da saƙo na ƙasar ruman da kewaye. Ko'ina ka leƙa zancen da ake kenan Tajwar Eshaan zai zauna da manema labarai a safiyar gobe insha ALLAHU. Kowa burinsa gari ya waye kawai, ba ƴan jaridar ba ba talakawan ba, hatta da manyan ƙasar ma masu manufofi daban-daban sun shiga jerin masu jiran.


    A daren shugabannin ƴan jarida na ƙasar ruman suka buƙaci zama na gaggawa, dan dolene su tattauna abinda ya dace kasancewar akwai tambayoyi fal zukatan al'ummar ƙasar ruman da ke son a amsa musu, kuma daga bakin Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed suke buƙatar ji duk da basu da tabbacin samu saboda abune mai matuƙar wahalar gaske kowa ya sani......


    ★•••• ★•••••


   Hankali a tashe suka iso ga Barbushi. Duk da tsalawar dare da na duhuwar jejin babu alamar tsoron abin cutarwar tattare da su saboda bushewar zukata. Hasalima su ba abinda zai basu tsoro anan bane damuwarsu. Wanda ya wuni basu tsoro da zama cikin wasi-wasi na rashin makamar riƙewa ne matsalarsu. Boka Barbushi da ƙazanta da dattin kafirci yay ma fuskarsa da gangar jikinsa ƙawanya ya tuntsire da wata irin mahaukaciyar dariya da sai da ta ƙular da Miran Arshaan da Miran Jasim. Sai dai basu nuna ba balle damar cewa wani abu. Sai da yay mai isarsa kafin ya tsagaita da maida hankalinsa garesu. Basu da matsala akan faɗin abinda ya kawosu, dan sunyi imanin ya san komai hatta gaibu (wa'iyazubillah 😭🙏), sakamakon idan sun zo wajensa tun kan su faɗi abinda ya kawosun shike zayyane musu. A yanzun ma dai yana rufe bakinsa daga dariyar tasa ya fara zayyano musu....

       “Sarƙa-sarƙar sarƙaƙiya ce mai cike da mugun ƙullin dake ɗaure da kowa. Babu mai iya gane tushen farawarta balle kamo bakin zaren ƙarshenta kasanwar anyi komai a cikin duhun da idanun kowa bazai gani ba ko wanene shi a hatsabibanci. Ina mai tabbatar muku shi ɗin hatsabibi ne ƙwarai da gaske. Kuma tabbas a yanzu ne aka fara wasan hhhhhhhh!!!! Hahahahahahaha!!!!...”

      Yanda mummunar daiyarsa ke amsa kuwwa a jejin haka sautin bugun zukatan Miran Jasim da Miran Arshaan ke bada nasu sautin a ƙirazansu. Hatta yawun dake gudana da kai kawo a bakunansu zuwa maƙoshi ya ƙame ƙaf. Hargitsatstsun idanunsu kawai suka iya zubawa boka Barbushi da ke kwasar dariya har yanzu. Cikin ƙarfin hali da tsawa-tsawa na fitar hayyaci Miran Jasim yay ƙoƙarin dakatar da shi a kausashe..

        “Koma mi ya taka ko yake taƙama da shi mu bai damemu ba. Muna son a ƙarasa mana rayuwarsa a wannan dare, haka itama yarinyar ta hanyar uwarsa Malikat Bushirat, asirinta ya tonu duniya duk ta shaida itace ta kashe yarinyar kaga sai ya gana da ƴan jaridar da hujja. A haddasa babban rikici tsakaninsu da talakawan ƙasar nan harma da tsohuwar can da rayuwarta ta zame mana ƙadagaren bakin tulu. Mu kuma zamuyi amfani da wannan rikicin wajen kawar da Eshaan ɗin ta hanyar aikin da likitoci zasu masa, sai kawai ace bugun zuciya ne dalilin abinda ke faruwa..”

       “Hhahahaha!!! Hhhhh!!!” Barbushi ya shiga kwasar dariyar wulaƙanci sa mai tsananin bada amsa kuwa. “Ina son mugunta da mugu hhhhh!!. Ina son naga ana mugunta HHhH!!. Koba komai ƴan wuta sun sami ƙaruwa hhhhh!! (Wa'iyazubillah. Ya rabbi badan halinmu ba ka karemu daga nema a wajen waninka, ka tsaremu daga shirka da mushirikai🙏😭). 

       Duk da kalamansa na ƙarshe basu ji ko gezau ba akan ƙudirinsu, duk da kuwa sunyi imanin UBANGIJI ya halicci (WUTA DA ALJANNA) babu kokwanton zai cikasu kuma kamar yanda ya alƙarwanta, sai dai son cikar burin duniya na ƙanƙanin lokaci ya rufe zukatansu da idanunsu, sun jima matuƙa tare da shi sai gabanin asubahi suka koma masarauta ta ɓarauniyar hanyar kamar yanda suka fita....



    *_WASHE GARI_*


  Ƙarfe goma na safe ƴan jarida da taron al'ummar ƙasar ruman sun cika ƙofar masarautar Ruman cika mai ban mamaki kai kace Tajwar Eshaan ɗin zai fito ne ƙuru-ƙuru su gansa kamar yanda suka jima suna bege a rayuwarsu. Dole aka baza jami'an tsaro saboda gudun abinda zaije ya dawo.........✍️








   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

No comments

Powered by Blogger.