Daudar Gora Book 2 page 58

 


Chapter: 58



Bayan sallar isha'i cikin dauriya Iffah ta amsa kiran Malikat Haseenat. Tafiya take cikin dabara dan ko yau din ma dai tanajin zafin, ga zazzabi tun dazu yaki saukar mata. Ita bata san randa zatai sabo da wannan

al'amari ba kamar yanda ya fada mata dazun. Ta dan yamutse fuska da cigaba da tafiyarta a hankali, dan ita kadai ta fito babu wani dan rakkiya, Tajwar Eshaan ma yana massalaci tunda ya tafi sallar magrib bai shigo ba. Kadan-kadan take dan cin karo da hadimai, duk da ko'ina na masarautar zagaye yake da haske ba ganeta suke ba, sai dai yanayin shigarta kansa su mata gaisuwar girmamawa kamar yanda suke ma duk wani ahalin masarautar babba ko yaro. Hannu ta dinga daga musu kawai dan batajin yin magana har takai sashen Malikat Haseenat din. Nan din ma bawani sun ganeta bane sosai, dan sanda take kokarin shiga falon Malikat Haseenat din da sauri Banou tai niyyar dakatar da ita. Sai dai mi, kallon ido cikin ido da sukai ma juna ya sa Hadima Banou din zubewa kasa cikin rawar jiki da tsananin kaduwa. Har taune harshe take wajen gaida Iffah da ke mata kallon tsaf kamar mai son gano ainahinta. Sai da ta mula dan kanta ta yamutsa fuska da watsa mata harara. "K! Har yanzu baki daina bibiyar mutane ba ko?Karki fasa ina tafe kanki ai". Ta fada tana wuceta batare  data amsa gaisuwar tata ba.


     Jagwab Hadima Banou ta zube zaune a wajen zuciyarta na wani irin masifar harbawa. Sosai take tsoron wannan baiwar ALLAH, dan ita kadai tasan mi take ganowa tattare da ita. Ta jima a wajen kafin ta mike cikin rawar jiki ta fita. Can baya ta nufa cikin karamin garden din Malikat Haseenat da takan hutawa, da ga cikin wasu dunkulallun fulawoyi ta zaro yar tukunyar kasa da bakinta ke daure da kyalla an nannade da zare. Warware zaren tai har yanzu jikinta na rawa, abubuwane a daddaure ciki kamar tsokokin nama, haka ta shiga fiddosu tana ware wasu a kasa, sai da ta gama zabowa ta maida sauran ta sake daurewa ta ajiye. Wanda ta fiddo din kam ta kwance hudu ta sakesu, biyu da ga ciki tasa a baki ta cinye tana faman tande lips. Duk abinda take yi tanayi ne tana waige-waige, har dai ta kammala ta mike da sauri ta fito..


Tarba ta mutuntawa Iffah ta samu da ga Malikat Haseenat. Dan an shiryama zuwan nata da zuwa na musamman kamar yanda akan yima Tajwar Eshaan idan zai zo. Iffah har mamakin hakan tayi, dan bata taba tunani ko tsammanin tanada kimar da wani zai mata haka musamman idan akai dubi da shekarunta da kuma gidan data fito na talakawa. Malikat Haseenat dame binta da Kallo kuwa a kallo daya da taima takunta ta fahimci halin da Iffah take, idanu ta dan lumshe tana mai jin tausayinta, dama tasan bazai iya hakurin barinta ta warke yanda suke bukata ba ai, dole ne sai ta dage ma yarinyar da abubuwan da zasu taimaka mata batare data dinga jigata ba. A zahiri kam hannu ta ware mata alamar tazo gareta. Iffah da ke murmushi kanta a kasa ta karasa a nutse ta ko shige jikin nata. Wata irin tagwayen ajiyar zuciya ta dinga saukewa a jajjere haka itama Malikat Haseenat din. Kusan minti biyu suna a haka kafin ta zaunar da ita kusa da ita gab-gab dan har cikin rai take jin kaunar yarinyar nan.


      Duk yanda Iffah ta dinga nuna jin kunya Malikat Haseenat bata barta ba sai da sukaci suka sha a tare cike da farin ciki, suna tsaka da cin abinci ne ma Daneen Ammarah itama ta shigo. Cike da girmamawa Iffah ta gaisheta, ta amsa mata da kulawa cike da so da kauna. Bayan sun kammala hadimai suka gyara wajen, Malikat Haseenat kuma ta bama Iffah wata yar madara a kofi mai dadin tsiya data kasa gane ma wace irin madara ce, dan an mata wasu hadi ne na musamman. Dagawa daya ta shanye ta ajiye kofin, karamin bowl dake dauke da hadadden hadin zuma da dabino da kwa-kwa dama abubuwan da bata sani ba nan ma ta bata tare da karamin cokali a ciki da zata dinga diba kadan-kadan tana ci.


"Hafidah!"


Malikat Haseenat ta kirata a hankali. Amsawa Iffah tai kanta a kasa. Mammah bata damu ba ta cigaba da fadin, "Kin san miyasa nace kizo ki sameni?". Kai Iffah ta girgiza mata ta ce, "A'a Jaddah"., Malikat Haseenat ta kalla Daneen Ammarah suka dan sakarma juna murmushi kafin ta sake maidawa kan Iffah. "Magana nake so muyi mai muhimmanci dan nasan bazakimin karya ba".


 "Insha ALLAHU Jaddah".


    "'Dazun a zaman shari'ar can kinyi wata magana ce data kasa barin raina akan ganin gawar Zawjata-almilk da kikai. Shin ko akwai wasu alamomi da kika gani tattare da ita? Ko kuwa kisa ne kawai na kai tsaye da raunika?"


     Shiru Iffah tai da dan mamakin tambayar a ranta, ta kasa gane wann al'amarin, shi mai matan yace bai taba ganinsu ba, bayanan suke mutuwa, kuma ko gawarsu baya gani. Shin itama Jaddah din du matsayinta a masarautar bata taba gain gawarsu kenan amma har wadan can rubabbun su Jasim ke iya gani ko mi?


''Ibnati"


Daneen Ammarah ta katse mata tunani. Firgigit ta kawo numfashi da kallonsu, sai kuma ta maida kanta ta risinar tana mai sauke ajiyar zuciya. "Jaddah zan fada miki duk abinda kike bukatar j, amma dan ALLAH ki gafarceni nima zanyi wat tambaya".


"Bismillah".


Malikat Haseenat ta fada kai tsaye cikin bata dama. Numfashi Iffah ta dan fesar ta nisa. Kafin tace, "Jaddah na kasa ganewa, shin duk matansa da suka rasu kuma baku taba ganin gawarsu ba kamar yanda shima yace bai taba gani ba kenan?".


    Daga Malikat Haseenat har Daneen Ammarah kallon Iffah suke mamaki fes a kan fuskokinsu. Daneen Ammarah ta ce, "Shi Abni din ya fada miki bai taba ganin gawar matansa ba?".


"Har suna raye bai taba ganinsu ba ma yace".


    Kallon juna Daneen Ammarah da Mammah sukayi, sai kuma duk suka dubi Iffah da itama su take kallo ta gefen ido. "Tofa babbar magana".Cewar Malikat Haseenat. Daneen Ammarah ta ce, "Babbar magana kam, ta gaske ma Mammah. Ni kaina ma ya sake kullewa akan Al’amurin”.


"Dole ne kam Ammarah. Amma Hafida-ti bara na baki amsar tambayarki, masarautar nan nada tsare-tsare irin nata da ka'idoji, a ciki harda zama iya huruminka, dan haka ni bana a cikin masu hurumin kan duk abinda ya shafi Zawjata- almilk na Hafidi, wannan hakkin mahaifinsa ce, ni kuma nawa hakkin a kansu yake tunda sune matan dana. Wannan ne dalilin da yasa ban taba gani ba. Kema da kike ganina tsaye a kanki saboda matsalolin da aka samu ne da har yasa ita Bushirat janyewa da ga al'amuran ki, ni kuma naga bazan iya yardawa ba na dauka na adana".


     Cike da gamsuwa Iffah ta jinjina kanta. Sai kuma ta cigaba da basu bayani akan abinda suke bukata. Riko hanunta Daneen Ammarah tai kamar a razane ta ce, , "Cizon maciji kuma?". Cike

da mamakin yanda suka razana Iffah ta gyada mata kai. "Eh Mamy saran maciji. Sai dai da alama kafin ma hakan tayi yunkurin kare kanta da har ya zamto dakin ya kasance a harmutse".


 "Ya rabba! Uwa. Mammah tabbas wannan alama ne na UWA. Itace, itace azzalumar bata barmu ba. Bata barmuba Mammah, tana raye why tana raye". Daneen Ammarah ta fada tana rike kanta da ke mata wani irin sarawa ta fara layi kamar zata fadi. Da sauri Iffah ta mike ta riketa cikin tashin hankali. Hakam Malikat haseenat duk ta rikice, dan ta fahimci ma tsahon shekaru data shude ce da ga garesu ke neman dawowa ga Ammarah din kanta. Da kyar suka iya samu suka kwantar da ita, a tare suka dinga tofa mata addu'oi. sannu a hankali ta fara lafawa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere sai kuma barci ya dauke ta mai nauyi.Ajiyar zuciya Malikat Haseenat ta shiga saukewa da sauri- sauri, yayinda Iffah sunan uwa da Daneen Ammarah ta ambata ke faman mata kaikawo kirjinta na wata irin bugawa..


"Jaddah waye UWA kuma?".


   Kalmar ta subuto da ga bakin Iffah batare da ta shirya hakan ba. Idanu kawai Malikat Haseenat ta zubama Iffah batare da tace komai ba. Har Iffah ma ta fidda rai da ga cewarta. Dan tsahon kusan mintuna biyar kafin Malikat Haseenat din ta nisa. "Uwa. Uwa.. uwa…. sanin wacece uwa na kunshe ne a cikin labarin masarautar nan Hafida-ti. Labarine mai tsaho da ya zama a cikin manyan labaran da suka kasance da ZUCIYAR ahalin Aliy Qutb gaba daya. Duk da ya shude, shudewa ta tsahon shekaru da muke tsammanin karnin ya shafe da fatan daina tunashi koda a cikin tarihinmu da alama hakan bamai yiwuwa bane."


"Jaddah idan na dage akan son na sani ban shiga cikin hurumin daba nawa ba? Dan ina mutukar so da zumudin na sani din".


  Murmushi mai ciwo Malikat Haseenat ta yi, sai kuma ta zuba idanunta akan Iffah tana dan jinjina kai. "Baki tsallake huruminki ba Hafida-ti,

tunda kin rigada kin zama mu mun zama ke. Sai dai dokar wanna zuri'a ta dade da shardanta goge wanna tarihin domin mantashi da daina tunashi garemu har abada..." taja nannauyan numfashi mai hade da ajiyar zuciya. "Da zan iya wofantar da bukatarki da nace karki sake tambaya. Amma inaji a raina bazan iya ba, dan inhar dai da gaske baya ce ke son dawowa ta maimaita kanta kamar yanda nake hasashe a kanki tun zuwanki masarautar nan dolene labari biyu ya dawo a lokaci guda domin

kasancewarsu cikin juna duk da raina namin wasi-wasin taya hakan zata kasance bayan anyi ruwa ne an dauke kasa ta shanye kayanta?"


      Sam Iffah bata gane cudaddun kalaman karshe ba, dan haka ta tsurama Malikat Haseenat idanu kawai ko kyaftawa babu.Murmushi Malikat ta sakar mata tare da lumshe idanu ta bude a kanta lokaci guda. "Idan har zan samu warwarewar lissafina zan sanar miki abinda kike son sani Hafida-ti. Zan sanar miki tarihi da tushen kasancewar uwa a cikin tarihin wannan DAULA kamar yanda kike bukata".


A hankali Iffah ta saki murmushi mai kayatarwa maimaita kanta kamar yanda nake hasashe a kankii tun zuwanki masarautar nan dolene dayan biyu ya dawo a lokaci guda domin

kasancewarsu cikin juna duk da raina namin wasi-wasin taya hakan zata kasance bayan anyi ruwa ne an dauke kasa ta shanye kayanta?"


   


A hankali Iffah ta saki murmushi mai kayatarwa da jinjina kanta. "Nagode sosai Jaddah, ALLAH ya kara girma da lafiya mai albarka da tsahon rai".


"Amin".


Malikat Haseenat ta amsa tana gyara zamanta cikin wheelchair dinta da fuskantar Iffah da kyau……….✍️


No comments

Powered by Blogger.